Please Wait
Dubawa
5910
5910
Ranar Isar da Sako:
2014/09/04
Takaitacciyar Tambaya
Wadananne ne muhimman siffofin tafsirin Kur\'ani na wannan zamanin?
SWALI
Ya matsayin da kuma mihamman abin da tafsirin wannan zamanin ya kebanta da su?
Amsa a Dunkule
Tsarin tafsirin wannan zamani na da kebance - kebance da kuma da nagartar da babu ita a cikin tafsiran da suka gabata: ta bangaren amsa shibuhohi da warware tambayoyi da lamurran da suke kai- kaiwa a kasuwar tunani da kwakwalen mutane, bisa dogaro da tafarkin yin amfani da hankali a fagen tafsiri, tare da bada mihimmanci a fagege guda biyu na tarbiya da na zamantakewa a cikin tafsiri da kuma warware lamuran da ke kai-kawa a wadannan fagagen.
Amsa filla- filla
Tsarin tafsirin wannan zamani na da kebance - kebance da kuma da nagartar da babu ita a cikin matakan da marhalolin tafsiran da suka gabata, wanda ya hada da:-
Amsa filla- filla
Tsarin tafsirin wannan zamani na da kebance - kebance da kuma da nagartar da babu ita a cikin matakan da marhalolin tafsiran da suka gabata, wanda ya hada da:-
- Amsa shibuhonin da warware matsalolin da ke tasowa a tsaka-tsakin fagen tunanin da mahangar mutane kan lamuran da al’umma ke ba wa muhimmanci sosai a fagen tafsirin Kur'ani mai girma a wannan zamanin kuma kakika lamarin fitar da hakikanin mahangar Kur'ani kan wadannan abubuwan ya ja hankalin mutane masu yawan gaske, duba ya zuwa canje-canjen da aka samu na sauyawar zamani tare da kokarin samar da mafita kan shubuhohi masu yawa da ke tasowa a wannan zamanin, wadannan shibuhohi sun dade suna kai-kawo a cikin tunanin mutane wannan zamani, wadanda aka kasa samun amsar su daga makarantu da kafafen da ba na addini ba tare da gazawar addinan da suke ba wadanda aka saukar sama ba wajen warware su: abin da ya hada da; hakkokin dan’adam, yancin tunani, fadin albarkacin baki, hakkokin mace, alaka tsakanin addini da kasa da tsarin duniya, hakkin marasa rinjaye daga ma’abota addini, da alakar tsakanin kasashe......... al’amarin da ya zama cewa ko wane daya daga cikin abubuwan da muka jero da su na bukatar amsa da warwara ta musamman wacce zata haska mana hakikanin lamarin loko-loko tare da warwara da kuma bada mafita gamsashshiya kan sa, hakika malaman tafsiri sun taka muhimmiyar babbar rawa a wanna fagen a matsayin su na makomar tunani wadanda ke da kwarewa wajen toshe kafa da kai dauki kan warware mas’alolin Kur'ani da fitar da lamura daga cikinsa ta hanya sa kaifin tunani yayin bibiyar ayoyi tare da tsinkaye da kuma gwama aya da aya (don fitar da fahimtarsu da ma’anarsu daidai). [1]
Kuma tafsiril Mizan na Allama Taba’taba’i na daga cikin sahun farko cikin wadannan sha-kuddum din na litattafan tafsirin da suka bawa wannan lamarin muhimmanci, hadi da tafsirul amsal fi kitabil llah na Shekh Makarim Sharazi da tafsiril kashif na Jawad Mugniyya; Amma tafsiran ahulussuna za mu iya yin nuni zuwa tafsirul munir na Wahbatu Al-zuhli da tafsirul shi’irawi na Muhammad mutawwali da tafsirul hadis na Gazwata Duruzata wadannan tafsiran makwafi ne kuma misali ne na tafsiran da ke dauke kuma suka tattaro wannan kebance-kebancen.
- Tafarkin sa hankali a cikin tafsiri
Tafsiran zamani sun bawa kaidojin hankali da abin da hankali ya yarda da shi suna masu bada haske bisa ma’ana ta hankali da hankalta ta yadda suka yi tsagaci kan bincike-bincike mabanbanta da ra’ayoyi daban-daban wanda ya hada da:-
- Hankali na kafa hujja da dalili: wannan na nufin warware matsalolin tafsiri da na addini ta hanyar warwara ta hankali da hankalta, kuma wannan tafarki ya dogara kan hankali da kafa hujja bisa dokokin mandiki wajen tabbatar da abin da yake so.[2] Kuma dalilin da ya sa suka dogara da dokokin hankali wajen warware lamura shi ne: maganganun ishkalin da wasu daga masu bincike ke ta yi na cewa wai Kur'ani ya wofinta ko ya yi nesa daga dokokin hankali a tsarinsa da zurinsa, don haka tafsirin almizan na Allama Taba-taba’i da tafsirul tasnim na shekh Jawadi Amuli da daga cikin sahUn farko na irin wadannan tafsirai ma’abota wannan tushe na hankali.
- Hankali na fidita (fitira) (wato dabi’a ta dan’adam wacce aka halicce shi da ita), wannan na nifin dacewar mahangar Kur'ani da abin da hankali yake riska a wannan duniyar ta yanda dan’adam zai iya fahimtar abin da ayoyi ke nufi da kuma inda ta dosa ta hanyar yin amfani da tafarkin hankali wanda Dukkanin masu hankali suka yarda da shi tare da alamomin da ke kewaye da ayar da kuma kalmomin na luga (harshe ko yare) da ma’anonin lafazozi da jimloli. A lokacin da mai bincike ya ci karo da yar nan matsa girma «یَدُ اللَّهِ فَوْقَ أَیْدِیهِمْ» (yadullahi fauka aidihim) wato (hannun Allah a saman na su hannayen).[3] “hankali zai yi hukunci da cewa wannan maganar zaurance (wato kinaya) ce kan cewa yiwa Annabi (s.a.w) caffa yi wa Allah Ta'ala ceffa ne, kai ka ce Allah ne ya dora hannusa a kan hannunusu, ba kawai Annabi (s.a.w) suka yi wa caffa ba, ballanta ma Allah, Kuma abin nufi da hannu a nan ba gabar nan ta jiki da ka sani ba domin Allah Ta'ala a hankalce ya tsarkaka ga barin ciki da abin da ke jiki yake bukata, kuma misalign irin wannan zaurance yana da yawa a cikin yaren larabci.[4]
Daga nan ne muke ganin da yawa daga cikin malaman tafsiri na zamani sun warware masalolin kalam wato ilimin akida da na falsafa masu yawan gaske na daga “mas’alar tilastawa wato jabru” warwarewa ta hankali kuma suka tafi kan bacinta da cewa ba daidai ba ce, kai ta kai ga cewa wasu daga cikin malaman tafsiri na sunna na zamani sun tafi kan rashin ingancin tilastawa ta hanyar yin amfani da ayoyi Ambato mai hikima, kamar sha’arawi da muragi da hibatul zuhaili ....... duk da karkatarsu zuwa ash’aranci.
- Bawa bangaren shiryarwa da tarbiyantarwa mihimmanci
Tun da Kur'ani ya kasance littafi ne na shiriya[5] kuma hakika yana shiryar da mutane zuwa hanya mafi daidata[6] babu shakku hadafin Allah Ta'ala bisa wannan littafi na sa zai zama shiryar da dan’adam da kuma jan ragamar sa zuwa tarbiyya ta gari da rabauta ta hakika. Don haka ne ma malaman tafsiri suka zage dantse suka yi tsayin daka don tabbatar da tabbatuwar wannan hadafi na Allah da wannan manufa ta nubangijintaka da kuma yin riko da hannayen mutane ‘yan zamani zuwa wannan matuka (wato manufa) ta hanyar shimfida tsarin tarbiyantar da kuma suka bube tagogi, don cimma manufifi na tarbiyar ruhi da irfani.
Kuma a nan za mu iya yin nuni zuwa cewa hakika wannan lamarin ya kasance ya takaitu zuwa wani haddi musamman a cikin tafsirai na irfani, wadanda suka shahara a zamanin da ya gabata, amma a yau a sakamakon kalu bale da matsalolin da dan’adam ke fama da su, an wayi gari mafi, yawan tafsirai na zamani suna bawa wannan bangare na dan’adamtaka mihimmanci kuma sun dage matuka wajen tabatar da wannan hadafi na Kur'ani mai girma.[7]
Daga cikin tafsiran da suka yi rawar gani a fagen warware lamarin tarbiyya a tsaka-tsakon tafsiran Shi'a, akwai: Tafsirul amsal da tafsirin min hudal kur’an na sayyid Muhammad Takiyi Ahmud Arrisi, da tafsiri Rushan na Hasan musdafa, da tafsiri Asan = muyassar, na Muhammad Alnajafi da tafsiri min wahayil kur’an na sayyin Muhammad fadhlullah. Amma tafsiran sunna da wadanda suka kunshi wannan bangaren wadanda suka zo a sahun farko daga ciki akwai altafsiril munir na Wahab Alzuhaili, da fafsiri aisarul tafasir na Abibakar Aljaza’iri da tafsiri fi Zilalil Kur'ani.
Kuma a nan za mu iya yin nuni zuwa cewa hakika wannan lamarin ya kasance ya takaitu zuwa wani haddi musamman a cikin tafsirai na irfani, wadanda suka shahara a zamanin da ya gabata, amma a yau a sakamakon kalu bale da matsalolin da dan’adam ke fama da su, an wayi gari mafi, yawan tafsirai na zamani suna bawa wannan bangare na dan’adamtaka mihimmanci kuma sun dage matuka wajen tabatar da wannan hadafi na Kur'ani mai girma.[7]
Daga cikin tafsiran da suka yi rawar gani a fagen warware lamarin tarbiyya a tsaka-tsakon tafsiran Shi'a, akwai: Tafsirul amsal da tafsirin min hudal kur’an na sayyid Muhammad Takiyi Ahmud Arrisi, da tafsiri Rushan na Hasan musdafa, da tafsiri Asan = muyassar, na Muhammad Alnajafi da tafsiri min wahayil kur’an na sayyin Muhammad fadhlullah. Amma tafsiran sunna da wadanda suka kunshi wannan bangaren wadanda suka zo a sahun farko daga ciki akwai altafsiril munir na Wahab Alzuhaili, da fafsiri aisarul tafasir na Abibakar Aljaza’iri da tafsiri fi Zilalil Kur'ani.
- Bawa bangaren zamantakewa muhimmanci
Malaman tafsiri bayan da suka bibiyi bukace-bukacen yau da kullum sun mihimmantar da nusar da mutane kan tushen zamantakewa a cikin Kur'ani mai girma kuma ba su isu da cirato ruwayoyi da hikayoyi magabata da ma’anonin luga ba, ballantana ma sun kutsa kuma sun yi nitso cikin can cikin kogin ayoyi masu girma don su cirato ilimomi masu yawa daga cikinsu, su warware matsalolin zamantakewa mutunen wannan lokacin ta yadda ma’anar zata yi daidai da yaren zamani ya yadda su wadanda ake magana da su suke ta hanya mai jan hanakali.
Hakika masu wannan mafuskantar sun iya su magance matsalar camfi da surkulli da rudani da tsammace-tsammace na karya daga fagen tafsiri kuma sun canja su da warwara ta hakika da ta yi daidai da hankali suna masu tabbatar da cewa Kur'ani ya cancanci ya magance matsalolin dan’adam a cikin dukkanin lokuta da zamanoni tare da ko wane irin sauyin da mutane suka sami kansu a ciki.[8]
Hakika masu wannan mafuskantar sun iya su magance matsalar camfi da surkulli da rudani da tsammace-tsammace na karya daga fagen tafsiri kuma sun canja su da warwara ta hakika da ta yi daidai da hankali suna masu tabbatar da cewa Kur'ani ya cancanci ya magance matsalolin dan’adam a cikin dukkanin lokuta da zamanoni tare da ko wane irin sauyin da mutane suka sami kansu a ciki.[8]
- Bawa dukkanin bangarorin tafsiri mihimmanci
Ya kamata ga malamin tafsiri ya zama bai kayyade kan sa da wani kaidi ko wata iyaka ba, kuma kar ya dogara da bin hanya daya jal, ya haramtawa kansa yin amfani da manuniya ta hankali da ta nakali ba, balle ma ya zama lalle ya dogara da sama da hanya daya kuma ya zama sama da salo daya a wajen tafsirin ayoyi tare da la’akari da manuniyoyin da kuse kewaye da ayar (na hankali da na nakali da na Kur'ani) kuma wannan ita ce hanyar da mafi yawan malaman tafsirin zamani suka zaba suka dagara da ita wajen yin tafsiri.[9]
[1] Alawi mihr Husain a cikin ashanyi ba tarikhi Tafsiri wa mufassirun, shafi 357 kom, markazul alami lil ulumul islamiyya, bugu na farko, 1384.
[2] Masdarin da ya gabata shafi 358. Da jawadi amuli Abdullahi a cikin tafsiri nasim, tahkikin islami, Ali j1 shafi 169-170, bugu na takwas 1388.
[3] Surar fath, aya ta 10.
[4] Makarim shirazi, nasir a cikin tafsirin amsal shafi na 38, kom nasli jawan, ba tarihin bugawa.
[5] Sarar bakara aya ta 185.
[6] Surar isra’i, aya ta 9.
[7] Ashanyi ba tarikhi tafsiri wa mufassirun, shafi na 360.
[8] Masdarin da ya ganata shafi na 361.
[9] Ridha’i, isfahani, Muhammad Ali dar amadi bar tafsiri ilmi kur’an, shafi na 130, kom uswah, bugu na daya, 1375.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga