advanced Search
Dubawa
12803
Ranar Isar da Sako: 2012/05/21
Takaitacciyar Tambaya
Mene ne Addini?
SWALI
Mene ne Addini?
Amsa a Dunkule

An yi nuni da ra’ayoyi kala-kala masu yawa a addini kuma an yi amfani da Kalmar “addini” a wurare masu yawa da ma’anoni kamar haka: 1. Duk wani imani da wani karfi boyayye na gaskiya ne ko na barna. 2-kawai addinin Allah saukakke.

Don haka a bayanin ma’anar addini zamu ga bisa la’akari da ma’ana ta biyu ne zamu ga ana magana kan addini na musamman da aka saukar da wurin Allah madaukaki.

Amsa Dalla-dalla

An kawo ma’anoni masu yawa a bayanin ma’anar meye addini gun yammancin duniya kamar Jon Haik a Hikimar addini da bayanai kala-kala bisa mahangogi mabambanta game da ma’anar addini:

a- Ilimin sanin yanayin matsalolin ran dan adam: Addini shi ne wasu akidu da ayyuka da jarrabawa mutane a lokacin da suke kebe, kai da duk wani abu da suke kira ubangiji na abin da yake gabansu. (William James).

b- Ilimin rayuwar al’umma: Addini wasu akidu ne da ayyuka da alamomi masu tsarki da al’adun addini wanda mutum ya ginu kansu a cikin al’ummu mabambanta. (Talkot Parsonz).

c- Ma’abota ilimin halittu: Addini wasu umarni da hani ne wadanda suke hana aikin ‘yanci halaye. (Ess Rainakh). Da wani bayanin kuma: Addini shi ne halayen da abin riska da motsa rai suke daukaka da shi, zafi da haske sakamakonsa ne. (Mathew Arnold).

d- Bayanin Addini: sun hada da kamar; addini wani tunani ne na gaske game da wani samamme na hakika da dukkan samammu na halitta suke masu nuni ne zuwa ga samuwarsa wanda yake ya fi karfi kuma ya wuce iliminmu da saninmu su kai ga gane hakikaninsa. (harbart Espensa)[1].

Yawan mahangai mabambanta na ma'abota sanin yammacin duniya ya sanya dole su yarda da cewa : "Addini ba shi da wata ma'ana guda daya da aka hadu a kanta gaba daya, sai dai yana da abubuwa masu yawa da suka hadu da ake kiran su da addini masu alaka da juna. Wata alaka ce da da wetgnashtain yake cewa da ita ta samu ne sakamakon kuskuren iyali[2], kamar yadda ya kira ta[3].

An yi amfani da kalmar addini a cikin wurare biyu a cikin Kur'ani mai girma:

1- addini shi ne dukkan wani imani da gaibi wanda yake na gaskiya ne ko na karya: "kuna da addininku ni ma ina da addinina"[4].

2- Addinan ubangiji kawai: "Addini kawai a musulunci shi ne musulunci"[5].

Sai dai mu a bayanin addnini abin da yake muhimmi a nan shi ne wanda ya kebanci addinin Allah madaukaki a dukkan fagage da marhaloli mabambanta a matsayin addini saukakke[6].

Karin bayani:

Mahdi Hadawi tehrani, wilaya wa diyanat, cibiyar al'adu ta Khaniye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.

Mahdi Hadawi tehrani, wilaya wa diyanat, cibiyar al'adu ta Khaniye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.

 

 


[1] John Hack: falsafe deen: s 22 – 23. Tarjamar: Bahram Rad, Tehran 1372.

[2] Family Resemblance

[3] John Haick: falsafe deen: s 23 – 24.

[4]  Kafirun: 6.

[5] Aali Imaran: 19.

[6] Marhalolin addini.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa