advanced Search
Dubawa
52368
Ranar Isar da Sako: 2012/05/05
Takaitacciyar Tambaya
shin labarin da ake cewa annabi ba ya barci har sai ya dora kansa a kan kirjin fatima ya inganta?
SWALI
Shin ya inganta labarin da ake cewa daga Imam Sadik (as) ne cewa ya ce: Manzon ALLAH (s.a.w) ba ya yin barci har sai ya dora fuskar sa mai daraja a kan kirjin Fatima (as)?
Amsa a Dunkule

kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina da su ko a dogara da su ba.

 Sannan kuma ruwayoyin da suka yi nuni ga soyayyar Annabi mafi girma (s.a.w) ga yarsa Zahara (as) suna da yawan gaske, kuma irin wadannnan ruwayoyin sun zo a cikin littattafan mazhabobin nan biyu, sai dai wannan ba yana nufin gaskata kowace ruwaya da take bayyana irin hanyar da Annabi (s.a.w) yake bayyana irin wannan soyayyar ba ne, zai yiwu ruwayar tana da rauni a isnadin ta, ko kuma a ma’anar da ta kunsa, ta yanda taci karo da irin kyawawan halaye na Annabi (s.a.w).

Idan muka koma ga ruwayar da aka ambata a cikin wannan tambayar, zamu ga tana da bukatar a yi bincike na isnadi da na ma’anar da ta kunsa.

 A bangaren binciken isnadi zamu ga ita wannan ruwayar, mai littafin al-bihar ne ya ruwaito ta daga littafin al manakib na ibn shahar ashuub, sai dai bai ambaci isnadin ruwayar ba, saboda haka ke nan ruwayar mursala ce, wannan ya nuna ba ta cika sharudda ba.

 A bangaren binciken abin da take koyarwa kuma, za a iya yin bincike a karkashin wadannan al’amura;-

 1- Abu ne da ya dace sosai a dora ita wannan ruwayar akan faifan tarihi, don mu ga irin dacewar ta da yanayi na tarihi.

 Idan muka dubi tarihin Manzo (s.a.w) zamu ga ya kai shekaru arba’in da biyar alokacin da aka haifi Zahara (as) wannan lissafin idan an dauka cewa an haifi Zahara (as) kafin aiko Annabi da Annabci da shekara biyar ne, abin tambaya shine a yaya yake barci a wancan lokacin? kari a kan haka kuma Manzo (s.a.w) yana da aure, yana da matar aure wadda wajibi ne ya kula da hakkokinta, da irin abubuwan da take ji a cikin ranta, itace sayyida Khadija (as) wadda yana tsananin girmamata da sonta.

A bayan rasuwar Khadijah (r. a) Annabi ba ya zauna ne ba tare da aure ba, a cikin kankanin lokaci yayi aure da saudah yar zam’ah, sannan ya auri wasu matan, a lokacin wafatinsa ya bar matan aure guda tara, to, ta yaya zai bar matan sa ya tafi yayi barci a dakin Zahara (as) ? ko ya kira Zahara (as) ta yi barci a wurin sa? .

 Kari a kan haka kuma, zamu ga ita Zahara (as) ta yi aure da wuri, a bayan hijira, a shekara ta farko ko a shekara ta biyu, ta tafi gidan mijinta Amirul muminina (as).

Abu ne sananne cewa al-amarin da aka kawo acikin wannan tambayar da ace ya inganta da ya jawo kishi daga su matansa, da kuma hadisai sun yawaita a kai, da cece kuce sun yi yawa a kai, don ba abu ne da ya dace da hankali ba Annabi yayi hakan, a ce a ko wani dare zai zo dakin Zahara (as) don yayi barci a wurinta ko ya sumbance ta a kirjinta, a mafi karancin kaddarawa da za a iya yi, sannan ya tafi gidan sa, da wannan ya jawo shishigi na mutane, za a yawaita yin magana a kai, da kuma an ruwaito shi kamar yanda tarihi ya ruwaito mana yanda yake tsayawa har tsawon watanni bakwai ko takwas ko tara, ajikin dakinta (as) a bayan da ALLAH ya saukar da Ayar tsarkakewa, yakan tsaya ya karan ta wannan Ayar tsarkakewa din.

 Tabari ya ruwaito a cikin tafsirinsa da isnadi zuwa ga Abul hamra’a, ya ce na yi Ribadi a garin Madina tsawon watanni bakwai a zamanin manzon ALLAH (s.a.w) ya ce: ina ganin Annabi idan Alfijir ya hudo yakan zo dakin Ali da Fatima (as) sai ya ce: Lokacin Sallah!iyaka kawai Allah yana nufin ne ya Tafiyar da Kazanta ga barinku Ahlul Baiti ya kuma Tsarkake ku iyakacin Tsarkakewa”

Daganan zamu san cewa, tarihi ya na kore waccar ruwayar, sannan kuma ga raunin isnadin sa.

2- Abu na biyu hakika wannan hadisin bai dace da gidan da ALLAH ya nufe shi da tsarkaka da kamewa ba, hakika Manzon ALLAH mafi girma shine abin koyi ga muminai, ba zai yiwu, su nuna, a game da soyayyarsu, abubuwan da zasu jawo wani kwarzane komin kankantar sa ba, ko kuma wani bakin fenti na nakasa, alhali sun san cewa abokan gaban su sun sa musu ido, suna Jiran Dan Kadan ne, don su kirkiro tuhumomi da rikitarwa don munana su.

 Hakika yazo a cikin hadisi, game da suffanta bayin Allah Salihai da cewa suna taka tsan tsan da wuraren da ke haifar da tuhuma.

3 - Hanyar nuna soyayya da tausasawa ga ‘ya’ya al’amari ne wanda gamayyar dabi’ar dan’adam ta ginu a kai, haka ma dukkan Annabawa, kuma Annabi mafi girma (s.a.w) a kebance bai fita daga ka’idar ba. saboda haka yana kan mafi kololuwar rahama da kyawawan halaye, da tausayawa dukkan mutane har ma yakan zamo kamar zai halakar da kansa, saboda tausayin halin da kafurai za su iya shiga, to ta yaya ba zai zamo mai tausayawa ga yarsa ba? wadda ita tsoka ce daga jikin sa? saboda haka zai yiwu Annabi (s.a.w), idan yarsa Zahara (as) ta kawo masa ziyara, zai mike mata ya sumbance ta, misali a jikin wuyanta, to amma masu ruwaya sai suka yi karin gishiri a cikin ruwayar, suka kuma canza ta zuwa irin yanda aka ambata.

Amsa Dalla-dalla

Hakika ruwayoyi gaba dayan su, za a iya kasa su, kaso biyu muhimmai,

  1. Ka so na farko dai, shi ne ruwayoyin da ake lura da su, wadanda ake ce musu ingantattu ko masu karfi da sauransu.
  2. Akwai kuma wasu ruwayoyi a wani kason, wadanda ake ce musu raunana, ko wadanda ba’a’sansu ba, wadanda irinsu ba’a jingina a kansu ko a dogara da su.

 A saboda haka ne zamu ga malamai da masu bincike kwararru sun gindaya sharudda game da yin aiki da ruwaya.

Akwai sharudda, wanda mafi muhimmancin su, shine binciken ruwaya a bangaren isnadin sa, wato a dubi isnadin ita ruwayar domin a samu nitsuwa akan lafiyar hanyar da ruwayar ta biyo ta ciki, idan isnadi ya tabbata, sai kuma a yi bincike akan abin da hadisin ya kunsa ta kowani bangare, don a samu nitsuwa cewa hadisin bai kunshi wani abun da ya kore akidu da kuma halaye na musulunci tabbatattu ba, saboda haka ke nan dole ne a shigar da wannan ruwayar da aka ambata cikin wannan tambaya a cikin bincike na isnadi da binciken abin da yake nunarwa, a saboda haka zamu iya cewa: Ita wannan ruwayar mai littafin al-bihar shine ya ruwaito ta daga Imamai biyu As-sadik da al-Bakir (as) cewa sunce : Annabi (s.a.w) baya yin barci har sai ya sumbanci fuskar Fatima (as), ya dora fuskarsa tsakanin nonunanta ya yi mata Addu’a, a wata Ruwaya kuma, har sai ya sumbanci Fuskar Fatima (as), ko kuma tsakanin Nonunanta[1] Abu ne a Fili cewa mai Littafin Al-Bihar ya ciro wannan Ruwayar ce daga Littafin Al-Manakib na Ibnu Shahar Ashuub, wanda ya rasu a shekara ta 588 bayan hijira, kuma bai Ambaci wani Isnadi ba, sai dai ya Ruwaito ta ne kawai a Matsayin mursala, sabanin mafi yawan Ruwayoyin wannan Littafin da yake Ambaton Isnadin (kowace ruwaya) ko da kuwa wanda ya Ruwaito daga Wurinsa Sunni ne ko Shi’a, saboda haka idan Ruwaya ta Kasance Mursala ce ke nan ta Riga ta Fadi da cikin Wadanda suka cika Sharudda, da za a iya dogara da ita.

 A ta Bangaren Abin da ta Kunsa kuma (Dilala) yana da kyau mu yi darasin al’amarin a karkashin wadannan gungun bincike masu zuwa:

1- Yana da Muhimmanci sosai a Dora wannan Ruwaya din akan Tarihi domin muga irin Dacewarta da Tarihi. Idan muka duba Tarihin Manzo (s.a.w) zamu ga cewa, sai da ya kai shekaru Arba’in da Biyar, a lokacin da aka haifi Zahara (as), wannan, idan aka hukunta cewa ita Zahara an Haifeta ne bayan aiko manzo da shekaru biyar, to, a yaya Yake barci awancan lokacin? wani kari akan haka kuma Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana da Aure, yana da Matar Auren da ya Wajaba ya kiyaye Hakkokinta, da Abubuwan da take ji a cikin Ranta, itace Sayyida khadija (as), wadda yake tsananin giramamata, da sonta, a bayan rasuwar khadijah (ra) kuma, Manzo (s.a.w), ba wai ya zauna ne ba tare da yin aure ba, a cikin kankanin lokaci ya auri saudat yar zama [2] sannan kuma ya auri wasu Adadi na Mata, har ma alokacin barinsa Duniya ya bar Matan Aure Guda Tara, to, shin ta yaya zai bar matansa na aure ya tafi yayi barci adakin zahara (as) ko ya kira zahara ta yi barci a wurinsa? .

 Kuma kari akan haka, zamu ga ita zahara (as) tayi aure ne a bayan hijira, ba da tsawon lokaci ba ko dai bayan hijira da shekara daya ko da shekara biyu, tayi aure ta tare a gidan mijinta, Amirul muminina (as). [3]

 kuma sanannen abu ne cewa abin da aka Ambata din acikin wannan Tambayar da ya Inganta, da ya jawo kishi na Wadannan Matan, da kuma an Tattauna yawa akai domin ba abu ne da ya dace da Hankali ba Annabi yayi irin wannan aikin, a ce a ko wani dare ya zo Dakin Zahara (as) don yayi Barci a Wurinta ko ya Sumbance ta a Kirjinta, a mafi Karancin abin da za a iya Kaddarawa, sannan ya koma gidansa, da wannan al’amari ya jawo Shishigi na Mutane, da an Yawaita Maganganu da Cece kuce a kai, da kuma an Ruwaito mana hakan kamar yanda Tarihi ya ruwaito mana Tsayawar da yake yi a Tsawon watanni Shida ko Bakwai ko Takwas, Ajikin Dakin ta (as) bayan ALLAH ya saukar da Ayar Tsarkakewa, yakan Karanta Ayar Tsarkakewa din.

 Tabari ya ruwaito a cikin tafsirinsa da isnadi zuwa ga Abul hamra’a, ya ce na yi Ribadi a garin Madina tsawon watanni bakwai a zamanin manzon ALLAH (s.a.w) ya ce: ina ganin Annabi idan Alfijir ya hudo yakan zo dakin Ali da Fatima (as) sai ya ce: Lokacin Sallah!iyaka kawai Allah yana nufin ne ya Tafiyar da Kazanta ga barinku Ahlul Baiti ya kuma Tsarkake ku iyakacin Tsarkakewa”) [4] kuma daga cikin abin da ke dada karfafa a binda muka fada akwai ruwayar da shi ibnu shahar ashuub da kansa ya ruwaito daga abu ubaidatul hazza’u da ma waninsa daga Imam sadik (as) cewa: manzon ALLAH (s.a.w) ya kasance yana yawan sumbantar Fatima (as) sai wasu daga cikin matansa suka yi masa mita, sai manzon ALLAH (s.a.w) ya ce: A lokacin da ALLAH yayi mi’iraji da ni zuwa sama Mala’ika Jibrilu (as) ya rike hanuna ya shigar da ni cikin Aljanna ya bani yayan itatuwanta naci, Acikin wata ruwayar kuma: ya bani Tufah na Aljannah naci, sai wannan Tufah din ta canza ta zamo Ruwan Maniyyi a cikintsatsona (kirjina) da na sauko duniya sai na sadu da khadija, sai ta dauki ciki da Fatima, saboda haka Fatima macen aljanna ce acikin mutane, a duk lokacin da na yi shaukin Aljanna sai in shaki Kanshin yata. [5]

 A ta haka ne zamu san cewa tarihi na hakika yana karyata waccan ruwayar, sannan ma dadin dadawa ga raunin isnadin ruwayar (ko ma rashin isnadin dunguru gum).

  1. Wannan ruwayar bata dace ba sam, da Gidan da ALLAH ya nufe shi da tsarki (Iyaka kawai Allah yana nufin ne ya Tafiyar da Kazanta ga barinku Ahlul Baiti ya kuma Tsarkake ku iyakacin Tsarkakewa””[6] kuma ya nufe shi da (iffah) wato cikakkiyar kamewa. hakika manzon ALLAH (s.a.w) shine babban abin koyin muminai, saboda haka ba zai taba yiwuwa, mutane, da irin wannan gidan, su nuna soyayyarsu a ta Hanyar da akwai Kazanta (gyambo) ko kuma duhu-duhun nakasa ba, Alhali sun san cewa Abokan gaba sunsa musu Ido suna jiran dan kadan ne kawai, don Watso Tuhumce Tuhumce da Shubuhohi masu Yawa don Muzanta su. Alhali yazo a cikin Hadisi game da Suffanta Bayin Allah Salihai da cewa suna : taka tsantsan da wajajen da suke Haifar da mummunar Tuhuma”[7] kuma Hakika yazo a cikin Ziyaratul Jami’a a wajen Suffanta Ahlul Baiti (as) da yabonsu cewa: Allah ya kiyaye ku daga Tuntube, kuma ya Tserar da ku da ga Fitinu kuma ya Tsarkake ku daga Dauda sannan ya tafiyar da Kazanta ga barinku, ya Tsarkake ku iya kacin Tsarkakewa. ”[8]
  2.  Da gaske ne Alakar Annabi da Zahara (as) Alaka ce mai zurfi sosai wanda ta Kunshi Dukkan Ma’anoni na Daukaka da Dacewa irin na Ruhi da ta Ma’ana, har ma da Al’amura na Duniyar Gaibu a ciki, kamar dai bisa dacewa da Ruwayar nan da Ibnu Shahar Ashuub ya Ruwaito kamar yanda ya gabata.
  3.  A hakika nuna Soyayya da Tausasawa ‘ya’ya Al’akmari ne da Dabi’ar Dan Adam Gaba Daya da Annabawa Gaba Daya ta ginu akai, kuma Annabi (s.a.w) a kebe bai fita daga wannan ka’idar ba, don yana a kan kolin kololuwar rahama da kyawawan halaye, da tausayawa dukkan mutane, kai har ma yakan zamo yana dab da zai cutar da kansa don tausayawa ga kafirai na halakar da zasu fada a ciki, to ta yaya ba zai zamo mai tausayawa ga yarsa ba wadda ita tsoka ce daga jikinsa? saboda zai yiyu yanda al’amarin yake shine shi Annabi (s.a.w) ya kasance idan ‘yarsa zahara (as) ta kawo masa ziyara yakan mike mata ya sumbance ta a wuyanta a bisa misali, to amma su masu ruwaya sai suka yi karin gishiri a kanj ruwayar suka canzata ta zo kamar yanda aka ambata din nan
  4. Littattafan Tarihi da na Hadisi sun kawo Ruwayoyi masu yawa da suke Bayyana Alakar annabi da yarsa zahara (as) bata tsaya akan zamowarta yarsa ce kawai ba. A’a sai dai a dalilin irin sonsa da tausasawansa ga zahara yana nufin bayyana wa al’ummar musulmi irin madaukakiyar daraja da take dashi, ta yanda ita daya ce daga cikin hujjojin Allah a kan bayinsa.

kuma akwai wannan hadisi, da mazhabobin nan duka biyu suka ruwaito, ya wadatar wajen nuna irin wannan darajar: Fatima tsoka ce daga jikina abin da duk ya bata mata rai to ya bata mini rai”[9] An ruwaito daga Ali (as) ya ce: Manzon Allah ya rike hannayen hasan da Husain, sai ya ce duk wanda yaso wadannan biyun da babansu da mahaifiyarsu to, yana a tare dani a cikin mukamin daraja ta a ranar tashin alkiyama”[10]

 


[1] Al manakib juzu’I na 3 shafi na 336da Bihaharul anwar juzu’I na 63 shafi na 62

[2] As siyratun nabawiyya na ibnu kathir juzu I na 2 shafi na 142

[3] A’ayanush shi’a juzu I na farko tarihin sayyida zahara (as)

[4] Tafsirut tabari juzu”I na12 shafi na 6 bugun beirut

[5] Al manakib juzu’I na 3 shafi na 335

[6] Suratul ahzab

[7] Bihaharul anwar juzu’I na 66 shafi na 313

[8] Mafatihil jinan 903

[9] Bihaharul anwar juzu’I na 31 shafi na 271

[10] Bihaharul anwar juzu’I na 37 shafi na 37

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa