advanced Search
Dubawa
10511
Ranar Isar da Sako: 2011/01/08
Takaitacciyar Tambaya
mene ne hanyar debe kewa da Kur’ani
SWALI
idan wani matashi ya nemi ku shiryar da shi ga hanyar son Kur’ani da debe kewa da shi da kusantar shi. Da me zaku ja hankalinsa a wannan babin.
Amsa a Dunkule

idan ya zama tilawar da mutum zai yi ta Kur’ani don neman kusanci ne zuwa ga Allah, da tadabburi da bibiyar aiki da shi, to zai zama tilawar ta kusantar da shi ga manufar Kur’ani sosai, zai zama son Kur’ani zai tsananta.

Amsa Dalla-dalla

An sami hadisi daga Imam Sadik (a.s) cewa ana yin la’akari da tabbata da rabauta ga matashi ta hanyar samuwa da debe kewa da tilawar Kur’ani, Imam ya ce: wanda ya karanata Kur’ani alhali yana matashi mumini, alkurani zai cudanya da jininsa da tsokarsa, kuma Allah zai sanyashi tare da jakadu masu girma (malaiku) Kur’ani zai zama mai kareshi ranar alkiyama. Kur’ani zai ce; ya Ubangiji kowane mai aiki an bashi ladansa, ban da wanda ya yi aiki da ni, ya Ubangiji ka bashi mafi girman abin bayarwarka 1 (ko a bisa ma’anar hadisin)

Yana daga dabi’a, dacewa da manufofin Kur’ani, ba abu ba ne na zahiri, yana bukatar kiyaye wasu sharuda ayyunannu. Mafi tasirunsu shi ne jin tsoron Allah, an so mutum ya kasance ko da yaushe yana lura da Kur’ani ta bangarori biyu. Ko dai ya yi riko danasiharsa ko ya riki wasiyoyinsa sannan ya tasirantu da su da aiki da su, kai tsaye don ya shiryawa gyaran ruhinsa da fa’idantuwa da koyarwar Kur’ani. A karshe idan ba haka ba, gundarin karatun Kur’ani da sanin wasiyoyinsa ba tare da aiki da suba, ba zai warware kowace kowace irin mushkilaba.

Yana da kyau mu kawo wasu ayoyin Kur’ani a wannan bigire muga me suka zo mana da shi:

  1. Kuma ka ce mun sassaukar daga Kur’ani abin da yake waraka ne da rahama ga muminai. Kuma ba ya kara wa azzalumai komai sai hasara.2
  2. Da mun sanya shi abin karatu na ajamanci, lalle da sun ce. Don me ba a bayyana ayoyinsa ba? ka ce ashe zai yiwu a sami littafi ba’ajame da manzo balarabe? Ka ce shi shiriya ne da waraka, wadannan anakiransu daga guri mai nisa. 3
  3. Lalle ne wannan littafi Kur’ani yana shiriya ga wadanda suke aikata ayyuka na kwarai lallei suna da sakamako mai girma 4
  4. Mu ne mafi sani game da abin da suke fadi, kuma ba za ka zama mai tilastasu ba. Saboda haka ka tunatar game Kur’ani ga wanda yake tsoron sakamako. 5

Saboda haka abin sone daga mutum ya nemi tsarin Allah kafin ya yi tilawa 6 An so daga gare shi idan ya karanta ayoyin Allah kar ya zama kurma, makaho.7 ya sunkuya zuwa ga Allah ta hanyar kaskantar da kai, kuka, da jin tsoron Allah8. bayan yaji maganar Allah da koyarwarsa jikinsa zasu raurawa saboda tsoron Allah ubangijinsa sanan zuciyarsa zasu tausasa da ambaton allah, sai ya zama ya shirya domin haduwa da shiriya madaukakiya daga Allah (swt)?

