An halicci mutum yana kan karkata zuwa ga riko da addini, kuma mafi yawan mutane sun amsa wannan kira, mutum a bisa zatin dabi'ar halittarsa yana kokarin fuskanta ne zuwa ga gaskiya da son hakika, sai dai yana fada wa kuskure ne a tsakiyar tafiya.
A bisa hakika da gaskiya akwai wasu abubuwa daga waje da cikin samuwarsa da suke sanya mutum ya samu karkacewa da rashin fuskantar gaskiya ne, daga cikinsu akwai shedan, da ran mutum mai umarni da mummuna ta wata fuskar, ta wata fuskar kuwa akwai kafafen sanarwa da yada labaru da kalle-kalle masu halakarwa da lalatarwa, kuma dukkan wadannan abubuwan suna kokarin su ga sun kange mutum ne daga gaskiya da samun shiriya. Rashin yarda da addini a rayuwar mutum da nisantar da shi daga siyasa da zaman al'umma duk yana daga cikin abin da yake na kuskure da coci-coci suka yi yayin da suka nuna addini da mummunar kama matuka. Kai sun nuna addini da yanayin da ya saba wa tunani da dabi'ar halitta ta gari, wannan lamarin ne kuma ya san aka samu damar wannan karkacewar ta fuskacin coci a matsayin wata dama da masu gaba da ita suka samu domn kawar da addini daga siyasa da zaman rayuwar al'umma, ta hanyar amfani da kafafen watsa labarai da hanyoyin isar da sako da koyarwa, wannan lamarin kuwa ya kai ga samun karkacewa mafi yawan al'umma a yammacin duniya, sai dai wannan lamarin bai iya gamawa da jin nan nan addini da yake cikin zatin dabi'ar mutane ba, yayin da zamu ga mafi yawan mutane suna riko da wannan shu'urin da suke ji, kuma da wannan ne zai bayyana cewa ba daidai ba ne a ce mafi yawan mutane 'yan jahannama ne!!. domin su suna masu rayuwar addini da wannan jin na halitta, sai dai su yayin da suke motsawa ne don neman gaskiya sai su fada cikin kuskure saboda ba zasu iya gano gaskiya ba, su sun samu takaituwa ne ba takaitawa ba, don haka su masu jahilci ne na takaituwa ba na takaitawa ba, don haka suna da nasu uzuri.
An halicci mutum yana mai dauke da halittar son karkata da riko ga addini da son kyawawan halaye, kuam mafi yawan mutane sun amsa wannan krain halittar, sun amsa wa jin riko da addini da yake tare da su, kuma malaman musulmi bisa biyayya ga kur'ani mai girma da ruwayoyi madaukaka sun yi nuni da wannan lamarin, sai dai wannan ba ya hana mutum fadawa cikin farfagandar da ake watsawa wacce take kira da kin addini da watsi da kyawawan halaye, wannan ne yakan sanya mutum karkacewa daga tafarkin gaskiya wani jikon wanda yakan kai mutum ga karkacewa wuirn zabar gaskiya a yayin dabbaka wannan karkata zuwa ga addini a zahiri. Da za a samu kawar da wannan shamakin da ya rufe gaskiya, wanda zai kawar da wannan farfagandar kafofin sadarwa da isar da sako, aka kawo gaskiya kamar yadda take ga mutane, da an samu mutane suna karkata kai tsaye zuwa ga gaskiya.
Don haka za a iya cewa: mafi yawan muatnen ba sa karkata zuwa ga fasadi da kin gaskiya, domin sun fada karkashin farfaganda ne mai kiyayya ga gaskiay, sun yaudaru da tunanin karkata mai gaba da addini, sai suka fada cikin munanan halaye maimakon su samu gaskiya, kuam sai suka rudu da aikin shedan da waswasinsa da rai mai umarni da mummunan aiki.
A wannan zamanin an samu mummuan jita-jita da yada farfagandar karya ta kyama da kin addini, da kuam yada kin kyawawan halaye musamman a tsakiyar karni na ishirin , kuma coci coci sun taimaka wurin samar da wannan yanayin ta hanyar nuna addini da wata sura mummuna ta hanayr zartar da dokoki da suka haifar da hakan game da addini da riko da addini, sai aka samu kyamar addini saboda munanan halayen malaman coci coci da kuma kawo dokokin da suke saba wa hankali da addinin kansa, sai dukkan wannan ya taimaka wa tunanin kin addini da guje masa da aka fi sani da Ulmaniyya ta samu kasuwar baje kulen ta da samun masu saya da cinikayya, amma duk da haka wannan ulmaniyya ba ta iya gamawa da tunanin riko da addini ba, kuma ta bayar da iyakacin kokarin ta kan hakan amma wannan dabi'ar halitta ta ci gaba da samuwa ga mutum.
Muna iya ganin abin da ya samu dan Adam a tsawon wannan lokacin da sunan kwaminisanci da abin da al'umma ta samu na kiyayya da gaba da tsanani da zalunci da danniya da kisa mai tsanani don kawai ta bar addini da kyawawan halaye, amma duk da haka masu karfi da iko ba su iya galaba kan wannan halittar ta son karkakata zuwa ga addini ba.
Sai ma muka ga bayan rushewar tarayya sobiyot mutane sun koma wa dabi'ar halittarsu sai fulawar addini ta sake budewa, wannan kuwa ba don komai ba, sai albarkacin wannan halittar da suke dauke da ita ta son karkata zuwa ga addini da Allah ya halicce su da ita.
Amma batun cewa mafi yawan mutane 'yan wuta ne wannan magana ce ba sahihiya ba, kuma ba ta doru bisa ilimi ba, sai dai mafi yawan mutane zasu kai ga aljanna ne, wannan kuwa domin musulunci ya kasa mutane gida biyu, bangare na farko su ne masu kin gaskiya bayan sun gane ta, sai suak yi gaba da ita don kin gaskiya, da kuma wasu jama'ar da su sun jahicli gaskiya ne, kuma suna son su kai gare ta, sai dai su a aikace sai su fada cikin kuskure, to musulunci ya bambanta tsakanin wadannan jama'o'I guda biyu.
Don haka ne yayin da musulunci yake sanya iyaka tsakanin akida ta gaskiay wacce manzon Allah (s.a.w) ya yi kira zuwa gare ta ya yada ta, da kuma akidar bata da mabiya shedan suke yadawa, sai dai yana da wani tausasawa ga masu jahilci wadanda suka takaitu ba suka takaita ba, domin wanda yake cancantar azabar Allah a mahangar musulunci shi ne wanda yake ya takaita ba wanda ya takaitu ba, wato su ne wadnda sako ya zo musu suka fahimce shi, suka gane shi, amma sai suka ki shi suka yi gaba da shi. Amma wanda sako bai zo masa ba, ko kuma ya zo masa amma a jirkice da jirwaye, sai suka yi riko da addininsu da aiki da gaskiya bisa akidarmu, to wadannan suna daga masu tsira.
A bisa gaskiya idan muka duba badinin samuwa muak nisanci zahiri, to zamu samu mafi yawan mutane suna karkata zuwa ga addini ne, kuam su zasu kasance daga mutanen aljanna daga karshe, ko da kuwa sun yi kuskure wurin dabbaka wannan tunanin nasu, wannan duk ba ya hana su amam samun azaba a kabari ko kuma a lahira , sai dai muhimmi shi ne daga karshe zasu samu zuwa da komawa zuwa ga aljanna, don haka masu dawwama a wuta su ne wadanda suka lalata fidirar halittarsu suka lalata halittar nan ta karkata a addini.
1- don karin bayani a duba littafin: fidira na shahid allama mutahhari, intisharat sadra, da kuma tafsirul maudhu'I alfitira fil kur'an, na sheikh jawadi amuli.
2- abin da ake nufi da kafiri a nan cewa wanda ya yi musu asasin addini ko wani laruri nasa, don haka ya hada dauk wani kafiri mai shisshigi da mai jahilici, sai dai mai shisshigi shi ne wanda ya ya yi musun ilmi da gaskiya da gangan, amma kafiri jahili shi ne wanda ya yi musu bisa jahilci ta yadda da ake gaya wa wanda ya yi musu bisa jahilci, wanda da ya gane gaskiya da ya karkata zuwa gare ta.
3- adalcin Allah na shahid mutahhari, kisimi na takwas, s 319 – 427, da kuma shafi na 424 – 427, a bayani mai taken ; khulasa wa natija.