A mahangar Shi'a, jagorancin malami a lokacin boyuwar Imam Mahadi (a.s), shi ci gaba ne na jagorancin imamai ma'asumai (a.s), kamar yadda su ma jagorancinsu ci gaba ne na jagorancin manzon Allah (s.a.w).
Mas'alar jagoranicn malami tana daga cikin abin da aka yi bincike kansa daga rukuni na asasi na fagen siyasar musulunci, kuma ana kawo wannan fage na jagorancin a cikin babutnwan zaman al'umma, da sauran bayanai na asasi da suak hada da rayuwar al'umma, 'yanci, al'ummar musulmi, makoma, da ake kawo su a matsayin wasu bayanai na ilimi da suak shafin tsarin siyasar musulunci.
A mahangar Shi'a suan ganin jagorancin malamai a lokacin boyuwar imamai ma'asumai (a.s), kamar yadda su ma imamai jagorancinsu ci gaban jagorancin manzon Allah (s.a.w) ne. don haka yarda da hakan shi ne yake sama da komai a cikin al'ummar musulmi a game da lamarin da ya shafi tafiyar da al'amuransu cewa: idan akwai jagoran ma'asumi to shi kansa shi ne jagoran, idan kuwa ba ya nan to malamai su ne suek da wannan nauyin a kansu, don haka wannan mahangar tana daga cikin muhimmin tunani da yake nuna asalin nauyin da yake kan hukuma a mahangar musulunci da ya shafi lamurra masu daraja na hukuncin ubangiji a cikin al'umma, kuma cewa domin samun wakanar wannan lamarin dole ne a samu jagoaran a sama masani da addini. Kuma babu makawa dole ne shi wannan mutum ya zama yana da masaniya mai fadi game da lamurran rayuwa gaba daya, ya kasance mai iko da qarfi wurin tafiyar da lamuraan al'umma.
Idan aka ciro:
Mahdawi Hadawi Tehrani, Wilaya wa Diyanat, cibiyar al'adu, Gidan Khirad, Qum, 1380.