Please Wait
12889
A cikin koyarwar musulunci, mata suna da matsayi na musamman, ruwawoyi na manzon Allah da a imam[a. s] sun yi bayanin a kan hakan. Ya zo a cikin ruwayoyin mu cewa mata salihai tushe ne na alkhairi da albarka kuma suna cikin abubuwa masu daraja da kima a cikin rayuwar duniya.
Musulunci ya yi hani a kan ladabtar da mata, duk mazajen da ke aikata hakan suna cikin munanan hallitu.
Sai dai guri daya ne musulunci ya yarda a ladftar da mata wadan da suke take hakkokin mazan su kuma an bi ta kowace hanya domin shiryar da su amma bai yi amfani ba.
Nushuz[guje ma muji wurin kwanciya] na mata da kuma ba da izini na dukan su wanda a kayi nuni a cikin aya ta 34 suratul nisa.
A cikin wannan ayar da farko anyi bayanin siffofin mata na gari masu biyayya. Sai kuma Allah ya yi ma mazajen da matan su ke nushuz bayanin nauyayain da suka doru akan su.
Mataki na farko shi ne wa'azi. Mataki na biyu nisantar su wurin kwanciya wannan matakin yafi na farko tsanani. Mataki na uku shi ne duka. Amma a wannan matakin dole ne mu kula da wasu abubuwa kamar haka:
1. wannan shi ne matakin na karshe amma in matakai biyu na farko suka yi aiki to bai dace ba a dauki matakin duka ba.
2. ladaftarwar jiki; akan asashin litafan fikihu, dole dukan ya zamo marar cutarwa wanda ba zai nuna alama ko rauni ba ko karaya ga jiki.
3. ladaftarwar jiki; yana da matakai ya zo a ruwaya cewa ana iya duka da asawaki. In wannan matakin ya biya bukata to bai dace ba a dauki matakin da yafi wannan tsanani ba.
4. wannan mas'alar bata takaita ba a kan mata kadai ba harda mazan da ba su dai dai tuwa da matan su hakim shar'I yana iya daukar duk matakin da ya dace ko da na duka ne domin ya fahimtar da wadannan mutane irin munana ayukan su.
Kafin mu yi bayanin mahangar masu tafsire akan Kalmar [ku doki mata] wadda ta zo a cikin aya ta nushuz.
Ya kamata mu yi nuni da matsayi da kuma darajar da musulunci yaba mata.
Koyarwa madukakiya ta addinin musulunci taba mata da mazajen su matsayi da darajoji masu yawa.
Ya zo a ruwaya, imam sadik[a. s] mafi yawanci alkhairi da albarka sun taru akan su[1].
Imamin shi"a na shida ya kasa mata ya zuwa kashi biyu masu kyau da munana {alkhairi da sharri} amma mata na gari sai ya ce: darajar su tafi zinari da azurfa ba wani abu mai daraja wanda ya kai su daukaka[2]..
Manzo Allah[s. a. w. ] ya ce: duniya gida ne najin dadi mafificin abun jindadi a cikinta su ne mata na gari.
Darajojin da ke tatare da mata anyi nuni cewa su magudaniyar alkhairi ne da albarka wannan yabo da bayane na masumai[a. s] suna nuni ga matsayi na samuwa da na badini wanda yafi duk wani abu mai daraja da ke cikin wannan duniyar daukaka[3].
Rashin halarcin ladabtar da mace:
Mulura da abubuwa muhimmai a nan: saboda duka da takura ma mata a dokoki na musulunci yana dai dai da mutumin daya aikata laifi ga iyalin shi. Mata kamar maza suma halitune masu daukaka da kima. Saboda haka dukan jikin su kamar dabobi bai halarta ba saboda ba dabobi ne ba su zukata ne masu rauni cike da kauna halitune madaukaka shi ya sa manzon Allah (s.a.w) wanda ya zo da musulunci ya haramta ladabtar da su.
Yana cewa: ku kiyaye su amana ce ta Allah a gurin ku yaku mutane ku sani cewa matayen ku da sunayen Allah na musamman suka zamo halal a gurin ku shin ya dace wannan amanar abun so da kauna ta zamo abun duka da cutarwa[4]?.
Ya kuma ci gaba da cewa: daya daga cikin alamomin mugun mutun shi ne wanda yake dukan matar shi da bawan shi, kuma bai zamo mai tausiyi ba gare su[5].
Amma wasu bangare na mata ba su kasance masu kiyaye hakkokin mazan su ba, kuma ba su biyama shi bugatar shi a gurin kwanciya suna fita gida ba tare da izinin ba. Munanan halayen su ya maida gida wanda yake cike da rahama ya zamo kamar jahannama suna ma mazan su shishigi a bisa a bunda be shafe su ba har kuma su yi tasiri akan mazan. Bangare na irin wannan matan a mahangar musulunci ba su da wata daraja, kuma addini ya yi Allah wadare dasu. Mazon Allah (s. a. w) yana cewa: mafi muni a bu a cikin wannan duniyar samuwa su ne miyagun mata[6].
A harshen Kur’ani da hadisi da kuma fik‘hun musulunci irin wadannan matan su ne ake kira nushuz {masu gudun mazan su} wanda girman kan su ya kai su ga haka. A takaice irin nau'in wadannan matan ba su yima mazan su biyayya sun mai da rayuwar mazan su ta zama mai daci da wahala. Addinin musulunci mai tsarki ya kawo hanyoyi na hankali domin ladabtar da irin wadannan matan. Kur'ani mai girma a cikin aya mai daukaka[ ayar nushuz] ta cikin suratul nisa ya yi nuni da wasu abubuwa muhimmai masu kyau a cikin rayuwar ma aurata da al'amuran gida wanda wasu ulum din zamani sun gano wasu bangare na sirin dake cikin ayar a hakika wannan ayar na cikin mu'uzizojin ilimi dake cikin Kur’ani mai girma. Ko da yake Kur’ani na dauke da mu'uzizoji daban daban.
A bayyane yake abin da ya shafi rayuwar gida musamman ma aurata ta na dauke da sauki da soyayya wanda ya kama ta ya bayyana a fuskoki da kuma boye fushi da bayyana so a fili. Kiyaye wadannan abubuwa biyun wato so da kuma gaba yana da wahala so sai. Falasafa da masana ilmin zaman takewa da tarbiya da masana ilmin tunani sun yi kokari da rubuce rubuce da yawa wajan gano hikimar da ke tsakanin ma aurata. amma kwarewa ta Kur’ani da ruwayoyin manzon Allah (s. a. w) da ahulbait [a. s] wanda a tagaice yake nuna ma dan Adam abubuwa masu muhimmanci cikin sauki da hikima wanda kowa zai fahimta ya kuma aikata ba da wata matsala ba.
A cikaken bincike da tantancewa na ayar 34 na suratul nisa mai daukaka dole ne mu yi nunin wasu abubuwa masu yawa. Amma a takaice abin da za mu iya cewa, shi ne a ayar madaukakiya nauyayain da ya doru na tafiyar da gida da kuma kiyaye bukata da abubuwan yau da kullun[ abinci] na gida yana a kan namiji, amma nauyin da ya doru akan mata na tafiyar da gida ya kasu kasha biyu.
Kashi na daya: salihai masu gaskiya: su ne basa wasa da nauyin da ya doru akan sun na tafiyar da gida kuma ko da ma mazan su ba su tare da su suna masu kiyaye wadannan nauyaye. A fili yake mazaje game da iran wadannan matan su zama masu girmama su da kiyaye gaskiya a tsakani.
Kashi na biyu: su ne matayen da ba su biyayya da kin aikata abun da ya doru akan su. Dan gane da irin wadannan matan Kur’ani ya yima maza bayani matakin da ya kamata su dauka daya bayan daya a kai ta kowace hanya dole su kiyaye kar su wuce hanya wato adalci. Ga marhalolin kamar yadda aya tai bayani:
Matakin farko: matayen da kuke gudun kaucewarsu to ku yi masu nasiha musamman ga wadan da suke kaucema tsarin gida to ya kama ku tunatar dasu ta hanyar abokantaka da kuma nuna masu munanan sakamako na aikin da suke a kai da kuma fahimtar nauyin dake kan su.
Mataki na biyu: in nasiha batayi amfani ba to ku nisance su gurin kwanciya aikata hakan yana nuni da rashin yardar miji akan halayen matarshi kila da haka wato nisantar kwanciya ya yi tasiri ga ruhin ta.
Mataki na uku: wazrbuhunna: [ ku bukesu] ladaftawar ta jiki, idan ta ki aikata nauyayan da suka doru akan ta da wuce gona da iri[ fita daga hadi] da kuma karya dokoki da gan_gan, wanda nasiha ko nisanta bai amfani ba to hanya mafi tsanani shi ne matakin gaba wato duka domin dawo da ita akan da'a da sanin nauyin da ke kanta.
Ba mamaki wani ya ce tayaya musulunci ya ba maza dama akan su doki matansu? Amsa shi ne bawani abu ne mai wahalar ganewaba in muka lura da ma'nar aya da ruwayoyin da suka zo da kuma bayani da ke cikin latafan fik'hu da kuma bayanen masana ilmin tunani ayau suka yi akan wannan mas'ala, saboda:
Na farko: ayar ladaftarwa na jiki akan matan da ba su aiki da abin da ya doru akansu kuma ba wata hanya da za'abi mai amfani domin farkar dasu. Sannan ba wani sabon abu ba ne wanda wa kadaita da musulunci ba a dokoki na duniya duk lokacin da hanyar sauki ko lalama ba tai aiki ba to dole a sa matakin tsanantawa.
Na biyu: ladaftarwa ta duka kamar yanda ya zo a litafan fik'hu dole ya zamo mai mai sauki da taushi wanda bazai kai ka karaya ko jimata rauni ko kuma alam ta bayana ajikanta ba.
Na uku: masana ilimin tunani na zamani, suna da imanin cewa wasu matan suna dauke da wani hali na nai man cutarwa, to in wannan halin ya tsananta gare su hanyar ladabtar dasu shi ne duka marar cutarwa. Saboda haka ba mamaki wannan ayar ta zamo tana bayanin irin wannan mata ne wadan da dole sai an doke su sannan su yi ladabi kila shi ma wani nau'i ne na magani a tunanin su wanda musulunci ya fara da nasiha ko nisanta ko kuma duka mai taushi domin magance wannan ciwan ba wai dan rabuwa ba saboda rabuwa na kawo fashewar gida da kuma haramta ma yaya tausayin da ya kamata su samu ga iyaye koma ya kan kawo rushewar al'uma.
Tabas indan daya daga cikin wadannan matakan suka yi tasiri kuma yasa mace ta fahimci nauyin dake kanta. Muji bai da wani dalili na cutar da ita. Wata jimla na cewa: in sun yi biyayya kada ku keta hakinsu.
Abun lura a nan shi ne haddi a cikin ladaftarwa jiki kada ta kai ka karaya ko rauni ko kuma alama ta bayyana ga jikin mace. Amma hadafi a nan shi ne dawo da mace akan da'a da biyayya da kuma barin halin nushuz[ kujema muji]. Don haka dole ne a kiyaye wadannan matakan in manufa da duka mai sauki ya biya bugata to mataki mai tsanani bai halarta ba. Ba mamaki ruwayar ku doki matan ku da asawaki[7] yana nufin kiyaye marhaloli ne na dukan a lokacin da aka yi nuni da wannan marhalar ma'ana amfani da asawaki, to bai dace ba a dauki matakin da yafi wannan.
Ba mamaki wani ya ce a cikin mazaje akwai masu irin wannan halin na wace hadi to suma irin wannan hukunci yahau kansu?
Amsa sai mu ce eh haka ne mazama kamar mata suke yayin da suka ki da'a da kin biyyaya suma za a hukun tasu, amma abun lura a nan shi ne irin wannan haling a wasu mazan nau'ine na ciwo[ son cutar da wasu] in cewon ya yi tsanani maganin shi ba shi ne duka bat a hanyar mace: saboda da farko mafi lokaci duka baya maganin irin wannan ciwon. Na biyu mafiyawan mata basa iya aikata hakan[wato horar da na miji]. Na uku: hakim shar'i ya doru a kan shi hukunta mutane masu laifi ko da ta hanyar ladaftarwa[ duka ]domin su san nauyayen dake kan su.
Allah madaukaki daga karshe wannan ayar yana mu a maza gargadi da cewa kada su yi amfani da damarsu na masu gida su cutar da iyalin su. Su yi tunani da ikon Allah wanda yake sama da kowane iko' saboda Allah mai girma ne abun girmamawa[8].
[1] Alkasirilkhai fi nisa, mallayahzarulfakih, jildi na 3, shafi na 385.
[2] Alkafi, jildi na 5, shafi na 332.
[3] Mustadarakulwasail jildi na 14, shafi na 150.
[4]. Mustadarakulwasail jildi na 14, shafi na 252
[5] Tahzibul ahkam, jildi na 7, shafi na 400
[6] 165 Mustadarakulwasail jildi na 14, shafi na
[7] Tafsirin burhan, jildi na daya, shafi na 367, {wanda a ka samo da ga tafsirin fazil, jildi na daya, shafi 523}
[8]Daga tafsirin namune, jildi na 3, shafi na 411-416.