advanced Search
Dubawa
8061
Ranar Isar da Sako: 2019/06/16
Takaitacciyar Tambaya
Shin mutum mai yawan tafiya zai yi kasaru kan hanyarsa ta tafiya ko dawowa wacce ba ta kai kwana goma ba?
SWALI
mutum mai yawan tafiya zai yi kasaru an hanyarsa ta tafiyan da bai kai kwana goma ko dawowa?
Amsa a Dunkule
Maraji”an takalid masu daraja, sun tafi kan cewa mutanen da tafiye tafiye ya kasance matsayin sana”a  garesu to wajibi ne su cika sallah su kuma yi azumin ramadana halin tafiyar sai dai cewa game da adadi da gwargwadon tafiyar da za ta kasance da wannan hukunci na cika sallah malamai suna da sabani kai amma ma fi karanci shi ne kwana daya cikin dukkanin kwanaki goma.
Duk da kasantuwar sana”ar ka shi ne tafiye tafiye sai dai kuma kwanakin tafiyar sun karanta to a lokacin irin wannan tafiyar kasaru za ka sallata sannan kuma ka da ka dau azumi sai dai idan gabanin azahar ba zaka isa ga garinku ba ko wajen da ka nufi zuwa har sai ka dauki tsawon kwanaki goma kafin risakarsa, to irin wannan yanayi za ka cika sallah ka kuma dau azumi.
 
Ayatollah sayyid ali kamna”i:
Idan nisa tsakanin garin da kake zaune da wajen da kake aiki ya haura kilomita 22/5 sannan kuma mafi karanci shi ne  a dukkanin sati ka na zuwa wannan waje sau daya to a irin wannan yanayi za ka cika sallah ka kuma dau azumi. [1]
 
Ayatollah nasir mukarim shirazi:
Idan ya kasance cikin kowanne wata biyu ko wata daya ka na tafiye tafiye sau uku cikin kowanne sati to a irin wannan yanani zaka cika sallah ka kuma dau azumi, idan ba haka ba to wajibi ne ka yi kasaru.[2]
 
Ayatollah sayyid Ali Sistani:
Sunan mai yawan tafiye tafiye na tabbata kan wanda ya kasance, a mafi karanci ya na tafiya sau uku cikin kowanne sati ko kuma kwananki goma cikin wata guda sannan kuma ya dau niyyar ci gaba da yin irin wannan tafiye tafiye wanda akalla za su kasance wata shida ko wata uku cikin kowacce shekara biyu da abin da ya yi sama da haka.
Sai kuma dole ne a watansa na farkon fara yin tafiya ya yi ihtiyadi wajen hada cikawa da kasaru.[3]
 
Ayatollah gulfaigani:
Idan ya kasance ya dau damara yin tafiye tafiye a kowanne sati tsawon kwanaki da ake la”akari da su kuma ya ci gaba da yin hakan to za a sanya shi cikin hukuncin mai yawan tafiye tafiye wanda zai dinga cika sallarsa.[4]
 
Ayatollah jawad tabrizi:
Idan ya kasance zai yi wana aiki tsawon watanni biyu ko sama da haka sannan nisan wajen aikin da garin da yake ya kai gwargwadon masafa ta shari”a sannan kuma mafi karanci a kowanne sati ya na kai kawo sau daya tsakanin garin da ya ke da wajen aikin sa, to a irin wannan yanayi zai cika sallah zai kuma dau azumi.[5]
 
Ayatollah Muhammad takiyu bahajat:
Mai yawan tafiye shi ne wanda mafi karanci a cikin kwanaki goma ya na kai kawo tsakanin garinsa da wajen da zai je da gwargwadon nisan masafar shari”a, da haddin da a al”adance mutane za su kidaya shi daga cikin masu yawan tafiye tafiye.[6]
 
 

[1]  An ciro daga tambaya ta 9153.
[2] Daga tambaya mai namba 16403.
[3] Taudhihul masa’il j1 shafi 704.
[4] Majma’ul masa’il j1 shafi 212.
[5] Istifta’at j2 shafi 81.
[6] Istifta’at j2 shafi 425.
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa