Ma’anar marja’iyya a mahanga ta shi’anci Abu ne biyu da a ka cakuda su suka ba da ma’an bai daya wato sha’anonin (Bada fatawa) da (jibintar malamin ko shugabancinsa), Hakika malaman addini masu girma sun tsaya kyam a fagen yin bayani da shiryarwa ta hanyar bayyana hukunce-hukuncen Allah a dunkule, kamar yadda bayanai suka yi tsayin daka domin daukar nauyin jagarancin zamantakewar al’umma, kai a wasu sashen lokuta ma sun kasance sukan yi alkalanci da tsaryarwa da kuma gudanar da hukunce-hukune a tsakanin mutane.
Amma idan muka warwarre kuma muka banbance tsakanin alamari bada fatawa da kuma jibintar Malami, muka taskace ma’anar marja’iyya da lamari na farko wato “bada fatawa” kawai, to a nan wasu tambayoyi za su yi ta taso da kansu suna jeho kansuda kansu, daga cikin wadanan tambayoyin akwai.
- Shin zai yiwu a raba tsakanin marja’iyya da jagoranci?
- Idan an kaddara hakan zai yiwu, to shin zai yiwu a sami jagoranci da marja’iyyanci masu yawa kenan?
- Idan mun kaddara cewa za’a iya banbance tsakanin marja’iyya da jagoranci, to shin zai yiwu wa ga al’umma ta iya komwa ga wanda ba jagora ba a cikin dukanin hukunce-hukunce na al’umma da na dai-daiku?
Ba da amsar wadannan Tambayoyi zai kasance ne ta hanyoyin nan masu zuwa:
- Cibiyar da aka gina hukumar Malami a kanta it ace kebantuwar da yake da ita a sanin fikihu da kuma ikon da yake da shi wajen fito da hukunce-hukunce na shari’a daga mabubbugar su ta asali, a dai dai lokacin da shi kuwa jagoranci, bayan sanin ilimin fikhu da iko wajen iya fitar da hukunce-hukunce na shari’a da malami yake da shi kari a kan haka ya ginu ne a kan wasu cancance – cancance na jagroanci wajen gudanar da al’amuran al’umma bisa ma’anoni da kimance-kimance na musulunci. (wato mahangar yadda mutum zai rayu a musulunci.)
Daga nan ne zai yiwu a sami wani mutum wanda wadancan martabobn da kwarewa madaukaka na sanin fikhu da ikon fito da hukunce-hukunce suka cika gare shi, to sai ya zama ya gabatarta a kan wanin sa a kan al’amarin marja’iyyanci, sai dai kuma ta bangaren jagoranci cancantasa a nan kasa take da cancnatar wanin sa wani (wani ya fi shi cancanta), to a nan wannann din sai ya zama shi ne abin rinjiyarwa wajen nadawa kan karagar al’amarin jagoranci.
A bisa wannann dalili ne, zai zama za’a iya banbance al’amarin marja’iyya da na jagroanci a hakalce, kai yin hakan ma a wasu lokuta ya zama dole.
- Ka’ida ta farko a al’amarin jagoranci it ace samun wahada wato zama abu daya, a al’amarin marja’iyya kuma a sami yawaituwa, duk da zama akasin hakan zai iya yiwuwa a kan al’amura biyu dukan su, kamar yadda yake cewa marja’iyya da jagoranci su hada a kan wani malami shi ma al’amari ne mai yiwuwa.
- Kamar yadda yake cewa bin umarnin jagora da aiwatar da horon sa al’amari ne da ya wajaba a kan kowa sannan bai halattta wasu malaman su rika warware hukunce-hukuncen sa ba, to ta wannann fuskar ne ya wajaba a kan al’umma ta rika yin biyayya gare shi da kuma aiwautar da ra’ayoyin sa a cikin al’amuran jama’a, bai halatta ga ita al’ummar ta rika dogare da wani ba a kan wadannan al’amura, abin da ya zo na amsa a kan tambaya ta farko ya kebanci matsalolin dai-daiku ne kawai ba wai ya kai ga al’amuran jama’a ba ne, domin a kan kewayen al’amuran dai-daiku ya halkatta ga mukllafi ya koma ya zuwa wanda ba jagora ba ne daga cikin marja’ai.
Manzo mafi karamci tsara da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya kasacne ma’abocin mukamai guda uku, na asali da tushe su ne:
- Mukamin isar da sako: Wato matsayin nan na isar da sakon ayoyin Alkur’ani mai hikima, da kuma sadar da hukunce-hukuncen shari’a ya zuwa ga mtuane da ganar da su.
