Please Wait
11570
Abin da zamu kawo a dunkule shi ne msar tambayar.
- Hakika Kur'ani tushe ne daga tushen shari'a, kuma shi ake komawa don gane ra'ayin addini.
- Ba hakan nan ake istinbadi da Al-Kur'ani ba sai abubuwa biyu sun tabbata: kafa dalilin tabbatar da Al-Kur'anin, sannan abin da ayoyin suke nufi (ma'anar ayoyin).
- Akwai abubuwa biyu (tushe) wadanda mujtahidi yake dogara da su wajen karba daga Kur'ani:
- Tabbatuwar Kur'ani
-
Ma'anar ayoyin
- Asalin tabbatuwar Kur'ani yana bayyana a kan cewa:
- Tabbas Kur'ani Allah ne ya saukar da shi.
- Hakika Kur'ani an kare shi daga juyar da shi zuwa ga ragi ko kari.
- Babu kuskure a cikin wahayi.
-
Annabin Allah ba ya kuskure saboda karbar wahayi da isar da sakon Allah, yana da kariya cikakkiya daga kuskure, mantuwa da rudewa.
- Hasken da Kur'ani ke bayarwa ya ginu a kan cewa:
- Allah yana nufin wasu ma'anoni a cikin Kur'ani.
- Dangane da bayanin ma'anar da Allah yake nufi a cikin hukunce-hukunce masu rassa, Kur'ani ya dogara a kan hanyar da kowa ke iya fahimta, da kuma hanyar masu hankali, littafin Allah bai kawo wani tsarin magana na ishara ba da kamantawa (wacce ba a gane ta da sauri).
- Kur'ani ya kawo shimfida wacce ta dace cikakkiya don masu hankali su fahimci ma'anonin Kur'ani da gane ma'anonin ayoyin hukunci (ayoyin da ake fitar da hukunce-hukuncen fikhu).
- Ayoyin Kur'ani sun game ko ina, ba su kebanta ba kawai wuraren da aka saukar da su ba, amma banda ayoyin da aka shafe, ko wadanda suke canjawa.
Kur'ani tushe ne na farko a Musulunci kuma mafi muhimmanci a wajen duk bangarori da duk mazhabobi na Musulunci, kowa ya yarda da shi tare da mika wuya zuwa gare shi, Kur'ani shi ne tushe na farko kuma na asali a wajen yunkurin gano ra'ayin Shari'a da fahimtar addini, shi ake komawa a duk yanayi kai koma a wane fage. Kur'ani mu'ujiza ec ta Allah wacce bata gushewa tabbatacciya wacce ya bawa Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, Kur'ani shi ne littasfin da ya rinjayi littattafan da suka gabata.
A wannan fagen an yarda da abubuwa biyu wajen riko da Al-Kur'ani:
- Al-Kur'ani hujjace amintacciya a kan mutane, tabbas abin da ke hannun mutane yanzu shi ne al-Kur'anin da Allah ya saukar, ba bu wani abu da aka kara da gangan ko da kuskure, abin da muke nufi Kur'anin da yake hannun mutane tabbas shi ne littafin Allah ba shakka.
- Nassin Kur'ani yana karbar fahimta kuma ana gane ra'ayin addini idan aka dawo gare shi. Ma'ana Kur'ani abin kafa hujja ne (wato ma'anar ayoyinsa dalili ne) da kuma tabbacin cewa Allah ne ya saukar da shi.
Dangane da wannan maganar, fakihi (mujtahidi) zai dauki Kur'ani asali na farko a wajen binciko hukunce-hukuncen wasu mas'aloli, ta yarda ijtihadin ba zai yiwu ba kai tsaye har sai ya duba littafin Alah kafin ya fara, sai ya kalli asali da ka'idojin da suka tabbatar cewa wannan shi littafin Allah (Kur'ani). Sannan sai ya kalli ka'idojin da suke nuni kan cewar wannan ayar tana nufin abu kaza. A bisa wannan tushen sai ya ajiye Kur'ani a matsayin tushen farko wanda za a dogara da shi lokacin yin ijtihadi da binkito hukunce-hukunce. Saboda karamar shubhar da take nuni a kan rashin ingancin Kur'ani ko ma'anar sa zata hana fakihi jingina ra'ayin da hukuncin da ya gano da Kur'ani dole ba zai jingina hukuncin da ya gano ba ga Allah ko addinin Allah.
Ka'idojin Da Suka Tabbatar Da Kur'ani:
Zamu iya rairayo tushe da ka'idojin tabbatar da Kur'ani:
- Wajibine mujtahidi kafin ya fara komai ya tabbatar cewa Kur'ani littafin Allah ne, idan Kur'ani ba littafin Allah ba ne kaga ba zai dogara da shi ba don ya gano hukuncin addini ba. Saboda haka idan aka ce Kur'ani daga Allah yake to hakan yana nufin abubuwa biyu:
- Duk abin da aka gano a ciki daga wajen Allah yake.
- Hakikanin lafuzza na Kur'ani da kalmomi da aka yi ayoyi da su duk na Allah ne; ai duk wadannan wahayin Allah ne.
-
Tsarin ayoyin da kuma jeranta su da sanya wannan surar bayan waccan duk wannan haka wahayi ya zo da shi.
- Ba makawa mujtahidi sai ya yadda (ya gamsu) da cewar wannan Kur'ani da ke hannun mutane shi ne Kur'anin zamanin Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, abin da ke tsa kanin bangon farko da na karshen wahayin Allah ne, ma'ana babu kari a ciki babu ragi, to dan haka ne wannan tushen za a iya tattare shi karkashin bayani a kan tahrif (kari ko ragi ko canja ma'ana) sai a karanta shi a cikin wannan maudu'i, kuma ba zai yiwu a shigar da wannan bayanin cikin mas'alar tawaturancin Kur'ani (riwaito Kur'ani ta hanyoyi da yawa har ya zamana an tabbatar da cewa daga Allah ne).
- Wajibi ne fakihi (mujtahidi) ya gamsu da cewa wahayi (Kur'ani) Allah ya kare shi daga duk wani kuskure, ai abin da ya sauka a cikin yanayi na wahayi ilimi ne na Allah har ya taho ya sadu da Annabi (SAW0 ba tare da an canja wani abu ba. Nan ba muna magana a kan cewa Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi bai taba furta abin da ba wahayi ba ko ace bai taba samun ishtibahi ba ballantana ya yi kuskure a cikin karbar wahayi ba. Maganar da muke yi kuskure da rikicewa ba su taba kasancewa ba lokacin tahowar wahayi zuwa ga Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi.
- Wajibi ne ga fakihi ya amince cewar Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ma'asumi ne (baya kuskure) baya kuskure ko rafkana ko rikicewa, ai bayan cewa baya kuskure a cikin wahayi, to hakika Annabi baya kuskure a wajen karbar wahayi, haka nan ma lokacin isar da sakon ga mutane.
Tushen da aka doru a kan sa wajen gano ma'anar Alkur’ani
- Dole ne mujtahidi ya yi gini a kan abin da kalmomin Kur'ani suka dauke da shi na ma'ana da Allah ke nufi. Bugu da kari wajibi ne ya komawa Kur'ani a kan wannan asalin maganar, wannan tushen ko da mai sauki ne a fili da kuma fitowar sa baro-baro, sai dai zai yiwu a zama abin tattaunawa tare da musu daga bangaren wasu bakin mazhabobi.
Wasu daga cikin masu tunanin "Romnotikin na sabi"[1] sun kudurce da cewa: Lokacin da mai zane ya zana sura a wani allo, abu ne mai yiwuwa idan muka ga surar mace wannan mai zanen ya bijiro da bakin cikin sa da bacin ran sa lokacin zanen, kuma bugu da kari wani idan ya zo zai iya cewa wannan mai zanen ya bijiro da farin cikin sa da jin dadin sa lokacin yin wannan zanen. Wani mutum (wato na uku) kuma zai iya cewa tabbas wannan mai zanen lokacin da yake zanen jijiyoyin sa a daddaure suke kuma yana cikin fushi, to a nan idan aka ce wanne magana ce dai-dai a cikin wadannan ra'ayoyi? To a nan sai a ce kowacce dai-dai ce hakika kowacce tana kaimu zuwa ga wani ra'ayi sananne, dukkanin fahimta da gano abu ai fahimta ce ingantacciya kuma ma'ana ta fito fili a lokacin da aka ga allon zanen. Hakika wannan abin da zuciya ta yarda da shi a ainihin yadda abin yake: wannan allon zanen baya dauke da wani sakon halin da mai zanen yake cikin ballantana a gwada fahimtar wasu. Ai abin da kowanne ya zo ya fahimta ya dangantu zuwa ga sakafarsa da basirar sa kuma shi ne dai-dai.
A bisa wannan tushen duk tafsirin nassi na addini yana tattaruwa karkashin fahimtar mai tafsiri[2] da wayewarsa har da yanayin al'adarsa. Hakika duk fahimtar nassin addini fahimta ce ta zamani wacce ta rataya da basirar mai tafsiri. An sami sautin wani daga cikin mufakkirai (malamai masu nazari tare da aiwatar da tunani) yana cewa: ba wata ma'ana daya tak a cikin ayoyin Kur'ani ballanta ace kowane malami sai ya gano tra ya bayyana ta, a takaice akwai fage mai fadi mayalwaci a wajen fahimtar ma'anoni, duk malamin da ya kai ga wata fahimta to wannan ita ce dai-dai.[3]
A kan wannan tushen maganar, fakihi zai amince cewa Allah Allah madaukakin sarki yana nufin wata ma'ana a cikin ayoyin Kur'ani, hakan kuwa saboda ma'anar istinbadi shi ne mujtahidi ya bada kokari don ya kai ga abin da Allah yake nufi. Sai fakihi ya dage don ya gani ma'anar dari bisa dari, daga nan zamu fahimci maganar da ake fada a fagen fahimtar Kur'ani da aikin fakihi "wanda ya dace yana da lada biyu wanda ya kuskure ladansa daya".
- Hakika Kur'ani mai girma idan mun kalli bayyana abin da Allah ke nufi zamu ga cewa ya nisanci kawo tsarin magana na ishara (nuni) a lokacin bayanin hukunce-hukuncen fikhu wanda aka dorawa mukallafai (ba ligai) a takaaitaccen takadiri,[4] ya zo da hanya sananniya wacce ta dace da hankali a fagen fahimta da yiwa mutane magana, ai shi Allah ya zabi hanyar masu hankali sai ya bayyana abin da yake nufi tare da gina maganar sa ga mtuane gwargwadon yadda zasu gane.
Hakika a cikin ilimin usulun fikh an tabbatar da "kafa hujja da zahirin lafazi" ma'anar wannan ita ce masu hankali suna dogara da zahirin ma'anar abin da mai magana ya fada, sai su danganta wannan ma'anar zuwa gare shi.
Sai dai meye alkar hakan da shari'a me tsarki? Yaya za a danganta waccen ka'idar mai gamewa ga bayanin shari'a? kuma ta yaya za a iya dorawa shari'a ma'anar abin da ya bayyana daga zancenta?
Hakan yana yiwuwa ne a hali daya kawai, wannan hali shi ne idan muka tabbatar da shar'a da Annabi har ma da imamai hakikanin hanyar da masu hankali ke bi tare da tsarin yadda suke fahimtar abu, basu kagi wata hanya ta su ta daban a wajen fahimta da muhawara ba, bayani mai gamewa sine gudanar da hukunce-hukuncen da aka saba ga maganar Shari'a wanda wannan maganar ta ginu a kan karbar asalin shari'a ita ma tana magana da irin hanyar da masu hankali ke yi, bata kebanta da wata hanya sabuwa ba.
- Share fagen fahiamtar ma'anonin ayoyin Allah a wajen fahimtar hukunce-hukuncen fikhu, a takaice an sami hakan tun zamanin saukar ayoyin Kur'ani, ai ayoyin hukunce-hukunce an kawo su da yanayin yadda za a fahimce su cikin sauki fahimta ingantacciya kuma yana yiwuwa a kai ga gano abin da Allah yake nufi abin da wadannan ayoyin suka kunsa, har ma a fito da hukunce-hukuncen da bayi zasu yi aiki da su.
Idan bai kai ga wannan manufa ba to hakan bai kasance don rashin yiwuwar sa bane ko kuma a ce cigaban wayewar wannan zamanin bata kai za a gane wannan ma'anar ba, sai dai a hankali nan gaba saboda ci gaban ilmi da karuwar basira za a riski ma'anar ta hakika. Amma rashin saituwar tunani da kuskuren tunani kai har ma da gafala su ne suka hana gane hakikanin mas'ala. Misali idan maruwaicin hadisi daga Imam amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya kawo ra'ayinsa a cikin mas'alar da ake magana a kan ta sai wani malami na zamani ya kai ga fahimtar ma'anar nassin da abin da nassin ya kunsa zata yiwu wannan fahimtar ta sabawa fahimtar maruwaicin, kuma bugu da kari ya dauka cewa fahimtar sa ita ce dai-dai daya fahimtar kuma kuskure ce. Idan zamu bijiro da tambaya a kan wannan mas'ala me ya sa bai dauki fahimtar maruwaicin ba tare da ka san cewar sa yana nan lokacin da aka fadi hadisin sai ya dauki wata fahimta sabuwa alhalin zamanin sa ya nisanci zamanin gangarowar hadisin? To zai yiwu ya bada amsar cewa: Hakika ma'anar da na gano a cikin riwayar zai yiwu a fahimce ta tare da gano ta a zamanin da aka fadi hadisin sai dai maruwaici ne ya yi kuskuren fahimta a wajen gano abin da riwayar ke nufi.
Fakihi ba zai ce abin da na fahimta a riwayar yana da alaka da wannan zamanim, riwayar kuma tana da wata ma'anar da ta rataya da zamanin gangarowar ta a wajen masu hankali ba. Saboda haka fakihi ba ya gamsuwa cewa fahimtar sa maimakon fahimtar magabata ce kuma fahimtar sa ta maye gurbin ta su, ba ya yadda cewa fahimta ta kan tafi bai daya ko kuma ta dinga canjawa, sai dai yana yarda cewa fahimtar magabata kuskure ce, magabatan ba su dace ba wajen gano ma'anar da ayar Allah ta kunsa ba, fakihin bai wajabta yiwuwar canjawar fahimtar addini ba, ba kuma amincewa komwacce fahimta ta kan zamanto dai-dai kuma ta dace da abin da shari'a take nufi ba, ya yarda cewa manufar addini tabbatacciya ce, abin da Allah ke nufi a cikin aya ko Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi a hadisi ita ce ma'ana ta ainihi wacce malami yake yunkurin ganota ko dai ya dace ko ya yi kuskure. Da fakihi zai ce: abin da fahimta ta ta gano shi a wannan zamanin ai saboda ci gaban ilimi ne, kuma ba wanda ya sami wannan fahimtar a lokacin saukar da wahayin, tabbas wannan maganar har ma da fahimtar sa zance ne kawai mara kima, saboda dai wadannan hukunce-hukuncen an fuskanto kowa da su kuma sun game kowa da kowa, al'amarin bai kasnace wadanda aka yiwa magana da hukunce-hukuncen Kur'ani mai girma ba za su zo bayan shekara dubu ba, ko kuma mutane kafin shekara dubu hukuncin su daban ne, ballantana ace maganar Allah ta kunshi manufofi masu yawa a cikin wannan aikin kawai,[5] tare da cewa wannan manufa ba zata tabbata ba har sai tarihin cigaba ya zo da sauyawar tunani da wayewa da canjawar fahimta al'amarin ba haka yake ba.
Abin da ya jawo a wannan zamanin muke da yawan bukatar ilimin usulul fikhi saboda doguwar tafiyar da ta raba mu da zamanin gangarowar nassin Kur'ani da hadisi madaukaki.
Hakika mutane a wancan zamanin - lokacin gangarowar nassi daga Allah - suna fahimtar abin da ya dace a fahimta a kan ka'ida, sai dai al'amarin ya sha ban-ban a zamanin mu, kuma hakan saboda banbancin zamani da sauye-sauyen cigaba na wayewa mai zuwa tsa kanin shari'a da masu binta (wadanda aka dora musu nauyin biyayya) an rasa su saboda rashin alaka ta lugga, wayewa da kuma zamanin da ke tsaknain mai magana (mai isar da sako) da wanda ake yiwa maganar (mutakallafai).
Saboda haka idan muna son mu fahimci ma'anar ayoyi da ra'ayoyin da suka zo sama da shekara dubu, to ba makawa sai mun yi amfani da mabudan fahimta wadanda basu kebanta da wani zamani ba, wadannan mabudai su ne a matsayin gadar da ta mike tsa kanin mai magana da wanda akewa magana, saboda ta wannan hanyar ne zamu tabbatar cewa ma'anar da aka fahimta yau ita ce dai wacce aka ganop ta tuntuni gwargwadon ka'ida da asalin fahimta. Wannan maganar ita ce a kan kawo ta a bangaren binciken lafuzza cikin ilimin usul[6]!
- Ayoyin Kur'ani basu kebanta da wuraren saukar su ba, tare cewa yawancin su suna da dalilin sauka kebantacce kuma iya kantacce, kuma suna duba waje kebantacce. Sai dai fakihi yana gano amsar tambayar a cikin su lokacin da zai bada amsar tambayoyin da aka yi masa, ba zai yiwu a dauki lokacin saukar da ayoyin a matsayin lokacin iya kantacce ba har ma ya shiga. Abin da ya sa muka ce haka don saboda wadannan ayoyin basu kebanta da wannan wajen ba kawai, duk abin da ya zo a cikin su yana da alaka da kowanne zamani kuma ya game kowanne waje matukar ba a shafe su ba.
A wani bayanin hakika ayoyin Kur'ani da hukunce-hukuncen da suke ciki sun game kowanne zamani da kowane waje, tabbatar da wannan maganar da kuma nazari mai zurfi don fito da shi fili yana jawo mutum ya karanta maudu'in Assabit walmutahawwit (tabbatacce da wanda ke canjawa) wannan ce maganar da Imam Khomaini (R.A) ya dauki lokaci yana nanata ta a maganganun sa, wanda wannan yana nuni ga cewa zamani da waje suna taka rawa a wajen yin ijtihadi.
Idan mun kalli bangaren bayani a kan tabbataccen hukuncin da mai canjawa magana game da wuraren ka'idar musamman zancen da ya gane da kuma tabbatar hukunce-hukunce kuma suna fa'idantar da samuwar abubuwan da aka togace samuwar hukunce-hukunce da ake gina su a kayyade kuma a wani lokaci iya kantacce. Wannan maudu'ine wanda ke bukatar bayani sosai. Magana a dunkule ita ce hukunce-hukunce masu canjawa masu kayyadadden lokaci suna fitowa ne daga tabbatattun hukunce-hukunce wadanda suka game, hakan dan saboda wadannan hukunce-hukuncen suna gangarowa a kan tushen maslaha ko mafsada tabbatacciya, sai dai suna zuwa tare da kulawa da sharudda na musamman.
Bincike game da tabbataccen hukunci da mai canjawa ana samunsa a filin tunani na fikhun fakihai magabata, hakika an amince da fikirar hukunce-hukunce masu canjawa a dunkule, saboda mafi yawancin hukunce-hukuncen addini ttabbatattu ne, shi yasa basu bawa mas'alar muhimmanci ba sosai sai suka sanya maslahar hakan a kan tushen da yake cewa: (Hakika hukunce-hukuncen addini tabbatattu ne, sai dai idan sabanin haka ya tabbata).[7]
[1] Hermenentic.
[2] Traditio.
[3] A bisa wannan tushen ustaz Hadawiy Tehrani ya karanta wannan mas'alar hermenentic ya tabbatar da canjawar sa da gabatar sa, bugu da kari akan wannan dan takaitaccen bayanin wannan ilimin da kuma kawo ra'ayoyi daban-daban a wannan fagen da abiknda Malaman Musulunci suka kawo a wannan fagen tun da har zuwa yanzu da kuma kulawa da ma'anar kalmar, da asalin amfani da ita, da hanyoyin gane ta. Mahdi Hadawiy Tehraniy, Ususul Kalamiyya lil ijtihad.
[4] Hakika wannan asalin yana da karfi a cikin hukunce-hukuncen Shari'a a takaice domin wani malami yana ganin wannan bahasin yana wajen fagen fikhu ne da hukunce-hukuncen sharia saboda Allah yana da wani launi na magana, da kalmomi na musamman, misali a fagen falsafa da bayanin ma'anoni na irfani madaukaka yaren ishara da buga misali su suka fi runjaye tsakanin Allah da wadanda yake wa magana (bayinsa).
[5] Muna fatan za'a gane cewa wannan bayanin ya sha banban da bayanin badinin Kur'ani, domin mas'alar badinin Kur'ani tana zuwa amma ba'a ayoyin hukunci da fikhu ba maganar farko kenan.
Magana ta biyu, wadannan ma'anoni masu yawa wasu sun zo bayan wasu gwargwadon matsayin zurfin su da tsahon su, ko a matsayin fadin su da kuma nisan da ke tsakanin su duk baki daya shari'a take nufi, dba wai abin nufi ace a zamani kaza abu kaza ake nufi ba abin da ake nufi a wancan zamanin ba, a bisa wannan tushen abinda wasu arifai suka gano daga wasu ayoyin Kur'ani wannan sakamakon fahimta ne wanda ba dalili na shari'a, kuma wannan ba zai yiwu a dauke shi badini daga cikin badinonin Kur'ani ba, kuma baya nuna manufar Allah game game da ayar.
[6] ka duba Sayyid Mohd Bakirssadr, Ma'alima Jadida, sh 51-54.
[7] Mahdi Hadawi Tehraniy, Ususul Kalamiyya lil ijtihad, sh 33-41.