Please Wait
15766
Tabbas Allah mai tsarki da daukaka mai hikima ne ta kowace fuska, sannan dukkanin ayyukansa ya yi su ne bisa asasi na hikima ta karshe, to doron wannan asasi dukkanin samammu Allah ya halicce su ne a bisa doron hikima ta karshe, kamar yadda ya suranta su a mafi kyan halin da ya dace da ita.[1]
Halittar Shaidan daga wuta ita ma ta dace da hikimar Allah ne, shi shaidan wani nau’i ne daga aljanu kuma an halicce shi ne daga wuta, sannan yana da jiki mai taushi ne. hakika an karkasa jikkuna da wani nau’i na kashe-kashe ya zuwa gida biyu:
- Jiki mai kaushi, kamar jikin dabbobi da jikin mutum, wanda aka halicce su da yimbu.
- Sai kashi na biyu jiki mai kaushi, kamar jikin aljanu wanda aka halicce su da wuta.
Wadannan nau’o’i guda biyu na jiki suna da girma da gwargwado, sai dai sun saba sabawa ta hakika a tsakaninsu, daga cikin jumlar sabawar tasu ita ce: Shi Shaidan ba zai yiwu mutum ya gan shi ba saboda shi yana iya shiga mabambantan yanayi, kuma zai iya shiga kowane irin wuri saboda taushinsa da kayensa, amma kuwa shi mutum shi shaidan zai iya ganinsa kamar yadda mutum bai da ikon canza wurinsa cikin gaugawa mai sauri da gaugawa irin wadda shaidan yake da ita, shi motsin mutum a hankali a hankali ne. zai yiwu mu narkar da hikimar da ta sa aka halicci shaidan da wuta ta hanyar abubuwan nan masu zuwa:
- An yi wa shaidan din jarrabawa da gwada shi, yayin da aka halicci shaidan din da wuta, shi kuma mutum aka halicce shi da yinbu, sai shaidan ya yi zaton cewa wuta ta fi kasa matsayi, sai ya kudurci cewa ya fifici mutum, saboda haka ne ya sa ya ki aiwatar da umarnin da Allah mai tsarki ya hore shi lokacin da aka umarce shi ya yi sujjada ga Adam amincin Allah su kara tabbata a gare shi. Idan haka ne babbar hikimar da ta sa aka halicci shidan da wuta ta boyu ne cikin yi masa jarrabawa da gwada shi, shin zai rudu ne da zahirinsa na cewa an halicce shi da wuta ne ko kuwa zai saura yana mai sauraron aiwatar da umarnin Allah mai tsarki da daukaka?
Tabbas shaidan ya bayyanar da wannan matsala a yayin da ya ki yin sujjada ga Adam amincin Allah su kara tabbata a gare shi, ya yi shisshigi a kan umarce-umarcen Allah mai tsarki. Ya ce: “Ka halicce ni da wuta, shi kuma ka halicce shi da kasa”.[2]
- Gwada mutum da yi masa jarrabawa, shaidan makiyin mutum ne wanda ya rantse cewa sai ya zamar da shi daga kan tafarki madaidaici, tare da kokarin rudar da shi a bangaren akida, zai wurga shi cikin shubuha (rudu) da zace-zace, sannan da sabo a fagen matafiya ta aiki. Shaidan shi ne mabubbugar wasuwasi da makirci da yaudara ya zuwa ga haddin da yake suranta masa barna da ba ta da wata hakika, amma sai ya bayyanar masa ita da kama ta gaskiya. Tsarinas sh ne yin wayo da dabara inda yake zo wa mutum ta boyayyar hanya wadda mutum din bai ganewa sai ya yaudare shi ya batar da shi cikinsa da badinin. Shaidan yana da ikon ya kutsa cikin jikin mutum, hakankuwa na faruwa ne sakamakon cewa ya mallaki tattausan jiki, amma fa kutsawar tasa tana faruwa ne sakamakon mummunan zabi.
Wato mutum shi ne yake ba da hanya ga shaidan ya saukake masa hanyar shiga jikinsa, idan kuwa ba haka ba da a ce mutum zai kafa nufinsa daram to shaidan bai da hanyar kutsawa cikin jikinsa. Duk da cewa mutum ba zai yiwu ya ga shaidan ba saboda yana tsoronsa, sannan kuma ya fita daga tsaikon ya gan shin sai dai duk da hakantilas ne ya kasance mai kula da sa ido domin ya nisanci aukawa cikin tarkon irin makiyi. Allah madaukaki yana cewa:
“Ya ku ‘ya’yan Adamu, ka da shaidan ya fitine ku kamar yadda ya fitar da iyayenku daga aljanna, ya cire musu tufafinsu don ya ga munanansu, shi fad a kabilarsa suna ganinku ta inda ku ba kwa ganinsu, h akika mun sanya shaidanu su zama ga wadanda ba su yi imani ba”.[3]
Wannan wani nau’i na jarrabawa da gwaji ga mutum a lokacin da ya sami kansa a fegen fafatawa da irin wannan makiyi!
[1] Tarea da cewa ba za mu iya fahimtar hikamar yin wanna ba, kum asakamakon karancin iliminda muke da shi ba ma iaya isuwa ga sanin da ya wa daga cikin hikimomin abubuwa da zahirin lamurra.
[2] Suratul a’arafi aya ta 12.
[3] Suratunl a’arafa aya ta 27.