advanced Search
Dubawa
26198
Ranar Isar da Sako: 2014/09/30
Takaitacciyar Tambaya
Duk da samuwar Ayoyi masu yawa na Kur’ani wadanda suke yabon Sahabbai, me ya sa muke ganin ra’ayin shi’a na zargin su?
SWALI
Duk da samuwar Ayoyi masu yawa na alkur’ani wadanda suke yabon Sahabbai, me ya sa muke ganin ra’ayin shi’a yana zargin su? Allah Madaukakin sarki ya fada a game da yabon Sahabbai cewa: ”Rahamata ta yalwaci komai a saboda haka zan wajabtar da ita ga wadanda suke jin tsoron Allah, kuma suke bayar da zakka wadanda kuma suke yin imani da Ayoyinmu.wadanda suke bin manzon nan annabi ummiyyi wanda suke samunsa a rubuce a wurinsu a cikin littafin attaura da linjila yana umartarsu da kyakkyawan aiki yana hana su mummunan aiki kuma yan halatta musu abubuwa masu kyau yana haramta musu abubuwa masu muni yana sauke musu nauyinsu da kunkuman da suka zamo suna kansu saboda haka wadanda suka yi imani da shi suka kwarzanta shi kuma suka taimake shi kuma suka bi hasken da ya saukar a tare dashi wadan nan su ne masu babban rabo” (suratul a’arafi aya ta 155 zuwa aya ta 157) da kuma fadarsa Madaukakin sarki: ”idan sun yi nufin su yaudare ka ne to Allah ya isar maka shi ne wanda ya taimakeka da taimakonsa da kuma (taimakon) muminai kuma ya hada zukatansu da ace ka ciyar da dukkan abin da yake cikin duniya ba zaka iya hada zukatansu ba sai dai Allah ne ya hada zukatansu hakika shi mabuwayi ne mai hikima (suratul anfal aya ta 62zuwa aya ta 63) da kuma fadarsa Madaukakin sarki: ”ya kai annabi Allah ya wadatar da kai da kuma wanda ya bika a cikin muminai” (suratul anfal aya ta 64) da fadarsa: (kun kasance mafi alherin al’umma da aka fitar a cikin mutane kuna umarni da abu mai kyau kuma kuna hani ga abu mai muni kuma kuna yin imani da Allah” (suratu ali imrana aya ta 110) da kuma fadarsa Madaukakin sarki: (Muhammadu manzon Allah ne wadanda kuma suke tare dashi masu tsanani ne a kan kafirai masu rahama ne a tsakaninsu zaka gansu suna ruku’u suna sujjada suna neman falala daga Allah da yardarsa alamunsu a jikin goshinsu yake na gurbin sujjada wannan shi ne misalinsu a cikin attaura misalinsu kuma a cikin linjila kamar shuka ce da ta fitar da dambarwar sa sai ya karfafa shi sai yayi kauri sai ya tsaya a kan tushensa yana burge manoma don ya fusata kafirai da ita Allah yayi alkawari ga wadanda suka yi imani suka yi ayyukan kwarai daga cikinsu gafara da lada mai girma” (suratul fathi: 29) da wasun wadannan nan Ayoyi masu yawa wadanda Allah yake yabon sahabban Manzon Allah mafi girma (sallallahu alaihi wa alihi wa salam). A tare da haka muna ganin shi\'a suna cewa wai su muminai ne a zamanin Manzon Allah (s.a.w) to amma wai sun sun yi ridda a bayansa, gaskiya wannan al\'amari ne mai ban mamaki, ta yaya dukkan wadan nan dimbin jama\'a zasu yi ridda? Kuma ma me zai jawo yin riddar a bayan rasuwarsa (s.a.w),? sai dai ku yan shi\'a idan zaku ce: sun yi riddar ne a saboda sun nada Abubakar a matsayin halifa a kan musulmi, to anan zamu ce muku: shin sun kasance suna tsoron Abubakar ne? kuma shin yana da wani iko ne ko sarauta, da zai iya amfani da su wajen kwatar mubaya\'arsu da karfi da yaji ? duk da sanin cewa ‘yan kabilar Baniy Tiaym (Kabilar Abubakar), ko kadan ba su kai yawan sauran kuraishawa ba. Mafi yawan mazaunan gari, ‘ya’yan kabilar banu Hashim ne, da banu Abdud dar, da Makhzum, to ta yaya, yayi galaba a kansu? Ashe kenan ba wani abu bane ya jawo taimaka wa Abubakar, da goyon bayansa, sai don imaninsu da imaninsa, da rigayensa a cikin musulunci.
