advanced Search
Dubawa
8529
Ranar Isar da Sako: 2006/05/22
Takaitacciyar Tambaya
Saboda Me Dukkanin Malamai Ba Su Kebanci Lamarin Shugabancin Malami Da Wani Fasali Ma Musamman Ba, Kuma Ba Su Yi Bayanin Dokokin Ko Kace Sharadan Wannan Shugabancini Ba?
SWALI
Saboda Me Dukkanin Malamai Ba Su Kebanci Lamarin Shugabancin Malami Da Wani Fasali Ma Musamman Ba, Kuma Ba Su Yi Bayanin Dokokin Ko Kace Sharadan Wannan Shugabancini Ba?
Amsa a Dunkule

Wasu daga cikin malamin ba su yi babi ko fasali na musamman ba ga wannan lamarin saboda suna ganinsa abu mai saukin ganewa, wanda kuwa ya sallama a kan sa, kuma babau bukatar yin bahasi domin tabbatar da shi, a yayain da suka bude babobi na musamman a domin su bayyana nauyaye nauyaye da kuma shu’unan shugabancin malami.

Dun da har amsa tambayoyin mutane na shari’a abu ne da ya hau kan malamai, wannan ya sa suka kasance suna kawar da bukatun mutane na shari’a kuma suna ganin hakan wani nauyi ne da ya hau kansu. Don haka ne ma sai ya zamo mafi yawan mas’alolin da suke zagayawa a wannan zamanin su ne wadanda mutane suka fi fama da su, gama cewa mas’alar shugabanci da mulki ba sa daga cikin mas’alolin da `yan shi’a suke fama da su kafin bayyanar daular safawiyya, sai wannan ya sa malami ba su himmatu wajen yin Magana da bincike kan lamarin mulki da na daula ba, sai suka takaita a yin bayani a kan wannan lamarin tahanyar `yan bayanai nan da can ta yadda zai isar ga bukatar muminai

Amsa Dalla-dalla

Ya zama wajibi mu waiwayi wasu matsikayoyi guda biyu a yayin da muka koma ya zuwa maganganin ko rubuce- rubucen malaman shi’a a kan a bin da ya shafi lamarin shugabancin malami:

  1. Wasu daga cikin malamai sun bayyana karara cewa lamarin shugabancin malami na daga cikin abin da malamai shi’a suka hadu a kan sa, idan har wani daga cikin su bai ware wa lamarin fasali na misamman ba to wannan na nufin cewa sun kasance sana daukar sa a matsayin lamarin da kowa ke ganewa da sauki (badihi) wanda kowa ya tafi a kan sa, don haka ba sa gani cewa yana da mihimmanci a yi bayanin kan sa a kuma kawo dallilai dahujjoji a akai.

Kari a a kan haka hakika suna kasance kuna yin Magana kan lamarin shugabancin malami da kuma abubuwan da ke kewaye da ita a babobi mabanmanta. Idan da za hada wadannan kalmomin da maganaganun madaidaita to sannu za mu iya tashin babi guda wanda ba zai gaza sauran baboobin fikihu ba, a kan wannan ne ma mai littafin Jawahir yake cewa: zantukan malamai sun yawaita kan maganar a kan komawa ga shugaba (malami)  hakika malaman shi’a sun saba da yawan ambaton shugabancin malami a mafi yawan bincike – bincikensu.[1]

  1. Gama cewa amsa tambayoyi da bukatun mutane abu ne da ya hau ka malamai masana, hakika sun kasance suna kawar da bukatun mutane na shari’a  kuma suna ganin wannan wani a bu ne da ya hau kansu, saboda haka ne ma mafi yawan mas’alolin da suke bayyanawa suke bada amsa a kansu na daga cikin mafi yawan abubuwan da mutane ke ta’amuli da a yau da kullum, kuma da yake lamarin shugabanci da mulki ba ya daga cikin lamarin da al’umar shi’a ke fama da shi, kafin bayyanar daular safawiyya, sai ya zama malamai ba su himmatu ba wajen bayyana hukunce hukuncen shugabanci da mulki irin na malamai ba, sai suka takaita da ambaton dan a abin da aba’a rasa ba a daidaikun warare (a cikin babobi daban daban) ta yadda zai wadatar da bukatar mumini.[2] Kuma za mu iya togace wasu daga cikin wadannan malaman kamar su Sayyid Murtadha da Hakimai (masana ilimin akida ko aka’id),  musalin khoja Nasirud Din wadanada suka rayu a wancen zamanin, ma’ana tun daga farkon gaiba babba har ya zuwa bayyanar daular safawiyya – wanna kuma ya faru a sakamakon kokarin das hi Sayyid Murtadha ya yin a karfaffar alakar da ke tsakanin  da mahukumtan Aali Bawaihi, da kuma sakamakon cewa khoja Nasiyud Dini ya karbi mastayin matemakin (mukamin matemaki na shugaba ko kuma na wani bangaren)  a cikin hukumar Holako na wani tsawon lokaci.

