Takaitacciyar Tambaya
Shin a cikin Kur”ani akwai ayar da ta yi bayanin cewa hakkin yin saki ya kebanta da namji?
SWALI
Shin a cikin Kur”ani akwai ayar da ta yi bayanin cewa hakkin yin saki ya kebanta da namji?
Amsa a Dunkule
Dun da cewa Kur”ani bai bayyana a sarari cewa hakkin saki ya kebanta da namiji ba sai dai dukkanin ayoyin da suka yi Magana kan saki suna fuskantar namiji ne kaitsaye bisa misali; ya zo a cikin wasu daga cikin ayoyi kamar haka:- {Idan kuka saki mata kuma suka gama idda kar ku hana su su kuma auran mazajensu na da}.[1] Da kuma fadin Allah {ya ku wadanda kuka yi imani idan kuka auri mata sannan kuka sake su kafin ku kusance su, to ba zasu zauna zaman yi muku idda ba “babu idda a kansu”..}.[2] da kuma {ya kai wannan Annabi idan ka saki mace}.[3]
Daga wadannan ayoyin da ma wasu da suka yi kama da su zamu fahimci cewa saki na hannun namiji shi kadai kuma mace ba za ta taba iya yin saki ba kamar yadda lamarin yake kan dawo da mace zuwa ga mijinta a kwanakin da take iddar sakin kome.