Please Wait
16316
Gwamuwar jin tsoron Allah da kaunarsa, a wasu lokutan kuma kaunarsa kawai, dangane da Allah ba wani al’amari ba ne da yake bako, domin shi ya cika dukkanin bangarorin rayuwarmu, amma saboda tsananin bayyanarsa sai mu din muka rafkana da shi.
Mu sani cewa har matafiya da muke yi wadda muke aiwatar da ita, ita kanta tana daga cikin sakamako na tsoro da kuma kauna da fata na Allah a kanta, domin ba don muna da fata da buriba to da ba mu tashi mun yi tafiyar ba, da a ce ba ma tafiya to ba za mu kai ya zuwa manufa ba, sannan da a ce ba ma tsoron da ba za mu taba hattara a cikin tafiyarmu ba game da abin da zai haifar mana da cutuwa, haka nan ma ba za mu taba kaiwa ya zuwa ga hadafi ba..
Wannan al’amarin yana bayyana karara a yayin da muke amfani da hanyoyin daukar kaya, ko kuma kayan na’urar lantarki ko na kayan zafi da makamantansu, saboda muna yin amfani da wadannan kayayyaki da na’urori ne cikin sauki, sai dai a ce yin amfani da su din ba mu gwama shi da jin tsoro da fata ba da kuma yin hattara, to kusantarmu da su zai zama dalili na halakarmu da rugujewa.
A kan haka sai ya zama wajibi mu ce lallai ya wajaba mu ji tsoron Allah kamar yadda ya wajaba mu kaunace shi da kyakkyawan fata a gere shi, domin kaunarsa da shaukinsa da fatansa shi ne zai tabbatar mana da alaka da shi ta wata fuska. Ta wani bangaren daban kuma wannan shi zai yunkura mu ya zuwa ga yin motsi da yin kai-kawo da rigegeniya sabida tsururutar abin da zai wajabtar mana da yardarsa, a karshe kuma mu kai ya zuwa ga samun kwararowarsa da tausayinsa da kuma falalar duniya da ta lahira. Jin tsoronsa kuma zai kai mu ya zuwa ga kankan da kai da mika wuya da gogoriyo domin yin biyayya a gare shi da kuma barin saba masa, da nisantar duk abin da zai wajabtar da tilascinsa da azabarsa da fushinsa.
Hadakar nan ta jin tsoron Allah da kaunarsa a wannan duniyar dangane da daidaikun mutane matsakaita ta kankasance dalili na samun sakina da nutsuwa da gasket daga dukkanin wata cutuwa da tsoro na lahira, wannan duniyar ita ce wurin da za a yi aiki da nema, wanda yin aikin da neman a cikinta yana da bukatuwa ya zuwa ga tsoro da sa ido da kuma kiyaye aikin da samun annaba, saboda mu kai ga samun bukatarmu a gidan lahira, idan har aikin ya zama kubutacce to a can babu bukatar tsoro wurin aiki da nema.
Jin tsoro shi kadai kawai zai zama dalilu na yanke kauna da tashin fata da kuncin fuska da damuwarta, haka nan kuma da fata kawai zai zama dalili na samun rudin kai da yaudaruwa da kan da kuma yin aiki kara zube da hauhawar zunubai dukkanin wannan al’amuran biyun abin zargi ne.
Jin tsoro da kauna da kuma fata suna daga cikin al’amura na halayyar gini tad an Adam wadda ba ta da bukatuwa ya zuwa ga bayanin ma’anar ta mutum yana da ikon da jin tsoro da firgici zai iya aurarsa sakamakon wasu al’amura da yawa daga cikin akwai:
- Gudun fadawa hadari da cutuwar mutum shi a kashin kansa, ko dukiyarsa ko kuma mutuncinsa da makamantansu.
- Fahimtar girma da haibar al’amari, ko kuma wani abu daban.
- Jahiltarsa ga karshen abubuwa da abin da zai biyo baya na aikace-aikacensa ko kuwa mai zai je ya dawo a makomarsa da makamancin haka.
Zai iya yiwuwa wadannan al’amuran baki daya su iya tattara a wasu lokuta a kan abu daya. Haka nan jin kauna da ta’allakuwa da wani abu zai iya haifar da wasu abubuwa daga cikinsu akwai:
- Jin kyau da fizga ne abin kauna da kuma danfaruwa da shi ta wata fuskar daban, tare da karkatuwa ya zuwa ga waccan kyan. Daya daga cikin mawaka yana la’akari da wannan kaunar cewa yana bubbugowa ne daga kaye na launoni kuma makomarsa tana kaiwa ne ya zuwa ga jin kunya da tsaraituwa, sai dai wannan abin ba ka’ida ce gamammiya ba ta dundundun, kadai wannan yana gasgatuwa ne kawai a yayin da wannan kyawun ya gushe ya lalace, ya kuma zama hoto.
Amma idan ya zama da kamalar kyau ne kima da halayya ko kuwa ya zama kyau ne na samuwa na hakika, to soyayyar a wannan lokaci zai zama dalilinta ba na launi ba ne, da rini kuma makomarta ba za ta zama ta abin kunya ba, kai karshen abin ma zai zama mu sayari rinuwa ne da tasirantuwa juna da juna tare da abin kaunar.
- Jin bukatuwa da talauci ya zuwa ga abin kauna da kuma tsammanin amfanuwa daga wanda kake kauna a kan tafarkin kaiwa ya zuwa ga manufa, to shi wannan mai kauna zai nemi abin kaunar tasa saboda ya amfana ba wai don zatin abin da yake kauna din ba ne kawai.
- Kaunar da samu ta hanyar jin a jiki na cewa tilas ne a gode wa wanda yayini’ima, kuma shi wannan mai kaunar ya danfaru da wanda yake wa kaunar sakamakon kyautatawa da ni’imomin da yake masa a inda ya zama abin jinginarsa ga wannan kyautatawar da yake a gare shi.
- Shi wannan abin da ake nunawa kauna zai zama mai neman kaunar wanda yake kaunar tasa, tare da son jawo shi da sauran ire-irensu. Akwai yiwuwa r wasu dalilai da yawa da za su tattaro na nuna kauna ya zuwa ga abin kauna kwaya daya.
A yayin da muka zurfafa bincike za mug a cewa dukkanin ayyukanmu da mayar da raddinmu, a hakika fassara ce ta jin tsoro da kauna wadanda suka tattara suka cakuda wuri guda, amma daya ya kanrinjayi guda a wasu lokuta, gwajin ba wai madauwami neb a a tsakaninsu, sai dai wannan haduwar da cakuduwar da yake tsakanin tsoro da fata wato (kauna) al’amari ne da ba zai yiwu a nisance shi ba. Na’am, za mu iya rafkana da shi a sakamakon tsanin bayyanarsa, saboda su wadannan al’amura guda biyu suna da tasiri a kanmatafiyarmu, a inda buri da kauna suke tsayuwa da yunkurarmu ya zuwa ga aiwatar da ayyukanmu na yai da kullum. Kai har ma sukan samu aiwatar da abubuwa masu hadari ma, a yayin da bangaren hattara da sa ido da kuma auna ayyukan da gwaji wajen abubuwan da suke haufarwa da kuma tanadar share fage su.
Da a ce fata da kauna su kadai ne kawai a samuwa to lallai a wannan lkaci ba za mu rika tunanin yin hattara ba, daga baya kuma mu auka cikin halaka ta gaugawa, haka da a ce tsoron ne shi kadai kawai to nan ma da ba mu sami damar mu iya gabatar da kowane irin aiki ba ko da misalin cid a sha ne, hakankuwa ya faru ne sakamakon tsammanin cewa akwai yiwuwa r a yayin da muke shan abin abin shan wani digo na ruwa, shan ya iya shiga wata kafa ta jijiya ko kuma wata loma ta abincin ta toshe wata hanya ta jijiyar yayin cin, wanda hakanzai iya jawo mutuwa. A kan haka lallai yana daga cikin abin da zai tayar da mamaki shi ne bukuntar iya haduwar tsoro da kuma dangane da Allah madaukaki, saboda haka zai ganar da mu fadakar sanin kanmu da halinta, karin bayani a kan haka:
Tabbas muna tsoro da fata da kuma kauna ga Allah madaukaki, darajojinsu sukan bambanta tsakanin wani mutum da wani hakankuwa daidai gwargwadon sanin mutum da Allah da siffofinsa na kyau da tajalli (bayyana), da kuma sauran sanin addini, wannan fa wata fuskar ke nan.
Ta wata fuskar kuma nutsuwar mutum ko rashin nutsuwarsa game da makomarsa da karshensa haka nan suma kawo gwargwadon darajoji ne, wadanda kwarjini da girma da bayyanar Allah ta ja su, su kuma wadanda suke aikata zunubai da sabon da ba sa kiyaye fadin Ubangijin nan to to tsoronsu ya kanrinjayi kaunarsa da fatansu. To haka nan akasin wadanda kyawun rahamar Allah madaukaki ta kanja su, su rika jin dadin tausayinsa da kulawar da yake musu, saboda a hakika sun kiyaye bangaren hattara game da ayyukansu da suka riga suka gabata na rayuwarsu sun kuma kuma da bangaren yi wa Allah ladabi a fadar Ubangiji, duk da cewa kafafuwansu a wasu lokuta sukan zama to sai su ga kofar tuba da rahamar Allah a bude, sai su tuba irin tuban nasuha, to irin wadannan kaunarsu da fatansu sukan rinjayi tsoronsu.
Amma wasu kuma wadanda suke tsaka-tsaki a ayyukansu su ba sa samun nutsuwa game da abin da ya gabata na ayyukansu da karbarsu, su ma suna jin tsoron rashin samun tsiransu a sakamakon fushin Allah da kyautarsu da mutuntukarsu, irin dai wadannan mutane za a iya samun gwaji tsaknin jin tsoron rashin samun tsiransu a sakamakon fushin Allah da azabarsa, a lokaci guda kuma suna fatan afuwar Allah da kyautarsa da mutuntakarsa.
Irin dai wadannan mutane za a iya samun gwaji tsakanin jin tsoronsu da fatansu da kaunarsu, sai dai abin da yake muhimmi shi ne mafi rinjayen mutane jin tsoro da fata a wajensu yana tasowa ne daga son raid a kuma dabi’ar nan ta jawo wa kai amfani da kare shi daga cutuwa. Abin da ake nufi shi ne, mafi yawan mutane suna jin tsoron ukubar Allah ne a ranar lahira, sannan haramcin da za su samu na rashin kwararowar falalar Allah da rasawarsu ga ni’imomi da jin dadin aljanna da matan Hurul’in da manyan gine-gine!
Su dai wadannan suna bayyanar da kaunarsu da fatan su ga Allah, amma kuwa wadanda kyawu da kamalar Allah ta fizge su ko kuma kwarjinin Allah da buwayarsa da girmansa ya firgita su, ko kuma wadannan al’amuran guda biyu suka tattara a gare su, duk da cewa irin su ‘yan kadan ne wadanda ba wanda yake kaiwa ya zuwa ga wannan matsayi in ban da annabawa da wasiyyarsu, sai kuma wasu ‘yan kadan da ba su ba.
Amirul muminin Ali amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya yi bayanin wadannan tattararrun abubuwa guda uku a cikin zantukansa na hikima inda ya ce: “Wasu mutane suna bukatuwa Allah don kwadayinsu a gare shi, to wannan ita ce ibadar ‘yan kasuwa, wasu kuma suna bauta wa Allah don firgita su da ya yi to wanan ita ce ibadar ba yi, wasu kuwa mutanen daban suna bauta wa Allah don gode masa, irin wannanan bautar ita ce ta ‘yantattu”[1], saboda wannan dalili ne sashen wasu malamai suka ce (lallai kauna) daya ce daga abubuwa manya-manya da ake tattauna su a cikin abin da ya shafi tarbiyya da koyarwa a cikin musulunci, kuma Kur’ani maig irma shi ne mai koyar da hali na gari shi kuma yana la’akari da cewa kauna tana daga manya-manyan abubuwan da ake tattaunawa a kansu a halayya.
Imam Assadik amincin Allah su kara tabbata a gare shi yana cewa: “Tabbas Allah mai girma da da buwaya ya ladabtar da annabinsa a kan ya kaunace shi”.[2]
Matsalar nan ta gargadi (tsoratarwa) da yin bushara (kwadaitarwa), sun zo da yawa a cikin Kur’ani mai girma da kuma ruwayoyin Alhlulbaiti amincin Allah su kara tabbata a gare shi, sai dai dangane da wadansu mutanen raunana ta kanzama ita ce marhala ta karshe, amma dangane da ‘yan tsakiya ta kanzama kamar share fage ne da tsani yayin da wannan ya kanmotsa mutum tun farkon faraway a kan hanyar ladabtarwa da kwadaitarwa, a hankali a hankali kuma yana zama wannan motsin nasa ya kai shi ya zuwa ga sanya kauna a zuci.[3]
A doron wannan asasi bai kamata a yi mamaki game da hadewar tsoro da fata ga Allah ba, kai hadewar tsoro da fata da muke magana a kansa ma ya zama wata larura daga tarbiyyar mutum da kamalarsa, domin da jin tsoron ne mutum zai nisanci sabo da fadawa halaka da kuma jawo wa kai abin da zai haifar da fushin Allah da azabarsa, sai dai kankan da kai da jin dukufawarsa da biyayyarsa ga Allah ya karu, ta hanyar so da kauna din kuma sai ya sami sauki da fuskantar sauke wajibai da nafilfili da yin rigegeniya ya zuwa ga abin da zai wajabtar da jin tausayin Allah da ni’imominsa da rahamarsa a gare shi.
Da wata fassarar takaitacciya kuma, sakamakon jin tsoron Allah da fatan wani abu a gare shi shi ke sanya a rika rigayeyeniya ya zuwa aikata alkhairai da ma sifantuwa da kyawawan dabi’u da kuma nisantar sharrance-sharrance da aikata sabo da kuma wofinta daga miyagun halaye, wannan ita ce kamalar da ake nema wadda Allah yake da hadafinta yayin da ya halicci mutum, wadda take nufin mutum da ya runu da rinin Allah don ya kai ya zuwa ga mukamin nan na halifantar Allah, da kuma ni’imtuwa da ni’imomin Allah a ranar lahira, ya kuma sami tsira daga cutuwa da firgici hakika Allah mai tsarki ya yi ishara ya zuwa ga wannan sakamako a wurare da yawa, kamar fadinsa madaukaki da ya ce:
“... Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira ya kuma yi aiki na gari, to ire-irensu suna da lada a wajen Ubangijinsu, sannan babu tsoro da bakin cikin a gare su”.[4]
Idan kuwa ba haka ba, tsoro kawai shi kadai yana haifar da Gajiyarwa da yanke tsammani da barin tuba tare da kuma dulmiya cikin zunubi da sabo da makamancin wannan, a karshe kuma ya kanhaifar da aukawa cikin damuwar duniya da lahira. Haka nan kuma ita kadai tana haifar da yin abu kai tsaye da hauhawar sabo da kuma tsammani na karya na rahamar Allah da hudufinsa, alhalin cewa matukar mutum ba ya kan hanya ta tsururutar dalilan da za su ya haifar wa kansa jinkai da rahamar Allah, to ba zai yiwu ya buraci rahama da tausayin Allah ba, saboda haka nan ne imam Husain amincin Allah su kara tabbata a gare shi a du’a’u Arfa yake cewa: Idanuwan da ba sa ganinka a matsayin mai sa ido ta makanta, yin tafin bawan da bai sanya kaunarka ta zama masa rabautuwa ba ta yi hasara.
Idan haka ne abin da ake samu game da wannan tsoro da kauna na sakamako yana bayyana ne a ranar lahira, imam dai lahira ta zama wuri na azaba da shan wahala tsantsa, hakanga wadanda ba su kiyaye wannan ni’ima ko kuma debe tsammani ya same su suka nutsa cikin sabo, ko kuma suka yaudaru ba su dauki wani guzuri ba a tare da su, ko kuwa dai lahirar ta zama wuri ne na ni’ima da samun tsantsar nutsuwa daga firgici da tsoro, wannan kuwa ga wadanda suka kiyaye daidaito tsakanin jin tsoro da fata, suka nisanta suka yi rigegeniya wajen neman guzuri a kan neman alhairai domin lahirarsu.
Domin yin mudala’a mutum zai iya komawa ya bincika tsoro da fata ko kuma da wilaya a litattafan Ahlak:
- Mata kanAkhlak a cikin Kur’ani na Ayatullahi Jawadi Amuli, shafi na 279-340.
- Sharhin arba’una hadisi na imam Khumaini, Allah ya tsarkake sirrinsa, shafi na 221-233.
- Akhlakul Kur’an na Muhammad taki Misbah Al-Yazdi, bincike a kan tsoro da fata.
[1] Nahajul balaga gsjerun kslmomi 273.
[2] Albiharul anwar l. 17:3.
[3] Abdullahi jawadi a muli marhalolin akhlak a cikin Kur’ani, shafi 220- 232.
[4] Albakara 62 da ma’ida 69.