Duk da akwai nazarin cewa idan muna son mu sanya dokoki da bai kebanta da wani wuri ko zamani ba, ba mu da wata hanya sai zaben da mutane zasu yi.
Kuma akwai hanyoyi biyu da suka shafi sharuddan zabar jagora kamar haka:
1- Zabe kai tsaye.
2- Zabe ba kai tsaye ba.
Tsarin zabe ba kai tsaye ba an rijayar da shi bisa tsarin zabe kai tsaye. Sai dai yanayin mutane hatta a nazarin da yake ganin cewa jagoranci kafa ne daga Allah madaukaki da imamai masu daraja (a.s) ba bisa zaben mtauen ba ne wanda shi ne sahihiyar magana, sai dai mutane suna da wata babbar rawa da suke takawa ba ta buya, domin su ne zasu ayyana wanda ya cika wadannan sharuddan na jagora malami kai tsaye ko bakaitsaye ba domin jagorantar lamurran al'umma, kuma su taimaka masa wurin gudanar da wannan lamarin muhimmi.
Duk da akwai nazarin kafa jagora (ba zabe ba) [1], idan muna son mu sanya dokoki da bai kebanta da wani wuri ko zamani ba, ba mu da wata hanya sai zaben da mutane zasu yi[2].
Duk da cewa babu wata masala wurin kafa malami wanda ya cika sharudda a matsayin makoma kan lamurran al'umma ta yadda kowane mutum yana iya samun malami da ya cika sharudda da zai koma masa a kan lamurran jagoranci[3], sai dai idan muka duba lamarin a matsayin wani lamarin al'umma da zaman tare, kuma hatta a wannan ra'ayi na kafa jagora wacce ita ce nazari sahihi ingantacce, ba mu da zabi sai mun samu hanyar yadda za a zabe shi. Ko da yake a nan lamarin yana komawa zuwa ga ayyana malami da ya cika sharudda, wato mutane suna da muhimmanci wurin zakulo jagoran da ya cika wadannan sharuddan, ba wai su zabi jagoran su ba daga cikin wadanda suka cika sharuddan.
Akwai hanyoyi biyu na zabe jagoran da ya cika sharuddan:
1- zabe na kai tsaye: a wannan yanayin malamai da suka sharuddan da wadanda suke ganin su kansu suna da wadannan sharuddan na ijtihadi zasu rattaba sunanyensu domin zama 'yan takarar zaba jagora. Sannan sai kuma wadanda suka cika wadannan sharuddan daga wadanda ba su rattaba sunayensu ba sai su zabi daya daga cikin wadanann malamai maimakon mutane.
2- Zabe ba kaitsaye ba: A wannan hanyar za a samu wasu mutane da za a zaba a matsayin wakilai domin su gano wani mutum daya wanda yake da wannan sharuddan don su zabo shi domin jagorancin al'umma.
Idan mun lura zamu ga a dukkan hanyoyin biyu samun kwararrun da zasu ayyana wanda ya cika sharuddan jagorancin wani abu ne na dole, domin ilimi wani kwarewace da babu makawa da shi, kuma kwararru ne kawai zasu iya gano hakan ga wani mutum don su karfafa shi su ayyana shi. Da wani mutum zai yi da'awar likitanci, ai da likitoci ne zasu iya gano ingancin hakan ko rashin ingancinsa.
Bambancin wadannan lamurra biyu shi ne; a yanayi na farko kwararrun malamai suna zabar wanda ya cika sharudda ne daga cikin malamai da suka rattaba kansu don zabe, amma a yanayi na biyu su kwararrun malamai suna zabar wanda ya fi cika sharudda ne daga cikin malamai da suka cika sharudda ne.
Da wannan ne zamu ga hanyar zabe ba kai tsye ba –wato zaben kwararrun ta hannun mutne, da kuma zaben jagora ta hannun kwararru, ya fi kyau fiye da zaben da mutane zasu yi wa jagora kai tsaye[4].
Sai dai yanayin mutane hatta a nazarin da yake ganin cewa jagoranci kafa ne daga Allah madaukaki da imamai masu daraja (a.s) ba bisa zaben mtauen ba ne wanda shi ne sahihiyar magana, sai dai mutane suna da wata babbar rawa da suke takawa ba ta buya, domin su ne zasu ayyana wanda ya cika wadannan sharuddan na jagora malami kai tsaye ko bakaitsaye ba domin jagorantar lamurran al'umma, kuma su taimaka masa wurin gudanar da wannan lamarin muhimmi[5].
Karin bayani:
1. Mahdi Hadawi Tehrani, Wilayat wa Diyanat, Mu'assar Al'adun Khaneye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.
[1]. Lamba na 259, (wilayate fakih wa intisab).
[2]. Khubrigan sun fifita zaben da ba na kai tsaye ba, saboda ya fi kama da na tsarin kafawa fiye da na zabe.
[3]. Shi ne dai tsarin da marja'ai suke a kai har yanzu tun da.
[4]. Wasu suna ganin tsarin zabe da yake cikin kundin tsarin mulkin kasa ya zama dalili ne zabar ra'ayin tsarin zabe.
[5]. Wasu sun yi kokarin ganin sun takaita nazarin kafawa da muhimmancin mutane, wacce take ba ta samu dacewa ba sosai da ra'ayin tsarin musulunci na jagorancin malami.