Please Wait
12296
Abin da ake nufi da ruwaya ta farko shi ne duk da kasantuwar masallatai su ne fiyayyun wurare na tsai da salla kuma salla a cikinsu yana da lada mai yawa. Sai dai fiyayyen masallaci ga mata shi ne dakunansu. Saboda yin hakan zai hanasu cakuduwa da bare. To wannan ruwayar bata hana mata halartar masallatai ba ne.
Ita kuwa ruwaya ta biyu tana maga ne a kan batun mata idan zasu halarci masallaci, suka nemi izininku to kada ku hanasu. Saboda rashin haramcin halarta ko da kuwa saboda salla ne. Domin sun zabi yin sallar ko da zasu sami lada ‘yar kadan. Kuma duk da haka musulunci baya kodaitar da mata su halarci masallaci domin yin salla, sai dai bai haramta hakan ba. Amma idan hakan ya hadu da wani sha’ani kamar sallar juma’a ko yin darasi da jawabai na ilimi da na addini, to lalle abu ne mai kyau.
Ra’ayin Musulunci game da cudanyar mata da maza shi nesantar juna, a ko ta wane yana yi cudanyar kuwa ta kasance, kuma kada su fita daga gida sai bisa lalura. Wadannan ruwayoyi biyun suna fassara wannan manufar. Dangane da ruwaya ta farko hakika Imam Sadik (a.s), ya ce: “Fiyayyun masallatai ga matanku su ne gidaje” Abin nufi a nan shi ne cewar duk da cewa masallatai su ne wurare da suka fi dacewa da tsai da salla, kuma salla a ciki akwai lada mai yawa idan aka kwatanta da salla a wani gurin. Sai dai mafi kyawun wurin salla ga mata, shi ne dakunansu. Dalili shi ne, wannan yanayin ba za su bar gida, su je su yi cudanya da wasu bare ba. Abin da Imam yake so ya ce a nan shi ne: “Cakuduwa ta bisa lalura tsakaninsu da bare ba abu ne da ake fatar kasantuwarsa ba, ko da zuwa masallatai ne ko yin sallar jam’e. A she ke nan abu ne da ba a bukata sai a bisa lalura. Don haka kamata ya yi a nisanceta. Amma duk da haka wannan ruwayar bata haramta wa mata halartan masallatai ba. Matukar akwai wasu abubuwa da ba salla ba -kamar tsai da sallar jam’e ko sanin wasu mas’aloli da suka wajaba mata su sansu. (ta yadda hakan ba zai samu a gidajensu ba) don haka ba zayyiwu a haramta wa mata su halarci masallaci ba. Ba za mu yi watsi da batun halaratar ba bisa dogaro da wadannan hadisai masu girma. Idan muka kalli bayanin da ya gabata, za mu fahimci ma’anar ruwaya ta biyu. Ya kamata a fahimci cewa ta biyun sam bata ci karo da ta farkon ba. Doman cewa take idan sun nemi izinku, za su je masallaci, to kada ku hanasu. Ku ba su izinin halartar masallaci. Domin halartar ko don yin sallah bata zama haramun. Ko da sun zabi su yi sallar su samu lada ‘yar kadan.
Kasantuwar halartar masallatan ya na kunshe da fa’idoji na ilmantuwa da ma’anoni daban-daban ta yadda idan ba su halarta a irin wadannan wuraren ba, ba zasu amfanu ba. Bisa la’akari hakan ya dace da ruwaya ta biyu, saboda Annabin Girma (s.a.w) yana cewa idan suna son zuwa masallaci to kada ku hana su.