Please Wait
Dubawa
12231
12231
Ranar Isar da Sako:
2011/03/31
Takaitacciyar Tambaya
mene ne Hikimar Tashahud da Kuma Sallama?
SWALI
mene ne Hikimar Tashahud da Kuma Sallama?
Amsa a Dunkule
Asirin da ke boye a cikin tashahud shi ne daidaita abin da harshe ke furuci da shi da kuma abin da zuciya tai imani da shi wato daidaita furuci da kuma aiki alokaci daya, ta wata fuska kuma shi ne fita daga wannan tsarin na duniya da komawa zuwa ga Allah shi daya makadaici wato kusanci gare shi abun bauta {mukamin wulaya}.
Sallama na daya daga cikin sunayen Allah madaukaki, sai ya sashi a cikin halittunsa domin bayinsa su rika bayyana suna, a cikin ko wane hali ta hanyar mu'amala yau da kullun da zamantakewa da amana da sauran al'amuransu na rayuwa ta yanda zai zamo abun Ambato {sallama} a tsakaninsu. Su kuma bayyanar da sunan a cikin maganganunsu da kuma aiyukansu. Wato su bayyanar da hakikanin sallama a cikin zuciyarsu da furucinsu da al'adunsu da kuma akidunsu da halayensu domin su tsira daga sharrin shaidan. Hanyar samun wannan tsarin ita ce tsoron Allah {takawa}. Dukkan wanda ya siffantu da takawa {tsoron Allah} Allah zai tsarkake mashi addinisa da hankalinsa da ruhi da kuma zuciyarsa kai da dukkanin gabobinsa daga zunubi.
Ya zo a cikin hadisi daga imam Sadiq (a.s)

Amsa Dalla-dalla
Hikima da Asirran Tashahud;
Tashahud, tsarkake Allah madaukakin sarki ne maimaita shi {tashahud} na nufin sabunta da kuma jaddada shahada ne da Allah da kuma manzonsa mai daukaka kuma jaddada imani ne da kuma musulunci, yayin da bawa yake furuci da Kalmar shahada a aiyukansa kuma yana aiki da Kalmar. Ita wannan Kalmar yayin da mutun yayi furuci da ita to ya zamar masa dole yayi aiki da a cikin kowane bangare na rayuwarsa ya zamo bawan cikkake mai biyayya ga umurni da hani na Allah madaukaki, saboda ka sani komai yana hannunsa babu wani abu ko wani aiki da zai faru ba tare da ikonsa ba sannan babu wani iko da ke da karfi a cikin wannan duniyar face shi.
Masallaci a yayin da yake tashahud cikin salla, bayan ya shaida da kadaita da kuma daukakar Allah mai girma sai kuma ya tabbatar da manzancin annabi Muhammad (a.s) cewa shi cikakken bawa ne na Allah kuma manzonsa kuma shi ne cikamakon annabawa (a.s), gabatar da bauta a kan risala {aike} saboda bauta wa Allah madaukakin sarki tana sama da dukkan wani mukami a wurin Allah mai girma da daukaka, manzanci wani bangare ne na bauta. Saboda manzon Allah mai tsira da aminci bawa ne cikake na Allah madaukaki, biyayya gare shi biyayya ga Allah ne kuma dole ne mutun ya kiyaye wajan yi wa manzon Allah (s. a. w) biyayya ya zamo bai takaita ba domin da'a ga manzo da'a ne ga Allah mai girma, soboda haka domin neman kusanci ga Allah mai girma da daukaka ya zamo dole mutun ya yi wa manzon sa mai tsira da aminci cikakar biyayya. Ka san cewa ta hanyar tawassali da manzon Allah da kuma imamai masu tsarki ne mutun zai samu kusanci ga Allah madaukaki[i].
An tambayi imam Sadiq (a.s) dangane da hikimar tashahud, sai ya ce: Tashahud a salla, yabo ne ga Allah madaukaki. Don haka ya kamata bawa ya sa Allah a cikin zuciyarsa, kuma ya zamo mai kaskanta da kai yayin da yake tashahud kamar yadda yake furuci da kadaitakar Allah da annabcin manzonsa mai tsira da aminci a harshensa da kuma addu'a, dole ne ya yi imani da abin da ya furta a cikin zuciyarsa. Abin da harshe ya furta dole ne zuciya ta yi imani da shi kuma ya zamanto ya ratsa zuciyar ya shiga har cikinta. saboda kai bawa ne na Allah mai girma shi ne kuma ya samar da kai {halitta} saboda ka bauta masa a furuci da zuciya a bayyane da boye. Da dukkan gabobi ka zamo mai yi wa Allah biyyaya da su, domin ka nuna kai bawa ne shi kuma ubangijinka ne. Kuma da burin cewa samuwa da rayuwa da yake ba ka kar ta yanke, kai kuma {bawa} bautar da yake masa kar ya yanke. Saboda haka bawa ya kamata ya zamo mai godiya ga Allah madaukaki a cikin ayyukansa kamar yadda yake furuci a harshe. Ya sallama wa umarnin Allah ta hanyar bauta masa kuma ya yi wa manzon Allah mai tsira da aminci salati da 'ya'yan gidansa kamar yadda Allah ya ummurce shi da yi, saboda haka a cikin salla dole ne mutun ya yi salati ga annabi mai tsira da aminci ya kuma hada biyayyar sa da biyayya ga Allah ta kadaita shi wurin bauta da kuma shaidawa da sakon sa mai tsira da aminci a wuri daya domin samun albarka wannan bawa nasa {annabi mai tsira da aminci}[ii].
A takaice, sirrin tashahud shi ne daidaita furucin harshe da iqrarin zuciya wato furuci da aiki ta wata fuska kuma fita daga cikin wannan duniyar ta samuwa zuwa ga samuwa daya wadda ba ta da na biyu {wato samuwar Allah madaukaki} da kuma kusanci da shi domin isa ga matsayin walitaka wato soyayyar ubangiji.
Hikima da Asirin Sallama
Kalmar sallama asalinta silm ne wato amintuwa daga miyagun abubuwa na fili da na boye[iii].
Dukkan wanda ya mika wuya ga umarnin ubangijinsa ya kuma yi aiki da kaskantar da kai ga sakonnin da manzon Allah mai tsira da aminci ya zo da shi, tabbas zai samu tsira daga bala'un duniya da na lahira; saboda ba zai taba faruwa ba mutun ya cika sallarsa kamar yadda aka ummar ce shi kuma ya zamo bai shiga cikin rahamar ubangiji ba, kuma ba zai yiwu ba mutun ya fahimci hakikanin sallama wadda daya ce daga cikin siffofin ubangiji kuma suna ce daga cikin sunayen Allah madaukaki amma ya zamo a cikin zamantakewarsa da mutane ya kasa aikata ita wannan sallamar kuma ba zai yiwu ba mutun ya zurfafa a cikin kusanci ga Allah madaukaki ta hanya salloli da karatun addu'a kuma ya sa Allah a cikin zuciyarsa amma kuma ya kasance a cikin rayuwarsa ta yau da gobe ya manta da shi Allah din, domin hakikanin bauta shi ne tunawa da Allah madaukaki a cikin kowane hali mutun ya samu kansa.
Hadisi mai tsawo ya zo daga imam Sadiq (a.s) akan asirin dake cikin sallama {tashahud a cikin salla} ga shi kamar haka a takaice; Ma'anar sallama a cikin salla, shi ne tsari da kiyayewa; wato duk wanda yai aiki da umarnin Allah da kuma sakon da manzon sa mai tsira da aminci ya zo da shi a cikin kaskantar da kai, to zai samu tsari daga bala'oin duniya da kuma tsira daga azabar lahira. Sallama suna ne daga sunayen Allah (a.s) ya kuma sa shi ya zamo amana a cikin bayinsa domin su yada shi a cikin rayuwarsu da zamantakewa kuma su siffantu da wannan siffar su zamo masu aminci da amincewa a tsakaninsu su kuma tsarkake addininsu da ayyukansu da zukatansu daga sabo da duhu domin dukkan wanda bai aiki da hakikar sallama ba kuma ya ki tsarkake addininsa da zuciyarsa da hankalinsa daga sabo da zunubi to sallamar sa ta zamo ta karya kuma sallamar ta salla ce ko ta cikin mutane ce; domin dukkan wanda zai furuci da kalma amma ya kasa aiki da ita a aikace to shi wannan mutumin makaryaci ne[iv] ''.
Saboda haka sallama suna ne daga cikin sunayen Allah (a.s) ya sa shi a cikin bayinsa domin su bayyana shi a cikin tsamantakewarsu ta yau da gobe, kuma su siffantu da ita fili da boye; kuma su karfafi gabobinsu na fili da na boye da kuma dukkanin al'adunsu da akidunsu da tarbiyarsu domin su aminta daga yaudarar shaidan. Hanyar samun wannan aminci ita ce tsoran Allah (a.s). Duk wanda ya siffantu da siffofin tsoran Allah, addininsa da ruhinsa da hankalinsa da zuciyarsa da dukkanin gabobinsa na fili da na boye zasu kasance cikin aminci[v].
A cikin salla akwai wasu asirai wadanda muka yi nuni wasu a cikin ruwayoyi masu muhimmanci a matsayin salla wurin gina mutun addinin musulunci ta hanyar yin wannan farillah mai muhimmanci da fahimtar asiran da ke ciki ne za a iya samu kyakkyawar rayuwa ga daidaikun mutane da al'umma baki daya. Kuma a samu rayuwa mai rabauta da arziki da zaman lafiya karkashin soyaryar ubangiji.

[i] Imam khumaini , ruhullah , adabu sallat , babi na bakwai a cikin takaitacen bayani akan tashahud , bugawa da yadawa mu'assasar asar imam khumaini { r . d }
[ii] Majalisi , Muhammad bakir , beharl anwar , jildi na 82 ,shafi na 284 zuwa da 285 , mu'assasr alwafa , berut , 1404 g : imam sadiq { a . s },jafar bin Muhammad { a.s} musbahul shari'at, shafi na 93 zuwa 94 , mu'assasar al'alimi lilmatbu'at , bugu na daya 1400 k
[iii] Farhadi , khalil bin ahmad , kitabl ain, jildi na bakwai shafi na 265, yadawa hijarat , qom , bugu na biyu .1410 k: ibin manzur , Muhammad bin mukaram , lisanul arab, jildi na 12 , shafi na 389.sader bairut , bugu na ukku . 1414 k; kureshi , sayyid Ali akbar , kamus kur'an , jildi na ukku , shafi na 296 , darulkitab islami. Tehran, bugu na shidda , 1371 sh.
[iv] Musbahul shari'at , shafi na 95 zuwa na 96; baiharul anwar ,jildi na 82, shafi na 307 da 308.
[v] Adabu sallat , babi na takwas a cikin adabu salam.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga