advanced Search
Dubawa
8779
Ranar Isar da Sako: 2012/04/11
Takaitacciyar Tambaya
Ku Malamai Kuna Cewa Addini Yana Tabbatar Da Hukuncin Hankali, Saboda Haka Ana Iya Dogara Da shi, To, Idan Al’amarin Haka Yake, Ke nan Zamu Samu Amsar Cewa Muna Iya Yin Hukunci Da Hankalin Mu Kawai? Kuma Shin Tun A Farko Ma Mene Ne Muhimmanci Ma’ana, Da Wajabcin Takalidi?
SWALI
Ku Malamai Kuna Cewa Addini Yana Tabbatar Da Hukuncin Hankali, Saboda Haka Ana Iya Dogara Da shi, To, Idan Al’amarin Haka Yake, Ke nan Zamu Samu Amsar Cewa Muna Iya Yin Hukunci Da Hankalin Mu Kawai? Kuma Shin Tun A Farko Ma Mene Ne Muhimmanci Ma’ana, Da Wajabcin Takalidi?
Amsa a Dunkule

Hankalin Da Shari’a Take Tabbatar Da shi, Ba Shi ne Wannan Hankali Na Lissafi Wanda Yake Tunanin Maslaharsa Kawai ba, Wanda Ako Yaushe Muke Amfani Da shi, Ko Da Yake Shi ma Shari’a Tana Tabbatar Da shi, Sai Dai Al’amarin Da Yake Bukatar Tuntuntuni Sosai, Shi ne Cewar Shi Hankali Yana Da Iyaka Na Ilimin Dake Riska, Ya kan Gano Jimillar Abu Ne, Amma Ba ya Iya Gano Filla Filla Na Bangarorin Abubuwa, Saboda Haka Shi Mutum a Cikin Al’amarin Da Ya Shafi Da’irar Bangarorin Abubuwa Daban Daban, yana bukatuwa ga wata mabubbuga ta Ilimi ta daban, wacce za ta taimake shi don gano kebantattun da bangarorin ilimomi. Wannan mabubbugar ilimin kuwa shi ne wahayi.

Za a Iya Suranta Ma’anoni Guda Biyu A kan Takalidi,

  • Dayansu Ma’ana Ce Mai Muni, Ta Yiwu Mutum Ya Guje Mata Idan Ya Suranta Ta Saboda Wasu Ta’adu.
  • Daya Ma’anar Kuma Ma’ance Mai Kyau. Takalidin Da Ke Cikin Ilimin Fikihu, Mauru”i Ne Na Fikihu Na Musamman, Abin da Muke Nufi Da shi A Cikin Hikima Ta Kalmomin Larabci Shi ne, ’Zuwa Wurin Kwararru A cikin Al’amura Na Kwarewa. ’Ba Zamu Yi Takalidi Ga Kwararre Ba Sai Saboda Zamowar Mu Ba Kwararru Ba ne, Mu Ba Mujtahidai Ba ne, A iya Ciro Hukunce-Hukuncen Addini.
Amsa Dalla-dalla

Hankalin da Shari’a Take Tabbatar Da shi, Ba Shi ne Wannan Hankali Na Lissafi Wanda Yake Tunanin Maslaharsa Kawai ba. Wanda Ako Yaushe Muke Amfani da shi, Ko da Yake Shi ma Shari’a Tana Tabbatar Da shi, Sai dai Al’amarin da Yake Bukatar Tuntuntuni Sosai, Shi ne Cewar Shi Hankali Yana da Iyaka Na Ilimin Dake Riska, Yakan Gano Jimillar Abu ne, Amma Ba ya iya Gano Filla Filla Na Bangarorin Abubuwa, Saboda Haka Shi Mutum a Cikin Al’amarin Da Ya Shafi Da’irar Bangarorin Abubuwa Daban Daban, Yana Bukatuwa Ga Wata Mabubbuga Ta ilimi ta Daban, Wacce Za Ta Taimake Shi Don Gano Kebantattun Da Bangarorin Ilimomi. Wannan Mabubbugar Ilimin Kuwa Shi ne Wahayi. Wanda Hakan Yana Bayyana A Cikin Wadannan Tushen Guda Biyu: -

  1. A Cikin Kur’ani: Wato Lafuzzan Kur’ani Wahayi Ne Daga Allah, Haka Ma Kuma Ma’anarsu, Fadar Da Wasu Su Ke Yi Cewa Ma’anonin Kur’ani Su ne Wadanda Wahayi Ya Saukar Da su a cikin Zuciyar Annabi (s. a. w), Amma Banda lafazin, Wannan Ra’ayin, Tabbas Batacce Ne, Wannan Kuma Shi ne Bambancin Da Ke Tsakanin Hadisul Kudusi Da Ayoyin Kur’ani A Cikin Ilimin Musulunci. Domin Abin da Hadisul Kudusi Ya Kunsa Wahayi Ne Na Allah, Amma Lafuzzansa Daga Annabi Ne (s. a. w). Amma Shi Kur’ani Lafuzzansa Wahayi Ne, Su ne Wahayi Ya Sauko Da su A Zuciyar Annabi (s. a. w).
  2. Wata Bayyanar Kuma A cikin Ka’idar Wahayi Ita ce Hadisai: Abin da Ake Nufi Shi ne Cewa Annabi (s. a. w) Ba ya Yin Magana Saboda Son Rai, Kamar Yanda Kur’ani Ya Yi Bayani’ BA YA YIN MAGANA A KAN SON RAI SAI DAI SHI WAHAYI NE DA AKAYI MASA”[1]

Kamar Yanda Yazo A Cikin Ruwaya Daga Abdullahi Dan Amru Ya ce: Na Kasance Ina Rubuta Komi Da Nake Ji Daga Manzon Allah (s. a. w) Ina Son In Haddace, Sai Kuraishawa Suka Hana Ni, Suka Ce: Zaka Dinga Rubuta Duk Abin da Manzon Allah (s. a. w) Ya Fada, Alhali Manzon Allah (s. a. w) Mutum Ne Shi Yana Magana A Yanayi Na Fushi Da Yanayi Na Yarda, Sai Na Bar Rubuta Wa Sai Na Fada Masa Labarin, Sai Ya ce: ’Ka Rubuta Na Rantse Da Wanda Raina Yake Hannunsa, Babu Maganar Da Take Fitowa Daga Gare ni Sai Gaskiya. ” [2]

Kuma Su Ahlul Baiti (a.s) Sun San Tawilin Kur’ani Kamar Yanda Kur’ani Mai Girma Yake Fasaltawa”BA WANDA YAKE SANIN TAWILINSA SAI DAI ALLAH DA TABBATATTU A CIKIN ILIMI SUNA CEWA MUN YI IMANI DA SHI DUKKANSA DAGA WURIN UBANGIJINMU YAKE BABU MASU WA’AZTUWA SAI MASU HANKALI”[3] Tabbatattu A cikin Ilimi Kuma Su ne Imamai (a.s) Kuma Su Sun San Ilimin Tawilin Kur’ani, Wato Sun San Asalinsa Da Cikinsa Da Asasinsa. Kuma Ba su Samu Hakan Ba Sai A dalilin Samun Ilimi Na Allah, Wanda Ya Bayyana A cikin Maganganunsu, Suka Kuma Isar Da su Garemu.

A Saboda Haka Idan Muna Son Sanin Wata Mas’ala daga Cikin Mas’alolin Addini, Ya Wajaba Mu Koma Ga Kur’ani Da Hadisi, Tare Da Sanin Cewa Fahimtar Ilimin Kur’ani Yana Da Bukatar Wasu Al’amura Daga Cikinsu Akwai: Fahimtar Harshen Larabci Sosai, Sanin Ilimomi, Da sanin Wayewa Irin Na Wancan Zamanin Da Kur’ani Ya Sauka A Cikinsa, Haka Nan Kuma Ya Wajaba Mu San Ruwayoyi, Don Su Suke Fassara Kur’ani, Zai Yiwu Su Kebantar Da Wsu Ma’anoni, Ko Su Yi Kaydin Ma’ana Ga Wasu. Kamar Yanda Sanin Ruwayoyi Yana Bukatar Sanin Isnadinsu, Ingantaccensu Daga Bataccensu, Shin Zai Yiwu A Yi Aiki Da Wannan Ruwayar Ko Waccan? Ko A’a. Kuma Wannan Binciken Yana Da Bukatar Wasu Bincike Na Manhaja Wadanda Za a Samu Darasinsu Ne A cikin Darasin Usulul Fikih.

Jimillan Wadannan Ilimomi Su Ake Dunkula Su A Kira Su Da Sunan Ijtihadi, Shi Ijtihadi Wani Nau’i Ne Na Kwarewa Da Ke Cancantar Da Mutum Ya Iya Ciro Hukunce-Hukuncen Shari’a Daga Dalilai Na Asalin Addini, Su ne Kur’ani Da Sunna Da Hankali.

Shi Kuma Fage Na Hankali Iyakantacce Ne Sosai, Kuma Da Yawa Daga Cikin Hukunce Hukuncen Da Mujtahidi Kwararre Yake Fitarwa Daga Ka’idoji ne, Da Lafuzza Na Kur’ani Da Sunna, Amma Ba Daga Hankali Ba. A Saboda Haka Yana Daga Cikin Abun Da Babu Makawa A Cikinsa, Cewa Ba Zai Yiwu Dukkan Mutane Su Zamo Mujtahidai, Kwararru, A cikin Ilimin Hukunce Hukunce Ba. Domin Ijtihadi Wani Al’amari ne Da Yake Bukatuwa Ga Samun Iko Da Shiri Masu Yawan Gaske. Kuma Kur’ani Mai Girma Yana Nuna Rashin Wajabcin Ya Zamo Dukkan Mutane Sai Sun Zamo Masu Kwarewa A Cikin Ilimin Addini. Sai Dai Ya Wajaba Ne A kan Wasu Kungiya Na Mutane Su Samu Ilimin ‘Tafakkuh’ Da Fahimtar Addini[4] Kuma Babu Wata Shakka Cewa Su Mujtahidai Su ne Babban Misali A Fili Na Wannan Kungiyar.

Za a Iya Suranta Ma’anoni Guda Biyu Game Da Takalidi:

  1. Korarriyar Ma’ana, Zai Yiwu Ya Zamo Ya Wajabta Idan Aka Suranta Wannan Korarriyar Ma’anar A Guje Mata A Al’adance, Domin Takalidi A Korarriyar Ma’anarta Yana Nufin Yin Makauniyar Biyayya Ba Tare Da Dalili Ba, To A Duk Lokacin Da Wani Abu Zai Zamanto Zamananci Ne Kawai, Sannan Mafi Yawan Mutane Su Bi Shi Ba Dalili, Wannan Yana Jawo Su Bata Da Rashin Samun Shiriyarsu Ga Hanya Madaidaiciya.
  2. Tabbatacciyar Ma’ana: Shi ne Irin Takalidin Da Aka Ambata A Cikin Ilimin Fikihu Mauru”i Ne Na Fikihu Na Musamman, Abin da Muke Nufi Da shi Shi ne, ’Zuwa Wurin Kwararru A cikin Al’amura Na Kwarewa’. A Lokacin Da Zamu Yi Takalidi Ga Kwararre Ba Don Komi Ba Sai Saboda Zamowar Mu Ba Kwararru Ba ne, Mu Ba Mujtahidai Ba ne A Cikin Ilimin Addini, Don Mu San Ra’ayinsa. Wannan Wata Hanya Ce Da Hankali Yake Aiki Da ita A Cikin Dukkan Al’amuran Da Suka Shafi Kwarewa.

Misali A Lokacin Da Mutum Ba shi Da Lafiya Zai Tuntubi Likita, Saboda Shi Ba Kwararre Ne A Cikin Wannan Fagen Ba.

A Saboda Haka Kasancewar Ba Zai Yiwu Dukkan Mutane Su Samu Kwarewa A Cikin Ilimin Fikihu Ba, Ke nan Ya Wajaba A Kansu Su Koma Ga Mujtahidi Kwararre A Cikin Al’amuran Addini. Wanda Wannan Al’amari ne Da ya Dace Da Hukuncin Hankali, Kuma Wannan Shi ne Takalidi Mai Tabbatacciyar Ma’ana. Yana Da Kyau A Duba Wadannan Darussa Masu Zuwa Don Samun Karin Haske A kan Ilimomin Takalidi.

- “Hankali Da Fagagen Ayyukansa”Tambaya Ta 1110 (Dandali: 1888)

- “Hankali Na gama Gari Da Zuciya Da Imani Da Soyayya”Tambaya Ta 839 (Dandali: 909)

- “Hankali Da Addini”Tambaya Ta 691 (Dandali5286)

- “Hikimar Takalidi Ga Maraji’ai Da Rashin Bayanin Dalilai”Tambaya Ta 2661 (Dandali16311)

- “Hujjojin Wajabcin Takalidi Ga Maraji’ai”Tambaya Ta 975 (Dandali1078)

- “Takalidin Da Ake Zargin Yinsa”Tambaya Ta 8165 (Dandali8320)

 

 


[1] Suratun najmi 2-3

[2] Ahmad bin hanbal al musnad juzu’I na 2 shafi na 162, da abin da aka ciro daga ja’afar subhaniy, mausu’atu tabkatil fukaha’I juzu’I na 1 shafi na 179 tantawiy-sayyid Muhammad, at tafsirul wasit lil kur’anil karim, juzu’I na 13 shafi na 59

[3] Suratu ali imran 8

[4] Suratut tauba, 122”

 

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa