advanced Search
Dubawa
11948
Ranar Isar da Sako: 2010/07/06
Takaitacciyar Tambaya
MENENE RA’AYIN MUSULUNCI GAME DA HALARTAR MATA MASALLACI.
SWALI
DANGANE DA HADISAN NAN BIYU MASU ZUWA MENE NE RA’AYIN MUSULUNCI GAME DA HALARTAR MATA MASALLACI DA YIN SALLAR JAM’E DA KUMA YIN SAURAN IBADU? AN RUWAITO DAGA IMAM SADIK (a.s), YA CE: “FIYAYYUN MASALLATAI GA MATANKU SU NE GIDAJE” WASA’ILUSSHI’A, J 2, SH 237. KANA DAGA ANNABIN GIRMA (s.a.w), YA CE: “IDAN MATAYENKU SUKA NEMI IZININKU ZUWA MASALLACI DA DADDARE TO KU BA SU IZINI” SAHIHUL BUHARI HADISI MAI LAMBA 865.
Amsa a Dunkule

Abin da ake nufi da ruwaya ta farko shi ne duk da kasantuwar masallatai su ne fiyayyun wurare na tsai da salla kuma salla a cikinsu yana da lada mai yawa. Sai dai fiyayyen masallaci ga mata shi ne dakunansu. Saboda yin hakan zai hanasu cakuduwa da bare. To wannan ruwayar bata hana mata halartar masallatai ba ne.

Ita kuwa ruwaya ta biyu tana maga ne a kan batun mata idan zasu halarci masallaci, suka nemi izininku to kada ku hanasu. Saboda rashin haramcin halarta ko da kuwa saboda salla ne. Domin sun zabi yin sallar ko da zasu sami lada ‘yar kadan. Kuma duk da haka musulunci baya kodaitar da mata su halarci masallaci domin yin salla, sai dai bai haramta hakan ba. Amma idan hakan ya hadu da wani sha’ani kamar sallar juma’a ko yin darasi da jawabai na ilimi da na addini, to lalle abu ne mai kyau.

Amsa Dalla-dalla

Ra’ayin Musulunci game da cudanyar mata da maza shi nesantar juna, a ko ta wane yana yi cudanyar kuwa ta kasance, kuma kada su fita daga gida sai bisa lalura. Wadannan ruwayoyi biyun suna fassara wannan manufar. Dangane da ruwaya ta farko hakika Imam Sadik (a.s), ya ce: “Fiyayyun masallatai ga matanku su ne gidaje” Abin nufi a nan shi ne cewar duk da cewa masallatai su ne wurare da suka fi dacewa da tsai da salla, kuma salla a ciki akwai lada mai yawa idan aka kwatanta da salla a wani gurin. Sai dai mafi kyawun wurin salla ga mata, shi ne dakunansu. Dalili shi ne, wannan yanayin ba za su bar gida, su je su yi cudanya da wasu bare ba. Abin da Imam yake so ya ce a nan shi ne: “Cakuduwa ta bisa lalura tsakaninsu da bare ba abu ne da ake fatar kasantuwarsa ba, ko da zuwa masallatai ne ko yin sallar jam’e. A she ke nan abu ne da ba a bukata sai a bisa lalura. Don haka kamata ya yi a nisanceta. Amma duk da haka wannan ruwayar bata haramta wa mata halartan masallatai ba. Matukar akwai wasu abubuwa da ba salla ba -kamar tsai da sallar jam’e ko sanin wasu mas’aloli da suka wajaba mata su sansu. (ta yadda hakan ba zai samu a gidajensu ba) don haka ba zayyiwu a haramta wa mata su halarci masallaci ba. Ba za mu yi watsi da batun halaratar ba bisa dogaro da wadannan hadisai masu girma. Idan muka kalli bayanin da ya gabata, za mu fahimci ma’anar ruwaya ta biyu. Ya kamata a fahimci cewa ta biyun sam bata ci karo da ta farkon ba. Doman cewa take idan sun nemi izinku, za su je masallaci, to kada ku hanasu. Ku ba su izinin halartar masallaci. Domin halartar ko don yin sallah bata zama haramun. Ko da sun zabi su yi sallar su samu lada ‘yar kadan.

Kasantuwar halartar masallatan ya na kunshe da fa’idoji na ilmantuwa da ma’anoni daban-daban ta yadda idan ba su halarta a irin wadannan wuraren ba, ba zasu amfanu ba. Bisa la’akari hakan ya dace da ruwaya ta biyu, saboda Annabin Girma (s.a.w) yana cewa idan suna son zuwa masallaci to kada ku hana su.

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

Tambayoyi Masu Fadowa

  • Me ye ma’anar ayyanawa da ma’anar zabi, wanne ne ya dace da wilayatul fakihi (Jagorancin Malami)?
    14049 Tsare-tsare 2012/07/26
    Wasu suna kokarin cewa akwai fahimtoci da yawa wajen malaman musulunci game da hukumar musulunci, har ma suna kokarin gina tunanin da ke tabbatar da ‘mahangar tabbatar da shugabancin fakihi (malami), daya daga cikin fahimtoci masu yawa a cikin wannan maudu’I ta tafi a kan cewa lalle ...
  • Zai yiwu ga fakihi ya damga ani ga Kur'ani alhalin ba shi da mukaddima ta ilmi?
    11180 Sabon Kalam 2012/09/16
    Abin da zamu kawo a dunkule shi ne msar tambayar. Hakika Kur'ani tushe ne daga tushen shari'a, kuma shi ake komawa don gane ra'ayin addini. Ba hakan nan ake istinbadi da Al-Kur'ani ba sai abubuwa biyu sun tabbata: kafa dalilin tabbatar da Al-Kur'anin, sannan ...
  • A lokacin da hura wa Annabi Adam (a.s) rai me ya fara cewa?
    4607 Hdisi 2017/06/17
    An rawaito cewa lokacin Allah madaukaki ya hura wa Annabi Adam daga ransa sai ya ta shi mutum madaidaici sai ya zauna ya yi atishwawa, sai aka yi masa ilhama da ya ce:≪alhamdu lillahi rabbil aalamin≫ “godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai” sai kuwa ya fadi ...
  • Mece ce mahangar mafi yawan malamai game da jagorancin malami bayan babbar boyuwar Imami?
    7964 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/24
    Sama da shekaru dubu ne malaman shi’a suke yin bincike kan mas’alar jagorancin malami, wasu kamar abussalah halbi, da ibn idris hilli, sun yi bayani dalla-dalla game da sharuddan malami mai maye gurbin imami ma’asumi a wannan zamani, wasu ma sun yi bayani kan ayyukan da suka ...
  • Yaya nau’ikan shiga jiki da hadewa a mahangar irfani, da kalam da hikimar muslunci suke?
    6522 اصطلاحات 2019/06/16
    Bayani kan menene (hulul) shiga jiki da ittihadi (hadewa) hulul a harshen larabci ya samo asali daga kalmar halla da ma’anar sauka[1] amma Kalmar ittihad ita kuma tana da ma’anar abubuwa biyu su hade su zama abu guda daya[2] Kashe kashen ...
  • Wane matsayi ne jagorancin malami yake da shi a shi'anci?
    7207 Sabon Kalam 2012/07/24
    A mahangar Shi'a, jagorancin malami a lokacin boyuwar Imam Mahadi (a.s), shi ci gaba ne na jagorancin imamai ma'asumai (a.s), kamar yadda su ma jagorancinsu ci gaba ne na jagorancin manzon Allah (s.a.w). ...
  • yaya masu tafsiri suka fasara Kalmar ku bugi matanku a cikin ayar nushuz?
    12458 Tafsiri 2012/07/25
    A cikin koyarwar musulunci, mata suna da matsayi na musamman, ruwawoyi na manzon Allah da a imam[a. s] sun yi bayanin a kan hakan. Ya zo a cikin ruwayoyin mu cewa mata salihai tushe ne na alkhairi da albarka kuma suna cikin abubuwa masu daraja da kima ...
  • Shin addini ya dace da siyasa?
    11718 Sabon Kalam 2012/07/23
    Addini ya zo ne domin rabautar mutum har zuwa karshen duniya, don haka ba yadda zata yiwu ya kasance bas hi da wani mataki game da abin da al’ummar duniya take bukata daya hada da jagorancin hukuma. Ta wani bangaren kuma yanayin dokokin musulunci sun tilasata wajabcin ...
  • Me ake nufi da gaskiya, kuma wace hanya ce zata kai ga samun hakikanin gaskiya?
    21912 Sabon Kalam 2012/07/24
    Gaskiya tana nufin hanya matsakaiciya, wato ana nufin maganar daidai da bin hakika, gaskiya ita ce sanya komai da hikima bisa mahallinsa da ya dace da shi. Sannan bin gaskiya da tafiya kanta bisa tafarkinta a fagen tunani yana nufin tanadin makamin ilmi da mantik ...
  • Ta wace Hanya ake mangance maita da kanbun baka?
    32782 Halayen Aiki 2017/05/21
    Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...

Mafi Dubawa