Please Wait
11436
Wannan ayar na nuni da halin da mujurumai suka samu kan su bayan an busa kahon tashin kiyama suna tambayar junan su kwana nawa mu ka yi a duniyar barzahu? Mujurumai sana tunani a duniyar barzahu kwana daya ko kuma kwana goma su ka yi sai wasu su ka ce kwana daya wasu kuma su ka ce kwana goma. Saboda zamani da lokacin da a ke zayawa a duniyar barzahu in a ka hada rayuwar lahira za a ga lokacin kadan ne {wato duniya barzahu in a ka hada da duniyar kiyama sai mu ga duniyar barzahu ba komai bane}.
Don haka kur'ani yana kwatanta rayuwar barzahu in a ka hada da ta lahira kamar kwana daya ne na lahira.
Domin samun Karin haske a cikin jawabin ya kamata a kawo fassarar ayoyin; ranar da a ka busa kaho za a tashi mujurumai da tabunna ajikin su zamu tara su a wannan ranar {102} sai suna tambayar junan su a hankali {wasu suna cewa} kun kasance kwana goma ne {dare da rana a duniya barzahu} {ba su sani ba zun zauna lokaci mai tsawo} {103} mu mun kasance masu sani a kan abunda suke Magana a kai, a lokacin da masanin su yake cewa: {kun tsayane kwana daya kawai} {104}
Idan mu ka yi amfani da ayoyin kur'ani mai girma zamu fahimci karshen duniya zai faru ne da canji biyu kuma ba tsammani kuma kowane daga ciki su a bayyana yana farawa da busa kaho.
A lokacin da a ka busa kaho mujurumai saboda tsoro da firgita da suke ciki a yayin da suka ga filin kiyama {tashin kiyama} ko kuma saboda tsanani gazawa da rauni da suke ciki sai suke tattaunawa a hankali da junan su dangane da rayuwar su ta barzahu kuma sai suna tambayar juna kwana nawa mu ka yi a barzahu {tsakanin duniya da lahira}?, wasun su suce; kun kwana goma ne ka dai {kwana goma dare da rana} a duniyar barzahu. Ba tare da shakka ba lokacin tsayawar su a barzahu mai tsayi ne, amma in aka yi la'akari da rayuwar kiyama sai mu ga kwanakin barzahu ba komai bane. Kur'ani mai girma da la'akari da amsar da suke ba juna sai ya ce; mu mun kasance masu sani a kan abunda kuke Magana akai' ko ku fada da karfi ko ku fada a hankali.
Acikin wannan yanayi sai wani wanda ya fi su sani da hankali ya ce: kwanan ku daya ne kawai.
Tabbas kwanakin da su ka yi a duniyar barzahu ya fi kwanakin da suke tunanin sun yi {kwana daya ko goma}. Amma kur'ani mai girma dangane da wanda ya ce sun yi kwana daya ne sai ya kwatanta shi a matsayin wanda ya fi su sani da ilimi. Domin kwanakin duniya da na barzahu in ka hada su da kwanakin lahira sai ka ga ba zai yiwu a kwatanta ba domin sharuddan sun sha bamban da juna saboda haka kwana daya na lahira ba za ka hada su da rayuwar barzahu ba[1].
Saboda haka kwana daya ko kwana goma shi ne mujurumai suke tsammanin sun yi a duniyar barzahu domin zaman su a barzahu in a ka hada da na kiyama {lahira} sai a ga ba wani abu ba ne. Saboda haka ne kur'ani kwana daya ya yi amfani da shi domin shi ne ya fi cancanta shi ya sa ma wanda ya ce kwana daya kur'ani yai amfani da sunan wanda ya fi su ilimi da hankali.
[1] Daga mukarim shirazi, tafsirin namune, jildi na 13, shafi na 299, darulkutubul islami, Tehran, bugu na daya, hijra ta 1374