advanced Search
Dubawa
22450
Ranar Isar da Sako: 2007/02/14
Takaitacciyar Tambaya
Nawa ne adadin ‘ya’yan Adam da Hawwa?
SWALI
Nawa ne ‘ya’ya mata da mazan Adam da Hawwa?
Amsa a Dunkule

Babu wani ra’ayi mai karfi – kamar yadda ya zo a cikin abubuwan da suka faru a tarihi masu yawa game da adadin ‘ya’yan Adam (a.s), don haka ne muka ga sabani mai yawa da ra’ayoyi mabambanta kan sunayensu da adadinsu, kuma zai yiwu a samu sabani mai yawa kan wannan mas’ala sakamakon tsawon zamani mai yawa da ya faru a marhalolin tarihi tun lokacin da aka fara rubuta tarihi da dawwana shi, ko kuma ya faru saboda babu wani muhimmanci da marubuta suka bayar tun farko ga ambaton sunayen ‘ya’yan annabi Adam (a.s).

Alkali Nasiruddin alBaidhawai yana fada a littafin “Nizamut Tawarikh an adadi auladi Adam wa Hawwa”: Duk sa’adda Hawwa ta yi ciki to tana haife namiji da mace ne ‘yan tagwaye. Kuma duk mace ta wani cikin to tana aurar wani namijin ne na wani cikin (wato aure ana kulla shi ne ga mace ta wani cikin da namiji na wani cikin ba wanda aka haife su tare ba), haka nan ya ci gaba da fada har ya kai ga cewa: Hawwa ta haifi ciki dari da ishirin ne, kuma ta haifi Kabila a ciki na hudu ne.

Kuma bayan shekaru biyar da mutuwar Habila dan Adam (a.s), sai ta haifi wani da guda daya ba tare da mace tare da shi ba, da aka ambace shi da “Shis”, ya ce: Wannan shi ne musanyar Habila, kuma shi ne da mai yawan albarka da zai zama annabi daga baya[1]. Bisa wannan ra’ayin: Adam da Hawwa (a.s) suna da ‘ya’ya 239 ke nan.

Dabari yana kawo ra’ayoyi uku musamman kan wannan lamarin yana cewa kamar haka:

1. ‘Ya’ya dari da ishirin maza da mata.

2. Arba’in ne maza da mata.

3. ‘Ya’ya maza ishirin da biyar da mata hudu.

Don karin bayani: Tarikh Tabari, Tarihul Umam wal Muluk, j 1, s: 145.

Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id

 


[1] Albaidhawi, Nasiruddin, da MirHashim, alMutahaddis, s: 5 – 6.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • Shin Da Gaske Ne Addinan Da Suka Gaba Ta Kamar Yahudanci Da Nasaranci Su Ma An Shar’anta Musu Yin Dalla Irin Tamu?
    6553 کلیات 2019/10/09
  • Me ake nufi da “ka da ku kirga ranakun sati sai su kirga ku”?
    9821 Dirayar Hadisi 2012/07/26
    Wannan magana ta zo cikin hadisin Manzo (s.a.w), abin nufi da ranaku a nan su ne ranakun sati, amma a mafiya yawan lokuta wannan ruwayar na nufin muhimmancin zamani da wajabcin rashin shakku zuwa ranaku ko rashin kudure su da zai sa a manta su ko muzantan ...
  • mene ne ma’anar Takawa?
    17176 Halayen Nazari 2012/07/25
    Takawa wani karfi ne cikin ruhin mutum mai tsawatarwa da hana shi aikata ayyukan kuskure, kamalar takawa na kasancewa in an hada da nesantar abubuwan haramun, kamar nesantar shubha. Kuma ita Takawa tana da marhaloli da rabe-rabe, da kuma alamomi, zamu bijiro da su a jawabi na ...
  • A lokacin da hura wa Annabi Adam (a.s) rai me ya fara cewa?
    5665 Hdisi 2017/06/17
    An rawaito cewa lokacin Allah madaukaki ya hura wa Annabi Adam daga ransa sai ya ta shi mutum madaidaici sai ya zauna ya yi atishwawa, sai aka yi masa ilhama da ya ce:≪alhamdu lillahi rabbil aalamin≫ “godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai” sai kuwa ya fadi ...
  • mi ake nufi da makamta a ranar lahira?
    15878 Tafsiri 2012/11/21
    Abun nufi da makamta a cikin wannan ayar[i] da sauran ayoyi makamantanta[ii] ba shi ne rashin gani irin na duniya ba {wato mutun ya zamo bai gani da idanuwan da yake dasu} , sai dai abun nufi shi ne mutun da ...
  • Shin wace hanya ko salo zan bi wurin yin wa’azin addini?
    14409 Sirar Ma'asumai 2012/08/15
    Wa’azi yana nufin isar da sakon Allah (s.w.t) zuwa ga jama’a. Kasantuwar sakonin Annabawa a dunkule abu guda ne, sannan sakon Fiyayyan Annabi (s.a.w) na masamman ne, da ya zo da nufin shiryar da bil Adama don fitar da shi daga duffai zuwa ga haske. A bisa haka ...
  • a kan matan aljanna {hurul'in} shin mata zasu samu hurul'in ka yi bayani?
    20743 Tafsiri 2012/07/24
    Daya daga cikin ni'imomin ubangiji a ranar lahira ga wadanda suka yi imani da kyakyawan aiki shi ne sakamako da aljanna da ni'imomin ta. Ba bambanci wuri shiga aljanna tsakanin mace da namiji daga cikin ladar da sakamakon da ubangiji zai ba ‘yan aljanna akwai {hurul'in} wanda ...
  • Wadannan Baitocin Waka Ammar Dan Yasir Ya Rera A Lokacin Da Ake Aiki Ginin Masallacin Manzo (S.A.W)?
    7515 Ilimin Sira 2018/11/04
    Allama majlisi a cikin biharu ya rubuta cewa: a lokacin da Manzo (s.a.w) tare da sahabbansa suka kasance suna gina masallaci sai wana sahabi ya zo wucewa ya tsaba ado yana sanye da tufafi mai kyau a lokacin Ammar Dan Yasir ya daga muryar ya yana mai ...
  • Ni saurayi ne kuma a yanzu ina da bukatuwar in san mene ne rayuwa da hadafinta.
    18668 Dirayar Hadisi 2012/07/25
    Akwai nassoshi masu yawa da suka zo a cikin koyarwa da dokokin musulunci wadanda suke nuni da hadafin rayuwa da cikakkiyar manufarta. shi Kur’ani Mai girma yana daukar cewa manufar rayuwa ita ce: “bautar Allah madaukakin Sarki, wadda ta hanyarta ce za a iya isa ga kamaloli ...
  • Tarihin Adam (as)
    20456 2019/06/16
    Amsa Filla-Filla: bayani kan rayuwar wasu nau”in mutane da aka fara halitta a bayan kasa, da kuma sanin shekara nawa kenan da halittar su zuwa wannan zamani da muke ciki? To hakika babu wata aya da ta yi bayanin hakan cikin kur”ani. Allama daba”ba”i cikin tafsirinsa na ...

Mafi Dubawa