Allama Majlisi (RA) ya ruwaito a cikin littafinsa Biharul-Anwar cewa: Wani mutum ya zo wurin Imam (a.s) sai ya ce da shi “Ya sarkin muminai, ka bani labarin mene ne, Wajibi, da, Abin da yafi wajaba, Abin mamaki da abin da yafi ban mamaki, abu mai wuya, da abin da yafi wuya, abin da yake kusa, da abin da yafi kusa.
Nan take, tun bai gama jan numfashi ba, tun harshensa bai gama motsawa ba, sai Imam Ali (a.s) ya amsa masa da baitukansa na waka, da cewa: Yafewar Ubangijin bayi wajibine ya yi a kansu,
Amma barinsu ga (aikata) zunubai, shi yafi wajaba.
Kuma zamani wajen caccazawarsa abin mamaki ne, amma gafalar mutane game da hakan shi ya fi abin mamaki.
Hakuri a cikin masifu na da wahala, amma kubucewar lada tafi wahala.
Dukkan abin da ake jira na kusa, amma Mutuwa kuwa ita tafi kusa.