Aure Mai Tsayayyen Lokaci Sunna ne daga Cikin Sunnonin Musulunci, Wanda Halaccinsa ya zo A Cikin Alkur’ani Mai Girma, Kuma Wannan Sunnar ta Gudana A Lokacin Manzon Allah Mafi Girma (s.a.w) da Lokacin Halifa na Daya, da Wani Sashi na Lokacin Halifa na Biyu, Har Lokacin da shi Halifa na Biyun Ya Hana, Kuma Imamai Ma’asumai (As) Suna Karfafa Mutane A Kan Yin Wannan Auren , Wanda Hakan Ya Faru ne Saboda Ita Wannan Sunna Ta Allah, A Wancan Lokacin, Ta Zamo Kamar Wata Bidi’a ce, Wacce Take da Bakin Fenti, Mai Kamanni da Haramun. To, Amma Ruwayoyin da Suka zo a Game da Wannan Mas’alar, Hukuncinsu Kamar Hukuncin Ruwayoyi ne Wadanda Suka zo Awasu Wurare Daban, Akwai Bukatar Ayi Darasin Su, A Kuma Tantance Su Ta Bangaren Isnadi, da Bangaren Abin da Suka Kunsa, Wanda Shi ne Abin da Zamu Yi A Yanzu, Dadin dadawa Kuma Dole ne A Yi Taka tsan tsan, Wajen Fahimtar Wadan nan Hadisan da La’akari da Irin Yanayin da Suke Zagaye da Wadanan Hadisan, da Irin zamanin da Hadisin Ya Fito A ciki, da Irin Wayewa na Ilimi, Wanda Shi ne Yake gudana a Wancan Lokacin,
Aure Mai Tsayayyen Lokaci Sunna ne na Musulunci Wanda An Bayyana Halaccinsa A Cikin Alkur’ani Mai Girma, Kuma Wannan Sunna Mai Kyau ta Gudana A Zamanin Manzo (s.a.w) da Zamanin Halifa na Farko da wani Sashe na Zamanin Halifa na Biyu, Har Lokacin da shi Halifa Na Biyun Ya Hana, Kuma Imamai Ma’asumai (As) Suna Kwadaitar da Mutane A ko Yaushe A Kan Yin Wannan Auren , Hakan Kuma Ya Faru Ne Saboda Ita Wannan Sunnar Ta yi Kusan ta Koma Kamar Wata Bidi’a ce Wacce ma Akayi Mata Bakin Fenti da Kamanceceniya da Haramun A Wancan Lokacin, Kuma Aikata Wannan Sunnar Ga su Muminai Ta Zamo Kamar Wani Raddi ne ga Ita Waccan Bidi’ar hanawar , Saboda Haka Son da Ake Yin a Aikata Wannan Auren A Bangaren Shi’a Ya Samu Dalilinsa Ne don Wannan Al’amarin, Wannan Kuma Wani Abin Lura ne Wanda Dole ne A dinga Halarto dashi A Cikin Rai A Lokacin da Ake Karanta Wadan nan Hadisan, Amma Game da Bincike na Ingancin Ruwayoyin, Wannan Bincike ne Wanda Yake da Matukar Bukatuwar Tantancewa, Saboda Haka Amfanuwa da Hadisai Yana Bukatar Ilimi Na Kwarewa, Dadin dadawa Kuma Akwai Bukatar A Bincika Isnadin Ruwayar, Wanda Wannan Binciken ne Yake Amsa Tambayoyin Da Suke Cewa Shin Asalin Fitowar Wannan Ruwayar daga Imami Ma’asumi Ta Inganta ? Ko bata Inganta Ba. ?
Dadin dadawa Kuma Akwai Bukatar Ayi Bincike Akan Abin da Hadisin Yake Koyarwa Wanda Zai zo Bayan An Riga An Hukunta Cewa Isnadinsa Ya Inganta, Wato Wannan Binciken ne zai Amsa Tambayar da Ke cewa Mene ne Ma’anar Hadisin? Kuma Mene ne Hadisin Yake Koyarwa? .
Daga Cikin Mas’aloli Muhimmai game da Fahimtar Hadisi Akwai Sanin Dalilin Fitowar Hadisin, Wannan Wata Mas’ala ce Mai Kama da Darasin Asbabul Nuzul Wato Sanin Dalilin Saukar Wasu Ayoyi Masu Girma, A Dalilin Haka Za’a San Shin Wasu Irin Yanayi ne, Hadisin Ya Fita A Cikinsu, Kuma Don Amsa Wace Mas’ala ce, Kuma Akan Wani Mauru’i ne Suke Karantarwa? , Saboda Haka Alokacin da mun yi Ittifaki da Kai Akan Wasu Sashe na Abin da Ka Kawo, Hakika Kawo Hadisai da Kuma Yin Sharhi Akansu Daga Mutane Daidaiku, Wadanda Su ba Kwararru Bane, Wadanda Basu da Kwarewa, da Hange Mai Zurfi, Wadatacce, Al’amari ne na Kuskure Wanda ba Ingantacce ne ba.
A Dalilin Haka ne ma har A Zamanin Imamai Akwai Mutanen da Ake Nuni dasu, A Game Da Ruwaito Hadisi , Wadanda Kuma Suke da Izini A cikin Wannan Fagen .
Don Yin Bincike Da Tantancewa A Kan Wadannan Hadisan da Kuka Yi Tambaya Akansu, Dole Ne Ayi Bincike Akansu Ta Bangaren Isnadi da Kuma Abin da Nassin Yake Karantarwa.
1- A Ruwaya Ta Farko Wannan Hadisin Ya zo Ne Acikin Littafin Al -Kafi Ne Mai Daraja, da Isnadi Kamar Haka: Wasu Gungu Na Sahabban Mu, Sun Ruwaito daga Ahmad Dan Muhammad Ban Halid Daga Muhammad Dan Ali daga Muhammad Dan Aslam daga Ibrahim Dan Fadl daga Aban Dan Taglib, Ya ce: Nace Wa Abu Abdullahi As na Kan Kasance A Wasu Hanyoyi, Sai In Hadu da Mace Kyakkyawa, To Amma Bani Da Nitsuwa na Tabbas Cewa Shin Tana Da Miji Ko Kuma Tana Cikin Karuwai ne. Sai Ya ce: Wannan Bai Hau Kanka Ba, Abin da Yake Kanka Shi ne Ka Gaskata ta Akan Abin da ta Kira Kanta Da Shi. ”
To, Acikin Isnadin Wannan Ruwayar Zamu Samu Muhammad Dan Ali Da Muhammad Dan Aslam, Wadanda Su Biyun Suna Daga Cikin Gullatu, Kuma Suna Daga Cikin Masu Rauni, Da Ibrahim Dan Fadl Al Hashimiy, Wanda Shi kuma Majhuli Ne Wanda Ba’a Sanshi Ba Samsam, Sai Dai Kuma Acikin Wannan Mauru’in na Cewa Za’a Gaskata ta, (Mace) A Kan abin da Ta kira Kanta da Shi, akwai Ruwayar Da Tazo A Bayan Wannan Ruwayar Wacce Ita Tana Da Isnadi Ingantacce Wato Ma’ana Dukkan Maruwaitanta Masu Bin Mazhabar Imamai Sha Biyu ne (As) Kuma Amintattu ne. Sannan Isnadinta Ya Isa Ga Imamai, Kuma Abin da Ruwatar Ta Kunsa Ya yi Kama da Abin da Wannan Hadisin da Aka Ambata Yakunsa, Sai Dai Kuma ba Makawa, Alura da cewa Acikin Ruwayoyi Akwai Wadda Ita Gamammiya Ce, da Kuma Kebantacciya, Akwai Sakakkiya Akwai Mai Kaidi, Kuma Awasu Lokuta Ana Samun Wasu Kalmomi Masu Warware Junansu, Ko Kuma Masu Rauni, Wadannan Wasu Al’amura ne da Suke Sabbaba Matsaloli Wajen Fahimtar Hadisai, Saboda Haka ba makawa Dole ne Akoma Zuwa ga Kwararru da malamai Na Wannan Fannin, Su ne Mujtahidai, Don Mu Tsira Daga Mummunan Fahimta, Ko Yin Tafsiri Da Ra’ayin Son Kai.
Ko Ma Ayaya Ne dai, Wannan Mas’alar ta Tabbata A Cikin Bincike na Fannin Ilimin Hadisi, Wato Cewa Ita Mace Ana Gaskata ta Akan Irin Sunan Da Ta Kira Kanta da shi, Idan Tace bata da Aure, Amma Abisa Sharadin Ta Kasance da ma Ba’a Tuhumarta da Karya. [1]
2- Ruwaya Ta Biyu, Wannan Bamu Same Ta A Cikin Littattafan da Suke nan ba. Saboda haka ba zai Yiwu Muyi Sharhi Na Nazari A Kanta ba.
3- Amma Ruwaya Ta Uku, Asalin Ruwayar Tazo Ne Kamar Haka An Ruwaito Daga Sa’ad, Daga Hammad Dan Ya’ala, Daga Babansa Daga Hammad Dan Isa Daga Daga Zarara, Daga Abu Ja’afar (As) Ya ce: Lahawun Mumini Yana Cikin Abubuwa Uku Ne, Jin Dadi Da Mata, da Yin Raha Da Yan’uwa, da Yin Sallar Dare.
A Cikin Isnadin Wannan Ruwayar, Akwai Hammad Dan Ya’ala, Da Babansa Ya’ala Dan Hammad, Dukansu Biyun Nan Majhulai Ne, Wato Wadanda Ba’a Sansu ba, Saboda Haka Ruwayar Tana da Rauni A Bangaren Isnadi, Sai Dai Kuma A Ta Bangaren Ma’anar da Ta Kunsa, Babu Mushkila A Cikinta Domin Shi Aure Mai Kayyadadden Lokaci Halal Ne, Kuma Shari’a Ta Yarda Dashi, Ko Da Kuwa Anyi Shi Ne Kawai Don Jin Dadi, Kari Kuma Akan Hakan Shi ne Tana Yiwuwa Kalmar Jin Dadi Da Mace A Nan Tana Nufin Aure Ne Na Da’imi, Dawwamamme. Saboda Haka Hadisin Zai Zamo Bai Ma Shafi Abin da Ake Tattaunawa A Nan ba.
4- Amma Ruwaya Ta Hudu Wacce Aka Kawo A Farkon Tambayar
An Ruwaito Tane Da Isnadi Guda Biyu Masu Rauni.
- Sai Dai Akwai Wata Ruwayar A wannan Babin Wanda Shi Isnadinsa Ingantacce Ne, Wato Dukkan Wadanda Suka Rauwaito Shi Masu Bin Imamai Sha Biyu Ne, Kuma Amintattune, Da Isnadinsa Wanda Ya Hadu Da Imami Ma’asumi, Saboda Haka Za’a Iya Samun Nutsuwa Akan abin da Hadisin Ya Kunsa A Bangaren Nazari Na Fikihu.
- Abu Na Biyu Kuma Ingantacciyar Ma’anarsa, Tana Nufin Mustahabbine (Amma Ba Dole Ba) Yabi Allah Ta Hanyar
Yin Auren Mutu’a, Don Ya Tsira Daga Rantsuwar Da Ya yi Ta Sabon Allah. Saboda Haka Abin da ya Doru Akansa Shi ne Ya yi Auren Mutu’a Sau Daya. [2]
- Amma Hadisi Na Biyar Shima Bamu Same Shi Ba Acikin Dukkan Littattafai Na ruwaya.
Saboda Haka Al’amari Na Auren Mutu’a, Al’amari Ne Wanda Yake Akwai Ittifaki A Wajen Dukkan Malaman Shi’a, Koda Kuwa Anyi Auren Saboda Jin Dadi Ne Kawai. Wannan Ma’anar An Samo Tane Daga Ruwayoyi Daban Daban, Banda Wannan Ruwayar Da Kuka Ambata, Wadanda Ruwayoyi Ne Masu Yawa Ba Kadan Ba, Wadanda Kuma Sun Cika Dukkan Sharudda.
Don karin bayani za’a iya duba wadannan wajajen: -
- Mauru’i Auren Mtu’a Da Sakina Lamba Ta 2935 A Dandali Na …………. .
- Mauri’in Auren Mutu’a A Karni da Tarihin Ma’asumai Lamba Ta 2965 A Dandali Na ………. .
- Mauru’i……Mushlilolin da Suke Haifar da Matsala Ga Matasa A Auren Mutu’a A Cikin Al’umma Lamba Ta 1431lambar Dandali Na 20100.
3- Shehus Saduk, Alkhisal Juzu’i Na 1 Shafi Na 161 Manshurat Jami’atul Mudarrisin Kum, Hijira Kamariyya 1403.
4- Al-Amili, Ash Shekhul Hur, Wasa’ilush Shi’a Juzu’i Na 31shafi Na 17 Babin Mustahabbancin Auren Mutu’a Ko Da Mutum Ya yi Alkawarin Zai Bari, Ko Kuma Ya yi Bakance Akan Haka, Muassasatu Ahlul Baiti As Kum Hijira Kamariyya 1409 Babin Son Da Ake Yi Mutum Yabi Allah Ta’ala Ta Hanyar Yin Auren Mutu’a Ko da sau Daya Kawai don Kawar Da Rantsuwar Sabo da Ya yi.
[1] Islam Alkulaini, Alkafi Juzu’i Na 5 Shafi Na463 Darul Kutubul Islamiyya Tehran 1365 Hijira Shamsiyya.
[2] Taudhihul Masa’il Na Imam Khomeini Juzu’i Na 2 Shafi Na 499 Mas’ala Ta 2456 Da Kuma Hashiya Na Manyan Mujtahidai Na Fadil Lankarani, Shistani, Makarim Shirazi.