Please Wait
16021
{Zaman lafiya tsakanin mazahabobi} na daya daga cikin fikra ta asali a musulunci ayoyi da yawa sun zo cikin Kur’ani mai girma ta fuskoki daban daban, a bayyane suna yin nuni da hakan {zaman lafiya}. A mahanga Kur’ani yaki na mazahaba saboda bambancin akida kamar yadda yake a sauran mazahabobi kamar irin yakokin salib na kiristanci bai dace ba, ya kuma haramta kiyayya ga sauran mabiya addinai, sannan yin amfani na cutarwa gare sub a hanya ce ba mai kyau.
Kur'ani mai girma ya yi nuni ta hanyoyi daban daban yadda za a iya zaman lafiya muhimman su kamar haka:
1. ‘yancin tunani da akida
2. lura da tushen da ya hada
3. kore bambamcin launi
4. tattaunawar zaman lafiya
5. karbar tayin sulhu
6. girmama hakkokin marasa rinjaye.
7. yarda da sauran annabawa da litafan sama a matsayin gaskiya ne
8. sulhu tsakanin kasashe
9. yaki da jin fifiko a kan sauran addinai
10. taimakekeniya a cikin masalahohi na tsakanin kasashe
{Zaman lafiya tsakanin mabiya addinai} daya daga cikin tushen tunani na musulunci shi ne zaman lafiya, ayoyi da yawa ta fuskoki daban daban kuma a fili suna ishara da hakan: amma a karni na 14 kalmar zaman tare tsakanin mazahabobi baya da wata ma'ana ga dan Adam.
A mahangar Kur’ani mai girma yaki da kiyayya saboda bambance bambance akida kamar yadda yake cikin saura addinai, misali yakin salibi na kiristoci Kur’ani bai yadda da shi ba. gaba da kiyayya ga sauran addinai bai dace ba, amfani da matakin wulakanci ko kaskantarwa ga sauran addinai hanya ce da bata addini ba.
Kur'ani mai girma yana nuni da wasu kungiyoyi na yahudawa da nasara da suka dauki hanyar kafirta juna da wulakanci atsakani su da kuma take hakin junansu, da kuma hura wutar yaki da sabani tsakani.
Yahudawa na cewa: nasara ba su kan gaskiya, nasara kuma suna cewa: yahudawa basa kan gaskiya: alokaci guda kuma suna karanta littafi: wasun su ba su san gaskiya ba, suna mai maita maganar juna ne kawai. Ranar kiyama Allah zai masu hukunci akan abin da suka yi sabani a kai. [1]
Kur'ani mai girma ya yi mana nuni da hanyoyi masu daman a zaman lafiya daya daga muhimman su:
1. yancin tunani da akida
A cikin wani sashe na ayoyin Kur’ani mai girma suna tabbatar da asalin yancin akida: cewa tushe na akidodi abubuwane da suke cikin zukata wanda ba bu tilastawa.
{cikin ayukan addini ba tilasawa, saboda hanya kowane lokaci afili take.}[2]
{da ubangiji madaukaki ya so dukkan mutane duniya ba tare da tsabiba da su yi imani, sai kai ne zaka tilasta mutane su zama muminai?} [3]
Manzo Allah an aiko shi ne domin isar da sakon Allah, ko da makiya su yi imani ko kar su yi: {wannan gaskiyace daga ubangijinka, saboda haka wanda ya so ya yi imani wanda ya so ya kafirta.}[4]
{da Allah ya so da ba su zamo mushirikai ba, saboda haka ba mu saka ka zamo mai gadi ba kuma kai ba wakilinsu ba ne}[5]
Imani da Allah da kuma addini ba wani zamani da yake tilas, sai dai hanyar shigarsa shi ne tunani da ruhi, mandiki da dalilai da wannan ne za a tabbatar ma mutane gaskiya da dokoki na Allah domin su fahimta su kuma karfa cikin yancin kansu da kuma yardarsu.
Abu na gaba shi ne {yancin fikra da tunani}. Kur'ani mai girma a cikin ayoyi da dama yana kiran dan Adam kan hankalta da tunani da takatsantsan a cikin al'amuran duniya, yana so da hankalisa {mutun} ya gane abu mai amfani da marar amfani gare shi sannan ya kamar hanyar neman kamal da yanci da kuma nisantar bata da barna.
{akwai hanzari a ciki akan mu nuna masu ayoyin mu a cikin ufukai dai da kuma rayukansu, har sai gaskiya ta bayyana: shin Allah bai isa shaida ba?}[6]
{sannan a cikin kasa akwai ayoyin mu ga masu yakini sannan kuma a cikin samuwar ku: shin baku ganine?}[7]
2. lura da tushen da ya hada
Musulunci addini ne da tun farkon zuwansa yake kira ga zaman lafiya da juna sannan kuma da haka ya shahara a duniya kuma da haka ya kira mabiya littafi {ahlilkitab} cewa: ka ce yak u mabiya littafi kuzo kan maganar da dake dai dai tamu {wato tushe} kuma mu tsaya a kai cewa bayan Allah ba wani abun bauta kuma kar mu sama sa abokin tarayya kada dayan mu ya dauki wani a matsayin Allah ; in sun saba, to ka ce: su shaida mu masu biyayya ne.}[8]
Wannan ayar na daya daga cikin muhimman ayoyi da suka kira mabiya littafi zuwa ga hadin kai. Dalilin da ke cikin wannan ayar ya bambanta da dayar ayar. Dayar ayar ta kira su ne kai tsaye zuwa ga musulunci, amma a wannan ayar abin da ta lura shi ne abin da ke tsakani musulunci da mabiya littafi.
Kur'ani mai girama ya koyama musulmi cewa idan wasu ba su da niyar hadin kai daku a cikin komai na ku, to kar ku zauna ku dage ganin cewa kun hadu akan abin da ya hada ku domin yin aiki tare kuma ku muhimmantar da shi {wato abin da ya hada ku}[9].
3. kore bambanci launi
Kur'ani mai girma ya yi hani da dukkan wani nuna bambancin launi dace dukkan mutane yayan Adam ne da hauwa saboda haka ba wani fifiko tsakanin kun a launi ko mazahaba.
{yaku mutane mun halicce ku ne daga mace da namiji kuma mu ka saku kabilu kabilu saboda kusan juna ;mafifici a cikin ku a wurin Allah shi ne mai tsoro; Allah masani.}[10]
Daya daga cikin kinshkin zaman lafiya shi ne dai daituwar mutane ;saboda bambancin launi, jin fifiko, da kaskantar da sauran al'umma da mazhabobi shi ne ke kawo matsaloli dayawa cikin al'ummar duniya. Daya daga cikin irin wadan nan akwai yakin duniya na daya da na biyu.
Bambanci kala, zuri'a da al'umma, ba shi ne dalilin jin fifiko a tsakani juna ba. ta mahangar Kur’ani bambanci harsuna ko kaloli na cikin ayoyi da alamomi na ubangiji kuma hanyace ta sanin juna a tsakani mutane; inda ace dukan mutane yanayin su daya kalarsu daya kuma tsayin su da girman su daya ne to da rayuwa ta zamo da wuya da kuma tsanani.
A mahangar Kur’ani ba wani fifiko tsakanin mutane sai dai wanda yafi takawa da tsoran Allah, dukkan mutane al'umma da zuri'a daya ce ;
{mutane da farko sun kasance al'umma daya, sai Allah ya aiko da manzanin shi domin su yi bushara da gargadi, kuma mun aiko su ne da gaskiya da littafi daga sama domin yin hukunci tsakanin mutane in sun samu sabani da junan su.}[11]
Mafiya yawan ayoyin Kur’ani na kiran mutane ne baki daya; kamar haka {ya ku yan Adam}[12] da kuma {ya ku mutane}[13] wannan kiran yana nuni da cewa mutuntaka wata ma'anace daya wadda ta hade dukkan mutanen dake rayuwa kan doran kasa. Mutanen wancan wuri ba su da sabani da fifiko da na wannan wurin. A cikin tarihi mutane sun sha bamban wurin harshe, kala, kabila da sauran su, amma ta mahangar musulunci dukkan su yayan uba da uwa daya ne {Adam da hauwa} saboda haka wannan bambanci bashi da wani tasiri cikin ‘yan adamtakar mutun. [14]
4. tattaunawar zaman lafiya
Kur'ani mai girma yana bad a umarni mai karfi ga musulmi cewa ku yi makabala mai kyau da kuma tattaunawar zaman lafiya, ku ce wa ah'lulkitab sannan ku yi mu'amala dasu a bisa tushen da ya hada ku.
Kada ku yi mujadala dasu sai ta hanya mai kyau sai dai wadan da suka yi zalunci da cutarwa; ku ce masu mu yi imani da abin da a ka saukar ma na da abin da a ka saukar maku Allah mu da Allah ku daya ne dukkan mu mu na masa biyyaya[15].
Ayar da ta gabata tana magana ne kan yadda za a yi mu'amala da masu bautar wuta wadan da suke jahilai ne saboda haka ayar ta yi magana da su kamar yadda suke, amma awannan ayar ana magana ne ta tattaunawar zaman lafiya da mabiya littafi ne; saboda su sun san wani bangare na dokokin ubangiji da wanda annabawa da littatafan sama suka kawo, don haka sun fi sauki su saurari kiran ubangiji madaukaki.
Kur'ani mai girma ya yi hani ga musulmi da su kira kafirai da masu bautar kunki da munanan suna; saboda suma za su yi kamar yadda ku ka yi masu {wato na bata masu abun bauta}:
Ya ku masu imani kar ku kira wadan da ba su bautar Allah da miyagun suna, domin kar su zagi Allah kan jahilci da rashin sani, wannan shi ne ke kawata ko wace al'umma kuma ga Allah za mu koma sanan zai sanar da su abin da suka zamo suna aikatawa {ko kyauta ko azaba}[16]
Dokokin musulunci ko wane lokaci suna dauke da mandiki {hikima} da dalilai da kuma zaman lafiya, ga wasu muminai da suke zakin masu bautar kumaka saboda sunki imani to addini ya yi hani da hakan; musulunci shi ne kiyaye tushen tarbiyya, kamun kai da kyautatawa ko da kuwa ga mafi munin addinai; saboda ko wace al'umma da kungiya na kishin akidojin su da ayyukan su. Zagi ko kuma mumunar mu'amala to zai sa su dage cikin akidojin su ne.
5. Karbar tayin sulhu
Duk zamani da sukabar yaki da ku kuma suka mika wuya, to babu wata hanya wadda Allah ya rage maku gare su. [17]
Kabilu biyu na larabawa masu suna {bani zamre} da {ashj'a} kabilar bani zamre sun yi yarjejeniyar dai na wulakanta juna a lokaci daya kuma kabilar ashj'a sun yi yarjejeniya da bani zamre….
Bayan wani lokaci musulmi sun samu labarin cewa kabilar ashj'a wadan da ba su wuce mutun 700 ba kar kashin jagorancin mas'ud bin rajila sun iso kusa da madina, da manzon Allah ya samu labara sai ya tura manzo zuwa gare su domin jin miyakawo su, lokacin da suka hadu da manzon da annabi ya tura sai sukace mun zone domin mu kula yarjejeniya tsakanin mu, lokacin da manzon Allah yaji sai yasa a ka kawo masu dabino mai yawa a matsayin kyauta ; bayan sun yi bayani dalilin su na neman sulhu kamar haka: ba mu da karfin fada da makiyan ku saboda yawan mu kadan ne kuma bamu da karfin fada da ku saboda mun yi kusanci da ku, saboda haka ne mukazo mu kula yarjejeniya. A lokacin sai Allah ya saukar da aya ya kuma ba musulmi umarni akan haka[18].
6. girmam hakkokin marasa rinjaye.
Ba bu wani addini a cikin addinai kamar musulunci wanda ya ba al'umma marasa rinjare yanci da kare masu hakkoki. Musulunci yana shimfida adalci a cikin al'umma kuma wannan adalcin ba wai ya shafi musulmine kadai ba harda ma wadan da ba musulmi ba dukkuwa da sabanin mazahaba, kabila, harsuna amma musulunci bai kula da wannan sabani, wanda a cikin sauran addinai ba zaka samu hakan ba {wato sa doka ta shafi kowa ba tare da nu na bambanci ba}.
Al'umma mararsa rinjaye {wato wadan da ba musulmi ba} bayan sun kulla yarjejeniya ta amana {da hukumar musulunci} suna da yanci su rayu kamar sauran mutane wato batare da dakura ba kuma yana kan hukuma ta kare lafiyarsu ta ciki da ta waje.
Alkur'ani mai girma ya yi bayani a bayyane kan siyasar musulunci wajen kare hakkoki na kasa da kuma na sauran mazhabobi kamar haka: {}[19].
Saboda haka musulunci ya ba mazhabobi mararsa rinjaye da kuma masu kiyayya da musulunci dama da yanci na rayuwa cikin al'umma ba tare da takurawa ba ; da sharadin cewa ba zasu kawoma musulmi da musulunci matsala ba ko kuma aikata abin da zai cutar da musulunci ba.
Wata ayar na cewa: {}[20].
Idan muka lura da wadannan ayoyi biyu, za mu ga siyasar musulunci wajen mu'amala da mazhabobi mararsa rinjaye da masu sabani da musulunci kamar haka: idan ya zamo mararsa rinjaye ba su keta hakin musulmi ba ko kuma yima musulmi da musulunci zakon kasa ba, to suna da yanci cikake a cikin kasar musulunci kuma dole ne musulmi su yi mu'amala da su cikin adalci da kyautatawa; amma in sun yi wani abu wanda zai cutar ko kuma suka hada kai da wasu domin cutar da musulmi da musulunci, to musulmi na da ikon hana su ayukan {hakkoki domin sun saba yarjejeniya} kuma kada su dauke su abokai har abada.
A cikin musulunci, yanci da girman da kafiran amana suke da shi kamar da wani da ga cikin kafiran amana zai aikata wani abu wanda a addinin su ba laifi ne ba amma a musulunci laifi ne kamar shan giya, to babu wanda ke da hakin ya yi masa magana da ga cikin musulmi; amma da sharadin ciwa aikin ba a fili da kuma yin tagama da aikin nasa ba, amma in ya yi tagama da aikin na sa, to ya na dai dai da karya doka ne {ta cewa musulunci zai kare su} kuma za a kama shi, amma in da zai aikata wani aiki wanda ko a cikin addinin su bai halatta ba wato laifi ne kamar zina da luwadi… wanda wadannan aikin hukuncin su daya a cikin kowa ne addini to a nan alkali yana da hakin ya zartar da hukunci kansa; ko kuma ya ba da shi zuwa ga al'ummarsa domin su yi mashi hukunci irin na su[21].
A cikin fikhun musulunci ya zo cewa, da mutun biyu da ga kafiran amana zasu kawo kara ga alkalin musulmi, to alkalin ya na da tsabi ya yi masu hukunci da dokokin musulunci ko kuma ya ne mi uzurin su {wato ya ki yi masu hukunci}, alkur'ani mai girma ya na cewa;
Idan ma'abota littafi suka kawo kara gare ka, to kayi hukunci tsakanin su ko kuma ka ne mi uzurin su[22].
Ba wai ana nufin cewa manzon Allah {s. w. a} ya nu na sa rai cikin yin hukunci da rashin yinsa. A bun nufi a nan shi ne in manzo Allah {s. w. a} ya duba yanayi sai ya ga a kwai masalaha akan ya yi hukunci to yana iya yi amma in ba masalaha to sai ya bari[23]. Baya da ga cikin masalahar a nan shi ne dubi ga mu'amala tsakanin ahlulkitabi da musulmi. A cikin wannan ayar tsamu ga ne cewa lokacin manzon Allah {s.w.a} zaman takewa tsakanin ahlulkitaf da musulmi ta kai ga har suna kai karar su zuwa ga manzo Allah {s. w. a} domin ya yi masu hukunci. Shi adalci kowa ne lokaci a bune mai kima da daraja kuma ba bam bamci tsakanin ko wace kunkiya. Inda za a zafi alkali ko daular musulunci a kan su yi hukunci ko shiga tsakani, dole ne su kiyaye adalci su kuma nisanci abubuwan da suka shafi nuna bangaranci da kishin kabila, domin san rai na kawo rashin adalci cikin hukunci.
7. yarda da sauran annabawa da litafan sama a matsayin gaskiya ne.
Dukkanin littatafan sama a tushin su a bu daya ne kuma suna da dai dai tuwa da junan su kuma suna da hadafi daya ne wato {tarbiya da kamalar mutun}; duk da cewa a reshe da kuma matakan kaiwa ga kamala suna da bam bamci da juna cewa duk addini da ya zo baya ya na daukar mataki na sama da kuma tsari cikakke. Alkur'ani mai girma yana girmama annabawa da littatafan sama wadan da suka gabace shi kuma yana gaskata su.
Mun saukar ma da littafi da ga sama {Kur’ani} mai gaskiya abun gasgatawa kuma mai gasgata littatafan sama wadan da suka gabace shi kuma ya na hukunci a kan su, saboda haka kayi hukunci tskanin su da abin da Allah ya saukar[24]……
Kusan ayoyi ashirin ne a cikin Kur’ani wadan da suke gasgata ataura da injila[25]. Wannan sunar Allah ce duk annabin da ya zo yana gasgata annabin da ya gabace shi, kuma kowane littafin sama ya na gasgata littafin da ya ga bata. Allah madaukaki ya tabatar da annabi musa da ataura ta hanyar annabin da ya zo bayan su, wato annabi Isa da kuma littafin sa injil;
Wadan da suka zo bayan sa {musa da ataura} mun aiko da Isa dan maryam mai sheda ne ga gaskiyar ataura wadda da gabace shi, kuma mun ba shi injila waddan haske ce kuma mai gasgata ataura ce wadda ta sauka kafin ta hanyar shiriya ce da kuma wa'azi ga masu tsoro[26].
8. sulhu tsakanin kasashe.
Tushen musulunci tun farko ya ginu a kan sulhu, kuma ya buda ma na hanyar sulhu da zaman lafiya tsakanin al'ummu duniya. Musan cewa ruhin musulunci shi ne zaman lafiya. Kamar yadda ya ke asalin Kalmar islam da ga {salama} ne wato aminci wanda ya ke nu ni da zaman lafiya da aminci; saboda haka Kur’ani ya na umarni da zaman lafiya a cikin al'umma;
Ya ku masu imani ku shiga cikin aminci {musulunci} baki daya[27]…..
Aminci ya na sama da sulhu, saboda aminci shi ne zaman lafiya al'umma.
Allah madaukaki ya ummurci manzon sa da cewa in makiyan ka suka zo ma da neman zaman lafiya kuma suka nu na kaunar su a kan hakan to kai ma {manzo Allah s. w. a} kayi amfani da wannan damar kuma ka yadda da su a kan haka;
Idan makiya suka bukaci sulhu to kaima ka karkata zuwa ga sulhun[28].
Musulunci ya na ba sulhu tsakanin mutane muhimmanci wanda har ta kai ya na ba masu imani umarni cewa nu na halaye na zaman lafiya tsakanin musulmi da makiya zai iya kawo abokantaka tsakanin su;
{ta yiyu Allah madaukaki ya sa kauna tsakanin ku da tsakanin mutanen da ku ke gaba da kiyayya da su saboda shi mai iko ne a kan aikata komi.}[29]
Mutanen da ba musulmi ba sun kasu kasha biyu: kashi na daya su ne wadanda suke kiyayya suka kuma dauki takobi a kan musulmi, suka kuma fitar da dasu a cikin gidajen su da garuruwan su da karfi, a tagaice su ne wadanda suka nu na gaba ga musulmi da musulunci ta aikinsu da maganarsu. Nauyin da ya dauru kan musulmi dan gane da wannan kashin na daya shi ne, su nisanci duk wani dare da abauta da su.
Misali bayyananne na irin wannan kashin su ne mushirikan makka, musamman shuwagabanin kureshi: wadannan kashin sun nuna ma musulmi gaba a fili wasu kuma sun taimaka masu akan haka.
Amma akwai kashe na biyu, su ne a lokaci daya kafirai ne kuma mushirikai, amma ba su damu da al'amuran musulmi ba. Ba su nuna masu kiyyaya ba ba su kuma damu da abin da suke ciki ba kuma ba su da niyar fitar da su daga garuruwan su da gidajen su ba: wasu ma da ga cikin su sun yi yarjejeniyar zaman lafiya da rashin fada tsakanin su da musulmi. Nauyi da ya dauru kan musulmi dangane da mu'amala da wadannan kashin na biyu shi ne, rige alkawali da kuma adalci tsakani. Irin wadannan kashin misalign su a fili kamar kabilar khajja'a da suka yi yarjejeniyar barin rikici da kuma neman zaman lafiya[30].
A takaice, musulunci a siyasar shi ta waje ya na koyan bayan zaman lafiya da sulhu tsakanin al'umma kuma ya na karfafa hakan. Alokaci guda kuma ya karfafa tarbiyyantar da runduna mai karfi saboda kare kai alokacin da bukatar hakan ta taso.
Musulunci yana ba tsaman lafiya da sulhu tsakanin al'umma muhimmanci, takai gacewa ko da cikin rigimar gida wato mutanen gida musulunci yana kiran su kan su yi sulhu da sasantawa {ku yi sulhu shi ya fi}.
9. yaki da jin fifiko akan sauran addinai
Wasu da ga cikin ayoyin Kur’ani mai girma suna yaki da akidojin wuce gona da iri da kuma ta'assubancin wasu addinai. Karkatattun akidu su ne tushen mafiya yawanci gaba da kiyayya da suke faruwa cikin addinai.
Littafin saman mu bayan kira ga mabiyansa akan zaman lafiya da sauran mazahabobi a lokaci daya yana rusa a sashen karkatatun tunani da akidoji munana na wasu addinai.
Yahudawa da nasara suna da akidar cewa su ne al'ummar da Allah ya tsaba; su kadaine suke da kusanci tabbatace wanda bai gushewa ga Allah; aljanna Allah tasuce ba wanda ya cancanci shigarta da ga sauran addinai; yahudawa da nasara ne kadai suka cancanci kirmamawa da kuma daukaka, sauran mutane gasgantartune kare su kuma dole su kirmama su[31].
{yahudawa da nasra sukace: mu ‘ya’yan Allah ne kuma abokansa kebabu, to ka ce: me ya sa ake hukunta ku sakamakon zunubban ku? Ku dai mutane ne da ga halittun da aka halitta. Yana yafema wanda ya so kuma wadan da suka cancanta, ya kuma ya kuma azabtar da wanda ya so mulkin sammai da kasa da abin da ke tsakaninsu suna gare shi kuma gare shi ne kowa yake komawa. [32]}
A cikin wata ayar ya zo: {sukace: ba bu wanda zai shiga aljanna sai yahudu da nasara; wannan gurin su ne. Ka ce ; su zo da dalili in sun zamo masu gaskiya; haka ne dukkan wanda ya sallama ma Allah kansa ya kuma yi aiki mai kyau sakamakon shi na ga ubangiji Allah; ba su da tsoro kuma ba su da bakin ciki;[33]} saboda haka aljannar Allah ba ta takaita ga wata kunkiya ba.
Akan haka za mu fahimta Kur’ani mai girma ya na yaki da munana tunani da kuma miyagun akidoji na girman kai da ta'assubanci na wadannan al'ummar biyu {yahudu da nasara} kuma yana nuni da dalilansu masu rauni.
Abu ne sananne cewa irin wannan munanan tunani da akidojin in suka zamo cikin al'umma. To zaman lafiya da sulhu tsakanin mutane zai wahala sosai kuma dukkan mazahabar da ke da irin wadannan tunani zai yi wuya su iya zaman lafiya da mabiya wata mazahabar daban. Kauda ta'assubanci da ji fifiko da kuma nuna bambanci launi tsakanin al'umma shi ne zai share hanya zaman lafiya tsakanin addinai da mazhabobi mabambanta.
Ta mahangar Kur’ani mai girma, ba wata al'umma da Allah ya tsaba kuma ba wadda ya kulla yan uwantaka da ita. Kirma da daukaka su na ga wadanda suke kaskantar ta kan su gaban gaskiya kuma ta'assubanci bai hana su karfar gaskiya.
10. taimakekeniya a cikin masalahohi na tsakanin kasashe
Ya na daya da ga cikin abubuwan da suke dole a cikin rayuwa yau da gobe, taimakekeniya da aiki tare. Rayuwar yau da gobe da tsarin kasa da kasa, ba zai yiyu ba ba tare da aiki da kuma taimakekeniya ba ta hanyoyi daban daban kamar siyasa, tattalin arziki, al'adu da zaman takewa. Ba makawa wajen kyara matsalolin kasa da kasa aiki tare da haduwa wajen taimakekeniya.
Kur'ani mai girma, taimakekeniya na daya da ga cikin asali na hankali, wanda kuma ya yi ishara ga re shi {kyakyawa da takawa} kuma ya yi hani da taimako a cikin sabo da zalunci.
{ku yi taimako cikin kyawawa da takawa ka da ku yi taimako cikin sabo da wuce kona da iri}[34]
A cikin tsarin tafiyar da duniya, kokari wajen samar da adalci, dai daituwa, sulhu, tsaro, suna cikin alamomi na {bir} kyakyawa kuma yaki da mulkin mallaka, danniya, ban bancin launi fata, da kuma dukkan wani nau'I na kokari wajen yaki da tushen wuce kona da iri a cikin duniya, kokari cikin tagawa da kusantar al'umma na cikin iko da bukata da ubangiji madaukaki, kuma dole ne mu nisanci duk wani taimakekeniya wajan sabo da zalunci[35].
Duk lokacin da muka ba abubuwan da suka hada mu muhimmanci, fahimta tsakanin kasa da kasa zaiyi sauki; saboda haka sulhu da zaman lafiya zai tabbata. Kur'ani mai girma yana kira ga riko da asalin da ya hada al'umma; {ka ce; ya ku ahlulkitab kuzo…} kira ga maimakekeniya a cikin tagawa da kyakyawa shi ne ya ba musulmi daman yin mu'amala ta tatalin arziki… da kuma cin abinci su banda giya da naman alade:
Abu ne sananne cewa mu'amala ta tattalin arziki da kuma cin abinci su ahlilkitab…suna cikin shimfida ne na taimakekeniya da rayuwa ta zaman lafiya a cikin al'umma. Ta mahangar musulunci, taimakekeniya na daya da ga cikin ‘yan adamtaka bawai sannan takalifi ne kuma a addini. Saboda haka mu yi amfani da arzikin da Allah yasa a doron kasa. Kuma hakan ba zai yiyu ba sai tare da taimakekeniya da aiki tare.
Da ga karshe, duk da cewa a cikin wannan ayar ba amfani da Kalmar taimakekeniya a fili ba; amma sai dai ta yi nuni da nau'I na taimakekeniya da kuma mu'amala da ahlulkitab, cin abinci ahlulkitab banda giya, da naman alade, afili yake ba da izini da aci abinci ahlulkitab… ya na daya daga cikin shimfida na yin mu'amala da yin aiki tare da kuma samar da zaman lafiya tsakanin su da musulmi.
[1] Yahudawa na cewa: nasara ba su kan gaskiya, nasara kuma suna cewa:yahudawa basa kan gaskiya: alokaci guda kuma suna karanta littafi: wasun su ba su san gaskiya ba, suna mai maita maganar juna ne kawai. Ranar kiyama Allah zai masu hukunci akan abunda suka yi sabani a kai{suratul bakara aya ta 13}
[2] {Bakara 256} cikin ayukan addini ba tilasawa, saboda hanya kowane lokaci afili take
[3] {Yunus 99} da ubangiji madaukaki ya so dukkan mutane duniya ba tare da tsabiba da suyi imani, sai kai ne zaka tilasta mutane su zama muminai?}
[4]{ Kahafi 29 wannan gaskiyace daga ubangijinka, saboda haka wanda yaso ya yi imani wanda yaso ya kafirta }
[5] {An'am 107} da Allah yaso da ba su zamo mushirikai ba, saboda haka ba mu saka ka zamo mai gadi ba kuma kai ba wakilinsu ba ne
[6] {Fusilat, 53} akwai hanzari aciki akan mu nuna masu ayoyin mu acikin ufukai dai da kuma rayukansu, har sai gaskiya ta bayyana: shin Allah bai isa shaida ba
[7]sannan acikin kasa akwai ayoyin mu ga masu yakini sannan kuma a cikin samuwar ku: shin baku ganine?{Zariyat 21-22}
[8] {Ali amran 64}ka ce yak u mabiya littafi kuzo kan maganar da dake dai dai tamu {wato tushe} kuma mu tsaya a kai cewa bayan Allah ba wani abun bauta kuma kar mu sama sa abokin tarayya kada dayan mu ya dauki wani a matsayin Allah ; in sun saba, to ka ce: su shaida mu masu biyayya ne
[9] Nasir mukarim shirazi tabsirin namune jildi na 2 shafi na 450
[10]yaku mutane mun halicce ku ne daga mace da namiji kuma mu ka saku kabilu kabilu saboda kusan juna ;mafifici acikin ku a wurin Allah shi ne mai tsoro; Allah masani {Hujrat, 13}
[11]{ Bakara, 213}mutane da farko sun kasance al'umma daya, sai Allah ya aiko da manzanin shi domin suyi bushara da gargadi, kuma mun aiko su ne da gaskiya da littafi daga sama domin yin hukunci tsakanin mutane in sun samu sabani da junan su
[12] Bayani akan dan Adam acikin ayoyi na 26, 27, 35, da 171 acikin suratul a'araf da kuma aya ta 70 suratul isra'i
[13] Infidar, 6 da kuma kusan ayoyi 60
[14] Yasir abu shabane acikin nizamuldaula aljadid binalwake'lhali waltasawurislami, shafi na 542-543
[15] {Ankabuti, 46Kada ku yi mujadala dasu sai ta hanya mai kyau sai dai wadan da sukayi zalunci da cutarwa; kuce masu muyi imani da abunda a ka saukar ma na da abunda a ka saukar maku Allah mu da Allah ku daya ne dukkan mu mu na masa biyyayd}
[16]kar ku kira wadan da ba su bautar Allah da miyagun suna, domin kar su zagi Allah kan jahilci da rashin sani, wannan shi ne ke kawata ko wace al'umma kuma ga Allah za mu koma sanan zai sanar da su abunda suka zamo suna aikatawa{ ko kyauta ko azaba}{An'am, 108}
[17] {Nisa, 90} Duk zamani da sukabar yaki da ku kuma suka mika wuya, to babu wata hanya wadda Allah ya rage maku gare su.
[18]Nasir mukarim shirazi tabsirin namune jildi na 4 shafi na 54.
[19]{ Mumtahin, 8}
[20] Mumtahin, 9
[21] Jafar subhani, mabani hukuma ta musulunci, tarjama dawud ilahi shafi na 526-530
[22] {Ma'ida, 42 Idan ma'abota littafi suka kawo kara gare ka, to kayi hukunci tsakanin su ko kuma ka ne mi uzurin su }
[23] Tabsirin namune jildi na 4 shafi na 386
[24]Mun saukar ma da littafi da ga sama{ Kur’ani} mai gaskiya abun gasgatawa kuma mai gasgata littatafan sama wadan da suka gabace shi kuma ya na hukunci a kan su, saboda haka kayi hukunci tskanin su da abunda Allah ya saukar{Ma'ida, 48}
[25] Ali imran 50 da nisa 47 ma'ida 46 saf, 6 bakara, 89 bakara, 101
[26] {Ma'ida 46} kuma mun ba shi injila waddan haske ce kuma mai gasgata ataura ce wadda ta sauka kafin ta hanyar shiriya ce da kuma wa'azi ga masu tsoro
[27] {Bakara, 208} Ya ku masu imani ku shiga cikin aminci{ musulunci } baki daya
[28] Anfal, 61}} Idan makiya suka bukaci sulhu to kaima ka karkata zuwa ga sulhun
[29] {Mumtahan, 7} ta yiyu Allah madaukakin sarki ya sa kauna tsakanin ku da tsakanin mutanen da ku ke gaba da kiyayya da su saboda shi mai iko ne a kan aikata komi
[30] Tafsirin namune jildi na 22, shafi na 31-32
[31] Muhammad mujahid shustari { zaman lafiya zakanin mazahabobi} maktab islam shaikara ta 7 shamsi shafi na 37
[32] Ma'ida, 18}. }yahudawa da nasra sukace: mu ‘ya’yan Allah ne kuma abokansa kebabu, to ka ce: me ya sa ake hukunta ku sakamakon zunubban ku? Ku dai mutane ne da ga halittun da aka halitta. Yana yafema wanda yaso kuma wadan da suka cancanta, ya kuma ya kuma azabtar da wanda yaso mulkin sammai da kasa da abunda ke tsakaninsu suna gare shi kuma gare shi ne kowa yake komawa
[33]sukace: ba bu wanda zai shiga aljanna sai yahudu da nasara; wannan gurin su ne. Ka ce ; su zo da dalili in sun zamo masu gaskiya; haka ne dukkan wanda ya sallama ma Allah kansa ya kuma yi aiki mai kyau sakamakon shi na ga ubangiji Allah; ba su da tsoro kuma ba su da bakin ciki{Bakara, 111-112}
[34]ku yi taimako cikin kyawawa da takawa ka da ku yi taimako cikin sabo da wuce kona da iri {Ma'ida, 2}
[35] Abbas amid zanjani, fikhu cikin siyasa jildi na 3, shafi na 441-461,