Please Wait
12411
A bisa ayoyin kuráni mai girma ibilis yana daya daga cikin aljanu, saboda yawan ibadar shi ya zamo daga cikin mala'iku, amma bayan Allah ya halicci Adam sai aka umarce shi da yi wa Adam sujada amma ya ki sai Allah ya nisantar dashi daga gare shi. Amma duk wani abin halitta mutum ne ko aljani ko dabba in ya zamo mai sabo to sunan shi shaidan, ibilis saboda sabon da ya yi na kin biyayya ga Allah madaukaki ake ce masa shaidan.
Saboda haka shaidan suna ne wanda ya hada da ibilis da wanda ma ba shi ba.
A kan wannan amsar dole ne mu lura da wasu kalmomi biyu wato shaidan da ibilis.
Shaidan asalin Kalmar daga [shadan] wato mai kangara, saboda haka duk wani kangarare mutum ne ko aljan ko dabba suna shi shaidan. [1]
Kalmar shaidan tana da ma'ana uku cikin Kur’ani;
1. shaidan kadai ba tare da an sa masa alif da lam ba to a nan shaidan bai da wata ma'ana daban ta shafi komai mutum ne ko aljan ko dabba kamar wannan ayar {waman ya’ashu an zikrir rahamani nagaziya lahu shaidan fahuwa lahu Karin}[2]. Ma'ana: Dun wanda ya manta da an baton Allah to zamu hada shi da shaidan zai zo ya zama tare da shi.
2. Shaidan dare da alif da lam a nan ana nufin ibilis ne ka dai. Kamar yanda ya zo a wannan ayar sharifa {allshaidan ya'idkumlfagara wa yantinnankum allshaidan kama akhraja abuwaikum minaljannati[3]} ya ku ‘ya’yan Adam ka da shaidan ya yaudare ku kamar yadda ya yaudari babanku da mahaifiya ku ya sa suka fita daga aljanna. Amma wani wurin ya zo da ma'ana mai fadi kamar wannan ayar mai tsarki [allshaidanu yuezukum allfagara wa yamurukum bilfahsha…} ma'ana shaidan yana tsoratar daku talauci kuma yana kiran ku zuwa ga sabo da alfasha [4]. A nan [alif wa lam] yana nufin fadin ma'ana na asshaidan: saboda tsoratarwa ga talauci da kuma kira ga alfasha wani lokaci shaidani na mutum ne ke aikata haka.
3. Shayadin cikin jam'I: yana nufin cewa shaidan na da ma'ana kala kala amma da Kalmar shaidan kebantacen suna ne wato ibilis ka dai amma a wasu ayoyin yana da ma'ana mai yawa kamar wannan ayar {wakazalika ja’alna likuli nabi adu shaiyadinal ins waljin} a kan kowa ne annabi muna dora masa makiya na shaidani mutum ko aljan. [5]
Iblis:
Iblis daga Kalmar {iblis} da ma'anar bakin ciki saboda tsanani yanke kauna da rashin buri. Allah madaukaki yana cewa: {wa wayuma takumu saatu yublisul mujrimuna[6]} ranar tashin kiyama masu sabo zasu zama cikin kunci da bakin ciki[7]. Saboda wannan dalilin ne ake kiran iblis da wannan sunan domin ya yanke kauna daga rahmar ubangiji madaukaki saboda sabama umurni da ya yi ma Allah madaukaki.
Kur’ani yana cewa: {ku tuna da lokacin da muka ce da mala'iku su yi sujudaga Adam, duk su ka yi sai iblis ka dai saboda yana cikin aljanu[8].. Sai ya fita daga umarnin Allah madaukaki} Allah ya tambaye shi: kai iblis me ya hana ka sujudi ga abin da na halitta da ikona? Shin girman kai ne ko kana jin ka fi shi? Iblis ya amsa da cewa: ni na fi shi saboda ka yi ni da wuta shi kuma ka halicce shi da kasa[9]. A nan ne Allah ya ba da umurni fidda shi[10] daga jerin mala'iku[11] ko da yake asali ba mala'ika ba ne sai dai saboda tsanani bauta da da'a da kusanci ga Allah ya sa ya zamo cikin jerin mala'iku[12].
