advanced Search
Dubawa
14790
Ranar Isar da Sako: 2012/05/05
Takaitacciyar Tambaya
Duk da yawan hadisai wadanda aka ruwaito daga Imaman nan biyu wato Imamul Bakir da Imamus Sadik (a.s). amma duk da haka ba a rubuta su cikin littafi guda daya mai cin gashin kansa ba?
SWALI
ana cewa mafi yawan hadisanmu an ruwaito su ne daga Imaman nan biyu wato Al Bakir da As Sadik (a.s), amma ban jib a cewar an tattara wadannan hadisai cikin wani littafi mai cin gashin kansa ba kamar ydda Sayyid Sharifur-Radi ya tattar a hudubobi da zantukan Imam Ali (a.s) cikin littafin Nahajul-Balagaba. Ina neman a aikomin sunan littafin (Hadisan Imamuan can biyu) in har akwai.
Amsa a Dunkule

Idan muka yi duba a nutse, a kan irin lokutan da wadancan Imamai guda biyu (a.s) suka yi rayuwar su, za a fahimci dalilin da zai sa zai yi wuya a samu daman rubuta hadisansu cikin wani littafi na musamman. Amma dai wannan baya nufin cewa al’amarin ya ci gaba har zuwa wasu zamuna da suka zo a bayansu, domin an tattara wadancan hadisai aka kuma rubutasu, cikin littafan da ake kira da “Usulul Arba’a mi’at” (Wato Usul dari Hudu), sannan aka sake tattarasu cikin littafai na tushen addini, wato sanannun littattafan hadisan nan na shi’a guda hudu. A karshe, sai ga Ayatullahi Hurul Amuli ya sake tattara wadancan hadisan cikin littafinnan nasa mashahuri mai suna “Wasai’lul shi’a” wanda yakai mujjalladai talatin. Ya ware hadisan ya tara su cikin babobin da suka dace, bisa asasi na fikihu. Haka nan akwai cikakkun littafan hadisai Imaman guda biyu kamar littafin “Musnad Imamul Bakir” da “Musnad Imamus Sadik” tailfin Azizullahi udaridi, akwai “kitabul tauhidul-mufaddal” da “dibbul-Imamus Sadik”.

Amsa Dalla-dalla

Amsa game da tambayar can shi ne, dole ne a lura da halin da zamunan da Imaman can suka rayu cikin su, bugu da kari da irin ra’ayoyin sauran mazhabobin musulunci game da su Imaman. da dalilin rubuta hadisai, hudubobi da zantukan Imamu Ali (a.s) cikin litttafin Nahajul-Balga” da rashin samun wani littafi guda daya tsayyaye wanda aka tattara da hadisan Imamul-Bakir ko Imamus Sadik (a.s) duk wannan na komawa zuwa ga wasu al’amira kamar haka:

  1. Cewar Imam Ali (a.s) shi ne Imami guda daya tilo da ya samu damar zama Khalifa cikakke, duk da cewa zamanin Khalifancinsa bashi da tsayi (Kamar sauran Khalifofi) lokacin da ya Khalifanci al’umma na tsawon shekaru biyar. A wannan lokaci, linzamin al’amuran musulmi na hannusa. Saboda haka yana da cikakken iko da ‘yancin karantar da al’umma ta hanayar dogayen hudubobi, wa’azozi, wasiku da sauran nasihohi da suka shafi al’umma. Haka nan a wancan lokaci maruwaita da marubuta na da cikkakken yancin ruwaitowa da rubuta hudubobin Imam, duba da cewa shi ne shugaba mai cikakken iko a lokacin, ta wani bangare kuma, sauran bangarorin musulmi na kallon Imam a matsayin daya daga cikin Khalifofin nan hudu, saboda haka suke nakaltar zantukansa a matsayin sa na Khalifan Manzo ko da kuwa ba su kallonsa a matsayin Imamin da ya wajaba a yi masa da’a kamar dai yadda shi’a ke kallonsa. [1]
  2. Haka yake cewa Imaman nan biyu Bakir da Sadik (Alaihimas salam)

sun sun yi amfani da dammar zamanin raunin karshen rushewar daular Banu Umayya da farkon kafuwar daular Abbasiyya. Don yadawa da bayyana asasi da ilimomin addini, ta hanyar tarbiyantar da dubban dalibai a wancan zamanin, amma duk da wannan yanayin ba su samu dammar kamar irin dammar da Amirul mumina Ali (a.s), ya samu ba. Na jagorantar gwamnati, Saboda haka suka dinga samar da wata hanya mai takatsan-tsan don kariya ga rayukansu, mabiyansu da ‘yan shi’arsu, da kuma kariya daga fadawa cikin hadari, da janye duk wata dama daga hanun magauta, don kada su yi mummunan amfani da wata dama don cutar da su.

Don haka ne za mu gansu, sun hanu daga yin hudubobi dogaye kamar yadda Imam Ali (a.s) ya kasance yake yi. Suka wadatu kawai da amsa tambayoyin da al’umma kan jefo musu. Yana da kyau mu ambaci cewa Imamul Bakir (a.s) ya kasace yana yin tsani (a wasu lokuta) wajen yada ruwayoyinsa ta hanyar nakaltowa daga sahabin nan Jabir bin Abdullahi daga Manzon Allah, (Sallal lahu alaihi wa alihi)

ko kuma da wasidar Amirul Muminin (a.s), ba kome ya sanya shi haka ba face don ya kwantar da duk wani tada jijiyar wuya ya kuma samar da yanayi nutsattse don sauran al’ummar musulmi su karbi ruwayoyinsa. [2]

  1. Kuma haka ne cewa abin da aka ruwaita daga Amirul Muminin Ali (a.s) da imamannan biyu (Watau Al Bakir da As Sadik (a.s) ba a tattara shi a cikin littafi guda ba a lokacin rayuwarsu. Sai dai kowanne maruwaici yana rubuta abin da ya ruwaita da Imamin (a.s), kamar yadda ake kiran wadan nan littafai da sunan “Al-Asl” san nan sai mai ruwaiya ya bijirar da hadisan ga waninsa (wato sauran maruwaita). Hakika Allama Majlisi (RA) ya yi nuni da sunannakin wasu daga cikin wadancan “Asul” din ya kuma ambacesu da “Al-majami’ul Auwaliyya”. Kamar yadda ka ambata a tambayarka cewa mafi yawan ruwayoyin sun kasance daga Imaman nan biyu ne (a.s), to wannan bai kasance ba face dama da ‘yancin yanayin, da suka samu a lokutan rayuwarsu.
  2. Kuma lokacin rayuwar Imamai (a.s) babu wani bukatar a rubuta littafai masu cikakkun babobi, wanda ya tattara dukkanin hadisai. Sai dai bukatuwar hakan ta zo ne bayan fakuwar Imamul-hujja (AF) lokacin da saduwa dasi (AF) ta kai tsaye ta yanke. Tun daga nan ne kuma bukatuwar tattarawa da wallafa littafai na hadisai da sauran Usul suka yawita, saboda haka aka samu cewa mafi akasarin manyan littafai na hadisai, an rubuta su ne a tsakanin karnoni na uku zuwa na biyar bayan Hijira. Daga cikinsu akwai” kutubul arba’a, da irin su “Tuhaful-Ukul”. Hakanan ma littafin Nahajul Balaga”. Wasu kuma daga cikin wadancan littattafan sun kunshi ruwayoyin dukkan ma’asumai (a.s), da wasun su, kuma sun kunshi ruwayoyin dukkan ma’asumai wasun su kuma sun kebanci hadisan ma’asumi guda daya kadai, kamar littafin Nahajul Balaga da “Gurarul-Hikam”.
  3. Hakanan abin da malaman Fikihu da masu zurfin bincike suke bukata na daga ilimomi na musulumci shi ne rarraba ruwayoyin a’imma na daga hadisai zuwa fasali da babobi bisa mauru’o’in ilmi, amma ba tattara hadisan kowanne Imami (a.s) cikin littafi guda mai cin gushin kansa, mai dauke da sunansa ko da yake yin hakan ma yana nasa irin fa’idar. To amma idan muka yi dubi da cewa zantuttukan ma’asumai (a.s) gaba daya sun yi tarayya na zamowa kalaman su hujja ce, da kimar ilimi na zamowa hujja duka iri daya ne, ta yadda babu wani bambanci ba a tsakaninsu, a wani bangare kuma a mafi akasarin lokuta, su malamai don kawar da shubhohi, da mushkilolin, da warware matsalolin da suke kawo musu cikas a game da fikhu, da tauhidi dss sukan rika komawa cikin wadancan littafai don fa’idantuwa daga gare su na daga babobi da fasaloli wadanda aka rarraba ruwayoyi a kansu don su amfanu da su. daga nan za a fahimci dalilin da yasa abubuwwan da suke hanun mu, suke da irin wannan babbar kima ta ilimi.
  4. Kuma suma sarakunan Abbasiyawa a lokacin mulkin su yanayinsu kamar yanayin sauran Ahlus-sunna wadanda basa jin wani dar dar a cikin al’amarin Imam Ali (SA). Hakan ne ya sanya shariful-Radi (RA) ya yi yunkurin tattara kalamn Amirul-muminin (a.s) cikin littafin da ya rada masa suna “NAHAJUL BALAGA” a kuma babbar birnin, mulkin Abbasiyawa wato garin Bagdad. Haka nan kuma Sayyid-Radi (RA) bai samu wani raddi ba ga wancan aiki nasa. Wannan kuwa saboda da yawa daga cikin abin da ya rubuta na nan fal a cikin littafansu su[3] kansu Ahlussunnah. Sai dai zai yuwu rubuta littafin da ya kunshi ruwayoyin Imam Bakir da Sadik (a.s) a lokacin mulkin Abbasiyawa, musamman ma Imamus-Sadik (a.s) [4]zai iya jawo “jan idon” sarakuna na wancan lokacin, Haka nan na sauran Imaman da suka biyo bayansa. Kuma rubuta littafi irin wannan zai kunshi hujjoji da ruwayoyin dake karfafa dalilan nassin halifancin kawai ga ‘ya’yan ali (a.s), wannan kuwa zai ci karo da kwadayin mulkin Abbasiyawa. A dalilin haka haka malaman shi’a suka rinjayar da wallafa littafai irin na wannan sananniyar hanyar da ke hanu.

Wato yin wallafar da take tattara ruwayoyin dukkanin a’imma da kuma sauran hadisan Manzon Allah (SAW), da kalmomin Amirul Muminin Ali (a.s). Kamar dai yadda Sikatul-islam al-kulaini ya wallafa “Alkafi” ko littafin At-tahzib da al fakih da wanda an yi hakan ne don sassauta dardar din da wasu da suka saba musu zasu iya samu.

  1. Haka nan irin wannan al’amarin aka ci gaba da shi a karnonin da suka biyo bayan. kuma kundayen littafin hadisai da aka wallafa a baya kamar littafan “Wasa’iulsh-shi’a”. da“Biharul Anwar” dss. Hakika kididdigan ruwayoyin da aka tattaro daga Imaman nan biyu (Wata Bakir da Sadik (a.s) ) sunfi na sauran Imamai (a.s) yawa, Sai dai babu wata bukatar rarrabesu daga waninsu. Kuma a shekarun da suka wuce na kusa-kusa damu an samu kokarin fitar da ruwayoyin da suke na kowanne Imami (a.s) kamar “Musnad Imamul-Bakir”, da Musnad Imamus-Sadik” (a.s) wallafar Azizullhai uddiridi. [5] Kowannensu kuwa ya kunshi mujalladai, hakan akwai yunkurin wallafa littafan hadisan sauran a’imma (a.s) wanda muke fatan samuwarsu nan ba da dadewa ba.

 


[1] Wannan maganar bata shafi masu akidar nasibawa da khawarijawa wadan da dama su ‘yan tsirari ne a cikin al’ummar musulmi.

[2] Rijalul kish shiy shafi na 14 na yadawar jami’ar mash had shekarar hijira shamsiyya ta 1348.

[3] A duba littafin ibnu abil hadid, sharhin littafin nahjul balagah, juzu’I na 1, shafi na 204, ofishin Ayatullahi mar’ashin najafiy, kum, shekarar hijira shamsiyya ta 1404

[4] A duba littafin biharul anwar wallafar Muhammad bakir al majlisiy, juzu’I na 47, shafi na 162, babi na 6, na kamfanin, mu’assatul wafa Beirut, labanon. shekarar hijira shamsiyya ta 1404

[5] Shi mawallafin ya yi kokarin ya yi irin wannan aikin game da sauran imamai.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa