Cigaba da wayewar al’umma yana daga cikin isdilahohin da suka yadu a cikin tunanin yammacin duniya da malam palsafar siyasar yammacin duniya da aka yi masa fassarori mabambanta daga cikin bayanai da aka yi wa wannan isdilahin, da muna iya gane cewa mahangar da ake da ita ga wannan ma’anar ba kawai ba ta dace da ta musulunci ba ne, sai dai ma muna iya cewa fikirar ciyasar musulunci ta kafu kan haka ne.
Ra’ayoyi kan hakan suna hada da:
1. Doka Ita ce ma’auni
2. Kariya ga hakkokin mutum
3. Daidaiton mutane a gaban doka
4. ‘Yancin al’umma
Da wannan ne muna iya tunanin cewa birnin annabi (s.a.w) yana daga cikin misalign wannan al’umma mai wayewa da cigaba a musulunci, kuma musulunci ya yi fintinkau a nan da kafa irin wannan al’umma.
Cigaba da wayewar al’umma yana daga cikin isdilahohin da suka yadu a cikin tunanin yammacin duniya da malam palsafar siyasar yammacin duniya da aka yi masa fassarori mabambanta daga cikin bayanai da aka yi wa wannan isdilahin, da muna iya gane cewa mahangar da ake da ita ga wannan ma’anar ba kawai ba ta dace da ta musulunci ba ne, sai dai ma muna iya cewa fikirar ciyasar musulunci ta kafu kan haka ne.
Shu’umin tunanin ra’ayin nan na Hobbez (Hobbes, Thomas) game da munin mutum da al’umma, fin karfi, son rai, tsoro, rashin amince wa juna, kwadayi, shi ne abin da yake gani a matsayin siffofin da cigaban wayewar al’umma yake kunshe da shi[1]. Don haka al’umma mai wayewar ci gaba gun Hobbez (Hobbes, Thomas), al’umma ce da take cike da halayen kuraye, da masu shan jinin mutane, da dabi’ar dabbobin jeji, da yake-yake[2].
A matsakaiciyar mahanga ta Jenjeaks Rozso (Rousseau, Jean Jackues) shi kuma yana ganin al’umma wayayya ita ce wacce take kafuwa sakamakon wani alkawarin hadakar zaman tare da kowane mutum zai yarda ya rasa ‘yancin kashin kansa domin kiyaye ‘yancin al’umma gaba daya na zaman tare.
Abin da yake nufin da ‘yancin nan na mutum daya shi ne ‘yancin da mutum yake da shi na kashin kansa da zai iya samun sa idan shi kadai yake rayuwa a lokacin da za a iya rasa al’umma mai rayuwar tare. ‘Yancin wayewa da ci gaban al’umma shi ne ‘yancin mallakar wani abu da mutum yake da shi a iyakacin abin da yake nasa a cikin al’umma da zai iya amfani da shi wurin cimma gurinsa da bukatunsa a al’umma.
Da haka ne zamu ga cewa ‘yancin dan’adam shi kadai ba shi da iyaka, amma ‘yancin dan’adam a cikin al’ummarsa yana da iyaka saboda yana cin karo da bukatun mutane.
Idan wannan bayanin shi ne ma’aunin da za a iya sanin al’umma mai ci gaba da shi, to lallai wannan bai yi daidai da abin da musulunci ya zo da shi ba. Sai dai a cikin bayanansu game da al’umma cigababbiya za a iya fahimtar cewa wadannan bayanai nasu ba kawai ya yi hannun riga da na musulunci ba ne, sai dai ma ya yi daidai kuma yana da mahada da tunanin siyasar musulunci.
Wannan mahada ta hada da:
1. Doka Ita ce Ma’auni: Wayayyar al’umma ita ce al’umma mai doka wacce doka ita ce ma’aunin alakokin zaman taren al’umma. Wannan kuwa wani lamari ne da yake a fili cikin fikirar siyasar musulunci domin tabbatar da tsari mai doka
2. Kariya ga hakkokin mutum: A cikin al’umma mai ci gaba dole ne a kiyaye hakkin mutane dukkansu. A fikirar siyasar musulunci haka nan ne cewa hukuma tana da alhakin kare hakkin kowane mutum a cikin daula.
3. Daidaiton mutane a gaban doka: A cikin al’umma mai ci gaba dukkan mutane masu daidaito ne a gaban doka ba tare da wani ya fi wani ba, kuma musulunci ya karfafi wannan daidaito.
4. ‘Yancin al’umma: ‘Yancin mutane shi ne ‘yancin da yake karkashin doka, kuma wannan lamari ne da yake karbabbe a musulunci.
Da wadannan bayanai zamu iya ganin cewa duk da bayanai masu wadancan ra’ayoyi suke gabatarwa game da al’umma mai ci gaba sun saba da bayanin musulunci kan hakan, sai dai sun hadu a kan wasu ma’aunai a dunkule.
Da haka ne zamu iya ganin cewa daular manzon Allah (s.a.w) ta kasance wani babban misali babba na daula game da ci gaban dan’adam da al’umma, kuma musulunci ya zama wani babban misali maras kama da ya yi fice a wannan fagen.
Duk da yana da fasila mai fadi tsakanin abin da ya kafu, da ra’ayoyinsa bisa mahangarsa ta asasi, sai dai ba shi da tamka ko tsara a mahangar da dokoki masu inganci da kyau.
Don Karin Bayani:
1- Mahdi Hadawi Tehrani, Wilayat ba Diyanat, Cibiyar al’adu ta Khaniyye Khirad, Kum, Bugu na biyu, 1380.