Please Wait
24267
- Shiriki
Yin ridda ita ce bayyana fita daga addini, mafi yawanci tana kasancewa ne tare da bada gudum mawar wasu. Horon mai ridda baya game wanda ya fita daga addini amam ya boye hakan bai bayyana shi ba don kar mutane su sani. A bisa wannan tushen horon da za a yi masa ya shafi laifin da ya aikata na zamantakewa, ba wai don ya bata akidar sa ba.
Wanda ya yi ridda ya ketare hakkin mutane, ba don komai ba sai don yrashin kiyaye ruhin addinin da ya ke shugabantar al'umma, saboda haka mai ridda, yana yiwa addinin mutane barazana, musamman wadanda ba su da ta cewa a fagen addini. A farkon Musulunci wasu makiya Musulunci sun kirkiro wata dabara, sai mutum ya shiga Musulunci a zahiri sannan daga baya sai ya yi ridda wai don saboda su raunana imanin Musulmi ta wannan hanya.([i])
Hakika Musulunci ya sanya horo mai tsanani ga wanda ya yi ridda don kawar da wannan dabarar ta su mai hatsari, sai dai kuma a dai-dai wannan lokacin Musulunci ya sanya hanyar tabbatar da ridda ta zama tana da wahala, ba ta da sauki, wannan ne ya jawo ba a zartar da hukuncin ba da yawa sai kadan a farkon Musulunci. Saboda haka, tasirin da wannan ukubar ke yi a cikin zukata ya fi girma fiye da tasirin ukubar a a kan kanta, saboda kaha ne ma wannan ukubar ta sami wajen zama a cikin zukatan mutane ta zauna ta yi daram.
Dole mu kalli wasu abubuwan don jawabi ya fito fili:
- Waye ya yi rid da?
Mai ridda shi ne wanda ya fita daga Musulunci, kuma ya zabi kafirci,([1]) fita daga Musulunci yana tabbata ne idan aka musa wani abu na addini (daruriy) kamar (tauhidi, Annabta, tashin kiyama) da sauransu, haka kuma idan aka kore abin da kowa ya sani da addini alhalin abin kowa ya san shi a addini a fili kara-kara (kamar salla, azumi, zakka, da sauransu) duk Musulmai sun sallama tare da yarda da shi, wannan korewar Manzanci ce domin abubuwa ne guda biyu wadanda ba sa rabuwa.([2])
Ridda ta kasu kaso biyu: Fidriyya da Milhiyya:
- MURTADDUL FIDRIY: Shi ne mutumin da dayan iyayen sa Musulmi ne lokacin samun cikin sa, sannan ya bayyana Musulunci bayan balagarsa, bayan nan kuma sai ya yi ridda([3]) (wato ya fita daga Musulunci).
-
MURTADDUL MILLIY: Shi ne wanda iyayen sa duka kafirai ne a lokacin samun cikin sa, bayan nan sai ya bayyana kafirci bayan balagarsa, sannan ya Musulunta, bayan nan kuma ya koma kafirci.([4])
- Bangare na biyu: hukuncin mai ridda a addinin Allah da mazhabobin Musulunci.
A fikihun shi'a wanda ya yi ridda yana da wasu hukunce-hukunce a babin gado da aure, a zahiri ba a yi tambaya ba game da wadannan hukunce-hukuncen ba. Amma sakamakon mai ridda: Idan mai riddar namiji ne kuma murtaddi ne fdriy to kashe shi za a yi, ba za a karbi tuban sa ba a wajen Allah. Amma murtaddi milliy za a nemi ya tuba da farko, idan ya tuba sai a sake shi, idan ya ki tuba to sai a zartar masa da hukuncin kisa. Amma macen da ta yi ridda ko murtadda ce fidriyya ko murtadda millatiyya ba za a kashe ta ba, za a nemi ta tuba idan ta tuba sai a a rabu da ita, idan ba ta tuba ba sai a daure ta a kurkuku.([5])
Amma a fikhun Sunna: a ra'ayin su wanda ya fi shahara wanda ya yi ridda kowanne iri ne (fidriy ko milliy) za a nemi ya tuba idan ya tuba ya bar wannan riddar sai a sake shi, idan kuma bai tuba ba to hukuncin kisa, za a zartar masa ba tare da banbancewa tsa kanin murtaddi fidriy da moliiy ba haka nan ma tsa kanin namiji da mace, ba banbanci.([6])
Yin ridda a ragowar addinan Allah banda Musulunci laifi ne zunubi ne wanda ake zartarwa mutum da hukuncin kisa.([7])
A bisa wannan zai yiwu muce ridda laifi ne kuma zunubi ne a kowanne addini haka nan ma a kowacec mazhaba ana yankewa mutum hukuncin kisa duk da akwai sabanin kan wasu sharudda.([8])
- Bangare na uku: Hikimar ukubar da sakamkon mai ridda:
Ba makawa za mu waiwayi wasu nukudodi dan bayyana hikimar sakamakon mai ridda.
- An kasa hukunce-hukuncen Musulunci zuwa ga hukuncin dai-daikun da hukuncin zamantakewa (na kowa da kowa), an sanya hukunce-hukuncen zamantakewa a kan tushe na maslahar al'umma, a wasu lokutan wadannan maslahohi suna kuntata fagen 'yancin dai-daikun mutane, kuma wannan a bu ne da ba a musun sa a ko ina a duniya.
- Idan wanda ya yi ridda ya bada kokari dan ya gane Allah Allah madaukakin sarki, to fa Allah zai yi masa uzuri idan ya yi ridda, amma fa bai zama mujrimi (mai lefi) ba a cikin hukunce-hukuncen dai-daikun a ainihin al'amarin ba.([9])
Amma idan ya takaita a wajen gano Allah, za a sake shi a cikin mujirimai a bisa hukunce-hukuncen daidaiku mutane.
A duk lokacin da mai ridda ya bayyana riddarsa a cikin mutane to fa wannan abin da ya yi a matsayin dakko hukunci ne zuwa ga fagen hukuncin zamantakewar al'umma kuma ya samar da barna mai girma saboda bayyana riddar da ya yi, ya zama mai laifi kenan ta wannan bangaren saboda abin da zamu kawo.
- Tabbas ya tozarta hakkokin wasu, hakan kuwa saboda ya haifar da shubha da kokwanto a zukatansu, kuma abin a fili yake cewa samar da shubhohi da yada su a cikin tunani mutane yana jawo raunana karfin imanin su a cikin al'umma, hakan saboda iya kawar da shubhohi tare da kwankwasar su ya kebanta ne ga masu basira da ilimi a cikin sha'anonin addini, amma mafi yawan mutane ba sa iya kare addinin su ballantana su kawar da shubha, hakkin su ne su rayu cikin nutsuwa da addinin su tare da gamsuwa, kar a bar su cikin kokwanto da shubhohi.
- Idan mun kau da kai daga cewa wajibi ne a kare musu imanin su domin hakkin su ne na zamantakewa, to Musulunci yana ganin hakan a matsayin gyaran al'umma ne, saboda haka yake kwadaita musu girmama abubuwan ibada tare da bincike,([10]) yana hana su wofintar da su ko kuma su wulakanta su.([11]) A karshe zamu ga cewa ridda ba laifi ba ce a bangaren mutum shi a kan kansa, ta bangaren hukuncin sa, amma ta bangaren hukuncin zamantakewa ana lissafa ta a matsayin laifi (ta'addanci) wanda ya yi ya cancanci ukuba.
- Idan mun kalli ridda a matsayin laifi (ta'addanci), zamu iya bayanin hikimar ukubar ta, ta hanyoyi masu zuwa:
Cancantar ukuba:
Ukubar mai ridda hukuncin sakamakon sa ne wanda aka sanya shi saboda bata tsarin dabi'un al'umma, duk lokacin da bata dabi'um mutane da addinin su ya girma har ya wuce gona da iri to ukubar da za a yiwa mutum babba ce kuma mai girma. Kowa ya san cewa duk al'ummar da karfi imanin ta da addinin ta yake ja baya, to wannan al'umma za ta nisancewa rabauta komai yawan cigaban da suka samu na ilimi da taknoloji, a bisa wannan maganar duk wani aiki da zai jawo raunin akidar mutane da imanin su to ukubar sa za ta zama mai tsanani, wannan saboda taba mutuntakar Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ne har ma da Imamai amincin Allah ya kara tabbata a gare su, hakan saboda rusa abubuwan addini masu tsarki ne a cikin mutane yana bude kofar canja addini da kau da shi gaba daya.
Hana mai ridda ci gaba da yada riddarsa.
Matukar mai ridda bai bayyana riddar sa ba bai aikata laifi a cikin zamantakewa ba, ukubar da aka sanya masa mai tsanani ai dan saboda hana yaduwar abin ne kar ya fadada.
Bayyana Muhimmancin addinin a cikin mutane.
Duk wani tsari na hakkoki da na sakayya yana bayyana muhimmancin wasu al'amura ta hanyar sa wasu dokokin hakkoki da samakon da ya kebanta da su haka nan sanya ukuba mai tsanani ga wanda ya yi ridda yana nuni ga muhimmancin kiyaye ruhin imani a cikin mutane.
Kwadaitar da tsawaita tunani game da addini kafin a shiga:
Hakika sakamakon mai ridda da ukubar da aka yi masa suna kwadaitarwa wadanda ba Musulmai ba da su kula su yi jinkiri su zurfafa tunani kafin su shiga Musulunci, wannan mas'alar tana maganin yanayi na raunin Imani da Imanin da ke rawa.
Saukake ukubar lahira:
Ukubar duniya tana saukake azabar lahira a nazarin addini da bayaninsa hakika Allah Allah madaukakin sarki mai yawan rahama ne ba zai yiwa mutum azaba sau biyu ba a kan laifi daya, haka riwayoyi suka bayyana a farkon Musulunci yin ukuba a duniya yana jawo mutum ya sami tsarkakuwa a lahira wannan ya jawo masu laifi suna furta laifin su, kuma su yadda a tsayar musu da haddi.
Tunatarwa: tare da cewa ukubar duniya tana saukake ukubar lahira to Allah Allah madaukakin sarki yana da wata kofar tsarkake mutum daga laifuffuka a lahira wannan kofar kuma ita ce tuba ingantacce, idan mai laifi ya tuba tuba na hakika to Allah zai gafarta masa zunubansa ba tare da bukatar yi masa ukuba ba a duniya.
- Yin ijtihadi (taka tsantsan) a cikin saya dokoki:
Abu ne mai yiwuwa cewa wurare nda aka ambata da alamar hikimar yin ukuba ga mai ridda, to haka nan ma ayoyin da suka sauka a cikin Kur'ani suke bayanin kaidin Ahlul-Kitabi da kutunguilar su[12] wanda hakan ba lalle ne ya tabbata a kan dukkanin masu yin ridda ba. Tabbas ba lallai ya zama wanda ya yi ridda yana da manufar rusa Imanin baki dayan mutane ba, ko kuma cutar da addini da al'umma ba, tare da haka Musulunci bai saukake masa ukuba ba. To menene dalilin hakan? A wata magana kuma: zai yiwu a ce wadannan abubuwan da aka fada ba su ne dalilin hikimar yin ukuba ga mai ridda a wasu lokutan ba, to me ya sa Musulunci ya gudanar da yi masa ukuba a wannan hali?.
Jawabin dai shi ne: Duk mai yin doka yana sanya da'irar mahallin hukunci har ma ya fi hikimar hukuncin da dalilin samar da shi fadi da yawa, wannan shi ne abin da suke kiran sa (ihtiyadi a cikin saya doka). Wannan mas'alar ta ginu a kan wasu nukudodi, zamu yi nuni ya zuwa guda biyu daga cikin su:
- hakika ka'idoji da sharuddan da suke kayyade lamari tare da ayyana shi a karkashin yanayi na kulawa da lura, a wani lokaci ba zai yiyu a jinginasu ko kuma a fawwala su ga mutane ba, misali, hakika mun san dalilin da ya jawo aka hana mota tsayawa a gefen kwalbati shi ne haifar da cinkoso da yin hakan kan jawo a mafi yawan lokaci, sai dai wannan dalili ba ya kasancewa lokacin da ba motoci a titi ko lokacin da motoci ba su da yawa. Amma tare da hakan zamu ga masu kula da titi suna hana tsayawar motoci a fili kullum, hakan saboda ba zai yiwu a bar gudanar doka da halin cunkoso ko rashin cukoso a hannun mutane ba.
- A wasu lokutan hukunci yana kasancewa gwargwadon muhimmancin sa sai ya jawo mai sanya doka ya fadada fagen wajen hukuncin, duk wannan saboda ihtiyadi har sai ya sami tabbacin cewa mutane za su kiyaye hukuncin tare da yin abin da aka dora musu. Kamar naha ketarawani mikidari na tazarar dake tsakanin mutum da wajen da aka yi sansanin sojoji ko barokin su. Idan muka yi misali da babban mazaunin sojoji wanda ba a so a matso kusa da shi gwargwadon kilomita biyar, amma a aikace sai kaga tazarar da a ka sa ta ninnika wacce aka fada a cikin doka sosai, wannan kuma saboda la’akari muhimmancin wannan mazaunin da kuma kokarin hana mutane su je wajen, to za mu yi kokarin janyewa wajen da kilomitoci da yawa, har sai mun sami yakinin haka. To fa kamar haka ne wajen sanya dokokin Musulunci, ta hanyar kiyaye wadannan abubuwan goda biyu Allah madaukakin sarki ya yalwata da'irar hikimar sanya hukunce-hukunce da dalilan su, hakan kuma bai zama dan komai ba, sai dan wajibcin kiyayewa da amintarwa da kare wannan hikimar (ta sanya doka) da dalilinta.
Duk wanda yake son karin bayani mai yawa game da hikimar ukubobi a Musulunci ya duba:
Falsafr hakkoki na Kudaratullah khasrushahi - Mustafa danash bajuh, shafi na 201-222, da kuma littafin aladlul ilahi na shahid mudahhari: a tafsirin aya
((لا إكرام فى الدين)) a tafsirin al-mizan j 2; tafsirul amsaliy J 2, a tafsirin wannan ayar.
[1] Imam Khomaini, Faharul Wasiyla, j 2, sh 366: Ibn Kuddama, Almugniy j 10, sh 74.
[2] Imam Khomaini, Fahrul Wasiyla, j 1, sh 118.
[3] Imam Khomaini, Fahrul Wasiyla, j 2, sh 366, wasu suna ganin shardanta Musuluncin daya daga cikin iyaye lokacin haihuwar sa. Khu'iy Takmitatu Mabanil Minhaj j 2, sh 451, wasu kuma suna ganin bayyana Musuluncin sa bayan balaga ba sharadi bane, Shahidussani, Masalikul Ifham, j 2, sh 451.
[4] Imam Khomaini, Fahrul Wasiyla, j 2, sh 366.
[5] Imam Khomaini, Fahrul Wasiyla, j 2, sh 444.
[6] Abdurrahmanul Jaziyriy, Al-Fikhu ala mazahibul arba a, j 4, sh 424, Abu Hanifa ya yi dai-dai da matafiyar shi'a a wajen banbancewa tsa kanin Namiji da mace, Abu Bakril Kasani, Ba'isussanay'i'u j 7, sh 135. Hasanul Basriy ba ya yadda da ace da mai ridda ya tuba, ibn Kuddama, mugni j 0, sh 76.
[7] Ka duba: Ahdul Kadiym: Sifruttawat, fasali 13, Kitabul mukaddas, tarjama ta Farisa waliyan klin, darussaldana, Landan, 1856 Mijladi sh 8-357, Kitabul mukaddas, daru mashruk Berut. Sifru tasnniyatul ishtira'I fasali 13, sh 80-579 Al'ahdul jahid, munazzamatu tarjamatil Kitabul Mukaddas, Tehran, sh 1357 sh 6-305.
[8]Wasu suna ganin hukuncin mutuwa da ake zartarwa da mai ridda ai hukunci ne na ta'aziyar (horon hukumush-shar'iy) baya daga cikin haddi, kamar yadda suka kudurce cewa ta'azizat a hannun hukumush shar'iy yake, yana da damar iya kance ukubar, ba ta da wani takamaiman yanayi a Musulunci a bisa wannan maganar ba zai yiwu a ce hukuncin wanda ya yi ridda a kashe shi ba. Ka duba: Husain Ali Muntazariy, dirasatun fi wulayatil fakihi da fikhuddaula al-Islamiyya, j3, sh 387, Haka ma ka duba isa wala'iy, Al-irtidadu fil Islam sh 129-148.
[9]Allah yace: "Allah bayan dorawa rai face abin da zata iya". Bakara, 286.
[10] Al-Haj, 32.
[11] Al-Ma'ida, 2.
[12] Ali Imran, 72.