Please Wait
6588
Bisa la'akari da tambayoyin da suka gabata amsa ta farko da ta biyu zasu kasance kamar haka ne:
a- Ba a yi bayani karara ba kan batun rashin shigar malami jagora a cikin doka ba. Don haka idan irin wannan ne jagora malami zai iya shiga kai tsayi cikin irin wadannan lamurran da aka ba wa wasu mutane hakkin tafiyar da su.
b- Rashin shigar malami jagora wajen abubuwan da ba a bayyana su a fili karara zai iya yiwuwa cikin bayanai masu zuwa kamar haka:
1- a yayin da maslahar da take cikin doka ta kasance tana nan ta wanzu ba tare da wani abu ya kawo cikar gareta ba.
2- Maslahar doka ta kasance tana nan ta wanzu, amma ba tare da an samu wani abu da yake kawo mata cikas ba.
3- maslahar da take cikin doka ta kasance ta canja.
A amsa ta farko, ya hau kan jagora ya yi aiki da doka. A amsa ta biyu; iyakacin yadda zai yiwu malami zai iya gudanar da doka matukar abu mai kawo cikas yana nan, kuma zai iya dakatar da gudanar da dokar zuwa lokacin da aka ayyana. Amma a amsa ta uku; samuwar wata dokar ta lizimta cewa bayan sabuwar doka, to biyayya gareta har ga shi kansa jagora malami ya zama tilas.
Tambaya ta uku bisa bayani na kasa:
Dokar asasi ta kasa wata doka ce da ta hau kan kowa a kasa hatta da wadanda ba su yarda da jagorancin malami ba ta wata fuskar, a daya bangaren kuwa an riga an yi bayanin shakalin hukuma a irin wannan dokar, kuma dogaro da karfafawa da goyon bayan mutane game da wannan zai samu tabbatar sa.
Dalilin jagorancin malami yana tabbatar da jagorancin malami da ya cika sharudda. Don haka idan akwai wata kasa da aka hukuma da take karkashin jagorancin malami wanda yake daidaita lamurran mutane, kuma ya zamanto akwai dokoki da suke da shiga kai tsaye wurin ayyana malamin da zai jagoranci hukuma, to a wannan lokacin ne za a samu irin wadannan tambayoyi suna zuwa:
1- shin malami zai iya shiga kai tsaye cikin abubuwan da suka zo na dokoki?
2- Kuma shin zai iya canja irin wadannan dokokin?
3- Mece ce kima wannan doka a tsarin jagorancin malami musamman a nazarin da yake ganin jagorancin kafawa ne wacce ita ce ingantacciyar mahanga[1]?
Amsar duka tambayoyi biyu zasu kasance kamar haka: A cikin iyakokin zabin[2] da jagoran malami yake da shi akwai dokokin da sharudda ayyanannu wadanda bisa la'akari da su ne yake yin hukuncinsa, kuma ya hau kan kowa ya yi biyayya gareshi.
Su wadannan dokoki a bisa hakika dokoki ne na jagoancinsa da suka damfaru da wasu ayyanannun sharudda, kuma matukar akwai wannan maslaha to sunanan, kuma ba mai ikon ya saba musu ko malami ko ba malami ba, ko jagora ko ba jagora ba.
Don haka ne matukar akwai maslaha a cikin wadannan dokoki to ya zama dole ne a kan jagora malami ya yi biyayya ga wadannan dokokin, sai dai idan akwai karo da juna tsakanin dokokin da dokokin shari'a.
Ko da yake wannan lamarin yana kasancewa ne yayin da aka fada a fili karara cewa bai halatta ga jagora malami ya shiga cikin wannan dokoki ba ya yi tasarrufi.
Amma idan an fada a karara cewa kai tsaye malami yana da hannu a cikin kamar a doka ta dari da goma ta dokokin kasar jamhuriyyar musulunci ta Iran, da lamurran da aka bayar da su a hannun bangarorin ma'aikatun gwamnati, ya kasance ba a shelanta wani hani ba ga shigar jagora malami cikin dokokin kasa, to jagora zai iya shiga cikin lamari bisa la'akari da ikonsa na matsayin jagora malami[3].
Idan maslaha ta kai ga cewa malami jagora ko kuma masu ba shi shawara kwararru suka ga canja wannan dokar ko maye gurbinta da wasu dokokin daban sababbi to zasu iya bayar da umarnin sake wasu dokokin ko sake duba cikinsu, kuma biyayyarsa ga kowa hatta da malamai ya zama wajibi a kansu.
Kuma idan aka samu tabbacin cewa wani abu da aka ayyana a cikin dokar bisa maslahar tsari ko hukucin musulunci bai dace ba, wato aka samu karo da juna, malami zai iya dakatar da gudanar da dokokin bisa wani lokaci ayyananne[4].
Amsar tambaya ta uku kuwa:
Tambaya ta uku ana iya amsa ta idan mun yi la'akari da wasu abubuwa kamar haka:
A kasar da take da tsari na hukumar musulunci wanda ya cika sharuddan jagoranci, ya kasance akwai wasu jama'a da su ko bisa nasu ijtihadi, ko takalidi ya zama ba su yarda da tsarin jagorancin malami ba, to bisa dokar rinjayi kan wadannan mutane 'yan kadan a cikin kasa, ya zama dole ne garesu malamai ne ko ba malamai ba, su yi biyayya ga jagorancin malami bisa wani sharadin zamantakewar al'umma da yake a kasashe. Kundin tsrin dokar kasashe ana sanya shi ne ga dukkan mutane baki daya.
Wannan lamarin shi kansa yana daga cikin maslahohi a samuwar dokar kasa ta asasi, da wannan kuma zamu iya kasancewa mun bayar da amsar tambaya ta uku ke nan.
Dokar asasi ta kasa wata doka ce da ta hau kan kowa a kasa hatta da wadanda ba su yarda da jagorancin malami ba ta wata fuskar, a daya bangaren kuwa an riga an yi bayanin shakalin hukuma a irin wannan dokar, kuma dogaro da karfafawa da goyon bayan mutane game da wannan zai samu tabbatar sa.
Karin bayani:
1. Mahdi Hadawi Tehrani, Wilayat wa Diyanat, Mu'assar Al'adun Khaneye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.
[1]. Akwai wadannan bayanai a tsarin kundin jamhuriyyar musulunci na Iran.
[2]. Fayel: Hakkokin Jagoran Malami.
[3]. Kamar yadda Imam Khomain (k.s) ya kafa majalisar ayyana maslahar tsari.
[4]. Kamar kotun musamman ta Malamai.