Please Wait
Dubawa
12720
12720
Ranar Isar da Sako:
2012/04/10
Takaitacciyar Tambaya
Ina son a kawo min hadisai da dama da ke Magana kan alakar da ke takanin mace da namijin da ba muharraman juna ba
SWALI
Ina son a kawo min hadisai da dama da ke Magana kan alakar da ke takanin mace da namijin da ba muharraman juna ba
Amsa a Dunkule
Alaka tsakanin wadanda ba muharramai ba na da fadin gaske wannan ba kokwanto a cikinsa duk da cewa wannan tambaya ba kai tsaye take nuna wace irin alka kake nufi ba maganar da ka yo na da harshen damo sai dai ba zai yiwu a amsa ta kamar yadda ya nema ba da dadi.
BAYANIN RUWAYOYI DA SUKAYI MAGANA KAN ALAKA TSAKANIN WADANDA BA MUHARRAMAI BA
- An karbo daga Sa’id al iskafi (mai gyaran takalma ko a ce shoe shiner) ya karbo daga abi Ja’afar imam Musal kazeem (a.s) yana cewa; wani saurayi a Madina ya hadu da wata mace tana mai fuskanto shi a lokacin mata sun kasance idan zasu yi lillubi suna sanya mayafin ko hijabin ya rufe kansu amma sai ya bi ta bayan kunnensu fuskarsu ta fito sosai saurayin nan nata kallonta tun tana nufo shi har ta wuce shi duk da haka ya ci gaba da kallonta har ta shiga lunguna ya bi ta yana ta kallon bayanta duk inda ta yi, yana cikin bintan bai kulaba sai ya bige da wani kashi ko kwalba da take jikin wani gini da aka sa don kariya ga masu tabawa ko haurawa, yayin da yarinyar ta bace masa da gani sai ya ga jini na zuba (kwarara) a jikinsa da kayansa, sai ya ce wallahi da zan je wajan manzo (s.a.w) da na gaya masa, sai mai ruwaya ya ci gaba da cewa, sai yaron ya je wajan manzo (s.a.w) yayin da manzo ya gan shi sai yake tambayarsa mene ne haka? Sai ya gaya wa manzo (s.a.w) abin da ya faru. sai mala’ika jibril (a.s) (1) ya sauko da wannan aya “Ka gaya wa muminai cewa su dinga rufe idanunsu da kame farjinsu wannan shi ne ya fi kyau a tare da su hakika Allah (s.w.t) mai ba da labara ne game da abin da suke aikatawa” (2)
- Hadisi yazo daga manzo (s.a.w) cewa: “dukkan wani ido mai kuka ne a ranar alkiyama amma ban da idanu uku su ne idon da ya yi kuka saboda tsoron Allah (s.w.t) da idon da ya runtse daga kallon haram da kuma idon da ya kwana bai yi bacci ba a tafarkin Allah (s.w.t) “ (3)
- Daga Littafin “Ilal” na Ibn Sinan daga imam Ridha (a.s), imam Ridha (a.s) ya rubuta wa dan Sinan ‘’An hana duban gashin matan aure har ma da ma wadanda ba na auren ba ma saboda abin da ke ciki na motsa zukatan mazaje motsa zukatan kuwa yakan kai su zuwa yin fasadi wanda kuma yin fasadi abu ne da bai halatta ba ‘’(4).
KARIN BAYANI DUBA WDANNAN FATAWOYI
Tambaya ta 1044 (mauki’i: 1110) alkar da ke tsakanin yaro da yarinya a musulunci
Tambaya ta 6669 (mauki’i: 6745) alaka tsakanin yaro da yarinya
- Al kulainy Muhammad dan ya’akub, alkafi bol 15 page 521 na darul kutubul islamiyya Tehran: 1365 hs
- Suratun nuur 30
- Al hurrul aamily, wasa’ilsh shi’a bol 7 page 75 na mu’assasatu ahlul bait (as) Kum 1409 ah
- Majlisi, Muhammad bakir, biharul anwar bol 101 page 34 darul wafa’a Beirut.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga