Please Wait
35871
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji.
Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta mini kuma ku tsai da salla domin tinawa da ni”, domin ALLAH mai girma ya yi tajalli a a cikin bawan sa sakamakon yin sallar.
Da zara ALLAH ya yi tajalli ga bawansa mai salla, sai ya bayyana a gar e shi kuma sai ya sami nutsuwar zuciya kuma daga cikin tasirin ta da zai samu shi ne zai sami kwanciyar hankali a zuciyar shi domin a cikin littafin shi mai girma yana Allah cewa “ku sani da ambatan ALLAH ne zuciyuyi suke samin nutsuwa” domin mai salla da sallar shi ne yake fin karfin zuciyar sa ya kuma raya tunanin sa ya rayu, hakika da ya daga cikin a bin da ya kemanta da s salla shi ne shi masallaci na raya tunanin sa, wadanda da suke tsai da salla da ya daga cikin abin da suke iya su samu shi ne kwanciyar hankali da nutsuwa, daga wannan abubuwa da suke samu sakamakon sallar su suke samin damar motsawa domin fuskantar duk wani cinje-cinje na rayuwa, ba za su taba samin sas-sauci ba yayin da suka fuskanci matsala kuma ba sa tsoran wahala, idan alheri ya same su suna tai makawa mutane, Ba sa hana mutane daga alherin da ALLAH ya ba su.
Hakika salla ita ce kogin da yake tsarkake mutum. idan mu ka ji cewa ba ma jin tsarkin zuciya wanda a ke iya a samu sakamakon tsai da salla, to zai zamo dole mu tabbatar da cewa ba mayin salla yadda ya kamata a yi ta.to zai iya yiwu wa ta fuskacin shari'a sallar da muka yi dai-daice, amma ALLAH bai karba ba, ALLAH bai karba ba ne sabo da sallar da ALLAH yake karba ita ce sallar da take tsarkake zuciyar dan Adam. yayin da dan Adam zai iya finkarfin zuciyar sa,yayin da yake salla, to sakamakon samun wannan nasara ne a cikin salla zai tai maka masa ya iya fin karfin jin sa da ganin sa a yayin da ba ya salla ko a wajan salla, hakika salla wata abu ce da take a matsayin saduwa tsakanin masoyi da masoyin sa a wata babar fada. ita salla wani lokaci ne na ganawa tsakanin masoyi da masoyi, ko wata gaiyata ta abin bauta guda daya. masallaci ko mai yin salla da zaran ya yi kabbarar harama zai fara farin ciki na saduwa da ubangijin sa, idan ya yi sallama zai fara farin ciki na saduwa ta gaba, idan mai salla bai san ALLAH ba ba ya shauki na ya sadu da ALLAH, yana karkatar da zuciyar sa zuwa ga wanin ALLAH yana gafala ko yana manta ALLAH, to yaushe zai san girman salla da mihimmancin ta?
Ya zo a wani yanki na waken da faiyad Al-kashani ya rera a yayin da yake ganawa da ubangijin shi da yaran farisanci ga ma'nar abin da yake cewa;
Ya wanda yake shi ne tamkar lokacin kaka ga zuciya, kamar wanda shi ne ainihin kaka.
Ka raya rayukammu da gajimaran rahamar ka.
Ya ALLAH ka da ka kwacce taimako da datarwar da ka yi mana.
ALLAH ka da ka janye taimakon ka da karfafawar da kake yi mana.
Ya ALLAH ka da ka jarrabce ni da wahala ta yin kaura.
ALLAH ka yi abiun da kake so da ni.
Ya wanda shi ne yake habbaka ko raya lambun masoya.
Inuwar ka ba za ta gushe daga gare mu ba.[1]
Ya Allah wane ne ya dandana dadin sonka da bautar ka sannann ya shagaltu da waninka?
Wane mutum ne ALLAH ya yanke masa talauci da mabubbugar nan ta baiwarka mara haddi har ya tsarkakakkiya, amma kuma ya butilce maka bai koma zuwa gareka ba? Wana mutum ne wanda ka halicce shi domin ibadar ka, sannan ya dandaina zakin son ka, kuma ba yafatan komawa zuwa gare ka? Ya ALLAH wana mutum ne ya kamu da son ka, ya kuma dandani zakin son ka, sannan ya kuma ga wanika sannan ya yi riko da wanin na ka?[2]
Salla ita ce abin hawa ko buraka domin tafiya zuwa ga fadar ALLAH, ita salla tana zamo wa abin hawa ne ko buraka ga masana ALLAH ko ga wadanda suka tsarkake zuciyar su. sannann salla ita wata abu
ce da take bambace mutane masu so so kuma zuwa ga ALLAH sannan kowa yana da rabon shi kwar-kwadan matsayin shi[3].
A yayin da al-kur'ani mai tsarki yake magana a kan salla zamo ga yana cewa اقم الصلاة
“Ku tsai da salla domin tinawa da ni”.[4] idan ALLAH ya baiyana ga mai salla zai sami nutsuwa da kwanciyar hakkali kamar yadda ALLAH mai girma yake cewa a cikin littafin sa mai tsarki “ku sani da ambaton ALLAH ne zuciyoyi suke samin nitsuwa”,[5] to ita zuciya ta mai salla za ta zama rayayyiya ce da kuma kunciyar hankali, sannan zai zamo ba ya tsoran kowa sai ALLAH. ko wana makiyi ne shin makiyi ne na cikin gida ko na waje, ba zai taba tsorata shi ba, domin mutane masu tsai da salla mutane ne da suka shagalta da ambatan ALLAH shi ambaton ALLAH sanadi ne na samun kwanciyar hakkali ALLAH mai girma a cikin suratul mu'iraj yana cewa “hakika din Adam abu ne mai kwadayi da kuma tsoro idan sharri ya same shi sai ya zama mai tsoro, idan kuma alheri ya same shi sai ya zama marowaci sai masu tsiyda salla su ne kawai ba su da wadannan munanan halaye su ne wadanda suka dauwama a tsiyda salla.[6]
Hakika mai salla yana finkarfin zuciyar shis sannann kuma yana raya tunanin shi, hakika raya tunani daya ne daga cikin abubuwa da suka kemanta da salla, hakika mutuman da yake tsai da salla shi ne wanda yake raya tunanin shi da fidirar da ALLAH ya halicce shi a kanta, hakika mai tsai da salla yana samin kwanciyar hankali da nutsuwa sakamakon sallar da ya ke yi sannann zai sami juriya a rayuwar shi ta yau da kullin yayin da ya sami kan shi a cikin wahala. shi mutum mai tsai da salla zaka same shi mai matsanancin hakuri yayin da ya shiga wahala, zaka same shi ba yajin tsoro yayin da ya fuskanci wahala, sannan yayin da alheri ya same shi za ka same shi mai taimakawa mutane ba ya hana mutane daga alherin da ya same shi[7]. Arrawaito daga imamu Bakir ALLAH ya kara yarda a gare shi, shi imam ya rawaito daga annabi Muhammad tsira da amincin Allah ua kara tabbata a gare shi ya ce idan bawa na gari ko mumini ya fara salla to ALLAH zai kula da shi[8] kulawa ta musammann har ya gama sallar shi sannan rahamar ALLAH za ta lulube shi ta samar kan shi zowa zuwa sama snna mala'iku za su kewaye shi, kuma ALLAH zai wakilta mala'ika a kan shi ya dinga cemi shi kai mai salla da kasan wanda kake ganawa da shi da ba ka taba tunanin ka rabuda shi ba ko da bakai fatan ka idar da sallar ka ba. [9]
Hakika ALLAH Madaukaki ya ba da labarin wasu mata da 'yam-mata wadanda suka yakke hannuwa su[10] yayin da sukaga kyau na annabi Yusif ALLAH ya kara yarda a gare shi, shi kyau na annabai Yusif kyau ne mai iyaka. to yaya kagani idan aka ce kyau ne na ALLAH wanda ba shi da iyaka da haddi. Wanda duk wani kyau daga shi ya samu asali? Musammann wannan kyau ya kasance a cikin zuciyar masana ALLAH da ma'abuta bauta da ibada.[11]
Sabo da mihimancin salla mugani a tarihi lokacin sallar la'asar a ranar tara ga watam muharram shekarar hijira ta sittin da da ya yayin da imamu husaini ALLAH ya kara yarda a gare shi ya cewa dan uwan shi Abbas ALLAH ya kara yarda a gare shi “ka koma zuwa ga mutananna “wato rindinar yazidu ALLAH ya nesantar da su daga rahamar shi amin” idan zaka'iya ka jinkirtadda su ko ka sa su suma kara zuwa dare ko lokacin sallar dare domin mu yi salla ga ALLAH cikin dare, mu kuma yi addu'a mu roke shi gafara domin ALLAH ya sani cewa hakika imam husaini amuncin ALLAH ya tabbata a gare shi yana son salla ga ubangijin shi da kuma karatun kur'ani da yawan addu'a da neman gafara.[12]
Sai dai a kwai bambanci da wanda zai ce ni ina salla da maganar imamu husaini amuncin ALLAH ya tabbata a gare shi yayin da yake cewa hakika mu roke shi gafara domin ALLAH ya san cewa hakika ni ina son salla.'ya'yan imamu sajjad da 'ya'yan imamu Bakir da wasu daga cikin daggin su sun kasance suna amfani da damar shagalta da wasa yayin da baban su ya fara salla, domin ba ya jin hayaniyar yara da kuma karan da suke yi yayin da yafara salla.[13]
Hakika akwai misalai da dama irin wadan nan na nutsaiwa ko narkewa a cikin salla daga jagororin mu amunci ALLAH ya tabbata a gare su wadanda su ka zo a cikin litatafai na tarihi da wadanda a ka rawaito a cikin littatafan hadisi marubucin littafinna na AL-BIHAR ALLAH ya rahamshe shi ya rawaito cewa a wata rana a gidan imamu SAJJAD amincin ALLAH ya tabbata a gare shi ya kasanci yana salla yayin da ya yi sujjada sai gobara ta kama sai mutanan gidan suka yi ta cewa ya kai dan gidan manzon ALLAH wuta wuta! Bai dago kan shi daga sujjadar ba har sai da wutar ta mutu bayan ya zauna sai a ka cemi shi ya dan gidan manzan ALLAH mene ne ya mantar da kai wannan gobarar? Sai ya ce wuta ta lahira ita ce ta mantar da ni wutar duniya.[14]
Sai dai abin da ake nufi da salla shi ne samin nutsuwa da duk fana'I ga mai salla dan gane da abin bautar shi da kuma rabauta na ganin abin bautar shi gani irin na zuciya. Sai dai mutuman da ya fara salla kafin ya kai ga irin sallar da ake bukata tana da wahala a gare shi yana bukatar hakuri da kokari domin tsallake matakai daban-daban da kokari mai yawa domin isa zuwa ga mukami na narkewa da nutsaiwa a cikin ALLAH yayin da yake salla, idan ba mu amfana da zuciyar mu ba wajan bautar ubangijin mu mahalicci na wani lokaci mai yawa ba zai ta ba yiwuwa ba mu san sirrika na salla ba, sai dai a nan zaiyiyu a yi nuni a duggule zuwa ga a bin da malamai suka ambata wanda suka iyakance sirrika na salla a cikin matakai guda shida su ne kamar haka;
- samun nu tsuwa ko kwanciyar hakkali yayin salla, abin nufi ka da zuciyar mai salla ka da ta ta'allaKa da komai yayin salla sai ALLAH mai girma.
- Fahimtar ma'anar a bin da yake karantawa daga al-kur'ani mai tsarki da zikiri na salla ta yadda zai zamo a kwai da cewa tsakanin abin da yake fada da fahimtar shi a cikin zuciyar shi.
- Girmamawa, abin nufi girmama abin bauta da abin da mai salla yake ganawa da shi yayin salla.
- Kwarjini, abin nufi jin girma da jin tsoro na ALLAH a zuciyar mai salla domin ka da wani nukusani ya shiga cikin sallar shi.
- Fata, abin nufu shi ne mai salla ya ji matsayi da girma da karamci da kyauta na ALLAH da jin cewa shi ne mafi karamci da ya kuma sani cewa ALLAH mai girma ba ya hana mu rahamar shi wacce take mai yalwa wacce tamamaye ko'ina a duniya sannan ya ji cewa da sannu ALLAH zai gafartamana laifukammu.
- Kunya abin nufi da ita mai salla ya kaskantar da kan shi ya kuma ji cewa sallar shi ba ta dace da girma ko matsayi na Allah ba duk yayin da ya tashi yin salla ya kasance mai kaskantar da kai da kuma tsoran ALLAH [15].
Dan uwa, ka sani wannan ita ce kololowar hanya ta zuwa garshi ga duk wani mutum ba tare da shamaki ba domin ganawa ko magana da ALLAH Madaukaki musamman ta hanyar maimaita jumlar “iyyak” wato “ kai kadai muke bautamawa sannann gare ka kadai muke neman taimako.” ALLAH siffantaka ba zai taba kaiwa kololowar matsayin ka ba. Sannann hankali ba zai taba isa kololowar kyan ka ba, ALLAH ! Ta yaya ganawar mu tauya yi ya za ta isa zuwa ga saninka mai fadi, sannann ta yaya hankalin mu zai iya daukan guziri na tafiya zuwa ga kololowar matsayinka?
ALLAH ! kasan yamu daga cikin wadanda kake tabbatar da sonka da shaukinka a cikin zuciyar su, da kuma cikin wadanda kake habbaka son ka da shauknka a cikin zuciyar su, ka kuma samu daga cikin wadanda suke tunani a cikin girmanka ka kuma san yamu daga cikin masu neman kusancin ka, ka kuma san yamu da cikin wadanda suke sha daga kogin sonka dan rahamarka da kaunarka da bayinka wadanda suka zabi mazauni kusa da kai sannann suka sha ruwa na kunya daga ruwa na rahamar ka, sannann suka sa kaya na rahamarka.[16]
Imamu SAJJAD amuncin ALLAH ya tabbata a gare shi yana cewa a cikin wani yanki na addu'ar sa[17] ALLAH Ka dandana mini dadin ambatan ka sabo damu bamu daandana dadin ambatanka ba ko zikirin ka sakamakon haka salla a gurin mu kamar wani abu ne da ya zame mana al’ada. domin sallar da muke yi wadda ba ma jin tasirinta sabo da muna yin ta ne ba tare da sanin ladibban ta ba ba tare da sanin sirrikan ta ba[18] arrawaito daga Ali shugaban muminai amincin ALLAH ya tabbata a gare shi lokacin da yake magana a kan salla ya ce annabi tsira da amincin Allah ua kara tabbata a gare shi ya kamanta salla[19] da kamar wata rijiyace a kofar gidan mutum kullin idan zai fita daga gidan shi yanayin wanka da rowan ta sau biyar, amma abin da yayina sabo zai saura a jikin shi kamar tsatsa.[20]
Salla ita ce koge wanda yake tsarkake mutum, ba shakka idai ba muji tasirin salla a jikin mu ba to ba makawa mu sami tabbacin cewa ba mu yi sallar muba yadda ya kamata mu yi, sannann ba mamaki mun yita dai-dai a shari'an ce, amma ALLAH bai karbaba domin sallar da ALLAH yake karba ita ce wacce take tsarkake zuciya da mutum. Domin mutum yana finkarfin zuciyar shi ne da kuma hurar da ita a yayin da yake salla, idan ya zamo yafi karfinta yayinasara akanta a wajan salla, abin nufi a halin da ba ya salla.[21]
Dan uwa! Kabi duniya da gagan jikin kakuma bi ALLAH da zuciyar ka domin ya zamo abokin hirarka da mai dauke maka kewa sannan zai samaka nutsuwa a cikin zuciyar ka, domin da cewa tsakanin zuciyar masoya tana nufin rashin shamaki tsakanin masoyi da masoyin shi, dan uwa ka yi kokari ko da yaushi zuciyar ka ta zamo tare da ALLAH, ba wai ta zamo tana wani waje dabam ba, musammanma yayin da kake salla ya yin ganawa da ubangijin ka[22].
Salla ganawa ce tsakanin masoyi da masoyin sa sannan ita ce a matsayin kebewa da masoyi, sannan ita ce karshin gurin da mutum yake kaura zuwa ga reshi kuma ita ce fadar sarki mai cikaken iko wanda wani lokacin kake buda baki da yaban shi ko godiya gare shi, kai wani lokacim ma ka kankasa yaban shi ko godiya a gare shi, wani lokacin kuma kana samin dacewa ka halarci fadar shi sannan ka bai yana bukatun ka a gare shi kana ganin girman shi, kana gudwa daga gurin kuntatacce zuwa fadar shi mai yalwa kana amfani da damar ka wajan ambatan shi da ganin girman shi domin ba ka ji fadar shi ba sai da kasami izini sannan ka kiyaye ladubban samin halarta zuwa fadar shi, ka kusance shi mafi kusanci, kuma ka gana da shi ganawa irin ta masoyi da masoyin shi irin ta bayi na gari ka ta'allaka kan ka da ambatan shi, irin na bawa na gari amincin ALLAH ya tabbata a gare shi sannan kana bakin ciki na karewar saduwar ka da shi. sannan kana shauki na saduwa ta gaba zaka yimi shi sallama ta rabuwa kana mai farin ciki mai-maita ambatan shi, rayuwar ka za ta dauwama a cikin ambatan shi. dan uwa! kasani duk wanda ba yada masoyi bai kuma san siffufi na masoyi ba, ba zai taba karkata zuwa ga gareshi ba, ba zai taba kokarin saduwa da shi ba, ba kuma zaiji kiran masoyi ba. Kai koda ya karkata zuwa ga masoyin shi mutikar bai sanshi yada ya kamata ya san shi ba to ganda da bacci da cushewar ciki da ayyuka na yau da kullin ba zasubar shi ya gana da masoyin shi ba, to ta yaya zai gokarin ganawa da shi. sannan ta yaya zai canza da kuma ya sami hankoro da shauki na saduwa da ganawa zuwa gare shi da tsoran shi? irin wannan mutum ta yaya zai sami da cewa ta ganawa da masoyin shi al-halin shi ya shagalta da kan shi, bai kuma yi wani yunkuri ba ko da taku da ya domin fita daga halin da yake ciki.
[1] Faidhul kashani , allama muhsin , diwanin (kundin) wakokia.
[2] Shaja ‘I sayyid ,ahdi dasti du’a cashme umid , munajati ta 15 da muana jati ta tara shafi na 81.
[3]Imam khamaini assalat shafi na 5.
[4] Sararu daha.
[5] Surar ra’ad aya ta 28.
[6] Surar ma’ariji aya ta 19, 23.
[7] Jawadi a muli littafi hikamar ibada shafi 95.
[8] Ko kuma ya ce: (kabbalalla lahu ta’ala).
[9] Man la yahdhuruhul fakih juzu’I na.
[10] Surar yusif. Aya ta 39.
[11] A- sibzaawari, almulla hadi, littafin asrarul hakim.sha fin a 528.
[12] Maktalul Husain na mukarram sha fi na 232.
[13]Al anwarul bahiyya shafi na 49.
[14] Biharul anwar shafi na 47 / 78.
[15] Littafin mikdadi isfahani juzu’I n a 1 shafi na 325.
[16] Shaja’ati dasti du’a’a cashmi umid munajati ta 12
[17] Mafatihul jinana munajati ta 15.
[18] Hukimar ibada na jawadi a muli shafi na 105.
[19] Dun wata idaniya da ruwa yake kwarara daga gar eta.
[20] Nahjul balagam, huduba ta 199.
[21] Hukimar ibada na jawadi a muli shafi na 115-116.
[22] Tazrhaye suluk na hasan zadhe a muli shafi na 12.