Please Wait
Dubawa
14035
14035
Ranar Isar da Sako:
2015/06/30
Takaitacciyar Tambaya
Menene ma’anar Kalmar tarjama da ma’anar Kalmar tafsir kuma menene banbancin da ke tsakninsu?
SWALI
Me Kalmar tarjama take nufi kuma me Kalmar tafsiri take nufi kuma menene banbancinsu?
Amsa a Dunkule
A wajen malaman lugga: T R J M, wadannan nan ne bakaken da suka hada Kalmar tarjama, wato jam’in (tarjiman) shi ne wanda yake yin tarjama, yake fassara magana, ana cewa wane ya tarjama maganar wani: ma’ana ya bayyana shi ya fayyace shi, haka ma, wane ya tarjama maganar waninsa. Ma’anar ya fassara ta da wani yaren da ba nasa ba. Amma a isdilahi (wato a wajen masana tarjama), tarjama ita ce cirato magana daga wani yare zuwa wani kamar a nakalto daga farisiyya zuwa arabiyya.
A yayin da ana tsago Kalmar tafsiri daga “fassara” ko daga “safara” mafi yawan masana lugga sun tafi kan cewa ma’anar Kalmar tafsiri da aka samo ta daga fasara tana nufin ya bayyana ya yaye. Kuma masana sashen suka ce ma’anar tafsiri ita ce, gusar wa lafazi murdiya da kullin da ke cikin lafazi mai mishkila, ma’ana lafazi mai matsala wajen bada ma’anar da ake nufi. Kuma allama daba’daba’i ya yi ta’arifin sa a inda yake cewa: shi ne bayyana ma’anonin aya da yaye manufofinta da abubuwan da take nuni zuwa gare su.
Hakika masu bincike sun yi nuni zuwa wasu tarin na banbance- banbance da ke tsakanin wadannan kalmomi guda biyu.
Banbanci na farko: hakika sigar tarjama siga ce mai cin gashin kan ta, an wadatu daga asalinta da kuma wata ta hau matsayinta (wata za ta iya zama a matsyainta), amma tafsiri ba haka yake ba, hakika shi a ko da yaushe a tsaye yake kuma kyam yake yana hade da asalinsa ta yanda ake kawo mufradinsa da murakkabi sannan a yi sharhi kalmominsa daidaiku da murakkabai, sannan ayi sharhin wannan mufradin ko murakkabin sharhin da yake hade da shi irin hadewan mubtada da khabari (mubtada shi ne; sunan da ya zo a farkon magana khabar kuma shi ne labarin da aka fadi kan mubtada).
Banbanci na biyu: be halatta a kara yawan zance a cikin tarjama ba- hakama ciratuwa daga wani mau’dhu’i zuwa wani- amma ya halatta a yi haka a cikin tafsiri, ballantana ma ta yiyu yawanta zance ya zama ya wajaba, wannan kuma saboda tarjama abin da ya kamata a cikin ta shi ne ita sura ce (hoto ce) da ta yi mudabaka da asalinta tana mai hakaito asalin don haka yana daga cikin amana ya zama ta yi daidai da shi tara de kula wa da kiyaye amana ba tare da kari ko ragi ba.
Banbanci na uku: A al’adance tarjama na bukatar a fitar da dukkanin ma’anar da maganar ta kunsa da manufarta amma shi tafsiri ba haka yake ba, shi ya tsaya ne kan yin cikakke bayani, kamar yanda muka ce a baya sai dai shi wannan bayanin a dunkule ne ko a fadade, yana mai yin bayanin dukkanin ma’anoni da da manufofi ko kuma yana mai takaitawa a cikin shashinsu banda wani shashi, dai dai da yanayin da malamin tafsiri ya sami kansa a ciki da kuma yanayin wadanda yake yin tafsirin don su.
Banbanci na hudu: A al’adance tarjama tana dauke da yin da’awar cewa akwai nutsuwa kan cewa dukkanin ma’anonin da manufofin da mai tarjama ya cirato shi ne ainihin manufar abin da maganar (da aka tarjama ta assail) take cewa, kuma abin nufi shi ne nakalto maganar mai magana ta Asali, Amma tafsiri ba haka ba ne, balle ma shi mai tafsiri wani lokacin ya kan yi da’awar yana da nutsuwa idan ya sami gamsassusn dalilai wani lokaci kuma ba ya da’awar hakan idan ya kasa samun wadannan dalilan.

Amsa Dalla-dalla
A wajen malaman lugga: T R J M jam’in tarjuman, shi ne: mai yin tarjama, mai fassara yare, ana cewa wane ya fassara zancesa, wato ya bayyana shi ya yi bayaninsa, haka ma ya tarjama zancen waninsa ma’ana ya fadi maganar sa da yaren da ba na mai magana ta asali ba. sunan wanda ya yi aki shi ne (tarjiman)[1] daga nan ne ake kiran litattafan da ake rubutawa don bayanin halayen mazaje da (kutubul tarajumi) wato litattafan tarjama, kuma ake kiran abin da aka wallafa kan mutum da tarjamar mai ruwaya ko mawallafi ko ......[2]. Amma tarjama a wajen malamanta, abin da take nufi shi ne, cirato zance daga wani yare zuwa wani yaren na daban,[3] kamar a cirato daga farisanci zuwa larabci ko Hausa.
An shardanta tarjama ingantacciya ya kasance mai tarjamar ya san yaren asali kuma ya kiyaye amana wajen takaltowa da ma’anar ya nakalto ma’anar maganar yare na farko zuwa yare na biyu. Balle ma ya zama lalle a kiyaye matashiya da manuniya da abubuwan da suke kewaye da rubutu ko nassin da ake tarjamawa. Bisa misali idan nassain da za’a tarjama ya zama yana dauke da nuna damuwa da radadi - ba bayanin ma’ana ba - to ya zama lalle ga mai tarjama ya kiyaye yanayin da ke nuna bakin ciki da radadi kuma kar ya tafi yana yin bayanin ma’anar Kalmar da cirato asalin ma’ana domin mai magana ba yana matsayin mai bayyana ma’ana ba ne ballantana mai yin tarjama ya nakalto hakan. [4]
Da wani yaren ya kamata tarjama ta kasance tsaftattacen madubi da zai nakalto dukkanin ma’anar da dukkanin abin da ke danfare da it ba tare da mafi karancin kuskurewa ba, a wajen cirato ma’anar da abubuwan da aka yi tsokaci da su a matanin wanda ake wa fassara, musamman ma idan matanin ta zama yana da alaka da litattafan sama (na addini) saboda mihimmancin da yake da shi na musamman ta yadda ya zama wajibi ga mai tarjama ya bada kulawa ta musamman a wajen yin tarjamar, daga nan ne tarjamar Kur'ani - wanda yake mu’ujizar Annabi Muhammad (s.a.w) ne shi - ta zama tana bukatar kulawa ta musamman kuma da bibiyar matanin sosai.
Hanyoyin tarjama
Za’a iya kasa hanyoyin tarjama zuwa ga nau’o’i uku, su ne:

- Tarjama ta harafi
Na daya: shi ne mai tarjama ya rika canja ko wane harafi da takwaransa na daya yaren sai ya sa dayar a mahallin waccen sannan ya ciratu zuwa kalma ta gaba ita ma ya canja ta da takwararta haka ma ta uku da makamancin haka ya yi tafiya kan wannan tsarin har ya zuwa karshen tarjamar damar idan ya tarjama “bismillahir rahamanir Rahim” zuwa yaren hausa ta wannan hanyar:-
Bismi = da sunan
Allah = Ubangiji
Arrahman = mai rahama
Arrahim = mai jinkai. Sai sakamakon ya zama da sunan Ubangiji mai rahama mai jin kai, wannan ita kake kira da tarjamar harafi ko tarjamar a karkashin lafazi kuma ita ake kira da tarjamar harafi, ko tarjama ta lafazi kuma wannan ce mafi munin nau’o’in tarjama, kuma mafi yawan lokaci ma’anar tana sabbaba rudani wajen fahimtar ma’ana ko ma ta kai ga ha’intar ma’anar magana tun da abin da tarjamar ra’ayi ke kai wa gare ta shi ne canja ma’anar zance baki daya don mai yin tarjama bisa wannan hanya yana kokarin ya ga ya kiyaye tsari da salon zance da ma’auninsa da balagarsa, don ya zo da maganar da ta yi kama da ita kai tsaye a tsari da salo, wanda hakan kwata- kwata ba al’amari mai yiyuwa ba ne saboda banbanci yare da banabncin tsarin balaga da isar da sako, haka ma wajen sanya manuniya da zurfafan ma’anoni wandanda suke akwai su a ko wane yare bisa yadda al’adun yarukan suke, da yawa zaka ga wani Karin magana ko zaurance wanda yake sananne a wani yare amma a wani yaren ba a san da shi ba, kuma be zama abin birgewa ba, da mai tarjama zai fassara wannan Karin maganar, da wannan tarjamar da za’a wayi gari ba a san ma’anar ta ba, wata kila ma irin wannan jimlar mai ban mamaki ta zama abar kyama a wajensu da yadda suke fahimta.[5] Da [6]

- Yantacciyar tarjama: nau’i na na biyi daga cikin kalolin tarjama ita ce mai yin tarjama ya yi kokarin sanya ma’ana a cikin wani sabon kwanso ba tare da ya kayyaduwa da tsarin magana ta asali da salon ta na bayani ba, Sai da abin la’akari shi ne isar da ma’anar ta asalin da bada ita cikakkiya ta yadda za a fahimci abin da mai magana ta asali yake so ya fada, da sharadin kada ya kara a wajen yin bayani ta yanda zai zama ya fita daga shingen tarjama zuwa na tafsiri zalla, tabbas, irin wannan tarjamar zata iya kai wa ga faduwar kimar magana ta asali da aka tarjama. Kuma wannan ba ya cutarwa matukar dai kubutar ma’ana ta zama abar kiyaye wa, kuma wannan nau’in na tarjama shi ne mafi fitar da cikakkiyar ma’ana kuma ita ce tafarki madaidaici, kuma ita masana fannoni suka rika. Kuma ba ta kayyaduwa da tsarin zancen da aka fassara, sai su gabatar kuma sun jinkirta, su tsara tarjama daidai da tsarin yaren da ake fassara zuwa gare shi kamar yanda ba sa yin kari mai yawa kan lafuzza da jimlolin da suka zo a cikin magana ta asali, idan har suka yi wani Karin mai yawa to ya zama sharhi, da tafsiri, sam - sam irin wannan ba ya daga cikin abin da ake kira da tarjama. [7]
- Faffadar tarjama: a irin wannan tarjamar mai tarjama yana fadada bayani yana mai yin shirhin manufar magana sharhi cikakke, kuma wana na daga cikin nau’o’in tafsiri da wani yaren, kuma baya daga cikin tarjama tsantsa kamar yanda wasu suke cewa. [8].
Tafsiri a lugga da isdhilahi
An cirato Kalmar tafsiri daga “fasara” da “safara” mafi yawna malaman lugga an samo kalmar tafsiri daga karmar fasara, ma’ana ya yi bayani ya yaye.[9]. Ragib ya ce “fasara da safara suna da ma’anoni makusanta, kamar yanda lafuzzan biyu suke da kusanci na ma’ana, sai dai ya sanya tafsiri don bayyanar da za’a iya hankalta, safara da kuma kan abubuwan da ido ke gani, ana cewa: “safaratil mar’atun an wajhiha wa asfarat wa asfaral al-suhbu)” wato “mace ta bude fuskarta kuma ta bude kuma safiya ta waye”, Allah madaukakin sarki yana cewa: {ba za su zo maka da wani misali ba face sai mun zo maka da gaskiya da mafi kyawon tafsiri} suran Fukan aya ta 33. Ma’ana bayani kuma fayyacecce.
A isdilahi kuma tafsiri shi ne: gusar wa lafazi murdiya da kullin da ke cikin lafazi mai mishkila ma’ana lafazi mai matsala wajen bada ma’anar da ake nufi.
Don haka tafsiri ba shi ne yaye mayafin lafazin da ya rikitar ba kawai balle ma shi kokarin gusar da abin daya buya daga abin da zance yaka nufi ne, don haka ba makawa sai ya kasance akwai wata fuska ta rikitarwa da lafazin yake da shi, ta yadda ya zama ya rufe wa ma’ana fuskarta kuma lamarin ya zama yana da bukatar kwatantawa da kokarin gaske har sai abin da ya buya ya bayyana a sarari, kuma an kawar da matsalar.[10] .
Kuma tafsiri na da ma’anar sa ta musamman a cikin - ilimin da ke wa - hankali hidima da ilimin gwaje- gwaje, don haka tafsiri a ilimomin hankali yana nufin yin sharhi da yin bayanin abin da litattafan ilimi na falsafa da na lkitanci ke kunshe da su, kuma yin amfani da Kalmar tafsiri ya takaitu da ilimin takaltowa ta hanyar yin sharhi da da yin bayanin kalmomin Kur'an mai girma kuma musamman ma bayanin kalmominsa da ayoyinsa.[11]
Wani lamari da ya kamata a ce an ambata shi ne lalle maganganun masana ta saba kan yiyuwar fassara kur’ani mai girma da kuma rashin yiyuwar hakan [12] ta yadda wasu daga cikin suke tafi kan kore yiyuwar a ti tafsirin Kurani mai girma, tafsirin da ka sa karshen kaifin basira da hankali balle ma ba zai taba yiyiwa a kusanci tarjama sa ba a matakin tarjama da ba ta karshen kwarewa ba, saboda Kur'ani ya fi karfin ya kasance a karkashin wata dokar ta wani ilimi da take yin aiki kan sauran ilimomi, a yayin wa wasu suka tafi kan yiyuwar hakan, kuma lalle Kur'ani sha’aninsa sha’anin sauran ilimomi ne da za’a iya yin ta’arifinsa a yi bayaninsa kuma ko wane dan adam zai iya - idan ya dogara kan wasa dalilai - zai iya yin tafsirin Kur'ani mai girma ya kuma san abin da ya kunsa. [13]
Kuma hakika da yawa daga cikin malamai da masu bincike daga musulmai sun ambaci ta’arifofi masu yawa ga Kur'ani kuma zamu yi nuni zuwa wasu misalsali daga cikinsu:
Zirkashi ya fadi a cikin burhan: Tafsiri ilimi ne da ake sanin fahimtar littafiin Allah wanda ya sankar ga annabinsa Manzon Allah Muhammad (s.a.w) da yin bayanin ma’anarsa da fitar da hukunce - hukuncensa da hikimominsa tare da yin amfani da ilimin luga da nahawu da sarfu da alimin bayani da usulul fikhi da ilimin kira’o’in Kur'ani, kuma da bukatar ya san dalilan saukar ayoyi da kuma ayar da ta shefe watanta da kuma wacce aka shafe. [14].
Kuma zarkani ya yi ta’arifin sa da fadin sa cewa: shi ilimi ne da yake bincike kan Kur'ani mai girma ta bangaren kasantuwarsa yana nuni kan manufar Ubangiji (abin da Ubangiji yake nufi) bisa gwargwadon kwarewar dan’adam. [15]
Kuma sayyin khu’i ya yi ta’arifinsa da cewa: shi ne bayyana abin da Allah yake nufi daga littafinsa mabuwayi. [16]
Kuma ya zo a ta’arifin almizan cewa: shi ne bayanin ma’anonin ayoyin Kur'ani ya yaye manufofinsa da abubuwan da yake nufi. [17]
Allama Jawadi Amuli ya yi ta’arifinsa da fadinda: Tafsiri yana nufin bayyanawa da yaye shinge daga fuskar kalma ko magana, wanda yake nuni zuwa gare shi bisa dokokin tattanawa da al’adu da salon fahinceceniya da ma’anar sa take kasancewa bayyananniya a sarari. [18]
Sayyid Mustafa Khomaini ya yi ta’arifinsa da cewa: shi ne sanin manufofi da abubuwann da suke boye a cikinsa ta hanyar kewayewa da su bisa gwargwadon iyawar dan adam kuma da rashin iya sanin abin da ke kewaye da shi kai tsaye hatta ga wanda aka saukar wa da shi (amincin Allah ya kara tabbata a gare shi) [19].
Zamu iya tattari abin da aka dauka daga ta’arifofin da aka ambata kamar haka:-

- Ana kiran tafsiri da ma’anar tarin wasu masaniya da ta rataya da bayanin fahimtar ayoyi da ma’anonin ayoyin Kur'ani mai girma da sharhin kalmominsa da fayyace ma’anar kalmomin Kur'ani mai girma da jimlolinsa.
- Ya kamata tafsiri ya zama daga cikin kalar manuniyar kalmomi kuma sabani a cikin tafsiri ya kadaita cikin yananyin bayani da isar manuniyar lafazozin ayoyinsa.
- Ya zama lalle akiyaye dangatakar da ke tsakanin lafazi da ma’anarsa in ba haka ba lamarin zai fita daga kasancewar sa yin bayanin zancen Allah kuma da zai yiyu a jingina ko wane zance zuwa ga Kur'ani mai girma.
- Ganganci ne wani ya yi da’awar samun wani tafsiri da ya tattaro dukkanin ma’anoni da manufofin Kur'ani mai girma, ko ma me muke da shi bai wuce kokartawa ba daidai gwargwadon iko da kwarewar da ko wani mai tafsiri yake da ita da kuma himmarsa wajen yaye mayafin wani bangare daga ayoyi masu girma.
- Akwai wasu gungu daga mafassara da suka isu da yin sharhin daidaikun kalmomin Kur'ani mai girma, suka yi bayanin ma’anoninsa na yare kadai, a yayin da wasu suka fadada sosai wajen yin bayanin ma’anonin ayoyi na lugga da ma’anoninsu su dauki bayanin daidaikun kalmomi a matsayin gabatarwa ga shiga cikin bayani da kuma sanin ilimomin da fahimtar da Kur'ani ke tattare da su, da kuma fayyace manufofinsa da hadafofinsa. [20].
Yana daga cikin abin da ya kamata a ambata, cewa hakika ma’asumai (a.s) su ne mafassar Kurani na hakika saboda cikakkiyar masaniyar da suke da ita kan hakikanin kaur’ani mai girma wacce Imam Ali (a.s) yake cewa a dangane da ita “....kur’ani ku yi magana da shi ba zai taba yin magana ba, sai dai ni zan baku labarin dangane da shi ku sani hakika a cikinsa akwai ilimin abin da zai zo nan gaba da labarin abin da ya shude da maganin cututtukanku da tsara abin da ke tsakaninku. [21].
Banabancin da ke tsakanin tafsiri da tarjama
Duk yanda tarjama ta zama ta harafi ko ta fassara to hakika kai tsaye wanin tafsiri ce ita dai-dai ne tafsirin ya kasance da yaren mutum ne ko da yaren asalin abin da ake fassara wa ne, sai sai da yawa daga cikin marubuta sun shiga rudani sai su ka yi tsammanin cewa tarjamar tafsiri ita ma tafsiri ce ba da yaren asali ba ko kuma tarjamar tafsirin asali ce. Kuma a nan zamu yi nuni zuwa wasu gungun daga cikin banbance-banbancen da ke tsakanin wadannan masu kamanceceniyar su biyu (tarjama da tafsiri):
Banbanci na farko: hakika tsarin tarjama tsari ne mai cin gashin kansa kuma a cikinta an wadatu ga barin asalinta da tsayawar wata (jimla ko kalma) a matsayin wanccen amma shi tafsiri ba haka yake ba hakika shi ya tsaya kan asalinsa ta hanyar zuwa da shi bisa misali: a kan fara da kalma daya ko sama da daya sannan a yi sharhin wannan Kalmar ko sama da daya sharhin da ke damfare da juna wanda ya yi kama da damfarewar (mubtada da labari) in ma bai zama daidai da shi ba, sannan ya ciratu zuwa yanki na gaba kalma ce shi ko jimla haka zai yi ta yi tun daga farkon tafsori har zuwa karshensa ta yadda ba zai yiyu a raba tafsiri a yanke igiyarsa daga tushen sa ba har a bada tamkar yadda bishiya take da reshenta kuma da za ‘a raba su da zancen ya daidaita, kuma da ya zama wargi ko abin da ya fi kama da wargi kuma ba zai taba isar da ma’anar zance lafiyayya ba, ballamtana kuma ya zama a matsayin wata jimla da bayaninta zai zama a matsayin bayanin ta na asali ba.
Banbanci na biyu: hakika be halatta a yi saki ba kaidi a cikinta tarjama ba - haka ma ciratuwa daga wani jigo (maudhu’i) zuwa wani ba - amma a tafsiri hakan ya halatta dalilin haka kuwa shi ne ita tarjama abin da ya kamata a cikinta shi ta zama makwafin asali na wanda take bada labara kansa, don haka yana daga amana a tarjama ta zama ta yi daidai tare da sa hankali sosai ba tare da kari ko ragi ba, ko da kuwa asalin maganar kuskure ce to ya zama wajibi ita ma tarjamar ta zama ainihin kuskuren, sabanin tafsiri, domin abin da yake tabbas dangane da shi, shi ne, shi bayani ne na asalinsa da kuma fayyace zancensa kuma wannan bayanin da sharhin suna hukunta mai tafsiri ya shiga mashigogi masu yawa, ya saki linzami don ya fuskantar da su sharhin da yake yi ko kuma ya haskakawa wadanda yake yi wa fassarar bisa gwargwadon bukatarsu a wajen fadadawarsa, kuma hakan na bayyana a cikin sharhin lafuzza na lugga musamman ma idan ya zama abin da ake nufi da lafazin wanin abin da aka (kirkire shi) ko sanya shi don shi, da kuma inda fahimtarsa ko gamsuwa da shi ta tsaya kan ambaton isdilahohi ko kawo dalilai ko yin bayanin hukuncunsa.
Kuma wannan shi ne sirrin da ke cikin mafi yawan tafisran Kur'ani mai girma ta yanda ya zama an yi shi da nau’o’in fadadawa a cikin ilimin luga da na akida da ilimin fikihu da usulu haka ma ilimin sababin saukar aya da na ayar da ta shafe wata da wanda aka shafe da ilimin halittu da na zamantakewa da makamancin haka.
Daga cikin kalolin irin wannan fadadawar, fadakarwarsa bisa kuskuren asalin idan ya zama akwai kuskure kamar yanda muke ganin wannan a cikin sharhin litattafai ilimi alhali mustahili ne ka ga wannan a cikin tarjama in ba haka ba to ya zama an fita daga wajabcin kiyaye amana da sa hankali kanta.
Banbanci na uku: hakika tarjama a al’adance tana yin da’awar cewa an kiyaye, an isar da dukkanin ma’anoni na asali da manufofinsa amma tafsiri ba haka yake ba, shi ya tsaya ne kan cikakken bayani kamar yanda muka fadi daidai ne wannan bayyanawar a dunkule ne ko dalla-dalla yana mai dauke da dukkan ma’anoni da manufofi ko kuma ya takaita wasunsu banda wasu, daidai da yanayin da mai tafsiri yake ciki ko wadanda yake yi wa ko yake rubutawa tafsirin.
Banbanci Na hudu: hakika tarjama a al’adance tana da’awar cewa ta nutsu da dukkanin ma’anoni da manufofin da mai tarjama ya cirato cewa shi ne manufar maganar asali kuma ana jingina maganar ga mai waccen ta asali, amma tafsiri ba haka ba ne, ballantana ma wani lokaci mai fassara na da’awar samun nutsuwa da - (da tafsirin da ya yi na wata aya) wannan kuma idan ya sami cikakkun dalilai wani lokaci kuma ba ya yin wannan da’awar, wannan kuma (na faruwa ne) idan ya rasa wadannan dalilan, sannan zaka gan shi wani lokaci yana bayyana cewa yana tsammanin kaza, yana mai ambaton wasu fuskoki na tsammani kan ababan rinjayar wa kan wasunsu wani lokacin kuma ka ga ya yi shi bai fito karara ba kuma bai rinjayar ba, kuma ta yiyu lamari ya kai shi ga bayyana gajiyawarsa ga fahimtar wata kalma ko jimla, yana mai cewa mahaliccin zance shi ne ya fi sanin abin da yake nufi da maganarsa kamar yanda muke ganin hakan ga da yawa daga cikin malaman tafsiri idan suka ci karo da ayoyin Kur'ani masu shubuha, da kuma farko ko mabudin surorin da aka sani (irin su: saad= (ص dss . [22]

[1] Al- duraihi, fakharuddini, maj’ma’ul baharaini, tahkikin al-husaini, al-sayyid Ahmad j 6 shafi 21, al-maktabatul murtadhawi, tahran, bugu na uku, 1375; al-fuyumi, Ahmad dan uhammad misbahul munir j 2 sh 74, mu’assar darul hihra kum, bugu na biyu.
[2] Al-haidari, Muhammad a cikim mu’ujamul af’alul mutadawilah, sh 79- 80 al-markazul aalami liddirasatul islamiyya, kum, bugu na daya, 1381.
[3] Ibni manzur, Muhammad dan akram, lisanul arab, daru sadirat j 12 sh 66 bairut bugu na uku, 1414;. Al-bustani fu’’adu afram, muhyar, Ridha, farhagi abajadi arabi,- farisi, shafi 222 bugun islamiyya Tehran, bugu na biyu, 1375.
[4] Ayatulla shekh ma’arifah, Muhammad hadi, tarikhu Kur'an , sh 183, samti Tehran, bugu na biyar 1382.
[5] Masdarin da ya gabata 184.
[6] Ainihin makomar da ta gabata
[7] Ainihin masdarin da ya gabata sh 185.
[8] Ainihin makomar da ta gabata.
[9] Ka duba al-farahidi, albasari, khalilu bini Ahmad, kitabul aini wanda makhzumi, Mahdi, al-samra’I, Ibrahim, ya yi wa tahkiki ya gyara, j 7 sh 247, hijira, kum, bugu na biyu, 1410;. Alwasidi, alzubaidi, muhubbud dini, sayyid Muhammad murtala, tajul arusi min jawahiril kamusi, wanda shir Ali ya yi wa tahkiki j 7 sh 349. Darul fikr ild diba’ati wan nashri waltauzi’I bairut bugu na daya, 1414.
[10] Al-tarsiru wal mufassiruna da ya gabata.
[11] Marwati sahrab, fajuhishi fairamune tarikhi tafsiri Kur'an - darasatun haula tarihu tafsiril Kur'an sh 18, nashri ranz, Tehran bugu na daya, 1381.
[12] Aldabrasi, fadhlu dan husaini, maj’maal bayan, fi ulumil Kur'an j 1 sh 60, darul ma’arifa, bairut, 1408.
[13] Amin khuli, mafradatul tafsir, da’ratul ma’ariful islamiyya, j5 shafi 348, fajuhishi feramone tarihi Kur'an hs 18 - 19.
[14] Zirkashi, Muhammad dan Abdullahi, alburhan fi ulumil Kur'an, j 1 sh 104 – 105, darul ma’arifa bairut bugu na daya 1410.
[15] Zarkani, Muhammad abdul’azim, manahilul irfan, fi ulumil Kur'an , j 1 sh 471, daru ihaya’il turasil arabi, ba ‘a san waje da lakacin da aka buga ba.
[16] Al-khu’i, al-sayyid abul kasam, albayan fi tafsiril Kur'an sh 397 muassasati ihya’I as aril Imam khu’I, kum, ba tarihin bugu.
[17] Daba-daba’I, al-sayyid Muhammad Husain, almizan fi tafsiril Kur'an, j 1 sh 4 maktabatun nashri wal’Iilmil islami kum, bugu nabiyar, 1417.
[18] Jawadi amuli, Abdullahi, tasnim, (tafsirul kur’anil karim), j 1 sh 52 (tare da yin tasarrufi) markazu nashri israa 1378.
[19] Al-allamal mukakkiik, ayatul llahi al-mujahid, al-shahid al-sa’id al-sayyid Mustafa khomaini, Allah ya tsarkake ruhinsa, tafsirul Kur'anil karim, miftahu ahsanil khaza’inil ilahiyya juzi’I na day ash 4 muassatu tanzimi wa nashri asarail Imam khomaini, Allah ya tsarkake ruhinsa, kum, bugu na biyu 1418.
[20] Fajus=hish firamoni tarikhi tafsiril kur’anilim, shafi na 20.
[21] Wanda ya hada ya shirya shi ne sayyid radhi, nahjul balaga, khuduba mai number 158, daga cikin khudubobin sa (a.s) yana mai fadakar wa a cikinta kan falalar Manzo (s.a.w) mafi girma da falalar Kur'ani, intisharat daratul hijra, kum.
[22] Zarkani Muhammad dan abdulazimi, manahilul irfani fi ulumil wur’ani j 2 sh 10 – 11 daru ihya’Il turasul arabi.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga