Please Wait
19171
Game da Tayar da Wanda ya Mutu a cikin Wata Duniya ta Daban ba wannan Duniyarmu ta Kasa ba, ya Wajaba da Farko mu san cewa ita Kasar da za a Tada Mutane a Cikinta ta Bambanta, Bambanci mai Girman Gaske kuwa daga irin abun da muke Suranta shi, domin Ayoyin Kur’ani suna nuna wannan Hakikar da ke cewa: ’RANAR DA ZA A MUSANYA KASA DA WACCE BA WANNAN KASAR BA DA SAMMAI” [i]
Za a samu Canje-Canje Muhimmai da za su Faru a Duniyar Samuwa, ta yanda Hatta Kasar da za a tashi Alkiyama a Kanta za ta zama ta dace ne da Rayuwar Lahira, da kuma samun Cikakken Tanadi na Yiwuwar ta Wanzu har Abada.
Kafin A Fara Amsa Wannan Tambayar Da Aka Gabatar, Muna Ganin Ya Kamata Muyi Ishara Da Cewa Shi Kabari Da Tashi Daga Kabari Ba Wai Lallai Yana Nufin Kabari Ne Wannan Na Jiki Ba, A’a, Akwai Hadisai Da Suke Ishara Da Cewa Abin da Ake Nufi Da Kabari Shi ne Duniyar Barzahu, Game Da Tayar Da Wanda Zai Mutu A Wata Duniya Ta Daban Kuma, Wanda Ba Wannan Duniyar Ba, Dole Ne Mu Koma Ga Fahimtar Cewa Ita Kasar Da Za a Tada Mutane A cikinta Ta Bambanta, Bambanci Mai Girman Gaske Kuwa Daga Irin Abun Da Muke Suranta Shi, Domin Ayoyin Kur’ani Suna Nuna Wannan Hakikar Da Ke Cewa: ’RANAR DA ZA A MUSANYA KASA DA WACCE BA WANNAN KASAR BA DA SAMMAI” [1]
Za a samu Canje-Canje Muhimmai da za su Faru a Duniyar Samuwa, ta yanda Hatta Kasar da za a tashi Alkiyama a Kanta za ta zama ta dace ne da Rayuwar Lahira, da kuma samun Cikakken Tanadi na Yiwuwar ta Wanzu har Abada. …….
Idan Kuma Muka Kalli Duniyar Samuwa A Gaba Dayanta Da Ma Dukkan Duniyoyin Da Suke Tare Da Ita, Suna Hade Ne A Matsayin Duniyar Kasa Ce Daya, Ba Tare Da Cewa Akwai Wasu Banbance Bambance A Tsakanin Duniyoyin Ba, To A Wannan Lokacin Ya Zamo Ke nan Ba Bukatar A ce Sai Shardanta Cewa Za a Tayar Da Mutum Ne A Wadannan Kaburbura Kasar Da Kebantacciyar Ma’anarta, Domin Dukkanin Duniyoyin Sums Kasa Ne A Gamammiyar Ma’anarta, Musamman Ma Idan Muka Yi Lura Da Cewa Canje-Canje Da Musanyawa Wadanda Zasu Shafi Tashin Alkiyama Ba su Takaita Kawai Ga Duniyar Kasar Mu Kebantacciya Ba, A’a Har Ma Da Sauran Duniyoyi Din.
Ko Da Yake Abun Da Yake Saurin Zuwa A Kwakwalwar Mutum Game Da Sunan Duniyar A Cikin Zantuttukan Kur’ani Mai Girma Ita Ce Wannan Duniyar Da Dan Adam Ke Zaune A Ciki A Yanzu, Amma Wannan A Babin Rinjayar Da Suna Ne Kawai, Saboda La’akari Da Cewa Mafi Yawan Wadanda Ake Magana Da Su, Suna Zaune Ne A Wannan Duniyar kuma Ba su Da Wata Damar, Awancan Lokacin, Da Ake Maganar, Har Ma A wannan Zamanin Namu, Babu Damar Yiwuwar Su Iya Rayuwa A Wata Duniyar Ta Daban, Saboda Haka Abun Da Yake Saurin Zuwa Kwakwalwa Na Dukkan Sunayen Da Suke Zuwa A Cikin Wannan Al’amari Din Suna Komawa Ne Ga Wannan Duniyar Tamu Ta Kasa Da Kuma Abun Da Ke Kewaye Da Shi, Ba Ma Wannan Kawai Ba Hatta Duniyar Wata A Ranar Tashin Alkiyama Za a Kirga Ta Ne A Cikin Wannan Kasar Tamu, Sai Dai Kuma A Game Da Wannan Tambayar Da Aka Gabatar, An Amsa Ta A Wasu Fannoni Na Mahanga Daban Daban, A Wasu Lokutan An Amsa Ne A Fannin Ilmul Kalam, A Wasu Lokutan Kuma An Amsa Ne A Fannin Ruwayoyi, Da Sauran Su, Da Sauran Su.
Saboda Haka Mai Son Karin Bayani Na Bincike Zai Iya Komawa Ga Wadancan Bincike-Binciken Da Aka Yi, Domin Samun Amsa Dalla-Dalla Da Magance Rikice Rikice Masu Yawa Da Aka Haifar A Cikin Wannan Mas’alar, Don Karin Bayani A Tuntubi Wadannan Bayanan: -
- Kasar tashi alkiyama, mai lamba ta 13990 a dandali mai lamba ta.
- Tayarwa da makomar jikkunan mutane, da rashin dawo da sassa na kari a jikkunan mutane 16616 dandali mai lamba ta 16773.