Please Wait
13988
Hankali shi ne hujjar Allah ta addini wacce ya ba wa mutum, hankali ke yi wa mutum jagora har ya kai shi ga samun cikakkiyar kamala, Shari`a hujja ce ta fili wacce take hana mutum gurbata da cutaya kuma ta kai shi ga samun cika da rabauta. A bisa wannan maganar ba zai yiwu hujja ta addini ta ci karo da hujja ta zahiri ba.
Hujja tana nufin a bin da ke nunawa mutum hanya, jagora shi ne wanda ya san hanya, ya san bayanan hanyar da abin da ya shafi hanyar, kuma ba makawa sai mun waiwayi cewa wadannan hujjojin na badini da na zahiri ba sa rabuwa da junan ako da yaushe a tare suke yin aiki, wato abin da ake nufi a nan shi ne daya ba ta iya yin aiki ba tare da taimakon dayar ba.
A lokacin da mutum ya kai ga cimma burin sa, to hakan yana nufin an sami dacewa da taimakekeniyar Hujjojin nan biyu.
A bisa wannan tushen rashin dacewar wani asali daga asulla na hankali tare da wata mas'ala daga cikin mas'alolin addini to hakan ko dai ya kasance saboda rashin kiyaye mukaddimat (abubuwan share fage) da dokokin inganta tunani na hankali wadanda ake amfani da su wajen kafa hujja ko bata dalili, ko kuma saboda kuskuren fahimtar nassin addini da kuma rashin gano ma'anar sa ta hakika.
Ba a samun sabani tsakanin Musulunci da hankali, sai dai wasu lokuta ana iya ganin wani abu ya fita daga da'irar addini, ko kuma kafa dalili da hujja ta hankali ba su zamanto a kan tushen mukaddamat da sharudda ingantattu ba, ko kuma a zabi wata ma'ana wace ta dace da hankali duk wannan n daga ikin abin da ke haifar da tunanin rashin dacewa tsakanin hankali da addini, don a gane ko wane sashe na wannan bayanin da ya ke sassabawa da yanayin mas'alolin, to ya zama lalle mu karanci wandannan abubuwan masu zuwa:
- HANKALI DA KUMA DACEWAR HANKALI A FAHIMTAR MALAMAN FALSAFAR MUSULUNCI:
Karfin tunani wanda shi ne mafi girmar baiwar da a ka ba bil’adama, tunani wani aiki ne na kwakwalwa wanda yake kwarara a kan mafahiym (gano abu a cikin kwakwalwa), ta hanyar gano abubuwan da ba a san su ba ta hanyar sanannun abubuwa da muka sani. Hanyar hankali ta kiyasi an gina ta ne a kan yushen nan na sharer fage na hankali tsantsn. Hanyar hankali da yake ginuwa a kan tushen wasu abubuwa na sharar fage kamar badiyhiyyatiy awwaliyya (abubuwan da kowa ya sani saboda a fili suke ba su da bukatar dalili) ko kuma suna takewa gare su (su badihiyyat auwaliyya), kamar yadda hakan ya tabbata a cikin kiyasin hujja wanda sau da yawa ana amfani da shi a falsafar farko (tsohuwar falsafa ta da) da riyadiyyat (lissafi da kirga) kuma da yawadaga mas'alolin ilimin falsafa. Banbanci tsakanin hanyar hankali da hanyar jarraba abubuwa shi ne dogaro a kan hanya ta hankali ya tsaya ne a kan badihiyyatul awwaliyya, alhalin jarrabawa ta dogara ne a kan hanyar share fagen gwaji ko gwaje-gwaje ko jarrabawa.[1] Amma falsafar Musulunci a wajen gane wujud (samuwa) da sanin Allah da gane mutum a duk wadannan guda biyun ta dogara ne a kan hanya ta hankali.
- HANYAR ANNABAWA DA HANYAR HANKALI:
Ba wani banbanci da sabani tsakanin hanyar Annabawa da kuma hanyar su ta kira mutane zuwa gaskiya da kuma abin da mutum ya gano da hanyar kafa dalili na mandik (wato tunani ko riskar hankali), idan aka sami fifiko to yana tabbatuwa ne saboda Anabi yana karbar wahayi daga wajen Allah, kuma yana sha daga wahayi mai tsarki, sai dai wadannan Annabawa masu girma duk da cewa suna saduwa da ilimi mai girma (wahayi) sai dai suna ajiye matsayin su gwargwadon fahimtar mutane su yi musu magana da harshen da za su gane tare da neman mutane su karfafa wannan fidirar mai karfi da dalilai na hankali da ganewa. Saboda haka Annabawa ba za su taba kiran mutane wai don su mika wuya mika wuya na makanta ba, ba tare da basira ba, da tunani da hankali, Al-Kur'ani mai girma yana cewa:
((قل هذه سبيلي أدعوا إلى الله على بصيرة أنا ومن اتبعني)).
"ka gaya musu wannan ce hanya ta wacce nake kria zuwa ga Allah a kan basira na ke ni da duk wanda ya bini".[2]
Addini da hankali, ko Sharia da hikima a hade suke idan an kalli manufa da hanya ba wani sabani tsakanin su, Addinin hakika shi ne addinin dake kiran mutane don su sami yakini in an danganta shi ga yanayin da ya sabawa dabi'a ta hanyar kafa dalili da hankali da hujja ta mandik (wacce aka riska ta hanyar tunani) saboda haka, hankali da riwaya tare suke, haka nan ma idan mun dubi Kur'ani da Hadisi duba mai zurfi, zai yiwu ka hadu da sakamkon nazarin hikima da falsafa. Addini da Falsafa bangarori ne biyu ga tabbataccen abu guda daya, kuma alamu ne ga tabbacin abu daya, hankali hujja ce ta boye ga mutum wacce take jawo shi zuwa ga kamala, sharia kuma hujja ce ta zahiri wacce take tserar da mutum daga afkawa cikin talaucewa har ma ta rike hannun sa zuwa ga samun kamala da arzikin mutuntaka. Imam Musalkazim (AS) yana cewa: "tabbas Allah ya hade hujjoji biyu: hujja ta zahiri da hujja ta badini, amman hujjar zahiri, sune Annabawa, Mursalai da Imamai, amma hujojin badini sune hankula”.[3]
A bisa wnanan tushen ba zai yiwu hujja ta badini ta ci karo da hujja ta zahiri ba. Saboda ma'anar hujja ai dalili ke nan da kuma alamar da take nunawa mutum hanya harma ta kai shi inda ya nufa, kamar yadda riwaya ta zo daga Imam Kazim amincin Allah ya kara tabbata a gare shi cewa akwai hanyoyi guda biyu wadanda suke kai mutum wajen Allah: Jagora mai shiryarwa na waje (Sharia) da kuma jagora mai shiryarwa na ciki (hankali). To a nan ba makawa sai mun waiga zuwa ga hujjojin nan biyu (ta boye da ta zahiri) basa rabuwa da junansu sanan daya bata cin gashin kanta ba tare da dayar ba.
Lokacin da mutum ya kai ga manufar sa to wannan yana nufin an sami dacewa da dai-daituwa tsa kanin wadannan hujjojin biyu.
Hujjar zahiri (Annabawa da Imamai) ba ta rabuwa da hankali da aiki da shi, saboda wasidan bayarwa (tsa kanin biyarwa) kullum dai shi ne ma'asumi, shi ne cikakken hankali, lafazin basira da ya zo a cikin aya ta 108 a Suratu Yusuf yana bayyana wannan mas'alar a fili.
Kamar yadda Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi yace: (wanda ba shi da hankali ba shi da addini).[4] To fa haka ne hakika hujja ta badini (hankali) bata wadatuwa daga barin addini da shari'a, kuma kamar yadda Imam Husain amincin Allah ya kara tabbata a gare shi yace: (Cikar hankali bin addini),[5] kuma kamar yadda ya zo a littafin Allah cewa Allah shi ne gaskiya,[6] kuma daga gare shi gaskiya take.
((الحق من ربك فلا تكن من الممترين)).
“gaskiya na wajen Ubangijinka kar ka zamo daga cikin masu kokwanto” [7]
Saboda haka, hankali yana samun kamala ne sanadiyyar bin gaskiya, bin hujja ta zahiri yana daga cikin abubuwan da Allah ya bada umarni, Allah yana cewa:
((يأيها الذين آمنوا أطيعوا الله وأطيعوا الرسول وأولى الأمر منكم)).
"Ya ku masu imani ku bi Allah da Manzo da wadanda suka jibinci al'amuran ku".[8]
Muhimmiyar mas'ala ita ce hakikanin abubuwan addini da koyarwar sa mai girma ta kan saba da hankalin dikarat (saboda dikarat yana ganin cewa hankalin kowa bashi da ma'ana ballantana a yi nuni gare shi) ya kafa himmarsa a kan hankalin da yake tsara abubuwa wanda yake dukan nesa, ko kuma wannan koyarwar tana cin karo da hankali a matafiyar 'yan barakmati (domin hankali a wajen 'yan albaragmatiyin shi ne yake samar da abu kuma mai fa'ida da amfani a wajen warware matsaloli da kulli a wajen jarraba abubuwa, ko kuma yana cin karo da hankalin nazari a wajen kant (yana ganin hankali na nazari baya iya warware masa'aloli, hakika hukunce-hukunecn hankali a wannan fagen ba su da kima ta ilmi).
A fili abin yake abubuwan fahimta na addini kamar fifita wani, ba da kai, shaida, ciyarwa, imani da gaibu da wasun wadannan na koyarwar addini wadanda ake dabbakawa (gasu a fili ana gani) wadanda addini ke gina hasashin a kai, ba zai yiwu a fassara su da hankalin wani ba ko hankalin da ya ke hango nesa ba, sai dai wadannan abubuwa masu kima ba zai yiwu ga daya daga cikin su ba ya ci karo da abin da falsafar hankali take koyarwa ba, kuma ba sa kore ji na gaba daya.
Sakamako shi ne: dangane da abinda ya gabata na dacewar bayyanawa da kuma dacewar hankali da addini, da bacin maganar kishiyantar junan su da warware junan su wato tsakanin Musulunci da kafa dalili na hankali. Hakan kuma saboda hadafin su iri daya ne, abu daya ne ya samar da su, kuma hanyar su ma daya ce. A yayin rashin dacewar asalin hankali da abubuwan addini wannan na komawa ne ga samuwar wasu barakoki a cikin mukaddimat na istidlali na hankali ko na burhan (hujja) ko kuma lamarin zai dawo ga rashin kiyaye ka'idoji tabbatattu lokacin fahimtar nassin addini fahimta ingantacciya da kuma kaiwa ga manufofin nassin.
FADAKARWA:
- Saboda kasancewar hujja ta hankali (burhanul akliy) hujja ce ta Allah, to duk wanda yake yin ta’muli na yau da gobe da nassoshin addini a bisa asalin fahimtar hankali cikakke to zai sami rabo mai yawa a cikin ilimin addinin kuma zai gano abubuwa da tyawa, ko dai daga nassin riwayar ko daga dalili na hankali.
Dalili na hankali kamar dalili ne na riwaya wanda aka yadda da shi, yana daga cikin ilhamar kokimsawar Ubangiji wacce take bayyana a lokacin gogayyar tunani a wajen mutane. A bisa wannan tushen duk wanda dauki hankali makami wajen yin gogayya da nassin addini mai tsarki har ya binciko abin da yake iya bincikowa, to hakika aikinsa ya yi kama da aikin wanda ya fassara aya da aya, ko wanda yake bayyana ma'anar aya ta hanyar amfani da riwayar hadisi, saboda wadannan abubuwan ba su yi wa nassi nisa ba sannan ba baki ba ne a wajen sa.
Na'am, idan ya yi gogayya da dayan nassoshin ta hanyar istikra'i tauyayyu (biyayya da bata game abin da ake so a gano ba) ko kuma tamsili mandikiy a wajen tabbatar da hukuncin wani abin ga wani abu) wanda ya ginu a bisa mugalada (kuskure), hakika wannan zai hana ma'anar nassin ta fito kuma zai cudanya shi da gurbatattun abubuwa, wanda wannan zai jawo wa fahimtar nassin gamuwa da abubuwa masu kura wadanda za su gurbata gano ma'anar nassin.
- Idan mai tambaya ya yi tambaya ya ce: Shin zai yiwu mu iya kare duk mas'alolin addini da hankali (na gaba daya dana wani bangaren). Amsar ita ce: dole ne a sa hankali a wajen gane addini, sai dai shi kadai baya gamsarwa, saboda haka ba za mu iya kare dai-daikun abubuwa na addini da hankali ba, domin ba zai yiyu a kafa hujja kan dai-daikun abubuwan ba kamar yadda yake a ka’idar ta kafa hujja da kuma ta dalili na hankali, daidai wadannan dai-daikun sun zamanto dai-daikun abubuwa ne a dabi'a ko na Shari'a. a wani bayanin kuma su dai-daikun abubuwa sun fi karfi a kirasu da abubuwa na ilimi ko su zama ayyanannu, na hakika ko I'itibariyya, (kamar mallaka, aure, bauta) duk wadannan ba sa shiga cikin kafa hujja ta hankali (burhanul akliy), ba komai ne hankali ke riska ba, to ba zai yiwu a ce yana da wani dalili na hankali ko tafsiri na hankali ba, tabba al'amarin ya sha ban-ban dangane da (kulluyyat) wato tarin abubuwa ko daukakin abubuwa da kuma abubuwa masu fadi (wadanda suke da abubuwa a karkashin su) idan an danganta su ga dabi'a da Sharia, duk wadannan suna karkashin hankali (domin yana riskar su) kuma suna karbar tafsiri na hankali.
Domin mu yi bayanin a kan haka dalla-dalla sai mu ce: sau da yawa hankali yana ganin kansa gajiyayye kuma yana bukatar wahayi, maganar wahayi tana rairayuwa idan hankali yace: hakika ni ban san abubuwa da yawa ba, tabbas ina bukatar wahayi.
A bisa asasin faffadar hujja ta Annabta hankali yana cewa: lallai ina da hadafi mai gamewa na har'abada, kuma ina sanin hanyar da za ta kai ga wannan hafadin, sai dai hanyar mai tsaho ce, kuma mai wahala, ba zai yiwu a bita cikin ta ba ba tare da jagora ba, hakika boyayyen jagora shi ne Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi. Ba makawa sai an saurari koyarwar jagoran a cikin abubuwa na gaba daya da na dai-daiku tare da dabbaka su da yin aiki da su, dan haka ba za a ce: saboda me muke yin sallar asuba raka'a biyu azahar hudu? Ko saboda me muke yin magriba karatun ta a fili azahar kuma a boye? Ko saboda me wannan kifin ya zama halal wancan kuma haram? To tun da hankali ya gajiya ya fahimci ya kuma riskar dai-daikun abubuwa, to shi da kansa yana cewa: ina bukatar Annabi, saboda haka hankali baya da'awar shiga cikin dai-daikun abubuwa, idan kuma aka dora masa irin wannan da'awar, to fa - mu sani - shi gajiyayye ne ba shi da ikon yin komai ba kuma zia kai ga cimma komai ba.[9]
Ka duba wadannan littattafai:
- Tabatabr'iy, Sayyid Mohd Husain, Aliyu wal-fasafatul ilahiyya.
- Tabatabr'iy, Sayyid Mohd Husain, Attafakkur fil Kur'an.
- Jawadiy Amuly, Alhiknatun nazariya wal amaliyya fi nahjil balaga.
- Jawadiy Amuly, Ashshari'a fi mis'atiy ma'arifa 199-224.
- Hadawiy Tehrani, Mohd; Yawarha wayarsashha, 51-58.
- Hadawiy Tehrani, Mohd, Al'ususul kalamiyya liy ijtihadi 280-284.
[1] Misbahul Yazdiy ta'aliymul falsafa Ji sh. 101
[2] Yusif 108.
[3] Ka duba muntakhabu mizaniy hikma, ciyy, Shahri sh 358, hadisi 4387.
[4] Ka duba muntakhabu mizaniy hikma, Riyyu Shahri sh. 357 hadisi 4363.
[5] Ka duba muntakhabu mizaniy hikma, Riyyu Shahri sh. 359 hadisi 4407.
[6] Lukman 30.
[7] Ali Imrana 60.
[8] Nisa'i, 59.
[9] Jawadiy Amuly, ma'arifatuddini (silsilatu abhasin falsafaiyya) sh. 127 – 174.