Please Wait
7890
Zancen isma da biyayya ga Imamai Ma’asumai (a.s) an tattauna a kansu tun zamanin Manzon Allah (s.a.w). Sai da zamanin Imamu Sadik (a.s) ya bambanta da sauran zamuna nan sauran Imamai (a.s). Damar da ya samu ta fuskar zamatakewa da wayewa babu wani Imami (a.s) da ya samu wannan damar. Dalili kuwa shi ne, a lokaci da gwamnatin Banu Umayya ta raunana take tangal-tangal da karfafuwar ikon Abbasiyawa. Wadannan sassa biyun sun yi ta fafatawa lokaci mai tsawo a tsakaninsu. A gefe guda a zamanin Imamu Sadik (a.s) dama ta samu saboda hali da mulkin ke ciki sai ya zamana lokaci ne na farfadowar Musulunci da bunkasar ilimi.
Zamu yi bahasi a batun isma da biyayya ga Imami ma’asumai (a.s) ta fuska biyu:
Na fako: Batun isma a zantukan Imamai (a.s):
Idan muka bi diddigi muka binciki nassosi da ke batu game da ismar Imamai (a.s) da yi musu biyayya, zamu ga akwai shi tun a farko-farkon zamanin manzanci a lokacin Manson Allah (s.a.w).
- Shafi’i ya ruwaito a littafin Manakib da isnadi zuwa ga Abdullahi bin Mas’ud ya ce: “Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Ni ne addu’ar Annabi Ibrahim (a.s).” Sai muka ce: “Ta kaka ka zama addu’ar babanka Annabi Ibrahim (a.s)? Ya ce: “Allah Ya yi wasici ga Annabi Ibrahim (a.s) “(ka ambata) zamanin da Ubangijin Ibramu Ya jarrabe shi da kalmomi ya ba da su cikakku Ubangiji Ya ce: “Hakika zan sanya ka abin koyi” Annabi ya ce: “Kuma ka sanya shugabannin nan daga cikin ‘ya’yana,” Ubangiji Ya ce: “Alkawarina na Shubanci ba ya samun azzalumai”.[1] Sai Annabi Ibrahim ya yi farinciki, ya ce: “Ya Ubangiji a zuriyata ma da akwai shugabanni irina? Sai Allah (SWT) Ya masa wahayi Ya ce: “Ya Ibrahim ba zan maka alkawari da ba zan cika maka ba. Ya ce: “Ya Ubangiji wane alkawari ne ba zaka cika mum shi ba”? Ya ce: “A cikin zuriyarka ba zan ba wa azzalumi shugabanci ba. A sannan sai Annabi Ibrahim ya ce: “Wane ne azzalumi a cikin zuriyata? Sai Ya ce masa: “Duk wanda ya yi sujjada ga gunki ya bauta musu ba Ni ba.” A sannan Annabi Ibrahim ya ce: “Ka nisanta ni da ‘ya’yana daga burin bautar gumaka, hakika sun badda mafi yawan mutane’.[2] Sai Annabi (s.a.w) ya ce: “Sai addu’ar ta iso gare ni ta iso ga Ali, a cikimmu babu wanda ya taba sujjada ga gunki, sai Ya zabe ni Annabi Ya zabi Ali wasiyyi”.[3]
- Kasim bin Kayis daya daga cikin sahabban Amirul muminina Ali (a.s) da Imamu Sajjad (a.s) na musamman ya ce: “ Ita da’a a kan yi ta ne ga Allah Shi kadai da ManzonSa da majibinta al’amarin da Allah Ya kusanta su a gare Shi da kanSa, inda Ya ce: “Ku bi Allah ku bi Manzo da ma’abuta al’amri daga cikinku. Allah Ya yi umurin da bin ManzonSa ne saboda ma’asumi ne tsarkakke kuma ba ya yin umurni a yi sabo, kuma Allah Ya yi umurni da bin ma’abuta lamari saboda su ma ba sa yin sabo kana ba sa umurni da a yi sabon Allah”.[4]
- A Nahjul balaga Amirul muminina (a.s) ya yi iShara game da batun isma:
A huduba ta 147 yana cewa: “Ba sa saban wa Addini, ba sa sabani da shi”.[5] Ba zai yiwu wani ya rasa sanin wani hukunci na Addini ba, balle ya samu sabani da masanin).
b. A huduba ta 131yana cewa bayan kore wasu sifofi ga buran Imamu Ali (a.s) ya ce: (s.a.w) “Ba mai watsi da hadisai ba ne, al’umma su halaka”.[6] A bisa dabi’a wannan na tabbatar da wajabcin biyayya ga Imami (a.s).
c. A huduba ta 105 yana cewa: Yaku mutane ku nemi haske da makamashin fitilar mai wa’azi da ya wa’zantu, ku kwankwada daga tataccen marmaro da ba ya gurbata.”[7]
Hakika an yi zantuka da dama da suka Shafi batun ma’asumai (a.s) a ruwayoyi a gurare daban-daban, amma zamu takaita a nan.
Na biyu: Dangane da dalilan da suka sanya yawan tattauna zancen akida a zamanin Imamai biyu watau Bakir da Sadik (a.s) fiye da a zamunan sauran Imamai (a.s) zamu bayyana a takaice. A bangaren siyasa, lokacin Imamu Bakir (a.s) musamman ma a lokaci Imamu Sadik (a.s) lokaci ne da gwamnatin Ummayawa ta raunana tana tangal-tangal, kana Abbasiyawa suka kara samun damar fada a ji. Kasantuwa lokaci ne da Umayyawa ke cikn tsaka-mai-wuya na siyasa ba su da wata dama ta tursasawa Imaman Shi’a (a.s) da cutar da su (irin lokacin Imamu Sajjad (a.s).
Sannan su Abbasiyawa sun daga tutar su ne da sunan kare Ahlin Annabi (s.a.w), da dauko fansar jininsu, kafin su hau kan mulki. A bisa kaskiya sun hau halifanci ne da wannan taken. Wannan shi ya sa babu wani tarihi da ya nuna an tursasa musu (a.s) a bangarensu a wanna lokacin. Wannan lokaci kyakkyawar dama ce ta yada ilimi da karantarwar Imamai (a.s). Kana daga cikin abubuwa da suka yi matukar tasiri a wannan batu (na akida) Sharuda na karantarwa na musamman da tattaunawa da sauran kunkiyoyi da mazhabobi na musulunci.[8]
[1] Bakara: 124.
[2] Ibrahim: 35-36.
[3] Sayyid Dawus, Aliyu bin Musa, a liffafin Dawa’if j1, sg78, daba’in Alkhiya’am.,Kum, 1400,HK.
[4] Salim bin Kayis Abusadik, a littafin Salim bin Kayis.sh884,, dabaa’in IntiShara’at Alhadi, Kum, 1415 HK.
[5] Nahajulbalaga zance na j1, sh 206 dabaa’in Darulhijra, Kum,
[6] A littafin da ya gabata sh153.
[7] A littafin da ya gabata 153.
[8] don karin bayani sai a dubi R.K: Imamu Mahdi, Siratul’a’imma, sh353, Mu’assasar Imamu Sadik (a.s) Kum,1415 HK.