advanced Search
Dubawa
10756
Ranar Isar da Sako: 2009/12/05
Takaitacciyar Tambaya
miya sa Allah madaukaki bayan siffar sa ta rahama {arhamar rahimin} kuma a lokaci daya yai ummarni da hukunci wanda zai iya kaiwa ga kisa {kamar kisasi, yanke hannu da kafa,}?
SWALI
miya sa Allah madaukaki a cikin Kur’ani mai girma bayan ya bayyana kansa mai rahama mai jinkai amma alokaci daya kuma yai ummarni da hukunci wanda zai iya kaiwa ga hadin kisa {kamar kisasi, yanke hannu da kafa}?
Amsa a Dunkule

Idan muka lura da ayoyi da ruwayoyi da suka zo za mu fahimci cewa Allah madaukaki bayan siffofi na mai rahama mai jinkai {rahmanin rahim} alokaci daya kuma ya na da siffofi na tsanani da fushi; ma'ana shi mai gafarta zunubi ne, kuma mai tsanani azaba ne.

A mafiya yawan lokaci a cikin Kur’ani mai girma duk yayin da maganar azaba ta zo a gaba kuma maganar rahama da gafartawa za ta zo. Amma ba makaki wannan na nuni ne da daya daga cikin falalolin mutun masu kyau shi ne rayuwa tsakanin tsoro da tsammani domin tsai da dai daito a cikin rayuwar sa yanda ba zai zama mai girman kai da ayoyin rahama ko kuma ya fidda rai daga rahamar Allah, saboda haka Allah madaukaki ba wai mai rahama ba ne kadai da mutun zai ce me ya sa ya yi ummarni da hukunci yadda har zata kai ga kisa {kamar yanke hannu da kafa} domin rahama da hukunci mai tsanani ba zaka hada su a wuri daya ba.

Tabbas dukkan wanda ka ga an hukunta ko kuma an yi ma sa kisasi to ya aikata laifine mai girma ko kuma ya take hakki na Allah ko na wasu mutane wanda aikata hakan zai iya kawo fasadi a cikin al'umma, saboda haka domin kiyaye al'umma da rayuwar yau da gobe dole ne a yaki irin wannan mugayen halaye. Da farko rahamar Allah ma nufin kiyaye al'umma da fadawa cikin fasadi.

Rahamar Allah ita ce ke sawa a shimfida dokoki, wanda sakamakon hakan zai sa laifuka su yi sauki. Don haka muna da yarda da cewa kisasi {kisa ko yanke hannu} da makamanci haka ba su da sabani da siffofin ubangiji na mai rahama mai jinkai ba sai ma dai mu ce mai rahama mai jinkai ya na nufin wanda zai shimfida dokoki domin gujewa al'umma fadawa cikin fasadi.

Amsa Dalla-dalla

Idan a ka lura da tambayar da a kayi a sama za aga cewa an kwama abu biyu ne wato sakama kon rashin bambamcewa tsakanin abu biyu;

1, shin Allah mai rahama ne kadai?

2, shin hukunci da kisasi ba su saba da siffar mai rahama mai jinkai na ubangiji ba ?

Idan muka lura da ayoyi da ruwayoyi za mu ga cewa Allah madaukaki ya hada siffofi masu kyau: ta wani bayanin Allah madaukaki ya hada dukkan siffofin da suka tabbata akan sa da wadan da suka koru a kan sa: da ma'anar cewa yanda yake da siffofi na rahamaniya da rahimiya, haka kuma yana da siffofin na fushi da tsanani, in ya yi bushara da aljanna sai kuma ya tsoratar da wuta[1]. in kuma ya yi albishiri da gafarar sa sai kuma ya tsoratar da azabar sa, saboda haka zamuga cewa annabinsa {s. a. w} mai bushara ne kuma mai gargadi ne[2].

Allah madaukaki mai gafarta zunubbaine kuma mai tsananin azaba ne, a cikin ruwaya da adu'oi na masumai (a.s) ya zo gare mu shi Allah {s. w. t} ta bangare daya mai rahama mai jinkai kuma da bangare daya ya bayyana kan shi da mai tsananin kamu[3].

Tsoro da tsammani

A cikin Kur’ani duk inda aka ambaci mai alkawali {na aljanna} kuma sai a ambaci mai bushara {da wuta} a kuma gefen mai bushara sai kuma mai gargadi ya zo, domin a samu dai dai to tsakanin abu biyu wato tsoro da tsammani: saboda mutum mai san kan shi ne da nai man dukkan abin da zai amfanin sa da kuma kare dukkan abin da zai cutar da shi[4]. A wani bayanin a cikin Kur’ani duk lokacin da maganar gargadi da azaba ta zo aci gaban maganar kuma mai rahama da gafara zata biyo baya, ba mamaki hakan sakamakon daya daga cikin falalolin dan Adam masu kyau shi ne ya na rayuwa tsakanin tsoro da tsammani domin dai daituwa domin kar yazama mai girma kai da rahamar ubangiji kuma kar yazama mai fidda tsammani daga rahama Allah {s. w. a} kamar yadda Allah {s. w. a} yake cewa: babu mai fidda tsammani daga rahamar Allah {s. w. a} sai al'ummar da take kafira[5]. Don haka dole ne ka zamo tsakanin tsoro da tsammani. ya zo a ruwayar ahlulbait (a.s) cewa: dole tsakanin tsoro da tsammani su zama tamkar abun ayo ta yadda ba wanda zai rinjayi wani. Tsoro da tsammani na daya daga cikin asali biyu na imani da akhlag imani ba zai taba cika ba face da wadannan abu biyu {tsoro da tsammani}[6].

Idan muka lura da wannan bayani za mu ga ne cewa Allah {s. w. t} bayai kawai siffar rahamani rahim ya kadaita da ita bad a za mu ce bata dace da hukunci wanda zai kai har ka kisa ko kuma yanke hannu da kafa. Shin in muka fidda sauran siffofin Allah {s. w. t} shin hukunci ko kuma kisasi, yasaba da siffar mai rahama mai jinkai?

Tabbas dukkan wanda aka yanke ma hukunci kisa ko kisasi toh ya aikata wani mumunan abu ne ko kuma ya take haki ne na Allah {s. w. t} ko kuma na mutum dan uwan shi, wanda aikata haka agaskiya zai jayo lalacewa da fasadi a cikin al'umma domin kare al'umma daga fasadi {wanda a cikin musulunci aka tanadi hukunci da kisasi} a nan akwai nau'I biyu na fito na fito, na daya fito na fito wanda ba tsanani cikin sa, kamar tara, ko kuma dauri gidan yari, sai kuma nau'I na biyu, kamar kisasi da hudud {kisa ko yanke hannu} wanda shi ne musulunci ya tsaba ; saboda a mahangar musulunci kamar yadda masu hankali ke cewa, mutunci da daraja ta al'umma yafi mutunci da daraja na mutun daya. saboda haka kisasi ba yana nufin ramuwa da daukar fansa ba ne a'a sai dai yana nuni da cewa rahamar ubangiji shi ne kare al'umma daga lalacewa da fadawa cikin fasadi saboda haka ne Allah {s. w. t.} ya shimfida shari'a domin tagaita aikata miyagu laifuka. Ta wata fuskar za mu fahimci cewa kisasi da haddi ba su kishiyanta da mai rahama mai jinkai ba sai ma dai mu ce mai rahama mai jinkai shi ne wanda zai sa dokoki domin kyaran al'umma. Kamar yadda Allah madaukaki ke cewa; a cikin kisasi akwai rayuwa ya ku masu ilimi ko kun samu tagawa[7].

A gaskiya kisasi da hadi a musulunci was u abu ne da suke shiryada mutun a cikin rayuwa shi kuma ya taimaka domin kyaran al'umma baki daya;

Saboda da Allah madaukaki ba sai dokoki da shari'a ba da miyagun mutane sun samu dama ta yadda za su cutar da marasa laifi. Kuma miyagun aiyuka zasu yadu a cikin mutane; amma in akwai dokoki shi kansa mai laifi zaiji tsoron aikata laifi din. a bangare guda dokoki suna kawo dai daito a cikin rayuwar yau da gobe, kuma suna hani ga daukar fansa kamar yadda larabawan jahiliya suka kasance in mutun ya aika ma wani laifi daya toh shi kuma wajan kokarin daukar fansa sai ta kais hi ka aikata laifuka masu yawa. Amma a musulunci abin da ka shufka shi ne zaka girba yadda kayi haka za a'yima.

In muka lura ko da a cikin ilimin likita da na noma za ka samu suna aiki da wannan dokar da hankali mutun ya tsara na cewa afitar da abin da yake marar kyau a cikin mai kyau domin kada wannan marar kyau ya bata abu mai kyau, likita yana yanke wani bangare daga jikin mutun domin ya lalace in kuma aka bar sat oh zai shafi bangare mai lafiya haka ma manoma suna cire wani reshe dan kada ya damu asalin bushiyar har yai mata illa.

Misali, masu cewa kashe wanda ya kashe wani kamar rage al'umma ne, toh sai mu ce mahangar wadannan irin mutane mahanga abu daya ne wato masalahar mutun daya, amma da zasu dubi masalah da baki daya da sun gano yadda kisasi yake taka muhimmiyar rawa wajan kyara da kuma tarbiyar al'umma, saboda haka kauda mayagun mutane daga cikin al'umma kamar yanke bangaren da ya lalace ne a cikin jiki ko kuma yanke reshe da ga asalin bushiya domin kar ya damu sauran,

Kuma har ya zuwa yau ba bu wanda ya taba magana domin ya ka wani na yanke bangare da ga bushiyar sa wanda kuma wannan bangaren da aka yanke in aka bar sa toh zai bata sauran itacen[8].

Daga karshe; da farko kamar yadda Allah ya ke da siffa mai rahama mai jinkai haka kuma ya ke siffa mai tsanani kamu.

Na biyu; hukunta masu laifi na mahanga ta farko kamar rashin tausayi, amma in kuma aka yi la'akari da aikin da suke aikawa za mu fahimci hikimar sa dokoki a cikin al'umma kuma zai sa al'umma da zama cikin aminci da amana don haka kisasi ko haddi a cikin al'umma ya zama dole.

Ya kama ta mu ambaci wani abu a nan kamar haka;

Ya zo cikin ruwaya cewa; dukkan wanda a kai ma hukunci a nan duniya sakama kon aikata wani laifi da ya yi ranar lahira ba za a hukunta shi ba;

Ta wata fuskar duk wanda a ka hukunta a wannan duniyar sakamakon ya aikata wani laifi toh gobe giyama ba za a sake yi masa hukunci ba sakamakon wannan laifin, wannan na daya daga cikin rahamar ubangiji madaukaki[9].

Afarkon musulunci da yawa wasu mutane domin neman guje wa azabar lahira sai suka kai kan su gurin Imam (a.s) domin ya yanke masu haddi[10] {hukunci} tun a nan duniya domin kamun ubangiji mai tsanani ne.

 


[1] Suratul yasin 63

[2] Suratul hud 2

[3] Tabarasi, tahzibul'ahkam, jildi na 3 shafi na 108, darulkitab islamiya, Tehran, 1365 h

[4] Mukarim shirazi, nasir, tabsire namune, jildi na 1, shafin na 273, bugawa darulkitabul'islami, Tehran bugu na daya, 1374 shamsi

[5] Yusuf, 87

[6] Amin sayyide nusrat, al'irfan acikin tafsirin Kur’ani, jildi na 2, shafi na 262 zuwa 263, yadawa nahazat zanan . bugun Tehran, 1361 shamsi,

[7] acikin kisasi akwai rayuwa ya ku masu ilimi ko kun samu tagawa Bakara, 791

[8] Mukarim shirazi, nasir, tabsire namune jildi na 1 shafi na 606 da 607

[9] Kulaini, kafi, shafi na 445 jildi na 6 amiralmumini {a. s} acikin tabsirin maganar Allah madaukaki ;

[10] Wata mace ta zo wurin imam ali {a. s} tana neman ya yanke mata hukunci sakamakon zina da ta aikata domin ta tsarkaka daga wannan zunubin tana cewa ina tsoron in mutu in bar duniya cikin kazanta. Ana iya neman cigaban wannan hadisin acikin baihar anwar jildi na 76, 45 da kuma manlai yahzarulbaki, tarjamar gaffari jildi na 5 shafi na 356 zuwa 358

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa