advanced Search
Dubawa
7603
Ranar Isar da Sako: 2006/05/22
Takaitacciyar Tambaya
me ye sharuddan jagorancin malami?
SWALI
me ye sharuddan jagorancin malami?
Amsa a Dunkule

Sharuddan asasi na jagoran musulunci sun hada da: ilimi, adalci, ikon tafiyar da al'ummar musulmi. Kuma a asalin doka ta dari da tara ta kundin tsarin dokar jamhuriyyar musulunci an yi nuni da wadannan sharuddan kamar haka:

Sharudda da siffofin jagora:

1- siffantuwa da ilimi don bayar da fatawa a kowane janibi a babobin fikihu.

2- adalci da takawa domin jagorantar al'ummar musulunci.

3- Basirar kyakkyawar siyasa da zamantakewa, lura, Jarumtaka,  tafiyar da lamurra da iko isasshe saboda jagoranci.

Amsa Dalla-dalla

A bisa asasin dalili game da jagorancin malami da ya zo, mutumin da zai iya jagorantar al'ummar musulmi shi ne wanda ya kai matakin ilimi, kuma yana iya fitar da hukuncin shari'ar Allah daga madogararta ta littattafai amintattau. Sai dai an yi nuni da wannan mutumin a ruwayoyi, da cewa shi ne "masu ruwaito hadisi ko sunnar imamai ma'asumai (a.s)".

A fili yake cewa wanda ake nufi da mai mai iko kan kan sanin hadisi ko sunnar ma'asumai tsarkaka (a.s) yana nufin mujtahidi, wanda ya san karo da junar dalilai da yadda za a warware wannan karon da kuma yadda za a hada ma'anonin hadisai, da sanadi nagari, da sauran lamurra irin wadannan, ya zama ya san wannan dalla-dalla.

Ta yiwu ya zama an kawo wannan kalma ta maruwaita hadisai da sunnar imamai ma'asumai (a.s) ne a ruwayar da nufin isdilahin "fakihi" ko "mujtahidi" ne yake nufi a wancan zamanin da ya kasance ba a san ta da wannan isdilahin na wannan zamanin ba ne.

Ko kuma zai iya kasancewa malamai a wannan zamanin suna cikin maruwaita ne, duk da kuwa ba dukkan maruwaita ne suke fakihai ba.

Komai dai meye ya kasance, ilimin fikihu yana daga cikin sharuddan wanda zai jagorancin al'ummar musulmi ne a lokacin boyuwar Imami, kuma abin da ake nufi da "ijtihadi maras kaidi" ke nan; wato mutumin da zai iya fitar da hukuncin duk wata mas'ala daga madogarar addini, kuma ya kasance ikon iya ijtihadinsa bai kebanta da wani wuri na musamman ba kamar yadda aka san wannan da sunan "ijtihadi mutajazzi" wanda kawai yana iya yin ijtihadi ne a wani bangaren hukuncin shari'a kawai[1].

Wani sharadin kuma na jagoarnin al'umma musulmi shi ne adalci. Duk da kuwa cewa a bisa dalilin shari'a da aka nakalto wannan sharadin bai zo ba, sai dai hukuncin hankali ba zai iya bayar da ragamar jagorancin al'umma ba wanda ya doru bisa akida ga wanda bai da wani damfaruwa da wannan akidar, kuma ba shi da wata lizimtuwa da dokokinta.

 Ta wani bangaren kuwa muna ganin ayoyi da ruwayoyi da suke kin yarda da biyayya ga fasiki da wanda ba adali ba ko mika masa jagoaranci[2]. Kamar ayar nan madaukaki ya mai cewa: "Kada ka bi wanda muka gafalantar da zuciyarsa daga ambatonmu kuma ya bi son zuciyarsa"[3].

Kuma ya zo a wata ruwaya a Usulul Kafi daga Imam Muhammad Bakir (a.s) cewa, ya nakalto daga manzon Allah (s.a.w) cewa: "Shugabanci da jagoranci ba su dace ba sai ga mutumin da yake da siffofi uku;

1- Tsentseni da yake kare shi daga sabon Allah.

2- Hakurin da yake iya mallakar fushinsa da shi.

3- Kyakkyawan jagoranci ga wadanda yake mulka, har yakasance kamar uba mai tausayi garesu[4].

A wannan ruwayar zamu ga ta kawo wani sharadi wanda hankali yake fahimtarsa, kuma wannan shi ne iya tafiyar da lamurran al'umma. Wato malami adali da zai riki lamurran al'ummar musulunci ya zamanto zai iya tafiyar da lamurran wannan al'ummar, wannan kuma bayani ne da hankali[5] yake karfafarsa[6].

Don haka sharuddan asasi na jagoran musulunci sun hada da: ilimi, adalci, ikon tafiyar da al'ummar musulmi. Kuma a asalin doka ta dari da tara ta kundin tsarin dokar jamhuriyyar musulunci an yi nuni da wadannan sharuddan guda uku ne kamar haka:

Sharudda da siffofin jagora:

1- siffantuwa da ilimi don bayar da fatawa a kowane janibi a babobin fikihu.

2- adalci da takawa domin jagorantar al'ummar musulunci.

3- Basirar kyakkyawar siyasa da zamantakewa, lura, Jarumtaka,  tafiyar da lamurra da iko isasshe saboda jagoranci.

A bisa doka ta farko wannan tana nuni ne da ijtihadin malami, don haka tana nuni a fili karara da samuwar siffantuwar malami da bayar da fata a babobin fikihu mabambanta ba a babi daya ba kawai ne.

Doka ta biyu tana nuni da adalcin jagora ne, kuma tun da adalci ana iya samunsa a darajoji mabambanta, a wannan bayanin an karfafi lizimci samun adalci ga jagoranin al'ummar musulmi.

A doka ta uku an yi bayanin isuwar jagora ne, wato ya kasance mai basira kyakkyawar siyasa da zamantakewa, lura, Jarumtaka,  tafiyar da lamurra da iko isasshe saboda jagoranci, da wannan yake nuni da ikon nazari da aiki na tafiyar da lamurran al'umma ne.

 

Karin Bayani:

1. Mahdi Hadawi Tehrani, Wilayat wa Diyanat, Mu'assar Al'adun Khaneye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.

 


[1]. Jawadi Amuli, wialate fakih, s 121 – 122, sayyid Kazim ha'iri, "Asasul Hukumatil Islamiyya, s 247.

[2]. Muntazari, wilatul fakih: j 1, s 289 – 300.

[3]. Kahf: 28.

[4]. Kulaini: alkafi: j 1, s 407.

[5]. Ana cewa da wannan: Irtikazul Akali.

[6] Muntazari, wilayatul fakih: j 1, s 319 – 327.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa