advanced Search
Dubawa
5479
Ranar Isar da Sako: 2010/08/31
Takaitacciyar Tambaya
Shin gaske ne Manzo (s.a.w) ya ce: da mutane sun san wasu daga karamomin Ali (a.s) da sun kafircewa Allah, sun kira Ali (a.s) Allah
SWALI
Naji Magana daga marawaita cewa da mutane sun san wasu daga karamomin Ali (a.s) da sun kafirce wa Allah, sun kira Ali (a.s) Allah, shin wannan Magana hakan take kuma inason naji wanda ya yi wannan Maganar, ina zaton daga Manzo (s.a.w) take amma ba ni da tabbas, kuma wannan danganta ta da nayi da Manzo (s.a.w) nayi masa karya? Ina bukatar a nuna min don ina tsoron yi wa Manzo (s.a.w) karya. Na gode
Amsa a Dunkule
Bamu samu wannan hadisi cikin manya manyan litattafai ba kamar yadda tambaya ta nuna , saida akwai hadisai da dama da sukayi Magana mai kama da wannan cikin Litattafanmu bari mu zabi wani da yazo cikin usulul kafy yazo da takaitaccen bayani irin na mai tambaya .
Abu basir yana cewa <wata rana Manzo (s.a.w) na zaune a lokacin imam Ali (a.s) na gabatowa sai Manzo (s.a.w) ke cewa da shi, kai kama da Isa dan Maryam, wata rana na zuwa al’ummata zata kiraka kamar yadda kiristoci suka kira Isa harma idan ka wuce ta inda suke zasu danga dibar kasar sawunka suna neman tabaraki daga ita.
 
Amsa Dalla-dalla
Bamu samu wannan hadisi cikin manya manyan litattafai ba kamar yadda tambaya ta nuna , saida akwai hadisai da dama da sukayi Magana mai kama da wannan cikin Litattafanmu, an rawaitoshi cikin mafiya yawan litattafai ta hanyoyi mabambanta, daga ciki akwai wanda aka rawaito cikin usulul kafy inda:
Abu basir yana cewa <wata rana Manzo (s.a.w) na zaune a lokacin imam Ali (a.s) na gabatowa sai Manzo (s.a.w) ke cewa da shi, kayi kama da Isa dan Maryam, wata rana na zuwa al’ummata zata kiraka kamar yadda kiristoci suka kira Isa harma idan ka wuce ta inda suke zasu danga dibar kasar sawunka suna neman tabaraki daga ita>>
Sai wasu mutanen kauye tare da mugira dan shu’uba da wasu daga kuraishawa da ke wajan sukayi fushi sukace: me zesa ya yarda idan ya yi misali zuwa amininsa misalin da saidai Isa dan Maryam sai Allah ya saukarwa Manzo (s.a.w) wannan aya, Manzo (s.a.w) ya karantota “yayin da sukayi misali da dan Maryam sai ga mutanenka daga gareshi ( shi misalin) suna masu dariya da izgili, suna cewa shin gumakanmu ne mafifita ko shi (annabi Isan)­­­?, basu buga wannan misali gareka ba saidan yin jidali, a’a su mutane ne masu husuma , shi (annabi Isan) bai zama ba face bawane da muka yi wa ni’ima, kuma muka sanya shi abin koyi ga ba ni Israel, kuma da munaso (mun ga dama) da mun sanya mala’iku daga cikinku (daga banu Hashim) suna masu halifanci a bayan kasa”.
Mai ruwaya ya ce nan take sa haris dan amirul fahry ya ce: ya Allah idan wannan gaskiyane kuma daga gareka yake cewa banu Hashim su ne masu halifanci bayan wannan annabcin Allah ka jefo mana duwatsu daga sama ko ka jefo mana da azaba mai radadi, sai Allah ya saukar masa irin abin da ya samu Haris, nan take wannan ayar ta sauka “kuma Allah bai kasance yana yi musu azaba ba alhalin kana cikinsu, kuma Allah bazai kasance yana yi musu azaba ba alhalin suna istikfari” sannan ya ce da shi ya kai dan amr kabita ko ka bari? Sai dan amr ke cewa ya Muhammad ina jiran naji daga sauran kuraishawa abin da kake tare da shi .
Hakika banu Hashim sun tafi da dukkan matsayen larabawa da dukkan mutane, sai Manzo (s.a.w) ya ce wannan nufin Allah ne ba yadda kake zato bane sai ya ce da Manzo (s.a.w) ya Muhammad zuciyata bazata taba barina nayima mu’bayi’a ba saidai ma ta kara nisanta ni daga abin da kake kirana, daga nan ya hau abin hawansa yayin da ya fita bayan madina sai azabar (jundia) ta sameshi, daganan wahayi ya zowa Manzo (s.a.w) aya ta sauka “wani mai tambaya ya yi tambaya game da azaba mai faruwa, ga kafirai bata da mai tunkudewa, …”. Sai Manzo (s.a.w) ya ce da munafukan da ke kewaye da shi ku koma zuwaga abokinku abin da ya roka ya sameshi (ya zomasa), Allah mai girma da daukaka ya ce “sunyi addu’ar alfanu (ga abin da yake gani gaskiya) kowane kangararre mai taurin kai ya tabe” .
Yana daga larura mutum ya dinga kokarin tace tambaya da Magana kafin ya dangantata ga Manzo (s.a.w) ko ma’asumai (a.s), idan abin da ya alakanta da wannan ruwaya a kebance wanda shima ya yi nau’i da ma’anar da aka kawo ta wannanan bangaren kenan, ta wani bangaren kuma idan an samu ruwayar da ma’anar da lafazin baya cutarwa, amma idan abin da aka nakalto ba gaskiya bane wannan kan iya jefaka zuwa ga aikata laifi.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa