Musulunci shi ne addinin karshe kuma mafi kamala, don haka ne a kowane fage na rayuwar mutum ko ta daidaiku ko ta jama'a muke ganin samun shiryarwa a dukkan wadannan fagage. A cikin tunanin fikirar musulunci akwai mahanga mai isarwa matsakaiciya game da gamewar addinin musulunci.
"akidar fikira rubutatta a musulunci" wata mahanga ce matsakaiciya domin nuna tsarukan musulunci a fagage mabambanta da aka nuna shi cikin wasu bayanai:
a- bayani ta farko: wata makala ce da take bayani game da "tsarin tattalin arziki a Kur'ani" (masu makaloli ne da aka rubuta so a tarun na biyar game da ilimomin Kur'ani mai girma, Kum, Darul kur'an, lokacin Zafi 1375, shafi; 425 – 330).
b- Bayani na biyu: "mahangar tunanin da aka rubuta a musulunci" (su ma wasu bayanai ne da aka rubuta su a taron bincike game da dokokin fikihu a mahangar Imam khomain ta tasirin zamani da wuri a ijtihadi, mujalladi na uku: Ijtihadin zamani da wuri. Lokacin zafi 1374, Tehran).
c- bayani na uku: Banagren farko na littafin "Wilayatul Fakih" (Daftare andisheye jawan, bangaren rubuce-rubuce da tunanin fikirar musulunci 1377, tehran).
d- bayani na hudu: Banbaren littafin "mabani kalami ijtihadi" (cibiyar al'adu, Khaneye Khirad, 1377, Kum bangaren farko na littafin "ofishin tsarin tattalin arzikin musulunci), "cibiyar al'adu ta Khirad".
Don haka zamu yi bayani a nan a takaice:
Musulunci addinin karshe ne kuma mafi kamalar addini da aka sauraki, don haka ne ya taba kowane bangare na rayuwar mutum a daidaiku da jama'u, kuma tun da haka ne ya kasance ya shiryar da mtuane kan kowane bangare na wannan lamuran, kuma wannan shiryarwar da koyarwar su ne suka hada abin da ake kira addini wadanda za a iya raba su gida biyu:
1- Bangarorin addini wadanda suke nuna mana tunanin fikirar musulunci a wani bangaren kamar siyasa, tattalin arziki, da kuma alakarsu da tunanin fikirar musulunci a matsayin cewa su wani bangare ne nasa, kuma su suna kasancewa ne daga mabubbugar asasinsa na akida da hikimarsa, kamar dai yadda zamu ga an samu mamayar ikon ubangiji a fagen siyasa , da arzutawarsa a fagen tattalin arziki da zamu ga ana kiran su da hikimar shari'ar Allah. Don haka ita siyasar musulunci wata baganre ce ta wannan jiki guda na addini da ta bubbugo daga gareshi.
2- Bagaren addini da suka bubbugo daga asasin fikirarsa musamman hikimarsa wadanda su ne suka hada mas'alolin da suek maganan kan abin da yake na tilas, sai dai su ma sun kasu guda biyu ne:
a- Bangaren da ya shafi wasu daga mas'alolin da suke su ne asasin bangare na biyu kuma da su ne ake bayaninsu, wadannan sun hada da asasi da dokokin da aka yi yarda da su aka yi ittifaki kansu da uska hada da wasu hadafofi da wasu asasai, da suka hada kamar "tsarin siyasa a musulunci" wanda yake tattararrun hadafofi ne da mas'aloli na asasin da hadafofin siyasar musulunci.
b- Bisa asasin wasu asasai domin mu kai ga hadafin a wannan fagen akwai wasu mas'aloil da aka nuna su a addini wadanda ake kiran su da "tsari" , wanda a bisa gaskiya suna da fadi da suak sahfin kowane bangare, don haka ne mu zamu ga a kowane fage na rayuwar mutum akwai bangarori uku: hikima, tsari, da tafarki, da zamu ga akwai alaka mai karfi tsakanin wadannan abubuwan.
Hikima:
Idan muka ce hikima to a nan ba muna maganar ilimin hikima da aka fa sani da "falsafa" ba ne da yake binciken abin da yake saman wannan halittar ta duniya, sai dai muna maganar kalmar hikima ce da ake raba ta ga ilimomi daban-daban kamar a ce: hikimar siyasar musulunci da sauransu. A bisa gaskiya wane bincike ne game da fagne muslunci a tsarin siyasar musulunci kamar dai sauran tarsi da zamu ga ni na kasancewar mamayar ikon Allah a matsayin mahangar da za a iya sanin mutum ta cikinta, da take bincike kan alakar ikon zabin da mtuane suke da shi da kuma nufin da Allah yake da shi, da kuma ubangijintakar Allah madaukaki da ikon da yake da shi kan mulki da siyasa.
Tafarki:
Shi kuam tafarki wasu tattararrun fikirori ne na asasi da hadafofi a wuri daya, kuma su ne abubuwan da ma'abota wannan tafarki suak sallama da su, a matsayin wasu kashin bayan da ginin tsari ya doru kansu. Amma hadafofi wasu abubuwan en da ake son a cimma su da addini yake son a kai gare su. Don haka ne tafarkin siyasar musulunci, ko kuma asasin siyasar musulunci da hadafofin siyasar musulunci, da lamura kamar cewa babu wani mutum da yake da iko kan waninsa sai dai inda Allah ya sanya masa ikon kan dan'uwansa mutum, da kuma batun cewa ikon ma'asumai tsarkaka yana da iyaka ne da idan suna rayuwa cikin mutanen, duk ana lissafa su ne cikin tsarurrukan asasin na musulunci. Kuma ana lissafa wasu kamar neman tabbatar adalcin zaman tare, kare hakkokin dan Adam na asasi, da yalwata wa al'umma don samun ci gaban mutum, duk daga cikin hadafofin siyasar musulunci.
Tsari:
A kowane fage musulunci yana da wasu hkunce-hukunce masu maye kowane gurbin rayuwar da suke da alaka da juna da suke hada wani tafarki bisa wasu dokoki na asasi, da zasu kai ga wani hadafi, kuma wadannan dokoki da suke kowane fage ana kiran su da "tsari", don haka ne "tsarin siyasar musulunci" shi ne kan dokoki gamammu na siyasar musulunci.
Kungiya:
Kungiya a wani tsari ita wani alami ne da aka tattabar da shi game da alakar mutane, kungiyoyi, da duk abin da ya shafi wannan fagen. Daga cikin asasin tsari guda hudu:
a- na duniya: tsari bai shafi wani bangare na al'umma ko kungiyoyi ba, abu ne mai fadi da ya shafe kowane janibi.
b- yiwuwar faruwa: tsari wani abu ne da yake hadafofi da zasu iya yiwuwa a samar da su a samuwarsu, kuma ya zama babu wani kokwanto zasu kasance a zahiri.
c- tsayuwa bisa tsari: dole ne tsari ya kasance ya kafu kan wasu dokoki da zasu iya kaiwa ga hadafofin da ake son a cimma su.
d- daidaito da hakkoki gamammu: dole ne a samu alakoki da suke ayyanannu sanannu a cikin tsarin dokokin mas'aloli a kowane fage.
Hakkoki ma a kowane fage (siyasa, tattali, tarbiyya da…) ana kasa su gida biyu ne:
1- Tabbatattun hakkoki: Wadannan hakkoki ana gaya wa dokoki da ka'idojin duniya ne wadanda kungiyoyin tsari suke da su, kuma bisa asasinsu ne ake gina mazhabobi.
2- Hakkoki masu canjawa: wannan kalma ce da ake gaya wa wasu dokoki da ka'idoji da suke da wani matsayi daban da yana iya samun canji sakamakon yanayin zamani da wuri da suka ta'allaka da abin da ya dace da yanayin. Wani lokacin an yi bayanin irin wadannan dokokin daban da wadanda suke ba sa canjawa a cikin addini, sai dai a wurare mafi yawa an yi bayanin hukuncinsu da na dokoki marasa canjawa a sake ne ba tare da karin bayanin da yanayin da suka ta'allaka da kowanne daban ba.
Banbarorin Dokokin addini da yanayin rayuwar mutum
Abin da musulunci ya kawo game da la'akari da rayuwar mutum, da kuma abin da yake faruwa a zahiri suna da alaka mai karfi matuka, saboda hikimar siyasa a musulunci kamar hikimar tattalin arziki ta samu asali ne daga shi kansa tunani da fikirar musulunci, kuma tafarki da tsarin siyasa ya doru kan wannan ne. don haka tsakanin hikimar tattalin arzikin musulunci da hikimar siyasarsa da sauran bangarori na mazhabar siyasar musulunci da mazhabar tattalin arzikin musulunci, ko kuma da tsarin siyasar musulunci da tsarin tattalin arzikin musulunci, dukkanin wadannan suna da wata alaka mai karfi a tsakininsu, ta yadda zamu ga wadannan lamuran suan da hadewa tsakaninsu a matsayin abu guda daya.
Kuma duk da cewa wadannan dokoki da tsarurruka ba wasu abubuwa ba ne da za a iya ganinsu, amma ana iya dabbaka su kan abubuwan da suke da samuwa a zahiri, kuma addini ana aiko shi ne daidai da yanayin wadanda ake yi wa magana da shi, kuma wannan addinin na karshe shi ma kamar haka yake.
Duk da abubuwan zahiri ana iya dabbaka dokoki da hukunce-hukunce a kansu, sai dai a musulunci abin da muke kira da hikima ko mazhaba bai kubuta daga tasirin zahirin abubuwan da suek wakana ba. Domin duk da cewa dokoki suna da yanayi ne na tabbata da rashin canji, amma a bisa zahiri duk wani abu da ya faru yana da wani tsari da hukunci da ya dace da shi ne. misali zamu ga tattali da siyasa a farkon musulunci sun dace da hukuncin da aka ba su na tattali da siyasa a wannan zamanin da manzon rahama (s.a.w) shi da kansa ya bayar, kuma a kowane zamani akwai canjin yanayin abubuwan da suke wakana da ya dace da tsarin da musuluncin ya kawo.
Don haka domin a samu tarin siyasar musulunci yana da kyau a lura da dukkan abubuwan da suke da tasirin wurin sha'anin siyasa a wannan zamani domin samar musu da tsarin da yadace na juya lamurran al'umma a tsarin siyasa.
An ciro daga:
1. Mahdi Hadawi tehrani, wilaya wa diyanat, cibiyar al'adu ta Khaniye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.
2. Mahdi Hadawi tehrani, mabani kalami ijtihadi, cibiyar al'adu ta Khaniye Khirad, Kum, bugu na daya, 1377.
3. Mahdi Hadawi tehrani, maktab wa nizami iktisadi islami, cibiyar al'adu ta Khaniye Khirad, Kum, bugu na daya, 1378.