- Mukamin zartar da doka: Matsayi na biyu na tsara da amincin Allah su kara tabbata a gare shi shi ne mukamin nan na yanke hukunci, da kowa karshen tashin-tshina tsakanin mutane. Mukamin jagoranci:
- Matsayi na uku, na Manzo (tsara da amincin Allah su kara tabbata a gare shi), shi ne na mukamin jagoranci da tafiayar da al’amuran al’ummar musulmi da juya k gudanar da al’amuran su.
Wadannan mukamai guda uku a zamanin gaiba suna ciratuwa ya zuwa ga malami, sai aka wayi gari malaman suna aiwatar da mukamin.
- Yin fatawa da bayanin hukunce-hukunce na shari’a a dunkule ga mutane da sanar da su kan lamarin su da kuma shiryar da su ta wannann nahiyar.
- Mukamin zartar da hukunuci da raba rigima
- Mukamin jagoranci da tafiyar da al’amuran al’umma.[1]
Ma’anar marja’iyya a tunanin shi’anci ya cakuda ne da abubuwa biyu wata ba da fatawa da kuma jibatar malami, hakika maraja’an addinin (Malamai) masu girma, sun tsaya da a matsayin su na bada fatawa da nunwa mutane abin da ya kamata ta hanary yin bayani dunkulallan hukunce hukunce na Allah. Kamar yadda suke tsayawa da daukar nayin jagroancin al’umma a dukanin al’amura na gefe da suka shafi al’ummmar, kai a wasu lokutan ma sukan tsaya a matssayin alkali mai yanke hukunci da kuma raba husuma a tsakanin mutane.
Amma idan mun raba tsakanin mukamin marja’iyya da wilaya (jibinta), muka takaita ma’anar marja’iyya da alamar ma farko wato ba da (fatawa) kawai to a nan za mu samu wasu tari na tambayoyi da za su bayyanar da kan su a gaban mu, na daga misalin:
- Shin zai yiwu a banbance tsakanin matsayin marja’iyya da na jagoranci? Da ma’anar shin zai yiwu wani mtum ya tsayu da makamin ba da fatawa na zamowar sa makoma a cikin dunkulallau hukunce-hunceu Allah ya zama makomar ga ala’umma, wanin sa kuma ya tsaya da jagoranci da gudanar da al’amuran da kasar al’ummar musulumi?
- Idan mun kaddara cewa hakan zai yiwu to shin ya halatta a sami jagorori da maraja’ai da yawa? Ko ko wajibi ne a hade mukaman biyu ga mutum daya? Ko kuma a kwai wani fifiko a tsakanin su ta wannann nahiyar?
- Idan mun kaddara cewa akwai rabuwa tsakanin marja’iyya da jagoranci to shin ya halkatta a raba wajen sanin dukkanin hukunce-hukunce na daidaiku da ma na al’umma?
Kafin a amsa wadannan tambayoyi da aka amnbata, titlas ne mu yi bayani takaitacce a matsayin share fage wajen fito da ma’anonin nan biyu wato “Fatraw” wadda ita ce a ke kiran mai bada ita (mufti) da kuma hukunci wanda shi ne yake zuwa daga jagora.
A yayin da Malami Mujahidi yake komawa ya zuwa tushe na asali domin gano hukuncin shari’a a duukule sannan yake dogaro da fitar da hukunci to yana tsayawa da neman fito da wannann hukunci ne domin ya gabato da shi gaban masu dogaro da shi ne, to a wannann lokacin ne ake ba da ma’anar (fatawa). Tun a nan ne zai yiwu mu ce fatawa it ace: fito da dunkulallen hukuncin addini a wani fage daga cikin fagage ta hanyar bibiyar mabubbugogi na tushe (Asali), tare da dogaro da wasu hanyouyi da salo sannane domin fitar da hukuncin.[2]
Haka kuma a yayin da jagora ya iyakance wasu aikace-aikace game da wata masala ta musamman a matsayin daidaiku ne ko al’umma yana mai riko da ababen lura na hukunce-hukuincen Allah gamammu da kuma lura da tsarin Musulunci tare da waiwaye ya zuwa wasu sharadan waje da yanayin da makallafai ke rayuwa to a wannann lakaci ne a ke kiran wannan aikin da sunan “hukunci” (ake bawa wannann kokarin –da marja’i ya yi - ma’anar “hukunci”).
To a nan sai mu ce: shi “Hukunci”, daga shi ne mai hukunci “Hikimi” ke sa idon basira wajen lura da hukunce-hukuncen Allah da wasu kimomi da manufofi na musulunci gamammu kuma dauwamammy, tare da lura da wasu yanayoyi na bigiire da kuma sharadiai da rayuwa ke gudana a kan su a cikin al’umma, kuma matukar wadancan sharadai da yanayoyin suna nan to hukunci zai ci gaba da zartuwa a hannun jagora ko na’ibin sa.
To abin da ya kamata mu ambata shi ne lallai mai shar’antawa mai tsarki ya tabbatar da wajabcin yin aiki da bin fatawar malamin da ya cika sharadai, kuma zamowar ta doka (shar’antuwar ta) halin ta da matsayin ta irin daya ne da halin hukuncin da hakimi (mai hukunci) ya zarta da kuma hukuncin da jagora ya zarta, wajibin al’amura,[3] amma akwai banbanci bayyyananne shi ne fatwar malami (fakihi) ta dogara ne a kan sa da kuma masu takalidi da shi a halin cewa hukuncin shugaba kuwa ya doru a kan kowa da kowa.
Bayan wannann gabatarwa, za mu bijiro da amsar tambaya da farko; wato masalar raba marja’iyya da jagoranci. Bisa dogaro da mallake – mallake da cancance-chancance na jagoranci da dalilan sa ne, malamin (fakili) da ya cancanci jagorartar al’ummar musulmai dai dai da tushe na ma’anunin addini, amma ita marja’iyya da ma’anar ba da fatawa tana da wata ma’anar ta daban, domin daga gefan maraja’iyya ne ma’anar takalidi ta samo asali, da ma’anar cewa a duk lokacin da aka sami wani malami da aka yi tabbatar masa da cewa abin komewa ne ta takalidi to a daya bangaren za’a sami wasu gungu na mutaune da suke yi masa takalidi.
Domin bayyaba ma’anar marja’anci a fili, ya zam tilas sai mun ba da haske a kan ma’anar takalidi.
Ma’anar takalidi a yaren Farisawa yana ba da wata ma’ana ta msuamman, sannan yana dauke da wata ma’anar mara kyau ta wata fuskar, ita wannann ma’ana na nufin yin biyayya da daukar wani malami ko mutum a matsayin jagora, ba tare da wani dalili ko hujja ba, wannan ne a bin da ikbal Allahuri ya yi nuni a kan sa a cikin shashi wakokinsa yana mai jibga dukkanin fushinsa da gabar sa a kan wannan nau’i na taklidi yana mai kiran sa da yin makauniyar biyayya ga wani, saboda haka ne ma zaka ga yana la’antar irin wannan taklidin kuma yana yin allawadai da shi.[4]
Amma idan kuma kalli taklida a gawayen ilimin fikihu, ko kuma mu ce; idan muka kalli abin da malamai suke nufi da wannan kalma ta fikihu za mu samu cewa wata ma’ana ta daban suke nufi da ita wacce ta saba da wacce muka ambata da mikdari nisan da ya kai kimanin daraja dari da tamanin (180), domin ba komai suke nufi da wannan ba face komawar wanda ba kwararre ba (wanda ba shi da masaniya ta musamman) zuwa ga wanda yake da masaniya, a cikin al’amura kuma yana nufin masaniya ta musamman (sepacialation) a kan wani ilimi na musamma, daga nan ne asalin wannnan ma’ana ta taklidi ta zama karbabbiya a hankalce a wajen jama’a kuma masu hankali su ka zama suna ganin ta da dukkkanin girmamawa da mutuntawa, suna ganin cewa wannan salo ne na wanda ya yi daidai da wannan yanayin da kuma hankali kuma ba shi da wani aibi kuma bai cacncanci zargi ba ballantana la’ana.
Sannan mafi mihimmancin dalilin da za a jingina da shi domin a tabbatar da wannan lamarin na taklidi a cikin hukunce- hukuncen shari’a shi ne wannan nukuda ta hankali da aka ambata, wacce ta doru a a kan larrurancin komawar mara sani zuwa wanda ke da masaniya, kamar yadda dukkanin dalilan na furuci da a ka tsayar a kan tabbatar da hujjar takalidi sun dogara ne da wannan ayan da ke cewa: {ku tambayi ma’abota sani idan har ba ku sai ba}. [5] da kuma ruwayoyin da suka zo a wannan fagen baki dayan su suna yin nuni ya zuwa ga wannan manuniyar ta hankali.
Daga nan ne ya zama cewa dalilin da ya sa ake komawa ga malami a cikin lamarin fikihu shi ne masaniyar da yake da ita a kan fikihu da kuma kwarewar da yake da ita a wajen fitar da hukunce- hukuncen shari’a daga mabubbugarsu ta asali. Alhali, hakika sharadan da jagarancin ya doru a kan su, - kari a kan kwarewa da kuma iya fitar da hukunce- hukunce - su ne cancance- cancancen (suffofi na musamman) da malami jagare ya tattara a wa jen gudanar da lamarin al’umma, bisa dokokin da kyawawan dabi’u na musulumci.
Bisa wannan asasin, za a aiya samun malamin da ya ciki wadannan siffofin a mafi girman da madaukakin matsayi a wajen ilimi da iya fitar da hukunce- hukunce, sai ya zama an gabatar da shi a kan wanin sa a marja’iyya, (marja’anci)[6] sai dai kuma a bangare jagoranci yana da karancin kwarewa fiye da wanin sa, sai ya zama wani malamin (wanda ya fi shi kwarewa) ya fi shi cancantar wannan ya rike wannan matsayin na gudanar da lamarin al’umma da jagorancin al’aumma.
Ta wannan mahanngar ne raba tsakanin marja’anci da shugabanci ya zama abin da ya yi daidai da hankali, kai a wani lokaci ma ya kan kai ga ya zama tilas a raba su.
Ammam dangane da tambaya ta biyu; samun shuwagabanni da marja’ai da kuma shugaba ko marja’i daya tal, bayan da muka tafi a kan yiyuwar a raba tsakannsu, ya zama lalle mu waiwayi wata nukuda mai mihimmanci; gama cewa komawa ya zuwa marja’I tamkar komawar jahili ne ya zauwa malami kuma kamar komawar wanda bai da kwarewa ne zuwa ga kwararre, samuwar kwararru masu yawa da marja’o’I da yawa, zai zama a bu ne mai yiyuwa a cikin al’ummar musulmai, ballantana ma abu ne mai da ake so ta yadda kowa zai iya komawa zuwa gare su da kuma karbar fatawa daga cikinsu ta hanya mai sauki ba tare da wahala ba.
Amma mas’alar jagoranci da jibintar lamari da gudanar da lamarin al’ummar musulmi gama cewa wannan lamarin na damfare da tsarin zamantakewa tare da cewa yawaitar wajen da umarni zai rika zuwa daga gare shi zai kai ga rudani da rikirkicewar lamura da lalacewar tsari. Dun haka yin biyayya ga jagora majibincin lamari guda daya ya zama wajibi ga dukkanin mutane kari da malamai (marja’ai) baki daya, daga nan ne yanayi ya hukunta wajabcin samun shugaba guda daya musamman ma idan muka yi duba ya zuwa ga mahangar na ta musulumci da ta ki yarda da samun shuwagabanni kuma ta tafi a kan cewa kasar musulumci gaba dayan ta kasa daya ce, ba a la’akari da wasu iyakoki a shenge-shinge iyakoni kasashen da aka kirkira a cikinta, na’am zai iya yiyuwa tare da la’akari da yanayi na musamman da kuma kallon maslahar musulumci a sami shuwagabanni mabanbanta a sama da kasa daya (kasashe daban-daban), ko kuma a yarda da gudanar da lamura da wani yanayi ko tsari na musammam daga cikin tsarin shugabanci, amma ya zama da sharadin kare maslahohin musulmai da kuma samar da hadin guiwa tsakanin shugabancin don kar al’ummar musulmi ta fada cikin dimuwa da daidaita da rarraba.
Amma a matakin fatawa da bada fatawa ba ma ganin tilascin kadaitar fatawoyin malamai, ballantanma ko wane malami abin kallafawa yin fatawa ne bisa a bi da ya ginu a kan sa na tunani da mahanga da kuma usulul fiihi da ma wanin sa na daga abin da ya dogara a kan sa.
Kenan kaida ta asalin dangane da shugabanci ita ce kadaita, dangane da marjaiyya kuma yawaitaka, tuk da cewa abu ne mai yiyuwa lamarin ya juya ya zama sama a kasa kamar yadda zai iya yiyuwa marja’anci da shugabanci su hadu a hannu mutum daya shugaba kuma malami (marja’i) a lokaci guda.
Amma dangane da tambaya ta uku, yiyuwar mutane su koma ga wanin shagaba a cikin dukkani hukunce-hukuncen zamantakewa da kuma kashin kai, amsa a kan wannan na bukawatuwa ya zuwa waiwayawa ga wata malura mihimmiya, wacce ita ce shi shugaba a yayin da ya zartar da hukuncin sa hakika da gaske yana lura - karin a kan dudan yanayi da sharadai da kuma mahallin da fatawar ko umarnin zai iyi aiki - da hukunce-hukuncen Allah ta’ala a dunkule da kuma daukakin tsarin musulumci, a bisa wannan sharadin ne yake yin fatawarsa ta yin umarni ko ka ce bada umarnin sa, wannan ta wannan bangaren kenan, ta daya bangaren kuma, tuni mun riga mun bayyana a baya cewa hakika hukunci mai shagabanci da jagora na hawa kan kan kowa kuma ya zama wajibi kowa ya aiwata da shi.
Anna kuma wannan matsalar ko tambayar mai zuwa za ta rika kutso kai da kan ta, tana cewa; to idan har ya halatta mutane su koma wa wanda ba jagora ba a cikin mas’alolin na zamantakewa da namusamman (na daidaiku), ta wani bangaren kuma ya zama wajibi mutum ya yi aiki da abin da jagora a ya ce, a nan akwai yiyuwar al’umma ta fada cikin dimuwa da rudani idan har fatawr wanda ba jagora ba ta saba da ta jagora, domin shi jagoran ya zantar hukuncin na sa ne saboda ya san cewa wannan shi ne ainihin hukuncin shari’a wanda ake su a zo da shi, kuma da ya san cewa ba haka hukuncin sa yake ba da bai bada fatawa da hakan ba, a lokaci guba kuma fatawar wanda ba jagora ba za ta zama ita ce ainihin hukuncin da jagoran ya yi jifa da shi ya ki yin hukunci da shi, a irin wannan yanayin ta yaya al’umma za ta zama ta lazimci yin biyayya ga jagora.
Tare da la’akari da wannan ishkali ko matsalar ko tambayar za mu iya cewa: abin da zai fara zuwa tunani a matakin farko shi ne cewa; tun da har yin biyayya ga jagora wajibi ne ga kowa da kowa kuma bai halatta ga wani malami ya warware hukuncin sa ba, kenan bai halatta ga al’umma ba ta koma ya zuwa wanin jagora ba a cikin lamuran na al’umma da zamantakewa ba, amma abin da ya zo a amsar tambaya ta farko wannan ya kebanta ne da lamura na kashin kai (na musamman) kuma wannan ba ya shafar lamuran al’umma wandanda jagore kadai suka shafa. Na’am, a cikin mas’aloli na kashin kai ya halatta ga mutane su kowa zuwa wanin jagora su yi takalidi da shi.
Domin karin bayani ka koma wa: mahdi mahdawi daharani a cikin littafinsa shugabanci da addini (wilayat wa diyanat) bugun mu’assatu farhangi khane khird (muassasatu darul hikima) Kun, bugu na biyu, 1380. Hijiri shamsi.
[1] Alanawinul murtabida: dalilan shugabancin malami.
[2] Imam khomaini (Allah ya tsarkake ruhinsa) ya bayyana wannan tafarkin a istimbadi “ alfikuhul sunnati ko kuma al fikihul jawahir”. Ka dunba mahdimahdawi daharani a cikin fikihu hukumati wa hukumatu fikhi , a rubutun san a ranar tunawa da rasuwar iamm khomaini (Allah ya tsarkake ruhinsa) shafi na 10-11 watan khurdad shekara ta 1373 hijiri shamsi.
[3] Daga nanan a wace okuta ake cewa hukunce-hukuncen shari’a sun kasu ya zuwa kaso biyu, hukunce-hukunce Allah da na biyayya, na farko ana kiransu da gamammun wadana da suka mamaye ko suka kewaye ko suka tattare dukkanin hukunce-hukuncen addini tabbatattu da fatawa, na biyu kuma sune hanunce-hukunceun da suka zo daga wajen majibincin lamari (jagora ko shugaba).
[4] Ikbal na fadia cikin wakarsa:
Ka yi watsi da yin takalidi da bayi* la’ana dubu sau biyu ta tabbata kan iran wannan takalidin.
[5]Surar nahli aya ta 43.
[6] Ana kiran wannan mas’alar da sunan sharadin kasantuwa mafi ilimi “shardul a’alamiyya” kadai yana wajaba a koma ga mafi ilimi a yanayoyi masu zuwa
- idan fatawa mafi ilimi ta saba da ta wanda bai kai shi ilimi ba.
- Idan ya zama tazarar da ke tsakanin mafi ilimi da wanin sa tana da nisan gasket a bangaren ilimi da kwarewa ta yadda fatawrwanda aka fi ilimi zata zama ba tada wata kima a mahangar kwarewa, ko da kuwa tana da kima ta kwarewa a wajen sauran mutane wadanda ba malamai ba.