Amsa a Dunkule
Mu munyi Imani da saukar Ayoyi masu yawa a kan yabon Sahabbai, kuma bamu tsammanin akwai wani Malami na Shi'a da yake musun haka, sai dai wannan ba ya nufin cewa wadannan daidaikun ko gungun jama'u, wadanda Allah ya yabesu a wani lokaci na musamman, a saboda wani aiki na musamman da suka aikata, sai hakan ya sa ya lamunce musu kenan, cewa a tsawon dukkan rayuwarsu ba za su aikata abin da zai jawo musu zargi daga Allah Madaukakin sarki, da zargi kuma daga sauran muminai ba.
Ba a ma lamunce hakan ga Annabi mafi girma ba (s.a.w).
ta yaya wanda bai kai shi ba zai samu wannan lamunin? Alhali shi Manzon Allah (s.a.w) ba za a iya kwatanta shi da kowa ba a kowani irin yanayi.
 hakika Allah ta'ala yayi ishara a kan haka a cikin fadarsa a littafin sa mai girma a inda ya ce: - "Da ace ya kirkiri wata magana a kan mu.da mun kama shi da tsananin karfi.sannan kuma da mun yanke masa jijiyar wuyan sa.kuma babu wani a cikin ku da zai iya kare shi”
Kari a kan haka kuma shi ne, a daidai lokacin da Allah yayi yabo a cikin Ayoyi masu yawa a kan wasu sahabban, sai kuma a wannan lokacin ya zargi wasu daga cikin wadannan sahabban, a cikin wasu Ayoyin masu yawa kamar misali, fadarsa Allah ta'ala, a kan zargin masu gudu daga filin daga a yakin Uhudu,: “Hakika wadanda suka gudu daga cikinku a ranar da rundunoni biyun nan suka hadu iyaka kawai shedan ne ya tabarda su saboda wasu abubuwan da suka aikata”.
 A dalilin haka ne yan Shi'a suka dauki matsakaicin mataki a bisa dacewa da Ayoyin yabo, da na zargi, ta hanyar bibiyan tarihin wadannan mutanen da bayyana irin rauni da karfin da suke da shi,
sai suka hukunta ko wani sahabi a bisa dacewa da abin da ya siffanta kansa da shi, abisa yanayin rayuwarsa da biyayyarsa ga Manzon Allah mafi girma (s.a.w) da biyayyarsa ga dokoki da tsarin umurni na Allah, wanda Annabi mafi girma (s.a.w) ya zo da shi, sabannin yanda wasu gungu, na yan'uwa musulmi suka kudurta, a kan cewa duk wanda yake raye a cikin zamanin Sahabbai yafi karfin a yi masa tankade da rairaya, kuma ko ma wane ne bai halatta ya kusanci tarihinsu ba, ko yayi tunanin yin suka ga wasu ayyukansu.
Shi kuma al'amarin kalmar ridda ba wai ana nufin yin ridda, da komawa ga bautan gumaka ba ne, a'a abin da ake nufi shi ne yin tawaye ga tsarin mulki da umarnin Allah, da yin musu ga Manzon Allah mafi girma (s.a.w) wanda yin haka ba wai ya faru ne kawai a bayan rasuwarsa ba, a'a har ma a lokacin da yake raye, (s.a.w) kamar gudu daga filin daga, a lokacin yakin Uhudu, da yakin Hunain.Da kuma kin bin rundunar yakin usama, da rashin bin umarninsa a lokacin da ya nemi su zo masa da tawada, da Allo, don ya rubuta musu wani rubutun da ba zasu bata ba a bayansa, sai suka yi ta jayayya, alhali bai dace a yi jayayya a gaban wani Annabi ba, sai suka ce: Manzon Allah yana sumbatu ne kawai, (s.a.w) kamar yanda Buhari ya ruwaito.
 
Amsa Dalla-dalla
Za a iya kakkasa wannan tambayar da aka aiko, zuwa tambAyoyi guda biyar, su ne kamar haka:
Shin alkur'ani mai girma ya yabi sahabban Annabi mafi girma (s.a.w) ?
Shin duk wanda alkur'ani ya yabe shi, daidaiku, da jama'u, wanann zai sa ya samu wata martabar, da zata sa bata ba zata shafe shi ba? Ko kuskure da tuntube?
Shin Ayoyin da suka zo a cikin wannan tambayar sun tabbatar da nuna cewa Sahabbai suna da kariya na ma'asumanci?
Shin yan Shi'a sun yi imani da cewa dukkan Sahabbai sun yi ridda a bayan Manzan Allah mafi girma? (Sallal lahu alaihi wa alihi)
 Shin mubaya'ar da aka yi wa Abubakar tana nuna shi ya cancanci zamowa Halifa?
A game da tambayar farko dai, E, munyi imani cewa akwai Ayoyi masu yawa da suka sauko a kan yabon Sahabbai, kamar misalin irin Ayoyin da aka rubuto a cikin wannan tambayar, da wasu Ayoyi ma daban, kuma bamu zaton akwai wani malamin shi'a wanda yake musanta hakan, sai dai, wannan ba ya nufin wadannan daidaikun mutanen da jama'unsu a dankule, wadanda Allah yabe su a wani lokaci na musamman, adalilin wani aikin da suka yi, wannan ba ya nufin anyi musu lamunin cewa a tsawon rayuwarsu mai zuwa ba zasu aikata abin da zai sa su cancanci zargi ba, daga Allah Madaukakin Sarki, da zargi daga sauran muminai ba.
Ba a ma lamunce hakan ga Annabi mafi girma ba (s.a.w) to balle kuma ga wanda yake a baya da shi, a wajen martaba, wanda ba za a iya kwatanta shi da kowa ba a cikin ko wani irin yanayi ba?!
Hakika Allah Madaukakin sarki yayi ishara da hakana cikin littafinsa mai girma a inda ya ce: ( Da ace ya kirkiri wata magana a kan mu.da mun kama shi da tsananin karfi.sannan kuma da Mun yanke masa jijiyar wuyan sa.kuma babu wani a cikin ku da zai iya kare shi.kuma hakika shi wa’azi ne ga masu tsoron Allah).[1]"
 Saboda haka su wadannan Ayoyi masu albarka sun sanya Annabi mafi girma (s.a.w) a matsayin abin koyi ga muminai, don kada su jingina kawai a kan sunaye da lakubba, kuma bai dace ba ga kowane mutum, kuma komi girmansa ya ketare iyakokin Allah.
Idan ya zamo maganar a kan Annabi aka yi, wanda shi zatinsa mai tsarki baya kuskure ko tuntube, to yaya ga sauran mutane?
 A saboda haka ne Allah Madaukakin sarki ya ce: ”Hakika shi tabbas wa'azantarwa ne ga masu tsoron Allah”
Hakika irin wannan yayi ta zuwa ba daya ba, ba biyu ba, a cikin al’amarin banu Isra'ila. duk da cewa shi Allah Madaukakin sarki ya yabe su a cikin Ayoyin a cikin alkur'ani mai girma, kamar inda Allah Madaukakin sarki yake cewa "Ya ku banu Isra'ila ku tuna ni'imata da nayi muku kuma tabbas ni na fifitaku a kan halittu) [2] to amma Allah mabuwayi ya zarge su da zargi mai tsanani a wasu wuraren, a wasu kuma ya tsine musu, [3] ya siffatansu da zalunci, [4] da wauta [5] da fasikanci, [6] da d.s.s a wasu wuraren.
 To, shin ba zai yiwu bane irin wannan al’amarin ya faru a cikin al'ummar musulmi, musamman idan muka yi la'akari da hadisan da suka zo a cikin littattafan hadisi na Ahlus-sunnah daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Hakika abubuwan da suka faru da banu Isra'ila zasu faru a cikin al'ummata, taku bayan taku"[7] to, shin yana daga cikin adalcin Allah ta'ala, ya zamo ya zargi sahabban Annabi Musa (a.s) saboda sunyi tawaye ga umarnin Allah, sun ki hanuwa, su kayi kamun kifi, a ranar asabar, [8] amma kuma ya kyale kura kurai, da tuntube na Sahabban Manzon Allah (s.a.w).
Abin da muka fada zai wadatar wajen amsa tambaya ta biyu, cewa yin yabo, ba ya nufin samar da kariya, a tsawon dukkan rayuwar mutum, shi dayan sa, ko jama'a, kuma duk da haka a saboda binciken, ya kamala, a surar da tafi dacewa, zamu yi karin bayani a kan Ayoyin da shi mai tambayar ya dogara da su, don mu ga ko suna nuna hujja a kan abin da yake da'awa a kai.
 
Na Farko:
 Idan mukayi dogon tunani a cikin Ayoyin nan da suke cikin Suratul A'arafi zamu ga cewa sun zo ne a tsakiyar magana a kan sahabban Annabi Musa (a.s)
 da yanda banu Isra'ila suka bauta wa dan maraki, a bayan fakuwar Annabi Musa (a.s), na dan kankanin lokaci, da irin tattaunawar da ta gudana a tsakanin Annabi Musa da Annabi Haruna (Alaihimas Salam) da kuma cewa babu wanda ya tsira daga wannan jarrabawar sai dai Annabi Musa da Annabi Haruna kadai, haka nan da magana a kan Sahabban Annabi Musa (a.s) wadanda ya zaba don ganawa da su, a saboda wautarsu:
 ”Musa ya zabi mutane saba'in don ganawar mu da tsawa ta rafke su sai ya ce Ubangiji da ace ka so ai da ka halakasu dani tun tuni shin zaka halaka mu a saboda wawaye daga cikinmu, wan nan dai jarabawarka ce kana batar da wanda kaso kuma kana shiryar da wanda kaso kai ne waliyyinmu saboda haka ka gafarta mana kayi mana rahama hakika kai ne mafificin masu gafara”[9]
a karshen al'amarin ne, kuma a cikin jerin wadannan Ayoyi ne, sai fadarsa Madaukakin sarki ta zo da cewa:
” wadanda suke bin manzo annabi ummiyyi wanda suke samunsa a rubuce a wurinsu a cikin littafin attaura da linjila yana umartarsu da kyakkyawan aiki yana hana su mummunan aiki kuma yana halatta musu abubuwa masu kyau yana haramta musu abubuwa masu muni yana sauke musu nauyinsu da kunkuman da suka zamo suna kansu saboda haka wadanda suka yi imani dashi suka kwarzanta shi kuma suka taimake shi kuma suka bi hasken da ya saukar a tare dashi wadan nan su ne masu babban rabo”[10]
A cikin marhala ta uku sai ta kara da cewa "Wadanda suka kyautata a cikinsu. Kuma sukaji tsoron Allah suna da lada mai girma"
To, anan zamu ga cewa ita wannan aya mai albarka ba ta bayar da kariya dawwamammiya ba, ga Sahabbai, sai dai ta hada samun rahamar Allah, da kyautatawa da tsoron Sa, idan har suka dawwama a kan haka to rahama zata samu, in kuma ba haka ba, to babu.
Na uku: shi mai tambayar ya dogara da fadarsa Madaukakin sarki a cikin Suratul Anfal”idan sun yi nufin su yaudare ka ne to Allah ya isar maka shi ne wanda ya taimake ka da taimakon sa da kuma (taimakon) muminai.kuma ya hada zukatansu da ace ka ciyar da dukkan abin da yake cikin duniya ba zaka iya hada zukatansu ba sai dai Allah ne ya hada zukatansu hakika shi mabuwayi ne mai hikima (suratul anfal aya ta…..zuwa aya ta….)”[11] Idan mutum yayi dogon tunani a kan wadannan Ayoyin, zai ga cewa suna nuna asalin yanayin dan adam gaba dayansa ne, cewa shi samun sabani a zahiri tsakani mutane, al’amari ne da ya game ko'ina, kuma suma sahabban, ba su fice daga wannan ka'idar ba, saboda haka ya kamata su dinga taka tsan-tsan a cikin tasarrufin da duk zasu yi, a harkokinsu, da kuma cewa mutum yana fuskantar yanayi daban-daban a cikin rayuwar sa wani lokacin ya fuskanci daukaka, a wani lokacin kuma ya fuskanci rushewa, ta yadda mutum daya a cikin sahabban Annabi Muhammadu (s.a.w) zai iya fuskantar kafurai da mushirikai guda goma: ”ya kai wannan Annabi ka kwadaitar da muminai ga yin yaki idan kuna da mutane ashirin masu hakuri zasu yi galaba a kan mutane dari biyu idan kuna da mutane dari zasu yi galaba a kan mutane dubu na wadanda suka kafurta domin su mutane ne da ba su da fahimta”
To, amma sai wannan lambar ta dawo da baya, ta yanda mutum daya a cikin muminai zai iya tunkarar mutane biyu ne kawai na mushrikai,: ”idan kuna da mutane dari masu hakuri za su yi galaba a kan mutane dari biyu, idan kuma kuna da mutane dubu za su yi galaba a kan mutane dubu biyu da izinin Allah”daga nan sai kur’ani ya ambata musu dalilin da ya jawo wannan rauni da kama bayan, a cikin karfin su: ”kuna son amfanin duniya ne Allah kuma yana son lahira ne” da ace mutum zai kudurta cewa, wasu manyan Sahabbai a bayan wafatin manzon Allah, sun samu rauni da dan koma baya, shin wannan imanin nasa, za a iya cewa ta yi hanun riga da abin da yazo a cikin wadan nan Ayoyi masu albarka.
Shin akwai wani dalilin da yake tabbatar da cewa su Sahabbai, Allah ta’ala ya kiyaye su daga faduwa da koma baya?
Na hudu: Game da fadar Allah Madaukakin sarki a cikin aya ta 110 ta cikin suratu Ali Imran: "Kun kasance mafificiyar al’ummar da aka fitar da ita ga mutane kuna umarni da kyakkyawa, kuma kuna hani ga barin munana kuma kuna yin imani da Allah”.
 ita ma wannan ayar akwai bukatar a yi tunani mai zurfi a cikin ta, ta bangarori masu yawa, da farko dai, ba mu da shakkar cewa ita al’ummar musulunci, (al’ummar Annabi (s.a.w) mafi girma) a dunkule, ita ce mafificiyar al'ummomi. Sai dai hakan, ba zai zamo dalilin da za a kidaya shi, a matsayin abin da zai tabbatar da abin da ke cikin wannan tambayar ba, domin zamu gani, a hankalce, an yi yakukuwa da sabani a tskaninsu, har ma da irin fadace fadacen, da suka faru a tsakanin Sahabbai bayan kaurarsa [12] wanda har ya kai wani haddi mai hatsarin gaske, har sai da yayi kusan ya halaka al’ummar musulunci. sai dai godiya ta tabbata ga Allah, saboda wadannnan da suka kauce din ba su samu daman ruguje dukkan dabi'un addini a cikin al’umma ba, a bisa misali, al’umma taci gaba a hade, da rike akidarta da Allah, da Annabi, da Alkur'ani, da salla, da alkibla, da azumi da haji da jihadi da ciyarwa da d.s.s.
Dabi'un addini sunci gaba har zuwa yanzu, an kiyayewa al’umma gadonsu, na wannan babbar wayewa, mai yiwuwa wannan shi ne dalilin da ya mayar da ita mafificiyar al’umma, saboda a wani addini ne zamu ga ayyukan ibada masu rai, da taron ibada mai girma kamar aikin hajii?
Wani al’amarin kuma na daban, a cikin wannan aya mai albarka shi ne zamu ga cewa ayar tazo ne a bayan wasu Ayoyin[13] da suke magana a kan ahlul kitabi, kuma tana yabonsu da cewa” (Daga cikin ahlul kitabi akwai wata al’umma tsayayyiya suna karanta Ayoyin Allah a cikin dare kuma suna yin sujjada. Suna yin imani da Allah da ranar lahira kuma suna umarni da kyawawa suna hani da munana, kuma suna yin gaggawa a cikin aikata ayyukan alheri kuma wadan nan suna daga cikin mutane salihai).to shin wannan ayar tana nuna cikakkiyar siffar su ne a koda yaushe,? A karshe dai, ita wannan ayar da aka kafa hujja da ita a kan adalar Sahabbai, ta siffanta wasu siffofi wadanda idan suka siffantu da su, to zasu cancanci siffantuwa da mafificiyar al’ummar da aka fitar ga mutane. To shin ita al’ummar ta cika wadannan sharuddan? Wadanda mafi muhimmancin su shi ne yin umurni da kyawawa da hana munana? Ko kuma al'ummar ta koma ga taimakon karya, da tsayawa wajen yakar kyawawan al’amura, da yakar gaskiya, wadanda suke tattare a tare da Iman Hussaini (S) jikan manzon Allah (S) a ranar Ashura, al’amarin da ya jawo shahadar sa, da mutanen gidansa, da sahabbansa masu daraja. (s) a cikin wani irin mummunan yanayin da aka kona tantunarsa, da kwashe abubuwan da suke ciki, da kamo 'ya'ya mata na Annabi (s) a matsayin ganimar yaki zuwa ga jabberin nan, Yazidu (tsinannen Allah) sannan kuma ita wannan ayar ba ta takaita kawai ga zamanin Sahabbai ba, a'a gamammiya ce, kuma idan ma muka suranta cewa ayar ba gamammiya ba ce, to, mun ga yanda tarihi ya tabbatar da tabbataccen tarihi, yana nuna mana yanda Sahabbai suka share daga, na sahu biyu, don yakar juna, a filayan yaki masu yawa, a sahu na daya ga Aliyyu Amirul Muminin, (A) a gefen Ammar dan Yasir, da Khuzaimatu dan Thabit, da sauran manyan Sahabbai na muhajirai, da darurrukan Sahabbai Ansaru, (R).
 A daya sahun kuma mu'awiya ne da Amru dan Ass, da wadanda suka taimaka musu daga cikin musulman kasar Sham da wasunsu, to anan wannan tambayar zata taso, shin a tsakanin wadannan sahun guda biyu na mayaka, wani sahun ne yake kan gaskiya, wanne ne ya dace da wannan aya mayar daraja? Idan aka ce dukkansu biyu suna kan gaskiya, to zai zamo babu wani ma'auni, da yayi saura, wanda za a dogara dashi na bambancewa tsakanin karya da gaskiya kenan, kuma yana da kyau a san cewa, mun yi imani da cewa rundunar da take karkarshin Amirul Muminin (a.s) ita ce a kan gaskiya, kuma ita ce ta dace da ayar fadarsa Madaukakin sarki cewa "Kun kasance mafifita al'ummar da aka fitar ga mutane" hakika anyi bincike da tattaunawa a tsakanin malamai, masana tafsir, a kan aya ta sittin da da hudu na suratul anfal, cewa shin kalmar kiyayewa da wadatarwa ga Annabi mafi girma, daga Allah ne? ko kuma kiyayewar daga taimakon muminai ne, da biyayyarsu a gare shi? An ce: Ma'anar ita ce Allah ya isheka, kuma muhajirai san isheka da ansaru. Kuma an ce ma'anar ita ce Allah ya wadatar da kai, kuma ya wadatar da wanda ya bika, [14]to, idan muka sallamawa ra'a yi na biyu, wanda yake shi ne ya dace da abin da mai tambayar yake nufi, to kafa hujja da wannan ayar ba zai cika ba, a bisa abin da ya nema tabbatarwa, domin fadarsa Madaukakin sarki da cewa: da wanda ya bi ka a cikin muminai yana nuna cewa siffar ta kebanta ne da muminai wadanda suka bi Annabi mafi girma (s) wanda dole ne wannan siffar ta ci gaba, amma babu wata iyaka ga yin biyayyar, ko wani iyakartaccen lokaci, wanda biyayyar zata kare a cikinsa. Irin wannan magana tana kama, a wasu fuskoki, da Ayoyin da suka zo a kashedin da aka yi, ga matan Annabi mafi girma (s) a cikin wata ayar, inda Allah ta'ala yake cewa: ”Idan ku biyun nan kuka tuba ga Allah to hakika zukatan ku sun karkata idan kuma kuka yi masa bore to hakika Allah shi ne mataimakinsa da mala’ika jibrilu da salihin muminai kuma bayan haka mala’iku ma zasu taimaka”[15]
Masu ruwaito hadisai sun karbo daga Halifa na biyu, Umar dan haddabi, cewa wadanda ake nufi a cikin wannan ayar su ne A’ishatu da Hafsatu.[16]
Haka nan ma kuma zamu yi nuni da cewa, abubuwan da suka zo a cikin suratul fathi na siffanta sahabban Annabi (S) da busharar gafara, da shiga aljanna, yana da iyaka da sharudda, wanda ya dawwama ne a kan matsayin da yake kai, na taimako da dafawa ga Annabi (S) ba zai taba yiwuwa ba a cikin kowani irin yanayi, ya shafi, wadanda suka gudu a yakin Uhudu da Hunaini, suka bar Annabi (S) a cikin hatsari mai girma! Shin siffan nan ta cewa: “Su masu tsanani ne a kan kafurai” ko kuma su: “masu rahama ne a tsakaninsu” shin wadan nan sunayen za a iya kiran wadanda suka kange, kuma suka yaki Amirul Muminin (A) a cikin wadannan yakoki guda uku? wadanda suka daidaita musulmai, suka halaka kyawawan dubban Sahabbai, da mutanen kwarai? Shin mutumin da ya bi bata, wajen tara dukiya, da taskance zinane da azurfa, ya gina koriyar fada, da gumi da jinin talakawa, da kwace loman tuwonsu, don shi ya rayu, da shi da fadawansa, a cikin almubazzarancin da babu kamar sa, shin za a iya kiransu da wannan siffar da ke cewa: (suna neman falala daga Allah da yardarsa)!?
 Wani abin jan hankali shi ne cewa ita wannan Sura mai albarka ta kunshi wasu Ayoyi masu zargi da yin gargadi ga wasu daidaiku, wadanda a zahiri a cikin musulunci suke kamar misalin, aya ta 6, da 11, da12, da 15.
A she kenan abune a fili, kuma tabbatacce a wurin mu, cewa akwai Ayoyin da suke yin yabo ga Sahabbai, da gwarzanta su, sai dai hakan bai nufin, a ko wani yanayi, wadannan sahabban, suna da kariya daga tuntube, da kuskure, kuma ya zamo bamu da cancantar bincika tarihinsu, da yin nazarin abin da suka yi, da sukar wanda yayi laifi a cikin wadannan kungu na musulmai.
Kari a kan haka kuma shi ne, cewa kamar yanda Allah ta'ala a cikin Ayoyi masu yawa ya yabi wasu Sahabbai, sai dai kuma a cikin wannan lokacin kuma, ya zargi wasu daga cikin wadannan sahabban, a cikin Ayoyi masu yawa.
 Misalin fadarsa Allah ta'ala a cikin zargin wadannan sahabbban, a cikin Ayoyi masu yawa, misalin fadarsa Allah ta'ala, a cikin zargin wadanda suka gudu daga fagen daga a yakin Uhudu, da cewa: "Hakika wadanda suka juya baya a cikinku a ranar da rundunonin nan biyu suka hadu iyaka kawai shedan ne ya tabar da su a saboda wasu abubuwan da suka aikata"[17].
 A wata ayar kuma nuni ake yi a kan wasu Sahabbai, da suke kushe Annabi (S) a lokacin da yake raba ganima, kamar yanda yazo a cikin fadarsa Allah Madaukakin Sarki: ”A cikin su akwai wadanda suke zundenka a game da sadakoki idan an ba su a cikin sa sai su yarda idan kuma ba a ba su ba sai su zama suna fushi” [18]har ma Alkur'ani mai girma yana nuna cewa wasunsu suna fakewa da kowace irin hujjoji don su shantake, suki bin Manzo (s), suna kuma gargadin muminai a kan kada su fita subi Annabi, kamar yanda Allah ta'ala ya fada: ”A lokacin da munafukai da wadanda a cikin zukatansu akwai cuta suna cewa ba abin da Allah da Manzonsa suka yi mana alkawari sai rudi kawai. A lokacin da wasu kungiyoyi daga cikin su suka ce yaku mutanen yasriba baku da wata mafita, saboda haka ku koma wasu kungiyoyi a cikinsu suna neman izini daga Annabi suna cewa gidajenmu a rushe suke alhali gidajensu ba a rushe bane kawai suna son gudu ne”[19].
 Har ma zamu ga alkur'ani mai girma yana gargadin muminai a kan labaran wasu Sahabbai, wanda aka siffanta da fasikanci kamar a cikin fadar sa Allah ta'ala: ”Ya ku masu imani idan fasiki yazo muku da labari to kuyi bincike, don kar ku taba wasu mutane da jahilci sai kuma ku wayi gari kuna nadama a kan abin da kuka aikata”[20].
A dalilin haka, kuma abisa dacewa da Ayoyin da suka yi yabo da wadanda suka yi zargi, yan shi'a suka dauki matsayi matsakaici, ta hanyar yin nazarin tarihin wadannan mutanen, da bayyana siffofin karfi da rauninsu, sai suka hukunta dukkan sahabi a bisa dacewa da abin da ya dora wa kansa, a cikin yanayin rayuwarsa, da biyayyarsa ga manzo mai girma (s) da biyayyarsa ga dokoki da tsarin umarni na Allah, wanda Annabi mafi girma (a.s) ya zo da su.
Sabanin wasu gungu na ‘yan‘uwa musulmi, wadanda suka dauka cewa, duk wadanda suke a zamanin Sahabbai sun fi karfin a yi suka gare su, kuma ba wanda ya isa ya kusanci tarihinsu da sukar abin da suka aikata.
 Al’amarin da ya tilasta musu karbar, tufka da warwara, domin kuwa, wani irin hujjace ta hankali da zata daidaita azzalumi da wanda aka zalunta, a tsakanin Ammar wanda Manzo ya ce masa: ”Ammar, batattun kungiya, su ne za su kasheshi, yana kiransu zuwa ga aljanna, su kuma suna kiransa zuwa ga wuta” [21] da kuma ita batacciyar kungiyar, wacce ta kashe shi, a karkashin fakewa da uzurin, ai dukkan Sahabbai adilai ne? zamu wadatu da dan wannan abin da ya samu na bincike, domin duba amsoshin sauran tambAyoyin sai a duba binciken da muka yi su, da amsa tambayoyi masu yawa a cikin wannan dandalin[22] to amma zamu fada a dunkule cewa; Abin da ake nufi da kalmar ridda, a nan, ba wai ridda ce, da komawa ga bautan gunki ba, sai dai abin da ake nufi shi ne yin tawaye ga tsari, da umarnin Allah, da yin musu ga Manzo mafi girma (s) kuma wannan bai kebanta ga bayan kaurarsa (s) ba kawai, har ma ya faru a lokacin rayuwarsa (s) zamu nuna wasu a matsayin misali na irin wadan nan matsaya na yin hamayya da sabawa, kamar gudu a filin daga a ranar yakin Uhudu, da ranar yakin Hunain, da rashin zuwa yakin Usama, duk kuwa da kwadaitarwa, da karfafawar Manzo, (S) da tursasawarsa a kan tafiya yakin, da kin bin Umarninsa (S) a lokacin da ya nemi, su kawo masa tawada, da Allo, don ya rubuta musu wani rubutun, da baza su bata ba a bayansa, wannan dai shi ne abin da littafin sahihul Bukhari ya kawo daga dan Abbas (R) cewa ya ce: "Ranar alhamis! mececce ranar alhamis!! sai yayi kuka har sai da hawayensa suka jika tsakwankwani, ! Sai ya ce: “Rashin lafiyar Manzon Allah (S) ya yi tsanani a ranar alhamis, sai ya ce "Ku zo, zan rubuta muku wani littafin da ba zaku bata ba a bayansa har abada” sai suka yi jayayya, alhali bai kamata a yi jayayya a gaban wani Annabi ba! Sai sukace Manzon Allah ya kidime (S) ne, sai ya ce: (S) (Ku rabu da ni abin da nake cikinsa, shi ya fi alheri a kan abin da kuke kirana gare shi) [23] wadannan wasu misalai ne.
Duk da sanin cewa al’amura na siyasa sun taka rawa sosai a cikin faruwar wadannan sassabawar, da dalilai na kabilanci, da wasunsu na dalilai, da sabubba, hakika kuwa irin wadannan misalai sun afku ga al’ummar da suka gabata, kamar misalin bautar dan maraki wacce Samiri ya kera wa banu Isra'ila.
Wannan ayar juzu'I na 19 shafi na 189, Suratul Hujurat 6 na Ayoyi masu albarka?.
Shin akwai wani dalilin da babu shakka cewa jerin wadannan Ayoyin ba wai sun zo ne don labarta kissar da kawo labarin kawai don jin dadi da hira ba, sai dai ta zo ne, don sahabban Annabi mafi Girma (S) su dauki darasi don kada abin da ya faru a kan banu Isra'ila ya faru akansu, kuma abin bakin ciki ne sosai yanda zamu ga wasu sahabban ba su riki wannan nasiyyar Annabin mafi girma ba (S) a daidai mintuna na ga karshe a rayuwarsa mayar daraja, da hanashi rubuta abin da yayi nufin ya rubuta to shi zamu sanya irin wannan aikin na wannan sahabin a sahabban, a matsayina girmamawa ne da kwarzantana da darajanta Annabi mafi girma (s.a.w) ko kuma dai yin wannana aikin ya kasance ne…!!.
Na biyu: a game da Ayoyi na 151-172 na suratu Ali Imrana tafsirunsu yana nuna marhaloli guda uku, a bisa wannan jerin da zai zo din nan. Zaiginsu da munana aikinsu a lokacin da suka gudu daga filin daga a ranar yakin Uhudu suka bar Annabi (S) da shi da wasu yan kalilan na muminai a tare da shi, to amam sai ta dawo ta yabe su a lokacin da suka dawo ga yan biyayya ga Annabi da yai aiki da umarninsa "Wadanda suka amsa wa Allah da Manzo a bayarda…….) sannan kuma a cikin da cigaba a wasu lokutan kuma yana fuskantar, faduwa da rushewa da yanda mutum daya a cikin sahabban Annabi (S) yna da ikon fafatawa da yakar mutane goma na Mushrikai da kafirai "Ya kai Annabi ka kwadaitar da muminai a kan yin yaki idan ya zamo kuna da mutane masu hakuriguda ashirin za suyi galaba a kan mutaune dari biyu, idan kuma kana da mutane dari zasu yi galaba a kan mutane dubu na wadanda suka kafirta domin su mutane ne da sabu da fahimta" to amma lambar adadin tana raguwa a wani yanayin ta yanda mutum daya a cikin muminai yina daidai ne da yakan mutane mushrikai guda biyu kadai (idan ya zamo akwai mutane dari masu hakuri zasuyi galaba a kan mutane dari biyu, idan kuma akwai mutane dubu daya a cikinku zasu yi galaba a kan mtuane dubu biyu abisa izinin Allah) sannan alkur'ani mai girma yana tunatar da su dalilinda ya jawo wannan raunin da koma bayan karfinsu (Kuna nufin amfani duniya ne Allah kuma yana son dauja lahira ne) da ace mutum zai yi imanin cewa manyan Sahabbai sunyi rauni a bayan rasuwar Annabi mafi girma (S) sun dan koma baya kadan, shin wannan akidar tasa ta saba da abin da yazo a cikin wadannan Ayoyin masu albarka? Shi akwai wani dalili dake tabbatar da cewa Allah ya kare Sahabbai daga faduwa da koma baya?.
 

[1] Suratul hakkah 44-48
[2] Bakara 47 da 122
[3] Suratun Nisa'I 64 da 67 da sratul ma'idah,  13 da 78.
[4] Suratul Bakarah,  51
[5] Suratul a'araf 155
[6] Suratul a'araf 163
[7]Sunan Turmiziy Darul Fikr beirut 1403,  Hijira kamariyya juzu'I na 6 shafi na 135
[8] A duba suratul Bakara 65 da suratun nisa'I 67 da suratul a'araf 163
[9] Suratul a'araf 155
[10] Suratul a'araf 157
[11] Anfal: 62-63.
[12]   A duba suratul bakara 253 da
[13] Suratu Ali Imrana 113 – 114
[14] Kurtabi, Muhammad bn Ahmad, aljami’u li ahkamil kur’an, j 21, intisharat Nasir Khusro, Tehran, 1364 H.Sh, j 8, shafi: 43.
[15] Suratut Tahrimi 4
[16] A duba tafsirin kurtubiy karkashin tafsirin.juzu’i na 29, shafi na 189.
[17] Aali Imran: 155.
[18] Taubah 58
[19] Ahzab 12 – 13
[20] Hujurat: 6.
[21] Musnad Imam Ahmad bin Hanbal Lambar Hadisi,  11629 da wasunsu na littattafan asasi na Malaman Ahlus sunnah.
[22] A duba binciken ridda a cikin wannan dandalin,  da yanda mubaya'ar Sahabbai ta zamo ga halifan farko.
[23] Sahihul Bukhari Darel Fikir Beurut 1401 Hijirra Kamariyyah juzu'I na 5 shafi na 137 0 138,  kuma a duba hadis mai lambar 3053.
 
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa