Please Wait
6600
- Shiriki
Shari’a ba ta hana mutum yai koyi ko ya kware kan wata sana ‘ar ba bayan wacce yake yi ko ya iya ko yin aiki sama da yadda ya saba abin kawai da shari’a ta hana kuma take kara tsoratarwa a kansa shi ne son duniya da nace mata, da nisantar ayyukan alherai da ke gina lahira da mantawa da lahira da kuma gafala daga gare ta, a hakikanin lamurra wannan shi ne ma’auni har ma wajan kwarewarsa kan dukkan ayyukan da yake yi (sana’ar) har ma zuwa ribar da ya kamata mutum ya samu, zaka samu wasu daga mutane sun kware kan sanao’i daban daban suna samun riba mai yawa, duk da haka wannan ba ya hana su tunawa da lahira tare da muhimmantar da nata ayyukan da kan gina ta ba kuma zaka ga sun kwallafa rai ga duniya ba. A nan abin magana shi ne, ya zama wajibin da ba mustahabbi ba ma a kan duk mutum ya yi aiki na biyu idan har aiki na dayan ba zai ishe su gudanar da rayuwa ba da a ce ya bar su suna rayuwa cikin wahala da kunci.
E (haka ne) aiki sama da ka’ida na nufin saba wa doka, domin haka idan aiki na biyun zai haifar masa saba wa doka tare da rashin yin na farkon yadda ya kamata kuma da rashin cika aikinsa, a nan yin aiki na biyun akwai matsala. Haka nan kuma idan aiki na biyun zai cinye masa gaba dayan lokutansa da zai ba wa iyalinsa tarbiyya tare da rashin kula duk abin da ya same su wanda shi ne abin da ya hau kansa mai girma.. wanda kulawa da iyalin nasa ya fi masa zama muhimmi a kan zuwa aiki na biyun ka ga aiki na biyun ya haifar masa da hadarin gaske, wanda ya kamata mutum ya dinga auna abin da zai amfani lahirarsu da duniyar su a lokaci guda tare da lissafa abu kafin farawa; ruwaya tazo daga IMAM HASSAN DAN ALIYU DAN ABI DALIB (a.s) cewa; na tambayi babana game da tsarin wajan manzo (s.a.w) sai ya ce da ni ba a shiga wajansa sai da izini, sannan kuma yana raba lokacinsa zuwa gida uku, daya na ganawa da Allah (s.w.t), daya na iyalinsa, dayan kuma nasa a kan kansa (s.a.w).