Please Wait
15735
Zai yiwu mu fara bayani a kan al’amarin 'yanci ta hanyar bincike da karatu dangane da ra'ayin addini ta fage biyu: 'yanci na ma'ana da 'yanci na zamantakewa da siyasa. Hakikanin mutum idan mun danganta shi ga ma'ana mai nisa (mai zurfi) ita ce nafsin ko ruhin sa (samuwarsa) wace take mujarrada (wace ta kubuta a zatinta daga wani abu da jiki har ma da siffofinsa, domin ita daga wajen Allah take wato wajen mulkinsa).
Amma ta fuskar kasancewa nafsa (rai) yana tare da jiki to fa an daure ta da madauri kara na abubuwa domin ta zauna a duniyar mu.
Mutum an dora shi a kan ya gudanar da al'amuransa a duniya don ya sami kamala, saboda haka duniya wajen shuka ne domin a sami amfani ranar lahira, sai dai wasu saboda hange irin na su na zahirin abin duniya sun dauke ta wajen shagala da wasa wanda hakan shi ya jawo suka rasa cigaba da daukaka har ma da rasa daraja wajen Allah, maimakon fuskanto abubuwa masu asali boyayyu na hakika sai ya zaci sashin wasu abubuwa da ake iya gani wai suna da asali tun tuni, wanda wannan ne ya sa shi ya shagala gaba daya ya mance da mulkin Allah da hakikanin abubuwan. Saboda haka ne masu neman duniya suke zaton cewa biyan bukata da cimma buri da kwadayin kayan kyalkyali wai duk wannan shi ne samun 'yanci da fita daga takura. 'Yanci dai shi ne kubuta daga afkawa duniya da kin bin son zuciya, irin wannan 'yancin shi ne wanda addini yake so tare da kwadaitarwa zuwa gare shi.
Sau nawa aka sami sarki wanda ya shifida mulki a masarautarsa mai girma amma a nazarin addini son zuciyar sa yake bi har ma ya zama ribataccen sha'awa, sau da yawa talaka mai fama da talauci amma ya mulki masarautar sa (nafsu) ya ki bin son zuciyar sa da sha'awarsa.
Sakamakon wannan magana shi ne: abin da masu neman duniya suke neman ba 'yanci ba ne 'yancin karya ne suna kawai suke bashi, amam abin da addini ke tabbatarwa shi ne 'yanci na gaskiya. Amma abin da ya shafi nisan zamantakewa dangane da mas'alar 'yanci hakika tunanin addini musamman tunanin Musulunci a fagen zamantakewa da siyasa yana kallon 'yanci ne kallo na hakika, ba zai halatta 'yanci ba har ya zama an shige gona da iri, ba za a takura mutum cewa dole ya karbi duk abin da zai cutar da shi ba kuma ya jurewa jagoranci na zalunci wanda yake cutarda mutuntakar sa tare da kawar na sa da izzarsa. Saboda haka za mu iya cewa: hakika 'yancin mutum daya dana zamantakewar mutane akwai shi a Musulunci amman ya sha ban-ban da yadda turawan yamma ke gani.
Kamar yadda nazarin addini dangane da akida yake nuna mana cewa asalin duk wani aiki fa daga Allah Allah madaukakin sarki yake, saboda haka dole ne ayyukan da mutum yake yi su dace da umarnin Allah da dokokinsa tare da neman yardarsa, kamar haka al'amarin yake ta bangaren aklak da wayewa domin Allah ya kira al'umma cewa, su shimfida adalci da gaskiya a cikin fagen rayuwa baki daya, ya kuma hana ketare iyaka a kan hakkokin mutane, ta wani bangaren Allah ya yiwa mutum wasiyya tare da kwadaitar da shi neman ilmi da gane hanyoyi masu inganci dan ya fa'idanta da wannan ilimi kuma ya yi amfani da shi.
Tun da nafsu da rai suka zama mujarradai to ba makawa su zama abin tsarkakewa ne a zatin su daga jiki da abubuwa, abin nufi nafsu da rai ba jiki bane kuma ba a kage su ba abubuwa sabanin jiki an halicce shi da kashi da nama da jini da sauran su sabanin nafsu, da rai, haka nan ma ba su da siffofin jiki, nafsun mutum ba ta karbar yanayin tsoho, fadi da zurfi da kuma yanayi na zati da sanyi da jihohi (sasanni) kamar sauka da hawa da kafin da bayan kai da baki dayan yanayin jiki.[1] Tunda ita nafsu tana da alaka da al'amari (duniyar umarni) tabbas tana duba tare da fuskantar wajen ta, kamar yada mawaki yake cewa:
Tabbas duk wanda ya nisanci mazaunin sa na asali
To ba makawa wata rana zai koma wajen sa[2]
Duk ababan halitta a cikin duniyar su ko dai su zamanto a cikin jakar duniya ta mulki da jiki da madda (abubuwan da ake halittar abu da shi) ko a same su a a kan na mulki a duniyar mulki da fajarrud da umarni.
A saman duniyar jikkuna wacce ta kunshi tsarin gudana sannu a hankali na wata duniyar da ta kunshi ababan halitta wadanda basu da alaka da zamani shi ne alamul amri (duniyar umarni) hakika ababan halitta na alamul amri sun kewaye ababan halitta na alamul kalki[3] (duniyar halittu) tabbas umarni da halitta na Allah ne kamar yadda Kur'ani ya fada:
((ألا له الخلق والأمر تبارك الله رب العالمين))[4]
FADAKARWA: Halitta ta Allah ce haka ma umarni, Allah ubangijin talikai ya tsarkaka, idan muka dubi nafsu zamu ga tana tare da jiki kamar ta zama a kasa take, an daure ta da turaku na kasa[5] (duniya).
Mutum tare da cewa ya doru a kan wucewa ta hanyar duniya don saduwa da madaukakiyar kamala, ba makawa sai ya koyi karatu a makarantar zamani (lokaci) da bibiyan abubuwan da karba kai har ma da zamani da ketarewa, canjawa, zamanin da kayan aiki domin ya kai ga tabbatattun abubuwa masu ma'ana dangane da abin da yake bayan madda da zamani (duniya wajen neman lahira ce)[6] sai dai fuskanto duniya da gurace - guracen karya idan aka dube ta duba na musamman zai hana mutum shiga hanyar cigaba domin ba zai dar su ba a zuciyar sa y7a matsa gaba a cikin alamul malakut (duniyar mulkin Allah), kuma tana yaudarar sa da kayayyakin ta masu wal-wal wadanda take kawata su gare shi har ya dinga ganin zai dauwama a duniya, kamar yadda Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya ce: "wanda ya kula da ita sai ta kara masa basiyra, wanda ya kalle ta sai ta ma kantar da shi".[7]
RAYUWAR DUNIYA:
Allah Allah madaukakin sarki ya siffanta rayuwar dniya a cikin Kur'ani mai girma yana cewa:
((إنما الحياة الدنيا لعب ولهو...))[8]
"Ita rayuwar duniya wasa ce da shagala".
Wasu shi ne aikin da bashi da wata ma'ana sai gizo da zato shi kuma lahwu shi ne abin da yake sa mutum ya shagala da kansa sai ya manta da wasu ba tare da ya waiwaye su ba, a bisa wannan maganar a cikin wannan ayar akwai nunin cewa nafsu tana tare da jiki, sannan jikin sa ne wasidar (tsarin) samun kamala, ya kuma sanya mutum ya shagala da kansa kuma ya mance ragowar mutanen da ke gefensa, asalin wannan mantuwar rayuwar duniya ce ta yaudari ruhi ta rude shi har ya kai ga zaton cewa ran da jikin duk abu daya ne, bayan wannan zaton mara tushe ne, sai rai wato ruhi ya yanke ya bar duniya da take bayan jiki, sai ya mance duk abin da yake dashi na kyau da girma da haske har da farin ciki a cikin halittar abin da yake kafin madda baya tun martabar kusanci da kuma tuna abin da yake tare da shi na abokai masu tsarki da debe kewa da haso da duk abin da ya bar shi a bayan sa, saboda haka ne sai kaga mutum ya karar da rayuar sa cikin shagala da wasa kuma ya dinga cin buri a rayuwar sa burin karya mara tabbas, da gizo da zaton samu, lokacin da yake kusantar abin da yake buri sai ya ga abin ya ki tabbata.[9]
Allah Ta’ala ya ce:
((والذين كفروا أعمالهم كسراب بقيعة يحسبه الظمآن ماء حتى إذا جاءه لم يجده شيئا ووجد الله عنده فوفاه حسابه والله سريع الحساب))[10]
"Kafira aikin su kamar kawalwalniya ne a fako mai kishirwa sai ya zaci ruwa ne, har sai ya zo wajen kawalwalniyar ba zai sami komar ba, sai ya riski Allah a wajen, Allah kuma ya yi hisabi game da abubuwan da ya aikata, Allah mai saurin yin hisabi ne".
ASALIN ZAHIRI DA BADINI:
Hakika mutumin da yake ma'amala da mutane da mulki a cikin wannan duniyar da abubuwan halitta masu jiki wanda ake ganin su har yake ganin su a matsayin abubuwa ne na asali tabbatattu, to duk himmar sa da shagaltuwarsa za su kasance a kan al'amura ne na kayayyakin duniya wadanda ake gani. Hakan zai sanya shi zama cikin shagaltuwa daga boyayyun al'amura da abubuwan da ke ciki na daga alamomin mulkin Allah, irin wannan mutum bai san ma'anar rayuwa ba ban da ci da sha da barci da jiye-jiyen dadi da wasa har ma da shagala kamar yadda Kur'ani ya fada: "Suna sanin zahirin rayuwar duniya alhalin sun gafala sun bar lahira".[11]
Amma mutumin da yake nazarin mulkin Allah Allah madaukakin sarki wanda sanadiyyar hakan yake fuskanto zahirin ke bada horon badini, zahirin reshen mulkin Allah ne kuma ya dogara a kan badinin saboda haka irin wannan mutumin yana ganin zahiri tamkar bawo ne wanda ke wajen abu, badini kuma shi ne bargon abubuwa da asalin su, idna haka ba zai bada asali ba dan saboda reshe da bawo ba, haka ma sayyadi Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi yake cewa: "Hakika waliyyan Allah su ne suke duban hadinin duniya a lokacin da mutane suke kallon zahirin ta, sun shagalta da ajalin mutuwa a lokacin da mutane suka shagala da abin duniya".[12]
GURACE-GURACEN KARYA:
Masu neman duniya suna zaton kaira ga burin su da abubuwan da suke so na duniya tare da ketare iyaka da bujirewa duk abin da ke tsawatar da su daga duniya, ba don komai ba sai don samun kayan ado da kawa na duniya, wai yin haka shi ne gata da fita daga takura, alhalin hakikanin lamarin ba haka bane, domin sauraren umarni da magangaun nafsu mai umarni da mummuna shi ne ke afkar da mutum cikin kukumi da mari, nafsu mai umarni da mummuna ita ce wacce ta damu da abin da ya shafi jiki (na kayan jin dadi), saboda haduwar nafsu da jiki sai ta sa shi ya zama ribataccen al'amura marasa lum'a sanadiyyar haka sai jiki ya dinga neman wanzuwa da tabbata a wannan duniyar, wannan shi ne yake sa mutum ya zama aibataccen kayan kwadayin da jiki yake so, sai ya karawa mutum nauyaye-nauyaye da suke daure hakikanin mutum da abin da ya kunsa.
Ainihin 'yanci shi ne fita daga hanun duniya da runjayen son zuciya da gurace-gurace na yaudara to irin wannan 'yanci shi ne abin da jiki yake so kuma yake kokarin tabbatar da shi.
Sanda yawa wani sarki ya kan shimfida mulkinsa a masarautar sa sai fadi sai dai a manufar addini bata ya ribace shiu har ya zama baran sha'awa. Sanda yawa wani fakiri wanda ke cikin takaici matsananci sai dai gashi ya zama sarki a masarautar sa ya mallaki ragamar son zuciyar sa da sha'awar sa. Duk lokacin da karfin fushin da sha'awar mutum suka rinjayi karfin hankali ba makawa mutum ba zai kame daga yin fasadi ba da rrusa abubuwa.
'Yanci na hakika yana karkashin rinjayen hankali da kuma sarrafawarsa a duniyar nafsu kuma fushi da sha'awa su karbi umarni daga gare shi tare da kare ta ga hukuncin da ya fito daga wajen hankali.
Addini yana ganin bauta tana cikin bawa sha'awa da fushi hukunci tare da fadawan hankali cikin ribawar karfin sha'awa ta fushi, kamar yadda Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi yake cewa: "Sau da yawa hankali ya kan zama ribatacce karkashin san zuciyar shugaba"[13] haka kuma ya kara cewa amincin Allah ya kara tabbata a gare shi "Shin akwai dan da zai bar kwadayin duniya ga ma'abota duniyar? Ai ba ku da wani amfanin da zaku samu sai gidan Aljanna kar ku sai da Aljanna saboda kwadayin duniya".[14]
'YANCIN MA'ANA DA NA ZAMANTAKEWA:
A lokacin da mutum ya kubuta daga son zuciya da karkacewar ta ya kama kudurce da asalin ransa da nafsinsa, to da sannu zai rabauta a fagen rayuwar zamantakewa da na siyasa da sarrafa (wayewar samun saiti), kamar yadda ya zo a ayoyi da riwayoyi tabbas mutum yana fuskantar makiya biyu: (1) Makiyin cikin gida (2) Makiyi na waje, duk suna kokarin ribace shi da rinjayarsa kuma cin nasara a kan wadannan makiyan da kubuta daga hannun su zai bawa mutum 'yanci iri biyu: 'yanci na cikin gida da na waje.
Abin bakin ciki da takaici an sami wata jama'a tuntuni har zuwa yanzu masu suna sufaye, duk da yake sun bada kokari a wajen samun 'yanci na ciki (gyara nafsu) da kubuta daga dabi'u marasa kyau da barin son zuciya zaka same su basu bada muhimmanci ga 'yanci na waje don su kubutga daga iyayen giji na karya da lullube gaskiya da bautawa duniya don samun dinare da dirhami. A dai-dai wannan lokaci kuma akwai wasu wadanda suka bada kokari don gyaran waje don samun kubuta a yanayin zamantakewar su da siyasa, suna kore duk nau'i na sanyawa al'umma iyakoki da dokoki domin hakan dai-dai yake da ribace mutum kuma shi ke jawo halakar sa da asara.
Sai dai an sami jama'a ta uku wadanda suke cewa mutum yana bukatar 'yanci har guda biyu ta haka ne zai kai ga kamala da rabauta har ma ya sami 'yanci na hakika. Saboda dangantakar da ke tsa kanin wannan 'yancin biyu angantaka ce mai karfi amintacciya ba zasu rabu ba, ba zai yiwu a sami 'yancin zamantakewa ba a aikace ba tare da 'yanci boyayye ba, wannan mas'alar a kan lizssafa ta a cikin masu wahala a zamantakewar mutane wanda ake kokarin samar da 'yanci na hakika. Idan mutum ya yi nufin gida na zamantakewa wacce ta dace da mutuntaka ba tsarin kai a ciki ba mushkiloli na jama'a da na dai-daiku tomakama sai ya nisanci shiga gona da iri da sakaci tare da barin kallon 'yancin bangare daya, zai kula da cewa akwai 'yanci kala biyu fa sai ya yi kokarin tabbatar da su.[15]
Dangane da wannan maganar tunani addini da musMusulunci ba ya halatta 'yanci ya kai ga matsayin shige gona da iri da samar da jin dadi, kamar yadda Musulunci bai halattawa mutum ya zuwa an yi masa dole ba dangane da yanayin da yake ciki ballantana ya amince da kowacce hukuma mara adalci wacce take kawar masa da mutuntakar sa da izzarsa.[16]
Ashe ana samun 'yanci na gaba daya dana dai-daiku a Musulunci, sai dai nazarin Musulunci yana sabawa nazarin turawan yamma a cikin wannan mas'alar.[17]
DANGANTAKAR DAKE TSA KANIN ADDINI DA DUNIYA:
Hakikanin zuwan Annabawa masu girma amincin Allah ya kara tabbata a gare shi sabdoa raya duniya da ginata, sai dai sun kalli duniya da idan lahira, duniya da ta kasance wajen neman lahira ce, duniya da muke neman lahira a cikinta ta hanyar ayyukan mu da maganganun mu a kowanne lokaci, wadannan Annabawan zasu ga ya irin wannan duniyar, hakika sun zo domin su koyawa mutane yadda ake rayuwa domin su sami arzikin lahira. Saboda haka, koyarwar Annabawa (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare su) ta himmatu da rayuwar mu, ai rayuwar mu ta wannan duniyar domin mu sami rayuwar arziki gobe kiyama.
ADDINI DA YALWATAWA:
Addini yana da ra'ayin yalawatawa haka nan abin aji aji ne kamar tattalin arziki, siyasa, zamantakewa, cigaba (wayewa). Addini bai bar wannan ba a hannun malaman zamantakewa ba, addinin da yake da'awar game duniya, yake duba ga baki dayan mutane a kan cewa su daliban sa ne a makarantar sa ba makawa ya zamana yana da mahanga da ra'ayi wadanda suka game duk abin da ya shafi cigaba da bunkasa daga nan ne zamu gane cewa sanin addini shi ne tushen komai, duk da yake a'amarin a kulle yake kuma mai wahala ne, domin addini ya kafu a kan ka'idoji na tushe guda uku, daya daga cikin ka'idojin ta tattara ne a kan abin da ya shafi nafsun mutum, guda biyun kuma sun shafi wajen nafsu ne, ka'idojin nan da ba su shafi cikin nafsu ba su ne abin da muke ce musu (Kur'ani da mutanen gidan Annabi). Ka'idar da ta shafi cikin nafsu ita ce akwai hankali da fidira, wanda hankali yana daga cikin dilla na Shari'a. ai duk abin da hankali ya tabbatar da shi hujja ce ta sharia'a don haka addini ya ginu aga riwaya da hankali.
INGANTA YALWATAWA DA BANGAREN AKIDA DA DABI'U DA SAKAFA (WAYEWA):
Tunda Allah Allah madaukakin sarki shi ne asalin komai, shi ne mahalicci mai saukar da komai, kuma amfanin sa mutum ke samu ko cutuwa duk a hannun Allah ne wanda ya halicci wannan duniyar. Hakika makomar mutum tana dawowa ne zuwa gare shi Allah madaukakin sarki. A bisa wannan wajibi ne ayyukan mutum da duk motsin mutum ya zama cewa yana gudana a kan tattalin arziki da wayewa da koyarwa... kuma ya zamana sun bullo daga wajen Allah Allah madaukakin sarki kuma ya zama sun dace da hanyar da Allah ke nufi kuma yake so. Hakika addini ya kira mutane su shimfidca adalci wanda zai gudana a cikin dabi'u ba wayewa da wasun su, kuma ya hana mutum yin ta'addanci da ketare iyakar hakkokin wasu. Ta wani bangaren Musulunci ya kwadaitawa mutum neman ilimi, kamar yadda ya bada wasiyya da cin mariyar abubuwa na ilmi da kyakkyawan yanayi mai fa'ida. Hakan kuma fa yana nufin cewa ba wani abu na dabi'a ko ilmiu na wajibi ko fa'ida da wani amfani har sai addini ya same wannan da koyarwar sa, har addini ya sanya yin aiki da su ko wajibi ko mustahabbi.[18]
'YANCI, YALWATUWA, ZAMANTAKEWA DA SIYASA
Addinin Musulunci addini ne na duniya irin wannan addinin yana cewa: zaku iya rayuwar zaman lafiya da aminci tare da duk wanda bai bijiro masa ba ko ya yake shi. Allah yana cewa:
((لا ينهاكم الله عن الذين لم يقاتلوكم فى الدين ولم يخرجوكم من دياركم أن تبروهم وتقسطوا إليهم)).
"Allah bai hana ku yin zaman lafiya tare da kyautatawa da adalci ga wadanda basu yake ku ba saboda addini bugu da kari basu fitar da ku daga gidajen ku ba".[19]
RABE-RABEN YALWATA:
Yalwatawa kala biyu ce: abar zargi (mara kyau) da mai kyau (wacce ake yabo) wacce duk zargi ita ce kamar ta'adi, jin dadi na alfahari, da takama da alfahari da sauransu, Kur'ani yana zargin baki dayan wadannan halayya, har ma a wasu ayoyi ya bayyana zargin masu ta'adi da barna da masu jin dadi na trakama da masu alfahari har Kur'ani ya ci gaba da zargin su da ganin bakon su, kuma ya siffanta wadanda ba sa tunani sai dai alfahari da kansu da yalwata abubuwan da suke so ba sa himmatuwa da komai sai da kawunan su.[20]
((والذين كفروا يتمتعون ويأكلون كما تأكل الأنعام والنار مثوى لهم))[21]
"Wadanda suka kafirta suna jin dadi suna cin abinci kamar yadda dabbobi suke ci wuta ce makomar su (wajen zama)".
Kuma haka Kur'ani ya zargi masu taskace dinare da azurfa (kudi) har ya yi musu alkawarin azaba.[22]
Hakika rowa matsananciya da kyashi suna yin sheke a cikin jikin mutum sai su zama tamkar daya daga makiyan sa.[23]
((ومن يوق شح نفسه فأولئك هو المفلحون))[24]
"Duk wanda aka kare shi daga kyashin kansa, to irin wadannan su ne masu rabauta ranar lahira".
A bisa wannan magana yalwatadde take da ma'ana alfahari da barna a al'amuran rayuwa aaboizaisi ce abarki.
Amma yalwatawa mai kyau (walle ake yabo), ma'anarta shi ne duk yayinda muka bada kokari a matsayin samadda abubuwa, ma'anar hakan mun ka sance masu dacewa, duk lokacin da muka kasance masu wadatar zuciya a ciarwarmu to zamufi samun hutu a rayuwarmu. Daga nan idan mutum yana kokarin biyawa kansa bukata tare da bukatar ragowar mutane, to irin wannan kokarin shi ake so kuma ake yabawa, amman yalwatawadda ake zaigi tace wacce take da alaka da tara dukiya aki taimalawa sai dai kawai ayita yin alfahari da ita, rin wannan alfaharin tara dukiya shi ne abin zargi.[25]
[1] Hasan zada Amuly, Nususul Hikam ala fususul hikam sh 180
[2] Maulawi, jalaluddin Mohd "Masnmawil ma'anawiy"
[3] Tabataba'iy, al insan minal bidaya hattal khitam.
[4] Suratul A'araf, 54.
[5] Malam Jalaluddin Mohd "Masnawil ma'anawiy".
[6] Muntakhabu mizanul hikma riwaya ta 2137.
[7] Nahjul balaga, huduba ta 82.
[8] Suratu Mohd, 36.
[9] Tabataba'iy, al insanu minal bidaya ilal khitman sh 51.
[10] Suratun Nur, 39.
[11] Suratur Rum, 7.
[12] Nahjul balaga, hikima 432.
[13] Nahjul balaga, hikima 211.
[14] Rioyyu shahriy Mohd, Miyzanul hikma j20 riwaya 3589.
[15] Mudauhariy, Ma'arifatuddiniyya tahliylu ru'uyatul mudahhari sh 36.
[16] Don karin bayani nemi Alwiyatu wattadayyunu, Mahdiy Haddawiy Tehraniy sh 131.
[17] Murtadha mudahhari, fi rihabussaura Islamiyya", sh 101.
[18] Jawadiy Amuly, Fawakku'atul Insani Minaddini" 210-213.
[19] Suratul Mumtahana, 8.
[20] Ali Imrana, 154.
[21] Mohd, 12.
[22] Tauba, 34.
[23] Nisa'i, 128.
[24] Hashri, 9.
[25] Jawadiy Amuly "Tawakku'atul insani minaddini". 210-222.