Please Wait
44133
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa.
Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya[1], kuma Allah ya hore masa fassara mafarki[2]. Kamar yadda ya fassara mafarkin abokan zamansa na kurkuku, da mafarkin Sarkin Misra, a wajen kurkuku ke nan dai fassarar mafarki, ko tawilin mafarki[3], a bisa irin kalmomin sunaye na Alkar’ani, shi al’amarine tabbatacce, na hakika, kuma wannan din wani ilimi ne wanda Allah ya sanar da wannan annabin, Annabi Daniyal yana daga cikin wadanda Allah ya ba su ilimin fassara mafarki[4]. Kuma hakika Kur’ani ya ambaci wasu shaidu na wasu Annabawan da Allah ya karfafa da gaskanta ingancin mafarkansu[5].
Game da rarraba ruwayoyi na nau’in mafarki, za mu ga kaso biyu na abubuwa da ake gani a cikin barci.
Wasu abubuwn da ake gani a cikin barci mafarkine na gaskiya, wasunsu kuma na karya ne[6]. ruwayoyi sun ambaci cewa; “Hakika mafarki na gaskiya wani yanki ne daga cikin yankin Saba’in na Annabaci”[7] shi irin wannan ilimin ba ana samunsa ne ta hanyar koyarwa da koyo ba, sai dai yana bukatar tazkiya da tsarkake rai, a saboda haka ne babu masu samun irin wannan baiwar sai yan mutane kadan kawai.
A cikin wasu littattafai na fassarara mafarki an ambaci wasu asasi da ka’idoji, sai dai ya wajaba mu lura da cewa wadannan asasin da ka’idojin, ba su ne komi da komi ba, kuma ba na gama gari ba ne, domin suna canzawa, a saboda bambaci su masu yin mafarkin, da wasu sharudda na daban. A saboda haka ba zai yiwu mu isa ga tabbatacciyar natija ba daga abubuwan da suka zo a cikin wadannan littattafaiba.
[1] Suratu yusuf, aya ta 4
[2] Suratu yusuf, aya ta 101
[3] Suratu yusuf, aya ta 101
[4] Littafin biharul anwar, wallafar allama majlisiy, juzu’I na 16, shafi na 371
[5] Suratus saffat, aya ta 105, da suratul fathi, aya ta 27.
[6] Littafin alkafiy, na kulayniy, juzu’I na 8, shafi na 91. bugun kamfanin, darul kutub al islamiyya.
[7] Littafin man la yahdhuruhul fakih, juzu’I na 2, shafi na 586