Imam Ridha {a. s} yana cewa: sunan iblis, {hirs ko kuma haris} amma saboda nisanta daga rahamar Allah da yanke kauna sai a ke kiran shi da iblis. [13]
Ibin arabi, mai littafin futuhatul makiyya a kan sama iblis wannan sunan ya ce: wanda a ka fara kira da shaidan shi ne haris, saboda haka Allah madaukaki ya sama sa iblis wato wanda ya yanke kauna daga rahamar ubangiji[14].
Kur’ani yana cewa: yayin da Allah ya fitar da shi daga jerin mala'iku sai ya ce: ya Allah ka yi mani jinkiri har zuwa ranar tashi, sai Allah ya ce kana cikin wadanda aka jinkirta masu ya zuwa wani lokaci bayyananne[15].
Lokacin da iblis ya tabbatar da zai jima raye sai ya ce: ina rantsuwa da girman ka sai na halakar da mutane sai dai bayin ka zababbu[16].
To shi makiyi ne na dan Adam wanda ya yi rantsuwa a kan gaba da mutum. Shi ya sa Allah yake tunatar da bayin shi shaidan {iblis} makiyi ne gare ku kuma ku rike shi makiyi[17].
Abin da ya kamata a lura a nan shi ne dukkan shaidanu suna karbar umurni daga iblis ne wato; Shaidan yana da iko a kan su shi ya sa suka manta da ambaton Allah, su suna cikin rundunar shaidan ku sani rundunar shaidan masu tabewa ne[18].
Sakamakon bincike:
Iblis, sunan shaidan ne wanda a sakamakon kin yi wa Allah biyyaya ya zamo abin korewa, shaidan ma'anar shi a jumla ce shi ne halitta masu sabo da wuce gona da iri wannan ya shafi iblis da sauran shaidanu na mutum da aljan har da ma dabbobi.
[1] Almunjid fillugat.
[2] Zukhruf,36.
[3] Aarab,27
[4] Baqara,268
[5] Anam,112
[6] Rum,12
[7] Almufradat fi gariblkur'an, ragib isfahani,
[8] Kahafi,50 [ya yin da mukace da mala'iku kuyi sujudi ga adam sai suka yi sai dai iblis day a zamo daga aljanu sai ya saba umurnin ubangijin shi. . }
[9] Suratul sa 75-76 [sai ya ce ya kai iblis mai ya hana ka yima abin da na halite shin girman kai ne ko ji fifiko?, ya ce ni naïf shi ka halitani daga wuta shi kuma daga yunbu.
[10] Suratul sa, 77-78 {ya ce fita daga cikin su kai korare ne daga rahama, kai lanane ne har zuwa tashin kiyama.
[11] Tafsir namune, jildi na 19 , shafi na 341.
[12] Tafsire namune jildi na 12 ,shafi 462
[13] Safinatulbihar, jildi na daya ,shafi 99
[14] Alfutuhatmakki, ibn arabi, jildi na daya shafi 134
[15] Suratul sa ,79-80-81{ya ce ya ubangiji ka jinkirta man har zuwa ranar tashi. Ya ce kana cikin jinkirtatu ya zuwa lokaci bayyanane
[16] Suratul sa 82-83{ya ce na rantse da girman ka sai n agama das u duka, sai dai bayinka makusanta
[17] Fadir 6 {shaidan makiyine gare ku kuma ku rike shi makiyi.
[18] Majadala,19 {shaidan ye galaba a kan su sai suka manta da ambaton Allah, to wadannan sune rundunar shaidan ku sani rudunar shaidan sune hasararu.