Wadanna malaman sun kasance suna fuskantar mas’alolin na (mulki) na hukuma kuma suna taka rawar gani a kai. Marigayi kashiful Gida’I ya danganta sababain karbar wadannan malaman ga wadanan mukaman ya zuwa yin imanin su da shugabancin malami, kuma ba su da wata hanya da za su iya karbar wannan hakkin sai ta hanyar wannan alakar sai suka dauki matakin cimma wannan lamarin ko da kuwa wani bangare ne na shugabancin,[3] kuma muhakkikul karaka ya yi dace (ittfaki) da Kashiful Gida’I a cikin wannan ra’ayin na sa kuma yana ganin cewa wadannan malaman na daga cikin matemaka ra’ayin nan na shugabancin malami.[4]

Bayan tabbatar hukumar safawiyya a a Iran sai yanayi ya canja canji mai girma, sai aka sami farkon daula ta shi’anci  a kasar, duk da cewa tsarin mulkin daular safawiyya tsari ne na sarauta kuma mafi yawan malaman shi’a suna ganin sa a matsayin hukuncin kwace da danniya, amma yanayi mai tsananin wanda duniyar musulunci ta sami kan ta a wancen lokacin da kuma munanan kai hari da barazanar da mulhidai da makamantansu ke kai wa kan musulunci, sai ya sa wasu daga cikin malamai suka yi aiki hannu da hannu domin samun mafita daga wannan mummunan yanayin mai matsi kuma sun kasance suna ganin cewa ta wannan hanyar ne kawai za a sami mafita wannan yanayin, sai wannan ya sa aka sami alaka mai danko tsakanin daular safawiyya da kuma wasu daga cikin malaman addini.

Bayan tsayuwar gwamnatin musulunci sai marigayi imam khomaini (Allah ya yi masa rahama) ya tsuro mana da sababbin bahasosi masu yawa wadanda ya tattauna iyakokin mabanbanta na shugabancin malami, wannan shugaban namu wanda ya daga tutar kabilar ko dangin makadaita (masu kadaita Allah ta’ala) kuma ya shugabanci jama’ar da ke neman adalci, bari mu sanya maganar wannan bawan Allahn wanda ya raya musulumci na hakika a lokacin da ko kuma zamani da yake na azzalumai kuma zamani sabuwar jahiliyya, ya zama turaren da za mu rufi maganbanunmu da shi a cikin wannan binciken:-

Shugabancin malami baya daga cikin sabon binciken da muka kirkira, ballantana ma wannan na daga cikin tsohon lamari. A lokaicn da Mirza Shirazi ya zartar da hukuncinsa a lokacin da aka yin boren shan taba, ya zama wahibi ga saura malamai su bi shi a wannan fatawar domin wannan hukunci ne na hukuma (kwanati)….. wannan ba hukunci ne na kotu ba ko kuma na sabani tsakani mutane biyu ko uku a kan wani lamari ba. Hakama hukuncin jihadin da Mirza Muhammad Takiyyi Shirazi ya zartar – wanda ya kira shi da kare kai a wancen lokacin wanda sauran malamai suka yi masa biyayya saboda hukunci ne na hukuma wanda ya zama wajibi a ayi masa biyayya a kai.

Har ma lamarin ya kai ga cewa an nakalto bayani dalla-dalla kan wannan batu daga marigayi Kashiful Gida’a, kamar yadda aka samo daga malaman sa suka zo a baya-baya cewa marigaya Annaraki cewa ya yi imani (ya kudurce da cewa) da tabbatar dukkani sha’anoni manzon Allah ga ga malami.

Amma Muhakk Anna’ini ya kasance ya na kafa hujja a kan wannan lamarin da hadisin nan karbabbe (makbul) na Hanzala. Abi sa ko wane hali, wannan lamarin ba sabo ba ne, kuma mu ba wani abu muka yi ba face sai karantar bahasin a fadade, tare da bayyana rassan hukuma da kuma kasha-kashen ta, kuma mun dora nauyin wannan bincikin a yuwan wadannan manyan bayin Allahn domin lmarin ya bayyana sosai a sarari… in ba don haka ba, mahallin binciken a nan shi ne abin da mafi yawan malamai suka isa ya zuwa gare shi, hakika mun yi namu bahasin kan asalin lamarin, don haka ya zama lalle ga `yan wannan zamanin da kuma `yan zamni mai zuwa (na baya) su ci gaba da yii bincike kan sassa da bangarorin lamarin (bahasin ko binciken) da kuma yin tunani a cikinsa domin su kai ga yin tahkiki a cikin sa……”[5]

Domin karin masaniya ka kuma zuwa ga:-

Mahdi hadawi daharani, a littafin wilayat wa diyanat, “al wilaya wad diyana” na muassatu farhangi khane khird “muassatu darula kal al sakafiyya” kum, bugu na biyu, shekara ta 1380, hijiri shamsi.

 


[1] Ashhekh Hasan najawi  jawahirul kalam  juzu’I na 15 shafi na 422 da juzu’I na 21 shafi na 395.

[2] Musalin hadisin shuhul mufid wanda yake yin muni baro-baro kan mahangar nan ta shgabanici u malami daga wannan babban malami tuk da cewa ya takaice maganar ta sa sosai.

[3] Hasiyar muhakkikul karaka da yayiwa littafin kawa’idi, rubutun hannu shafi na 36.

[4] Rasa’il na muhakkikul karaka juzu’I na 1 shafi na 270.

[5]  Imam khomaini , a cikin walayatul fakih shafi na 172-173.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa