advanced Search
Dubawa
5732
Ranar Isar da Sako: 2019/06/16
Takaitacciyar Tambaya
Assalamu alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Shugaban mu, Sayyiduna Muhammad Dan Abdullah, da Iyalansa tsarkaka da sahabbansa managarta. Bayan haka ina mai gaisuwa a gare ku da fatan Allah Ya karfafe ku kan wannan aikin da kuke yi, ameen. Ina da wata tambaya ce ko kuma na ce neman gamsasasshen bayani kan wani hadisi da wani ya ce min ya gani a littafin mu na Shi”a wato Furu”ul Kaafi na Sheikh Ya”kubal Kulayni. Cewa a shafi na 246 an ruwaito daga Aba Ja”far (AS) ya ce: dukkan mutane sun yi ridda a bayan wafatin Manzo (SAWA) banda Abu Dhar, Mikdad da Salman (RA). Sai ya ce in haka ne ina musuluncin wadanda muke cewa sun fi kowa a bayan Manzo (SAWA), wato Ashabul Kisa” (AS). A nan na so a min bayani shin wannan hadisin ya inganta? Akwai shi a littafin? Kuma menene hakikanin abin da hadisin yake nufi? Don ni ba ni da ilimin addini kuma na bi da masaniya sosai a kai lamuran addini.
SWALI
Assalamu alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Shugaban mu, Sayyiduna Muhammad Dan Abdullah, da Iyalansa tsarkaka da sahabbansa managarta. Bayan haka ina mai gaisuwa a gare ku da fatan Allah Ya karfafe ku kan wannan aikin da kuke yi, ameen. Ina da wata tambaya ce ko kuma na ce neman gamsasasshen bayani kan wani hadisi da wani ya ce min ya gani a littafin mu na Shi”a wato Furu”ul Kaafi na Sheikh Ya”kubal Kulayni. Cewa a shafi na 246 an ruwaito daga Aba Ja”far (AS) ya ce: dukkan mutane sun yi ridda a bayan wafatin Manzo (SAWA) banda Abu Dhar, Mikdad da Salman (RA). Sai ya ce in haka ne ina musuluncin wadanda muke cewa sun fi kowa a bayan Manzo (SAWA), wato Ashabul Kisa” (AS). A nan na so a min bayani shin wannan hadisin ya inganta? Akwai shi a littafin? Kuma menene hakikanin abin da hadisin yake nufi? Don ni ba ni da ilimin addini kuma na bi da masaniya sosai a kai lamuran addini.
Amsa a Dunkule
Batun Riddar  sahabbai ya zo cikin ingantattun riwayoyin Ahlus sunna masu tarin yawa wasunsu ma mutawatirai ne, a daidai lokacin da riwayoyi da suka zo kan batun riddar sahabbai a littafan shi”a ba su wuce riwayoyi guda uku ba gaba daya, kamar yadda idan muka bi isdilahin ilimul hadis ba su ketare riwayar kabarul wahid ba, ragowar riwayoyin kuma su na da matsalar isnadi wadanda ba zai yiwu mu dogara da su ba, saboda haka ya zama tilas yan”uwa ahlus sunna su ba mu amsa kan tarin riwayoyi da aka samu cikin ingantattun litttafansu game da riddar sahabbai da  wacce ma”anar ridda suke bayani?
Sai dai cewa su malaman shi”a sun tafi kan cewa riwayoyin da suka zo da batun riddar sahabbai ba zai taba yiwuwa a dora su kan ma”anar kafirta ba da fita daga muslunci da komawa bautar gumaka sakamakon su wadannan riwayoyi sun ci karo da nassi da matanin kur”ani da abinda masadir din tarihi suka tabbatar, dalilin haka ne dukkanin malaman shi”a  suka fassara riddar da ma”anar  karya alkawarin wilaya da sabawa umarnin manzon Allah {s.a.w} cikin al”amrin halifancin sarkin muminai Aliyu dan abi Dalibi {as} sakamakon kasantuwar kadan daga cikin sahabbai suka wanzu  bakin rayukansu suna masu bada kariya ga Aliyu dan abi dalib {as} kamar yadda a ka ce shi Aliyu dan abi dalib {as} ya kirasu kan cewa su aske gashin kansu su yi salsali su zo da takubba zararru don ba shi kariya. Kamar yadda ya zo cikin wasu sashen riwayoyi cewa daga cikin wadanda suka shiga cikin ayarin masu taimakwa Ali {as} akwai ammar dan yasir {rd}.
Amma su ahlul baiti baki dayansu sun tsaya kyam wajen bawa Ali {as} kariya bayan manzon Allah {saw} kamar yadda riwayoyi da tarihi suka nuna haka, idan an samu wani waje da su ka yi shiru suka kame bakinsu to sun yi hakan ne don kiyaye maslahar muslunci, sai dai cewa don mutum na cikin banu hashim wannan da dalili ne kan cewa shi shi”a ne ba. kuma hakan ba ya nunu cewa ya wanzu kan hanyar gaskiya tsawon rayuwarsa.
Amsa Dalla-dalla
Domin samun cikakkayar amsar wannan tambaya a kula da abubuwa masu zuwa:-
Na daya: Magana kan riddar sahabai ta ya zo a cikin litattafai da yawa daga cikin littafan ahulussunna a cikin wurare masu yawa, ya kai matsayin tawaturi. A nan za mu fadi wasu daga cikin inda ruwayoyin suka zo.
  1. Shahin Sahihu Muslim  na Nawawi j15-16 shafi 5 da 59.
  2. Umdatul kari’i 23/135.
  3. Sharhin Sahihul Bukhari, na Kirmani 23/63.
  4. Al-tamhid na Ibni Abdulbarri 2/291.
  5. Sahihul Bukhari, a tittafin bayi babi na 53 hadisai na 6212;2115.
  6. Sahihu Muslim, littafin falaloli, babi na 9.
  7. Masabihul sunna na Bagawi 3/537.
  8. Al-targib wal-tarhib, na Munziri, 4/422.
  9. Al-Nihaya fi garibil Hadis na Ibni asir 5/274.
  10. Fatahul bari, na Ibni Hajar 11/475.
  11. Umdatul kari’I na Aini 23/142.
  12. Irshadul sari na Kasdalani, 9/342.
A nan zamu ambaci ruwaya daya daga cikin ruwaoyin ahlussunnan a matsayin misali, sannan zamu bar sauran binciken a hannun masana.[1] Abu Huraira ya rawaito daga manzon rahama (saw) yana cewa: “a lokacin da na ke tsaye a gefen tafki, sai wasu daga cikin sahabbai na su zo wadanda na san su (sai wani mutum wanda yake daga dakarun ubangiji) ya shiga tsakani na da su, sai ya ce: ku taho, sai in tambaye shi na ce: ina za su tafi? sai ya ce: na rantse da allah zuwa wuta za su tafi, sai in tambaye shi me ye laifin su? sai ya ce: ai bayan kabar su sun koma kan akidarsu da ayyukansu na jahiliyya. Sai ga wasu gungu wadanda suma na san su, sai wani saga cikin dakarun ubangiji wanda yake kula da su ya shiga tsakani na da su, sai ya ce: ku zo mu je! Sai in tambaya, zuwa ina? sai ya ce: zuwa wuta. Sai in tamaya meye laifinsu? Sai ya ce: wadannan sun koma kan tunanin su na da bayan da ka barsu. Ba na tsammanin wasu daga cikin su zasu tsira face kwatankwacin agowar garke” wato adadin rakuman da ke nisantar garke saboda rashin makiyayi a kusa wadanda ke bacewa a nemesu a rasa.[2] (wannan Karin Magana ne da ke nuna cewa wadanda zasu tsira ‘yan kadan ne sosai)[3]       
Amma cikin littafan shi”a kadai cikin litattafai guda biyu riwayoyi suka zo kan wannan fagen litattafan kuwa su ne {al”iktisas} na shaik mufid da {rijalil kashshi} wadanda dukkaninsu raunana  ne a mahangar isnadi, kadai dai riwayar da cikin isnadinta akwai Ali dan Hassan faddal sikka da kuma riwayoyi uku daban za iya kidaya su cikin ingantattun riwayoyi.[4] [5]
Mu ma kaddara cewa wadannan riwayoyi guda hudu ba su da wata matsala cikin isnadinsu amma duk da kasantuwar hakan ana kidayasu ne cikin kabarul wahid a ilimin hadisi wanda ba dukkanin malamai suka tafi kan kasantuwarsa hujja ba, idan shi ma kabarul wahid mun kaddara cewa hujja ne to da wacce ma”ana ridda ta zo?
Bisa la”akari da yawan riwayoyin da suka zo cikin littafan ahlus sunna kan riddar sahabbai ya zama tilas su ba mu amsa kan riddar sahabbai da kuma ma”anar da ta zo cikin wadancan hadisai na su, dukkanin ma”anar da suka ba wa hadisan to mu kuma a shirye muke mu karbi wannan ma”ana da suka ba wa riwayoyin.
 
Na biyu: Sannan wannan riwaya ba ta daidaita da abin da tarihi ya zo da shi ba, to ta kaka za a ce kadai mutum uku ne kacal suka baiwa Ali dan abi dalib kariya dai dai lokacin da malam dan kutaiba da malam dabari sun fadi cewa wasu jama”a daga banu hashim tare da wasunsu sakamakon rashin lamintarsu ga halifancin Abubakar sun fake cikin gidan Aliyu dan abi Dalibi {as} kuma sun ki fita daga gidan har sai da aka yi musu barazanar kona gidan suna ciki.[6]
Na uku. Shaik Saduk cikin littafinsa al-khisal ya yi ishara da sunayen wasu da suka ki karbar halifancin Abubakar ya kuma ya yi bayani kan tawayen kowanne dayansu.
Na hudu. Samuwar matsala da raurawa cikin matanin wani adadi daga hadisan na iya sanya shakku cikin ingancinsu.
Na biyar.  Ta kaka zai yiwu a ce  an yi inkarin imanin sahabban da shi”a da sunna suka yi ittifakin kan girman matsayinsu, kamar misalin bilal bahabashe da uwaisul karani da hujuru dan addi da dai sauransu, da banu hashim da ba su taba juyawa matafiyar Ali {as} baya ba, kadai dai saboda koyi da shi da kiyaye babbar masalaha ta muslunci suka kame bakinsu.[7]
Na shida. Wannan batu da aka ambata cikin wadannan riwayoyi malaman shi”a sun mata tawili daban daban, misali babban malamin shi”a na wannan zamani ayatollah jafar subhani {dz} ya tafi kan cewa wannan ridda ba ta da ma”anar kafirci da inkarin ubangiji da kuma komawa bautar gumaka ta jahiliya da suka bari ba, kadai dai abin da ta ke nufi shi ne rashin cika alkawarin da suka dauka ranar taron gadir da aka yi shi bayan dawowa daga hajjin bankwana. Sannan riwayar da ke bayanin cewa Aliyu dan abi dalib {as} ya nemi su aske gashin kansu su yi sassali su zo da takubbansu a zare daga gidanta wadda kadai mutum uku suka aikata hakan, to ita kanta wannan riwaya shaida ce kan cewa abin da ake nufi da riddar wadanda ba su zo ba shi ne guduwarsu daga yin yaki tare da Ali {as}.[8]
Imam komaini {r.a} cikin littafinsa mai suna daharat ya yi bahasi kan cewa shin wadanda suka sabawa shi”a za a kirasu da kafirai ko kuma ba kafirai ba ne? Imam ya bada amsa kan cewa wadanda suka yi imani da Allah da annabta da ranar alkiyama za a kirasu musulmai.
Ya tafi kan cewa shi imamanci na daga cikin usul din shi”a wanda ake kidaya wanda bai imani da shi ba matsayin wanda ba dan shi”a ba, amma ya na nan a matsayinsa na musulmi, imam ya yi bahasi ya yi bincike kan riwayoyin da suke danganta kafirci ga ahlus sunna, imam ya tafi kan cewa wadannan riwayoyi ba su da ma”anar kafirci a ilimin kalam. Saboda akwai tarin riwayoyi da ke bayanin dangantakar zamantakewar da ke tsakanin Imaman Ahlul baiti da Ahlul sunna (koda ma a inda ake tsammanin takiyya) hakika ruwayoyin sun saba da waccan Magana ta cewa sunna sun kafirta.[9]
Saboda babu wata mafita da ta wuce mu dora ire-iren wadancan riwayoyi kan badini ba, na cewa ana nufin ahlus sunna ba su da wani lada a lahira matukar sun mutu kan haka, ko kuma mu ce ana nufin wani mataki daga matakan kafirci kamar yadda aka danganta kafirci ga mazinaci da mai wasa da sallah.
Sannan ba zai yiwuwa mu karbi maganar cewa su wadannan mutane a hakikance kafirai ne kadai dai ana yi musu hukuci da musulmai a zahairi ba, sakamkon shi muslunci  ba wani abu ba ne face imani da kadaituwar Allah da kuma imani da annabta da ranar kiyama.[10]
Imam komaini ya yi karin bayani cikin wadancan riwayoyi na riddar sahabbai ya ce abin da ake nufi da ridda cikin hadisan shi ne karya alkawari a zahirance ko a takiyance, ba wai fita daga muslunci ba.[11]
Malam mirdamad cikin littafin annibrasul dhiya’i; shi ma na cewa wannan ridda na nufin kau cewa hanya da kwace hakkin ahlul baiti.[12]
Na bakwai: ta yiwu wadannan riwayoyi na riddar sahabbai su kasance aikin gullatu masu wuce gona da iri ko kuma hashawiyyar shi”a, ayatollah jafar subahani cikin karshen bahasin wadannan riwayoyi ya na cewa: ni ina zaton cewa wadannan riwayoyi na daga kirkirar gullatu da hashawiyya don karfafa al”amarin wilaya da yin dabara don samar da ikhlasi tsakanin yan shi”a sun manta da cewa wadannan riwayoyi na su na riddar sahabbai sun ci karo alkur”ani da hadisan sarkin muminai Aliyu dan abi Dalib[13] da Hadisan imam Sajjad[14] da suke yabon wasu daga sahabbai.[15]
Na takwas. Mahangar shi”a game da sahabbai misalin mahangar kur”ani ce kan sahabbai, kur”ani ya ya bi sahabbai a wurare da dama wasu wuraren kuma ya zarge su. Cikin ayoyi masu yawa misalin ayar mubaya”ar kasan  bishiya ya girmama sahabbai, dai dai wannan lokaci kuma kur”ani ya zargi munafukan  da ke ciki sahabbai, saboda ba zai yiwu a ce dukkanin sahabbi adalai ba ne ko kuma a ce dukkaninsu sun yi ridda sakamakon hakan ya ci karo da kur”ani.[16]
Kuma kamar yanda ya zo a ruwayyoyi cewa ma’abota bai’a gaba dayansu sun bawa Imam Ali (as) kariya amma maganar kasancewa lalle ne su zama daga cikin banu Hashin wannan ba dalili ne da ke tabbatar da cewa lalle su yan shi’a ba ne. kamar yadda ba za a iya tabbatar da cewa sun kasance kan gaskiya a dukkanin mataki a rayuwarsu ba.
Domin samun karin bayani sosai a kamowa tamabaya mai namba 1589.
 

[1] An dakko daga tambaya ta 2077 (site 3502) a karkashin jigo; Riddar Sahabbai.
  1. [2] “A yayin da na ke tsaye sai ga wasu gungu daga cikin Sahabbaina, na sansu sai wani mutum ya shiga tsakanin na da su sai ya ce ku taho! , sai in tambaye shi na ce: ina za su tafi? sai ya ce: na rantse da allah zuwa wuta za su tafi, sai in tambaye shi me ye laifin su? sai ya ce: ai bayan kabar su sun koma kan akidarsu da ayyukansu na jahiliyya. Sai ga wasu gungu wadanda suma na san su, sai wani saga cikin dakarun ubangiji wanda yake kula da su ya shiga tsakani na da su, sai ya ce: ku zo mu je! Sai in tambaya, zuwa ina? sai ya ce: zuwa wuta. Sai in tamaya meye laifinsu? Sai ya ce: wadannan sun koma kan tunanin su na da bayan da ka barsu. Ba na tsammanin wasu daga cikin su zasu tsira face kwatankwacin agowar garke” Sahihul bukhari, a tittafin bayi babi na 53 hadisai na 6212;2115. Lisanul Arab na inbi manzur 15/135. Al-targib wal-tarhib, na Munziri, 4/422. Al-Nihaya fi garibil Hadis na Ibni asir 5/274. Fatahul bari, na Ibni Hajar 11/475. Umdatul kari’I na Aini 23/142. Irshadul sari na Kasdalani, 9/342.  
[3] An cirato daga tambaya ta 1589. (site 1970) jigo: ma’anar riddar sahabbai da tabbatar hakan.
[4] Ma”as shi”a fi aka”idihim na Ja’afar Subuhani shafi: 177
[5] Ma’ash Shi’a imamiyya fi akaidihim na Ja’afar Subuhani shafi 177-178. Bugu na daya. Darul Adhwa’i Bairut 1414 bayan hijira.
[6] Ma”ash shi”a fi aka”idihim na Ja’afar Subuhani shafi: 1780.
[7]  Ma’ash Shi’a imamiyya fi akaidihim na Ja’afar Subuhani shafi 180-181.
[8] Ma”ash shi”a imamyya fi aka”idihim na Ja’afar Subuhani shafi: 181
[9] Imam khomaini, Kitabul  daharat juz 3b shafi 437
[10] Imam khomaini, Kitabul  daharat juz 3 sh 438
[11] Imam khomaini, Kitabul  daharat juz 3 shafi 446.
[12] Nibras diya na Mir Dammad a cikin sharhin babi bada’I da kuma tabbatar da tasirin addu’a, sh 54
[13] Nahajul balaga khuduba ta 56 da 182.
[14] Sahifa sajjadiya kamila Addu’a ta dudu.
[15] Ma’ash Shi’a imamiyya fi akaidihim na Ja’afar Subuhani shafi 181 Bugu na daya. Darul Adhwa’i Bairut 1414 bayan hijira.
[16] Ma”alimul madrasataini na sayyid murtadhal askari juz 1 sh 130-135. bugu na hudu, Muassat bi’isat. Tehran 1412, bayan hijira.
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa