advanced Search
Dubawa
10727
Ranar Isar da Sako: 2006/05/31
Takaitacciyar Tambaya
Yaya za a azabtar da mutanen da suka kirkiro wani abu mai amfani ga dan'adam alhalin ga hidimar da suka yi?
SWALI
Sau da yawa muna ganin da yawan wadanda ba musulmi ba ne ko wadanda ba shi'a ba ne sun siffantun da kyawawan siffofi na yabo da kyawwan halaye, sun yi wa dan'adam wata hidima mai girma da daraja da ayyuka masu yawa abin yabo kamar kirkirowa da gano wasu abubuwa masu amfani, to shin ya kyautu kuwa a ce duk wadannan mutanen an haramta musu ni'imar lahira, kuma zasu fada cikin azabar Allah ce a ranar lahira?
Amsa a Dunkule

Zamu iya kasa mutanen da suka riki musulunci zuwa jama'a gida biyu ne:

1- Jama'ar da ake kira jahili mai takaitawa ko kafiri mai takaitawa, ana nufin su ne wadanda kalmar gaskiya da sakon gasiya na sama na adinin musulunci ya je musu, suka san gaskiya, suka gane hakika, hujja ta hau kan su karara da mafi karfin dalili, sai dai sun ki bin gaskiya, suka karkata zuwa ga bata, suka dage a kansa da girman kai da tsaurin kai, to babu makawa wannan jama'ar tana cancantar azabar Allah da dawwama gidan wuta.

2- Jama'a ta biyu kuwa ita cewa wacce ake cewa da su jahilai masu takaituwa, ana nufin mutanen da sakon Allah da kiran gaskiya na Allah bai je musu ba, ko kuma ya je musu amma ba shi da wani bambanci sosai da abin da suke kansa na addinin wurinsu. Zai iya yiwuwa ma addinin da suke kai ya fi karin haske gare su fiye da wanda ya je musu ma, ko da ko da kuwa wannan addinin ya kai kamar matakin addinin Hindu, da Sin, sai kuma wani addini ya je musu kamar Kiristanci ko Yahudanci.

To wannan al'ummar saboda gaskiyarsu da kyawawan halayensu da lizimtarsu da koyarwar addininsu sun saba da ja'ma'ar farko, don haka aikinsu da kyakkyawan halayensu zasu kasance masu amfani gare su da tsiran su.

Amsa Dalla-dalla

Ba makawa cewa musulunci shi ne addinin gaskiya wanda ya zo da bayanai da akidoji da hankalin mutum yake karfafa da goyon bayan su kamar yadda ya zamu ga cewa shari'ar musulunci shari'a ce mai sauki da saukin faimta da kowa zai iya karbar ta ya shiga karkashin inuwarta.

Kuma kamar yadda musulunci ya nuna mutum yana da hujjoji biyu da zai iya amfana da su don karbar akida: hujjar zahiri da hujjar badini. Wato hujjar zahiri su ne annabawa da waliyyan Allah, amma hujjar badini shi ne hankali ta wata fuskar, wannan kuma wani abu da nuni da shi ya zo a littattafan musulunci, kai ma ya zo da shi karara a littafin Kafi[1].

Sannan kuma musulunci bai yarda da cakuda addinai a akida ba, (wato mutum ya ga cewa addinai mabanbanta duk da sabawarsu amma duka daya ne) domin cakuda addinai yana ginu a kan cewa dukkan akidu abu guda ne madaidaita, kuma musulmi da bayahude, da kirista, da dan hindu, dukkansu madaidaita ne a matsayi da sha'ani, kuma mutum ya ga cewa babu wani dalili a kan bacewar kowacce daga cikin wadannan akidun. Wannan kuwa domin yana kaiwa ga cewa kaiwa ga gaskiya wani abu ne mustahili da ba zai samu ba ta wata fuskar, ta wata fuskar kuwa shi ne zai sanya addini ya zama wani lamari da ba shi da hakika tabbatatta, wanda zai zama ke nan addini wani abu ne na ganin mutum a kashin kansa kawai, sai ke nan gaskiyar kowane addini ya zama ta doru ne bisa abin da shi mutum da kansa yake gani a kan kansa. Kuma idan haka ne tun da mahangar mutane tana da yawa kuma tana da bambanci, sai ya kasance ke nan gaskiya tana da yawa tana bambanta. Daga karshe sai a samu hanyoyin da zasu kai zuwa ga gaskiya da tsira da arzutar duniya da lahira da dawwamar gidan lahira duk sai su bambanta ke nan.

Wannan mahanga tana hannun riga da addinin musulunci, kuma ba zata yi daidai da shi ba a matsayinsa na addini da yake da asasi da akida da rassan ilimi da shari'a da halaye na gari[2].

Don haka ne sai muka ga musulunci yana magana kan wani nau'I na yawaitar al'amura, yawaitar da take nufin yawaitawa a cikin mahangar aiki da halaye, wato kamar sanin iya zama da mtuaen, da kyawawan halaye, da mu'amala kyakkyawa da mutane wadanda suka nesanta daga hakikanin musulunci, da bambantawa taskanin wadanda gaskiya ta isa gare su, da wadanda gaskiya ba ta kai gare su ba, ta kasance tauyayya wacce aka gurbata, da kuma wadanda suke kin gaskiya masu husuma da ita suna sane, don haka sai ya kasa mabiya wasu addinai zuwa gida biyu.

Ta farko: Jama'ar da ake kiran ta da jahila mai takaitawa, ko kafira, wato wannan yana nuni ga wadanda suka san gaskiya da ta isa gare su, kiran musulunci da gaskiya sakon Allah ya je musu, kuma suka gane gaskiya ne, sai dai suka yi taurin kai, da tsaurin kai cikin gaba da kiyayya, suka ki shiga cikin addinin musulunci,  da kin karbar sa bisa girman kai da shisshigi, wannan a fili yake cewa su masu kin gaskiya ne kuma sun cancanci azabar wuta, domin sun san gaskiya da hakika sun gane ta, sai da suka ki karbar ta da kansu, suka zabi makanta kan shiriya, suka fifita bata kan daidaito, wadannan su zasu iya zabar hanyar tsira, su kasance daga cikin mutanenta, sai dai sai suka zabi hanyar halaka da bata, da boye gaskiya da kin ta, don haka sai wannan sakamakon zabin nasu ya kasance wuta ce da azabar jahannama, ko da kuwa a fili sun siffantu da kyakkyawar siffa a zahiri.

Ta biyu: jama'a ta biyu ita ce jama'ar da aka santa da jahila maras takaitawa, kuma ana nufin ita ce jama'ar mutane wacce kiran musulunci bai je musu ba, kiran gaskiya bai kai musu ba, a tauye ne ko kuma a jirkice, nesa da gaskiya, kuma abin da ya je musu ba shi da wani sabani mai yawa da abin da suka saba da shi na addinin da suke kan shi, kuma ta yiwu addinin da suke kansa ma ya fi bayyana da karbuwa gun hankali fiye da abin da ya je musu, wannan kuwa ko da wadannan addinai suna kan matsayin irin addinan hindu, da na kasar sin ne, kuma sai musulunci ko kiristanci ko yahudanci ya je musu.

Irin wannan bayanin ya shafi mutane mabambanta, suna zama ne a cikin jahilcin nan na dazukan afrika, ko kuma a cikin dazukan amerika, ko suna zama a kasashen tura ko amurka, da kasashe masu ci gaba, da dauloli masu wayewa, to tun da su ba ma su takaitawa ba ne a matsyin da suka samu kansu gme da musulunci, kuma ba su samu shiga karkashin inuwarsa, duk da kuma hakan, amma azaba ba zata shafe su ba, domin azaba tana hawa kan wanda gaskiya ta zo musu ne amma ba su karbe ta ba saboda girman kai da tsaurin kai, amma wanda gaskiya ba ta kai musu ba, ko kuma ta kai musu a jirkice, ko kuma ta je musu ba tare da gaskiya tana kunshe a cikinta ba, to wadannan ba masu takaitawa ba ne a matsayinsu wannan, balle kuma a kira su masu laifi, har kuma wannan ya kai ga sanya su cikin masu shiga wuta.

Abin takaici matuka shi ne sai ga shi an samu kafafen watsa labarai masu yada farfaganda kan musulunci suna da yawa matukar gaske ta yadda suka iya sanya shamaki mai yawa tsakanin mafi yawan mutanen duniya da hasken shiriyar da musulunci yake kunshe da shi, kuma wannan ya sanya mafi yawan wurare masu yawa duk da suna da ci gaban ilmi na kere-kere da masana'antu, amma sun wanzu har zuwa yau suna nesa da sanin me ye musulunci da gane gaskiyarsa, kamar yadda duk da ci gaban da aka fada wadanan mutanen suna rayuwar rushewar halaye na gari, da nisantar duk wani kyakkyawan halin kirki.

Kamar yadda abin haushi kuma akwai jama'ar wasu kungiyoyin mutane da suka iya lalala surar musulunci suna kuma masu kiran kansu musulmi. Wannan addini da yake cike da rahama da tausayi da kyawawan halaye da kira zuaw ga ilimi da sani da alheri da aminci da gyara ga al'umma, sai ga shi sun nuna shi a matsayin wani addini mai neman ci baya, sandararre, mai mayar da hannun agogo baya, mai ta'addanci, da ci baya, da kisa, da kishirwar zubar da jini, da zalunci, da rashin bayar da 'yanci ga dan Adam, da sauran siffofin da suke munana wacce musulunci ya barranta daga gare su baki daya.

Don haka ne musulunci yake ganin irin wadannan mutanen marasa sanin musulunci da zasu lizimci al'amuran da kyakkywar dabi'ar halitta ta gari ta yarda da shi, suka lizimci kyawawan abubuwan da addininsu ya zo da shi; kamar nisantar zalunci, da karya, da ninstar duk wani abu da zai cutar da mutum, to zasu kasance cikin masu tsira a ranar lahira.

Sannan wannan lamarin haka nan yake ga masu kadaita Allah da sauran mabiya wasu addinai wadanda su ma sakon gaskiya bai kai gare su ba, kuma wannan ne yake ga wanda yake ba dan shi'a ba daga sauran masu bin sauran mazhabobi daga mutanen da su ma sakon gaskiya sahihi da yake cikin shi'anci na biyayya ga tafarkin alayen manzon Allah (s.a.w) bisa inganci bai kai gare su ba.

A takaice: duk wani wnda bai yi riko da gaskiya ba kamar yadda ya kamata idan ya kasance saboda takaituwa ne da ya samu da jahilci, ba bisa takaitawa da kin gaskiya da tsaurin kai ga barin shiriya ba, to wannan bai cancanci azaba ba idan ya lizimci kyawawan halayen da suke cikin addininsa, da riko da abin da kyakkyawar dabi'ar nan ta halitta ta gari ta zo da shi. Amma kuma duk wanda ya yi gaba da gaskiya ya kutsa cikin husuma yana sane da fadake yana mai takaitawa, to wadannan su ne masu laifi, kuma sun cancanci azabar lahira da wannan[3].

 


[1] Usulul kafi, 1 / 25, hadisi 22, daga kitabul akal wal jahal.

[2] Don karin bayani; duba littafin Nakd, na hudu, shekara ta 1376. H. Sh.

[3] Duba littafin adalcin Allah: Shahid mutahhari; shafi: 319 – 427.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa