advanced Search
Dubawa
4848
Ranar Isar da Sako: 2019/05/15
Takaitacciyar Tambaya
Yaushe Aka Haifi Ammar Dan Yasir Kuma Wace Irin Rawa Ya Taka A Kwanakin Musulunci Na Farkon?
SWALI
Ina Son bayanin Rayuwar (ko Halayen) Ammar Dan Yasir?
Amsa a Dunkule
 Ya Dan’uwa mai girma muna masu baka hakuri sakamakon jinkirin da aka samu wajen aiko maka da amsar tambayarka/ki a sakamakon yanayin ayyuka da suka sha kanmu.
“Ammar Dan Yasir Dan Aamir” ana yi masa alkunya da ‘Abu YaKazan” kuma ya kasance abokin rantsuwa ne shi (wato maDaurin alkawari ne)[1] ga Kabilar banu makhzum. [2] Dangantakar Ammar na tuKewa da nasabar “Anas Dan Malik” daga Kabilar KahDan mazauna yeman. Yasir baban Ammar ya iso makka yana saurayi kuma a nan ya zauna kuma ya kasance abokin rantsuwa ga banu makhzum.[3]
A nan zamu yi nuni kan wasu jigogi na abin da ya shafi rayuwar Ammar Dan Yasir:
  1. Ammar tare da babansa da babarsa na daga cikin waDanda suka gabata a shiga musulunci. [4] bisa wata ruwaya, Ammar ya musulunta bayan mutum talatin da wani abu[5] a wata ruwayar kuma ya kasance daya daga cikin matane bakwai na farkon musulunta. [6] Kuraishwa su azabtar da Ammar da Dan’uwansa Abdullah da babarsa sumayya da Yasir babansa da bilal da khabba, da suhaibu don su fita daga musulunci, kuma a sakamakon wannan azabtarwar ne sumayya da Yasir suka rasa rayukansu suka zama farkon shahidai a musulunci.[7]
Kamar yanda mushirikai suka tilasta wa Ammar ya faDi mummunar kalma kan Manzo (s.a.w), amma Manzon Allah (s.a.w) ya karBi uzurinsa kuma ya gaya masa cewa idan suka kuma tilasta maka ka kuma faDa. Kuma a kan wannan abin da ya faru ne wannan ayar ta sauka tana cewa: {Duk wanda ya kafirta bayan ya yi Imani da Allah (sakamakon haka azaba ce mai girma) in banda wanda aka tilastawa alhali zuciyarsa cike take da Imani, amma wanda zuciyar sa ke cike da kafirci Allah ya yi fushi da shi kuma azaba mai girma ta tabbata a kan sa.[8]    
  1. Wasu daga cikin bayanai na tabbatar da cewa Ammar na daga cikin waDanda suka yi hijira zuwa habasha ma.[9]
  2. Ammar na daga cikin na farko farkon waDanda suka yi hijira zuwa Madina kuma yana daga cikin waDanda suka yi aikin gina masallacin Kuba, wanda shi ne masallacin na farko da aka gina a musulunc.[10] Kuma yana daga cikin sahabban da suke kamusanta wajen Manzon Allah (s.a.w) kuma yana daga cikin waDanda suka taka raWar gani a yaKoKin da ya halarta tare ma Manzo (s.a.w).[11]
  3. An rawaito falalolin Ammar daga bakin Manzon Allah (s.a.w), waDanda daga ciki akwai cewa: “aljanna na shauKi zuwa Ali da Ammar da Salman da Bilal”. [12]
“Ammar na tare da gaskiya kuma gaskiya na tare da Ammar, Ammar na juya wa tare da gaskiya duk inda ta juya”.[13] “kuma wanda ya kashE Ammar Dan wuta ne” . [14]
  1. Ammar tare da salman da MiKdad da Abuzarri na daga cikin na gaba daga shi’ar Ali (a.s) wanda tun a zamanin Manzo (s.a.w) aka sansu da wannan sunan. [15] kuma Ammar ya ki yiwa Abubakar muba’aya a kokarinsa na kare hakkin Imam Ali Dan abi Dalib (a.s). [16] amma bayan da Imam Ali (a.s) ya yi wa Abubakar mubaya’a ya yi, kamar yadda Imam Ali (a.s) ya yi na yin aiki tare da hukuma. Kuma a lokacin halifa na farko ya halarci yaKin yamama kuma a wannan yaKin ne aka cire masa kunne.[17]
A lokacin shugabancin Umar Ammar ya kasance gomnan kufa kuma shi ne shugaban sojojin musulmai na garin. [18] Alokacin da yake gomnan kufa ne ya jagorancin yaKin Nahawand kuma ya buDe wani bangare daga kasar farisa (Iran). [19] Amma bayan wani lokaci sai aka ciri shi daga wannan muKamin. [20] mafi yawan litattafan tarihi ba su bayyana dalilin cire shi ba a sarari, sai dai wasu daga ciki sun bayyana cewa, dalilin cire shi shi ne kai kukan da mutane su ke yi kan raunin Ammar da kuma rashin masaniyarsa kan al’amarin siyasa! [21]
A lokacin halifa na uku an sami taku saka mai tsananin tsakanin sa da Ammar, saboda wasu dalilai, amma Daya daga cikin waDannan dalilai su ne rashin nuna amincewar da ya yi kan nisanta (korar) Abuzarri zuwa rabaza da usman ya yi, wanda ya hakan ya sabbaba jayayya mai tsananin tsakanin usman da Ammar wanda har ta kai ga umsan ya bada umarni da a doki Ammar mummunan duka. Kuma usman ya yi nufin ya nisantar da Ammar kamar yanda ya yi wa Abuzarri sai banu makhzum da Imam Ali suka hau kujerar na Ki don haka sai umsan ya haKura a dole.[22]
Wasu bayanai sun tabbatar da cewa dalilin da yasa aka doki Ammar kuma ya sha zagi ta uwa ta uba shi ne, ya yi naKadin halifa usman kan yanda yake raba dukiyar baitul mali kuma ya tabbatar da kuskuren da Usman ya ke kai na bayanin da shi usman din ya yi wanda a cikin sa ya nuna cewa yana da hakkin yin tasarrufi (yin yanda ya ga dama) da dukiyar alumma. [23]
Wasu ruwayoyi na nuna cewa Ammar ya kasance tare da waDannan suka yi wa suman tawaye kuma ya haDa kai da wasun su a kasar misira haka ma a madina ya shiga cikin gungun waDanda suka kewaye gidan usman. [24]
Ammar Yasir na daga cikin waDanda suke goyen bayan imama Ali (a.s) kuma a lokacin da umar ya mutm, Ammar ya yi Magana da Abdurrahman bin aufin dangane da lamarin shurar mutum shida (waDanda zasu zaBi halifa) kan su zabi Ali (a.s) don kar kawukan mutane su rarraba. [25] bayan kashe usman Ammar ya kasnace daga cikin mutanen da suka riKa kiran mutane zuwa yi wa Imam Ali (a.s) mubaya’a.[26]
A lokacin hukumar Imam Ali (a.s) ya halarci yakokin jamal da siffin. A yaKin jamal ya kasance jagoran mayakan kasa na hannun hagu, na rundunar Imam Ali (a.s). [27] kuma a rana ta uku a yaKin siffin ya kasance shi ne kwamandan sojin Imam Ali (a.s) baki Daya.[28]   
  1. A yaKin siiffin ne a shekata ta 37 bayan hijira Ammar ya yi shahada.[29] Bayan shahadar Ammar Imam Ali (a.s) ya yi masa salla. [30] shahadar Ammar a yaKin siffin a hannun sojin mu’awuya ta bangare Daya ta zama dalili kan kasancewar Imam Ali (a.s) kan gaskiya a wannan yaKin ta wani Bangaren kuma ta zama dalili kan kasancewa mu’awiya Dagutu ne, dalilin wannan mas’ala shi ne shahararren hadisin nan na Manzon Allah (s.a.w) da yake yin bayani ka waDanda zasu kashe Ammar a inda yake cewa: tarayyar ko gamayyar azzalumai ne zasu kashe Ammar (ma’ana gungun waDanda suka fita daga yi wa shugaba adali biyayya su ne sazu kashe Ammar). [31] Kuma wannan hadisin na daga cikin mafi ingancin hadisi wanda yake mutawatiri ne a cikin litattafn sunna da na Shi”a baki Daya. [32]           
 
 

[1] Abokin rantsuwa shi ne wanda aka kulla alkawarin da shi ta hanyar yin rantsuwa da Daukar alkawari kan duk masoyinsu to masuyin abokin rantsuwarsu ne. kama ma maKiyinsu kuma wanda ya yake su to su ya yaKa, dss.   
[2] Ibn Asir juzuri, Ali dan Muhammad, usudul gaba fi ma’arifatul sahaba j 3 shafi 626 bairut darul fikir 1409.
[3] Adreshin da ya gabata shafi 627; da Dabari abu Ja”afar  Muhammad Dan Jariri, tarihil umam wal muluk, (tarihul Dabari), j 11 shafi 563, bairut darul turas bugu na biyu 1387.
[4] Usudul gaba j 3 shafi 627.
[5] Wanda ya gabata; da balaziri ahmad Dan yahaya, ansabul Ashrafi, j 1 shafi na 158, bairut sarul fikri bugu na daya 1417.
[6] BaihaKi abubakar ahmad Dan husain, dala’ilun nubuwa wa ma’arifatu ahwali sahibul shari’a, j 3 shafi na 281, Beirut, darul kurubul ilmiyya, bugu na Daya, 1405.; ibni hajarul asKalani Ahmad Dan Ali, Al- Isaba Fi- Tamyizil Sahaba, J 4 sh 473, Beirut, darul kutubul ilmiyya bugu na daya 1425.
[7] Usudul gaba j 3 shafi na 627; yaKubi Ahmad Dan abi YaKub, tarihul; yaKubi, j 2 shafi na 28. Beirut daru sadirat bugu na Daya ba tarihin bugu.
[8] Surar nahli 106, Kumme Ali Dan Ibrahim tafsirul Kummi, j 1 shafina 39, Kum, darul kitab, bugu na uku, 1404.; usudul gaba j 3 sh 627.
[9] Ibni Hisham, Abdul malik, Al-sira annabawiyya j 1 sh 330 da 367, Beirut darul ma’arifa buguna Daya ba tarihin bugawa; Tarihil umam wal muluk, (tarukhul Dabari) j 2 sh 330; ansabul Ashrafi j 1 sha 211.
[10] Usudul gabati, j 3 sh 630.
[11] Ibni sa’ad kitabul waKidi, Muhammad Dan sa’ad, alDabaKatul kubra, j 3 sh 190. Beirut, darul kutubul ilmiyya, bugu na biyu, 1418.
[12] Ibni abdil barri abdul barri, yusif Dan Abdullah, al- isti’ab fi ma’afifatul ashab, j 3 shafi 1138, Beirut sarull jaili, buguna daya 1412; majlisi Muhammad BaKir, biharul anwar, j 31 sh 202 beirut, daru ihya’il turasul arabi, bugu na biyu 1403.
[13] Shekh saduK, ilalul shara’I’I, j 1 sh 223, Kum, furushi dawari, bugu na Daya 1385; muttaKa hindi al’uddin Ali bini husamul ddin, kanzul ummal fi sunanil aKwali, wal af’ali, j 3, sh 539, Beirut mu’asssar risala, bugu na biyar, shekarar 1401.
[14] Kanzul ummal, fi sunanil aKwali, wal af’ali, j 3, sh 539.
[15] Nobakhti, hasan Dan musa, firaKul shi’a sh 18, Beirut, darul adhwa’I bugu na biyu shekarar 1404.
[16] Tarikhul yaKubi, j 2 shafi 124. 
[17] Al’isti’ab j 3 sh 1136.
[18] Tarikhil umam wal muluk, (tarukhul Dabari) j 4 sh 144.
[19] Adreshin da ya gabata, sh 138, dinori, abu hanifa Ahmad Dan dawud, al-akhbaril Diwal, sh 134, Kum, manshuratil radhi, shekara ta 1368.
[20] Al’isti’ab, j 3 sh 609.
[21] Balaziri, aul hasan Ahmad Dan Yahaya, futuhul buldani, sh 274, Beirut, daru wa maktabatul hilal, 1988; zahabi, Muhammad Dan Ahmad, Tarikhul islam, j 3 sh 580, Beirut darul kutubul arabi bugu na biyu, 1409.
[22] Tarikhul yaKubi, j 2 sh 173, ibni a’asamal kufi, ahmad Dan a’asam, al-furuh, j 3 sh 378, Beirut darul adhwa’a, 1411.
[23] MuKaddasi, mudahhar Dan dahir, albada’u wal tarikh, j 5 sh 202 – 203, bur sa’id maktabatul sakafatul diniyya. Ba taruhi.
[24] Ansabul Ashrafi, j 5 sh 549.
[25] Albad’u wal tarikh, j 5 sh 191.
[26] Dusi, Muhammad Dan husain, al-amali, sh 728, Kum, darul saKafa, buguna Daya 1414.
[27] Shekhul mufidi, aljamal wal nasrah, li sayyidil itrati fi harbil basarah, sh 336, Kum, konKore shukh mufid, bugu na Daya.
[28] Ansabul Ashrafi, j 2 sh 303.
[29] Ansabul Ashrafi, j 2 sh 303 da usudul gaba, j 3 sh 632.
[30] Al-dabaKatul kubra, j 3 sh 198.
[31] Al-dabaKatul kubra, j 3 sh 190 - 192.
[32] Al’isti’ab j 3 sh 1140.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa