Please Wait
10907
- Shiriki
Mayaka yayin mubaraza a zamanin da su kan yi amfani da wani zaurance (don shaida juna ko ba da sako a tsakaninsu) don haka su kan rera baitotocin waka don samar da karfin gwiwa ga mutanensu da raunana abokan gaba. Imam (a.s) da mutanensa sun yi amfani da take iri-iri da baitoci don ba da kwakkwarar hujja dake dauke da mahimman sakonni a ranar Ashura. Daga cikinsu akwai dan uwansa Abulfadal Abbas (a.s) da ya yi ta rera baitoci masu dadin gaske a lokuta daban-daban a ranar Ashura don zaburar jama’ar Imam Husaini (a.s) da kwantar da hankalinsu musamman yara da mata don tabbatar musu da cewa yana raye ba a kasheshi ba. Za mu kawo wasu daga cikinsu kamar haka:
Alokacin da yara suka riku daga murya da kuka saboda tsananin kishin ruwa, sai Imam Husaini (a.s) ya aiki dan uwansa Abbas ya debo ruwa a bakin kogi. Abbas ya tunkari dakaru 4000, masu tsaron ruwa don su hana shi diba, sai ya fuskancesu yana rera baitoci yana gunji kamar haka:
“Zan yaki mutanen da zuciya ta shiriya
Ina mai kare jikan Ahmadu (Annabi)
Ina saranku da tokobi mai kaifi
Har sai kun kauce wa yakar shugabana
Ni ne fa Abbas mai nuna kauna ga
Zuriyar Aliyu Murtala karfafaffe”.
Sai ya rika korar su gefen dama da hagu, ya kashe musu mutane masu yawa, yana gunji da baitoci:
“ba na shayin mutuwa idan mutur ta zo
Ko da zan gamu da wahala yayin gamuwar
ni Abbas na yi nufin shayar da ruwa
ba na shayin mutuwa a ranar gamo”
Bayan ya isa bakin ruwa sai ya kamfata da hanunsa ya debo don ya sha sai ya tuna kishin Imam Husaini (a.s) sai ya watsar da rowan ya na mai rera wake yana fadi:
“Ke rai bayan Husaini kin tozarta
A bayansa bai dace ki rayu ba
Ga can Husaini na tinkarar mutuwa
Amma zaki sha ruwa mai sanyi
To wallahi Addinina bai ce haka ba”
Sannan sai suka fara ruwan kibau da na masu a kansa, Zaidu ibin Warka ya lababo ya sare hanunsa na dama, (bai kareya ba) sai ya rike tokobinsa da hanunsa na hagu yana mai rera baitoci:
“Wallahi don kun yanke mun hanun damana
Har abada zan ci gaba da kare addinina
Zan kare Imamina na gaskiya bisa tabbas”
Tsatsaon Annabi Maitsarki Amitattace[1]
Wannan wani sashe ne daga cikin baitocin Abbas da kuma kirarinsa a ranar Ashura. Zance na cewa ya zabi yin kabbara a matsayin alama ta nuna yana raye a lokacin da ya je debo ruwa, bamu samu wata kafa da ke nuna wanna bayanin ba. Sai dai a kwai wasu alamomi na (na sadarwa) da nuna wani abu ya faru da suka danganci kabbar irinsu “Babu wata dabara babu wani karfi sai na Allah” Wannan na cikin fitattun alamomi na nuna faruwar abu a tsakanin rundunar Imam Husaini (a.s). Kasantuwar Ubaidullahi bin Ziyad da yan kanzaginsa irin su Umar bin Sa’ad da waninsa wai suna yakar Imam Husaini (a.s) ne da sunan Musulunci haka fafatawarsu da Kawarijawa, babu mamaki suma su yi ammfani da wannan taken.