Wannan zai zama mataimakinsa kuma abin dogoransa a kowane matsayi na rayuwa. Sai dai idan ya zama manufar karatun Kur’ani ya saba ma wannan, ya zamo izgili agareshi da koyarwarsa.10 ko kuma manufar cudanya da da shi ya kasance domin abin duniya ne. To a nan ba, zai zama mafi kaskancin matsayi, wanda bashi da wata alaka da Kur’ani.

Akwai ruwayoyi masu yawa game da nau’ioin alakar mutane da Kur’ani. Da warwarewarta, zamu zo da wadansun su.

  1. Manzo Allah (s) ya ce: - wanda ya fi tsoron Allah a mutane a sarari da boye shi ne mahaddacin Kur’ani, wanda ya fi cancanta a sarari da boye ko ya fi samun ladan sallah da azumi shi ne mahaddacin Kur’ani, sai ya yi kira da mabaukakin sautinsa ya ce; ya mahaddacin Kur’ani ka kaskantar da kanka, Allah zai daukaka ka, kar ka nemi girma da shi sai Allah ya kaskanta ka. Ya mahaddacin Kur’ani kayi wa Allah kwalliya da shi, Allah zai yi maka kwalliya da shi, kar kayi wa mutane kwalliya da shi, sai Allah ya muzantaka da shi, wanda ya sauke Kur’ani kamar an shigar da annabta ne ajikinsa, Sai dai ba a masa wahayi. Wanda ya haddace Kur’ani kuma yake karantashi ba zai jahiltar da shi tare da wadanda suka jahilce shi ba, ba zai sa cikin wadanda ya yi fushin da su ba, ba zai sa shi cikin wadanda zai razanar da su ba, sai dai za’ai masa afuwa za a kauda masa kai, a gafarta masa, ayi masa hakuri saboda girman Kur’ani (a bisa ma’anar hadisin).

 

  1. An karbo hadisi daga Imam Jafar (a.s) ya ce: makarantan Kur’ani sun kasu kashi uku.
    1. Wanda ya karanta Kur’ani sai ya mayar da shi haja ko ya zagaya da mulki da shi, ko ya mayar da shi abin girma kai ga mutane.
    2. Wanda ya karanta Kur’ani sai ya haddace haruffansa ya wulankanta ayoyinsa, ya rike shi abin nemansa, to kar allah ya yawaita irin wadaannan mutanen a cikin mahaddata.
    3. Wanda ya karanta Kur’ani sai ya sanya warkarwar Kur’ani a zuciyarsa. Ya raya darensa da tilawarsa, ya raya yininsa da karatunsa, ya tsaya da shi agurin sallolinsa, ya rika tilawarsa a kan shimfidar barchinsa, to wadannan ne Allah mabuwayi yake ingije bala’oinsa. Da wadannan ne Allah mai girma da buwaya yake juye makiya. Da wadannan ne Allah yake saukar da ruwan sama. Na rantse da Allah wadannan a cikin karatun alKur’aninsu sun fi daraja fiye da Jan Kibriti12 (ma’adani ne)

An karbo daga Jabir daga Imam Jafar (a.s) sai na ce mutane idan suka ambaci wani abu a Kur’ani ko aka ba su labari da shi sai dayansu ya sume har sai munga da za a yankewa dayansu hannaye ko kafafuwa ba zai ji komai ba. Sai Imam ya ce tsarki ta tabbata ga Allah wannan daga shaidan ne. Ba da wannan muka umarcesu ba. Kurum dai shi tausasawa ne.

  1. Kulaini Muhammad bin Ya’akub, Alkafiy2.2, sh603, j4 Darul Kitabul Islamiyah, Tehran1365, Hijri.
  2. Isra’I 82
  3. Fusilat 44
  4. Isra’I 9
  5. Kaf 45
  6. Nahli 98
  7. Furkan 73
  8. Maryam 58 Isra’i 157-159
  9. Zumar 25
  10. Jasiyat 45
  11. KAFIY J2 SH604, J5
  12. KAFIY J2 SH627 J1
  13. KAFIY J2 SH616, J1

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa