advanced Search
Dubawa
17945
Ranar Isar da Sako: 2019/06/16
Takaitacciyar Tambaya
Tarihin Adam (as)
SWALI
Kur”ani bai kawo tarihin rayuwar annabi Adamu {as} ba, sai dai cewa masadir din tarihi sun bayyana cewa an halicci Adamu shekaru 6000 zuwa 7000 da suke wuce, sai dai cewa hakan bai kore abin da masana suka tafi kai cewa wasu nau”in mutane sun rayu a wannan duniya a miliyoyin shekaru da su ka gabata, sakamakon hakan bai ci karo da kur”ani da hadisi ba.
Amsa a Dunkule
Amsa Filla-Filla:
 bayani kan rayuwar wasu nau”in mutane da aka fara halitta a bayan kasa, da kuma sanin shekara nawa kenan da halittar su zuwa wannan zamani da muke ciki? To hakika babu wata aya da ta yi bayanin hakan cikin kur”ani.
Allama daba”ba”i cikin tafsirinsa na almizan ya na cewa: yahudawa sun kawo cewa shekarun wasu nau”in daga mutanen da aka haliccce su a ban kasa bai zarce shekaru 7000 ba, kuma hankali na karfafa wannan tarihi da suka kawo.
Sakamakon tsarin hayayyafa na ninkawa ta yanda dukkanin mutum biyu suna zamowa mutane 1000 bayan shekaru 100, saboda haka wannan lissafi zai ta hauhawa har tsawon shekaru 7000 ma”ana za mu yi ta cigaba har zuwa karnoni 70, da sannu zamu ga adadin mutane zai kai ga biliyan biyu da rabi wanda shi ne adadin mutanen wannan zamani da mu ke ciki yanzu wanda masana kidayar adadi mutanen duniya suka tabbatar.
 
Wannan shi ne abin da hankali ke fadi wanda tarihi ya tabbatar da hakan, sai dai cewa masana masu binciken doran kasa {geology} su sun tafi kan cewa nau”o’in daban-daban na dan Adam sun rayu kan wannan ban kasa fiye miliyoyin shekaru a baya, suna kafa dalili da wasu burbushi da kufaifayi da alamomi da kasusuwan kwarangwal din Dan adam da suka zama duwatsu da ke tabbatar da rayuwar dan adam a wancan lokaci, sannan kuma sun yi amfani da ilimin zamani da ya tabbatar musu cewa kowanne dayansu ya haura shekaru 500,000.
Wannan shi ne abin da masana kasa suka tafi kai, sai dai kuma dalilin da suke kawo ba dalilai ba ne masu gamsarwa dari bisa dari da za su iya tabbatar da cewa wadannan burbusai da kufaifayi da kwarangal din da suka zama duwatsu sune kakannin mutanen wannan zamanin ba. haka babu wani dalili da zai iya kore abin da suke tsammani da cewa wadannan kwarangal da suka zama duwatsu na danganewa da daurar wasu mutane da suka rayu wani zamani da ya shude ba, saboda ta iya yiwuwa hakan ta faru, mu kuma daurar mu ta kasance daban, kai ta iya yiwuwa su ne mutanen da suka rayu gabanin zuwan Adamu wanda daga baya suka kare ya zama babu su babu labarinsu.[1]
Mai yiwuwa dan adam ya samu a wannan ban kasa sai ya kare sai aka kara samar da shi ya kuma kara karewa akai ta maimaita hakan har zuwa daurar mutanen wannan zamani na mu. ta yiwu wannan ya karfafi dalili kan cewa  halittar annabi Adamu {as} na da dangantaka da samuwar sabuwar zuriyar mutanen Adam din mu, kuma gabaninsa an yi wasu Adam Adam da yawa wadanda suka shude, zuriya bayan zuriya suna karewa kuma Allah Ta’ala yana halittar wasu. Kuma dukkaninsu sun rayu a bayan wannan duniya sannan kuma suka kare labarinsu ya kau. Kamar yadda sassan jikin da ke tsinta wanda bincike ke nuna suna komawa ga miliyoyin shekaru ko kuma wadanda ke kumawa zuwa shekaru dubu 15 baya duk suna daga cikin karshe-karshen mutanen da a ka yi a doron kasa. Kuma tabbas al’kur’ani[2] mai girma da ruwayoyi[3] sun yi nuni zuwa ga wannan hakika.
 

[1] Tarjamar tafsirin mizan ta farisanci juz 4 sh 222
[2] A sarari kur’ani yay i Magana kan al’ummun da aka halitta kafin wannan saukar annabi adam duniya, wadanda suka rayu a wannan duniyar , a in da Allah ta’ala ke fadi { zan sanya halifa a doron kasa) sai  mala’iku suka ce {shin ka sanya zadanda suke yin barna a cikinta suke zubar da jinni}.
[3] Imam Sadik yana cewa “ta yiyu ku yi tsammanin cewa banda ku allah bai halicci wasu mutane ba kafinku, alhali bah aka ba ne miliyoyin Adam wanda ku ne tsatson Adam na karshe (Tauhid shafi 277 j2 bugub Tehra).
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

Tambayoyi Masu Fadowa

  • mece ce mahangar musulunci a kan samuwar halittu masu rai a sauran duniyoyi?
    10333 Tafsiri 2012/07/24
    Akwai tunanin cewa a cikin sauran duniyoyi shin za a samu halittu masu rai ko hankali, daya daga cikin tambayoyin da dan Adam ke neman bayanin su, amma har yanzu bai samu ba. Wasu bayanai a Kur’ani na nuni da samuwar wasu halittu masu rai a duniyar ...
  • ina aka samo asalin madogarar gabatuwar jagorancin malami
    8253 Tsare-tsare 2012/07/24
    Mas'alar jagorancin malami a matsayin shugaban al'umma a musulunci wani hakki ne da aka sanya shi ga wanda ya kai matakin ijtihadi. Wasu suna ganin lamari ne sabo a cikin fikirar musulunci, sai dai jagorancin malami a matsayin wani umarni na mai shari'a mai tsarki a lokacin ...
  • Yaya nau’ikan shiga jiki da hadewa a mahangar irfani, da kalam da hikimar muslunci suke?
    6499 اصطلاحات 2019/06/16
    Bayani kan menene (hulul) shiga jiki da ittihadi (hadewa) hulul a harshen larabci ya samo asali daga kalmar halla da ma’anar sauka[1] amma Kalmar ittihad ita kuma tana da ma’anar abubuwa biyu su hade su zama abu guda daya[2] Kashe kashen ...
  • me ake nufi da duniyar zarra
    9295 Tsohon Kalam 2012/07/26
    Duniyar zarra ko kuma duniyar alkawari, na nufin wani lokaci ko wata marhala ko mahalli ko kuma wata duniya ce wacce Allah ta’ala ya fitar da rayukan dukkanin mutane daga cikin tsatson Annabi Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi), a bisa kankanuwar sura sosai, kuma ...
  • Yaya aka samu sauyi a addinin Kiristanci, kuma da wane dalili ne ya samu karkacewa da jirkicewa
    11807 Sabon Kalam 2012/07/23
    Yayin da masu biyayya ga addinin Isa (a.s) suka haramata wa kawukansu wannan ni'ima ta samuwarsa a cikinsu, har ya samu hawa zuwa sama, sai manzanninsa da 'yan sakonsa suka ci gaba d aisar da sakonsa, kuma suka fuskanci wahalhalu masu yawa a kan hakan.
  • Yaya asalin mutum yake?
    20926 Tafsiri 2012/07/25
    Littattafan riwaya da na tarihi sun tabbatar cewa dan’adam wanda ke kan doron kasa bai kasance an same shi daga Habilu da Kabilu ba, shi dai an same shi daga dan Annabi Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) na uku mai suna Shisu ko Hibatullah.
  • Wasu irin hadisai ne suka zo a kan Hukuncin dan zina?
    13472 Dirayar Hadisi 2012/07/25
    Ruwayoyi na musulunci daga annabi (saw) sun yi magana da bayyana hukunce hukuncen dan zina, za mu kawo irin babobinsu Gadon dan zina;- Babin cewa dan zina, shi wanda ya yi zinar ba zai gaje shi ba, da ita mazinaciyar, ko wanda ...
  • Duk da samuwar Ayoyi masu yawa na Kur’ani wadanda suke yabon Sahabbai, me ya sa muke ganin ra’ayin shi’a na zargin su?
    24422 صحابه در نگاهی کلی 2019/06/15
    Mu munyi Imani da saukar Ayoyi masu yawa a kan yabon Sahabbai, kuma bamu tsammanin akwai wani Malami na Shi'a da yake musun haka, sai dai wannan ba ya nufin cewa wadannan daidaikun ko gungun jama'u, wadanda Allah ya yabesu a wani lokaci na musamman, a saboda ...
  • Menene Hukuncin musulmin da ya kashe kafirin da ba bazimme ba?
    6046 حدود، قصاص و دیات 2017/05/22
    Hukuncin musulumci kan kisa idan na gangan ne kisasi za a yi (Kisasi shi ne kashe wanda ya yi kisan kai) idan kuma ba na gangan ba ne diyya za abiya. Amma kafin a yiwa wanda ya yi kisan kai Kisasi akwai sharaDai da ya zama idan ...
  • Mene ne ma’anar shirin Ubangiji wato (makru) a cikin Kur’ani mai girma?
    13884 Tafsiri 2012/07/26
    (Almakru) Yana zuwa da ma’anar shirya wani abu da kuma neman wani abu wanda yake shiga cikin ayyukan alheri da na sharri saboda haka ne aka yi amfani da ita a cikin Kur’ani mai girma abar jinginawa da siffa mummuna wato makirci. Tanadin Ubangiji: Da ...

Mafi Dubawa