advanced Search
Dubawa
5039
Ranar Isar da Sako: 2016/08/29
Takaitacciyar Tambaya
Akwai wani mutum da Manzon Allah (s.a.w) ya taho da shi daga Kasar roma, shin wannan mutumin shi ne dai Yasir baban Ammaru?
SWALI
Akwai wani mutum da Manzon Allah (s.a.w) ya taho da shi daga Kasar roma, shin wannan mutunim shi ne dai Yasir baban Ammar ko kuma wani mutumin ne daban ba shi ba, ina fatan zaku yi mini bayani.
Amsa a Dunkule
Baban Ammar sunansa Yasir Dan Aamiru Anasi, ya kasance mutumin Yeman ne[1] daga yankin muzhij, daga Kabilar “Anas”[2] har lokacin da ya isa samartaka ya kasance ya na rayuwa a Yeman, yana da Yan’uwa guda uku sai aka rasa Daya daga cikin su (ya Bata) don haka shi da ‘yan’uwansa guda biyu waDanda ake kira da Malik da Haris suka haDu suka biyo sahun Dan’uwansu da ya Bata har suka iso makka suka fara bincike suna nemansa, amma kash har suka Debe tsammani daga samunsa. Sai Malik da Haris suka koma Yeman, amma Yasir, sai ya zauna a maka kuma ya Kudurci zama na dindindin a nan.[3]
Amma mutumin nan mai suna Yasir wanda Manzon Allah (s.a.w) ya taho da shi daga kasar roma a zahiri wannan mutumin ba shi da samuwa a sarari, kamar yanda, a lokacin da inbi Hajar AsKalani yake jero sunayen sahabban Manzo (s.a.w) da ya zo kan masu suna Yasir, sunan mutum uku kaDai ya jero: Yasir Dan Aamir Anasi, da Yasir Dan suwaidul Juhaini da kuma Yasir Abul Rabda’ul Balawi, [4]  wanda ba Daya daga cikin su da ya fito daga kasar Yeman.   
Tabbat akwai wani mutum mai suna “Suhaibu” wanda ya kasance daga cikin sahabban Manzon Allah (s.a.w) wanda asalinsa balarabe ne amma da yake ya zauna tsahon lokaci a kasar rum, sai ya zamana ya shahara da sunan “Suhaibur Rumi” (Suhaibu Dan rum).
 

[1] Ibni hajar al-asKalani, ahmad Dan Ali, al-isaba fi tamyizis sahaba, j 6 sh 500, bairut darul kutubul ilmiyya bugu na Daya, shekara ta 1415.
[2] Ibni sa’ad, kitabul waKidi, Muhammad Dan sa’ad, alDanaKatul kubra, j 4 sh 101, Beirut, darul kurubul ilmiyya bugu na Daya shekara ta 1410.
[3] Adreshin da ya gabata.
[4]  Ka koma Al-isaba fi tamyizis sahaba, j 6 sh 500 – 501.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • Shin ruwayar tashi daga Iran a karshen zamani abin la’akari ce (akwai kuwa)
    8497 Dirayar Hadisi 2012/07/26
    Duk litattafan Shi’a da sunna sun hadu kan cewa bayyanar imam mahdy (AF) wata saura zata share fagen zuwansa (bayyanarsa) zai zama ma’abocin bakaken tutoci a wannan saura su ne masu shimfide alamar kafin bayyanarsa.[1] hukumar iran da aka same ta ta kasu gida ...
  • Yaya asalin mutum yake?
    21891 Tafsiri 2012/07/25
    Littattafan riwaya da na tarihi sun tabbatar cewa dan’adam wanda ke kan doron kasa bai kasance an same shi daga Habilu da Kabilu ba, shi dai an same shi daga dan Annabi Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) na uku mai suna Shisu ko Hibatullah.
  • Mene ne ma'anar jagorancin malami?
    12276 Sabon Kalam 2012/07/24
    Kalmar Wali da larabci tana da ma'ana guda uku: 1-masoyi, 2-aboki, 3-mataimaki. Bayan haka akwai wasu kalmomi kuma da suke nufin; 1-Salladuwa 2-Jagoranci da shugabanci. "Wilaya" kalma ce da ake amfani da ita da ma'ana biyu a isdilahin fikihu: 1- Wuraren da wanda ...
  • Me ya sa Kur\'ani ya fifita yahudawa kan sauran mutane?
    8335 Tafsiri 2017/05/21
    Allah madaukaki ya yi magana kan jikokin Annabi Yakub yana mai cewa {yaa bani isra’ila ....... inni fadhdhaltukum alal aalamin} {ya ku ‘ya’yan Yakub ....... hakika ni ne na fifita ku a kan sauran mutane}. Tabbas wannan ayar ba ta magana kan yahudawan zamanin Manzo (s.a.w) da ...
  • Bisa wane dalili ne zamu yarda ingancin Mu’ujizar Annabawa, ta yadda za’a banbantasu da kwararrun matsafa, da masu rufa-ido?
    5976 ارتباط میان نبوت و معجزه 2017/05/21
    Dalilin gaskata Annabawa a kowa ne zamani shi ne abin da karantarwarsu ta kunsa wadda don ita suke bayyana mu’ujizozi da kan gagari a kwaikwaya. Su wadannan mu’ujizozi suna daga cikin hujjoji bayyanannu da ke kiran mutane zuwa ga imani. Bayan haka akwai bambance-bambance na zahiri tsakanin ...
  • Mene ne feminism? (matuntaka)
    11255 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/09/16
    Feminism lafazin faransanci ne, kuma kalmace ta asalin yaran latin kamar haka ne ta zo da wani banbanci kadan a wasu yarukan kamar turanci da jamusanci, ana amfani da ita da wata ma'ana sananniya feminine, ma'ana ai mace (jinsin mace), femenism kamar wata kalma ce da ked ...
  • Me yasa Allah bai nufin shiryar da mutane gaba daya ba, kuma kowa ya sami alheri?
    12391 Tsohon Kalam 2012/09/16
    Tabbas abin da aka gano a cikin wannan ayar ta 13 cikin Suratul Sujada mai albarka cewa Allah bai so mutane gaba dayansu su sami shiriya ba, wannan maganar ba haka ba ce, hakika abin sabanin haka ne domin Allah ya so kowa ya shiryu domin samun ...
  • Saboda Me Dukkanin Malamai Ba Su Kebanci Lamarin Shugabancin Malami Da Wani Fasali Ma Musamman Ba, Kuma Ba Su Yi Bayanin Dokokin Ko Kace Sharadan Wannan Shugabancini Ba?
    8707 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Wasu daga cikin malamin ba su yi babi ko fasali na musamman ba ga wannan lamarin saboda suna ganinsa abu mai saukin ganewa, wanda kuwa ya sallama a kan sa, kuma babau bukatar yin bahasi domin tabbatar da shi, a yayain da suka bude babobi na musamman ...
  • Illolin wasa da azzakari, manyan zunubai, wankan janaba, dalilan haramci
    86051 2019/06/16
    Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
  • Me ye gwargwadon ikon da aka ba wa wilayatul fakih (Jagorancin malami)?
    7953 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Dalilan shugabancin malami (wilayatul fakih) suna bayyana cewar, fakihi shi ne wanda yake jagorantar al’umma ta musulmi, kuma yake maye gurbin imamai ma’asumai (amincin Allah ya tabbata a gare shi) a zamin da imami yafaku (boye). Ta wannan matashiyar wilayatul fakih (Shugabancin malami) tana da abubuwan da ...

Mafi Dubawa