advanced Search
Dubawa
11087
Ranar Isar da Sako: 2007/11/17
Takaitacciyar Tambaya
Shin da wacce mahanga Kur’ani ke kallon mutum? a matsayin wanda yake yin zalunci da jahilci, ko kuma halifan Allah a bayan kasa?
SWALI
Shin da wane ido kur’ani ke kallon mutum? a matsayin wanda ke yin zalunci da jahilci, ko kuma halifan Allah a bayan kasa?
Amsa a Dunkule

1- Kur’ani ya yi nuni a wasu ayoyi cewa mutum na da matsayi madaukaki sai dai amma a wani bangaren da mafiya yawan ayoyi yana zarginsa da tare da yi masa gargadi

2-matsayin dan Adam dan Adam na da wani abin mai ban mamaki wajan kololuwar darajar da Allah tya yi masa da kuma wajan fadowarsa a daraja wanda tazarar daukakar da kaskancin ya fi nisan sama da kasa, saboda irin wannan abin mamakin da mutum ke da shi za ka samu yana da wasu abubuwan da suka sabawa al’ada.

3- mutum nag a bangare biyu na samuwa, bangaren ransa wato samuwarsa da bangaren jikinsa na zahiri.

4- mutum na da halayyar da ta sabawa sauran dukkan halittu domin anyishi da damar zabar hanyar da ya ga tafi dacewa da shi, tare da dabiantuwa da duk yanayin da ya smu kansa a ciki.

5- daga mutane ne a kan samu wadanda aka kira su a matsayin halifofin Allah a bayan kasa kuma suka cananci a kira su da wannan matsayi babba, wadannan su ne wadnda Allah ya shirye su da shiriyar sa domin sun yi nisa da dukkan abubuwan kyale kyalen rayuwa da kuma son ransu suka kuma sanya shi karkashin hukuncin mahaliccinsu wanda shi ne ya fi dacewa a wajan su.

Amsa Dalla-dalla

Idan muka yi la’akari da wasu ayoyi daga kur’ani,ai girma muna iya kaiwa ga natija kamar haka; mufara duba ayoyin da suke magana a kan daukakar sha’anin dan Adam da fifikonsa kan dukkan halittu tare da nuna abubuwan da ya kebanta da su kamar; “hakika mun girmama dan Adam kuma muk daga shi a cikin kasa da ruwa (teku) kuma muka azurtasu daga abubuwa masu dadi tsarkaka kuma muka fifita su a kan mafiya yawa daga cikin abababan halitta fifitawa”[1]             “a lokacin da ubangijinka ya ce da mala’iku babu shakka ni mai sanya halifa ne a bayan kasa”[2]             “lallai mun bijirar da amana ga sammai da kassai da duwatsu suka ki daukarta kuma suka ji tsoronta amma sai mutum ya dauka domin kuwa shi mai yawan zaluci ne kuma mai yawan jahilci”[3] da dauransu   wannan bangaren yabo ke nan.

 Bangarorin ayoyi na biyu kuwana zargi mutum tare da tsawatar masa daga ayyukann da ke kaskantar da zuciya kamar fadin Allah cewa “mutum na da yanke kauna da kasawa”[4] “da Allah ya shimfida arzikinsa ga bayinsa shimfidawa da sun yi zaluncin da rarraba kan jama’a a cikin kasa”[5]        “mai yawan zalunci ne kuma mai yawan kafirci”[6] “ya kasance mai yawan zaluntar kansa kuma mai jahilci”.[7] “mai yawan husuma ne tare da bayyana ta”.[8]  “lallai mutum na cikin tabewa (hasara)[9]     

A bisa assin wadannan ayoyin da suka gabata muke kara dora tambayarmu da cewa; menene sirrin hakan kuma me wadannan ayoyi da ke karo da juna a zahiri ke nufi waja nesan da suka yi a kishiyantar juna ? yadda za mu iya ba da amsar wannan tamba ya shi ne;            yana da kyau mu kara komawa zuwa ga kur ‘anin kansa domi wasu daga ayoyin wannan saukakken littafi mai girma na fassara junansu kamar yadda muke karantawa daga suratul baiyyinat cewa; “hakika wadannan da kafirta daga cikin ma’abot littafi (wadanda aka saukarwa dalittafi) da mushrikai na cikin wutar jahannama kuma masu dawwama ne a cikinta kuma su ne mafi ashararan mutane (talikai) lallai wadanda sukai imani tare da yin aiki na gari wadannan su ne mafifita alherin mutane (talikai)”[10] daga cin wadannan ayoyi biyu mun samu cewa mutum na da nauo ‘i biyu daga ciki ya kan iya zama mafi kyan halitta kuma mafi girmansu a daraja, da kuma zama mafi munin halitta mafi kaskancinsu a wulakanta, wannan aya ta yi bayanin yadda mutum kan zama mafi daraja a tsakanin sauran halittu, da kuma zama mafi kaskancin halittu, abin nufi mutum ma’abocin imani da yin aiki na gari ya kan zama mafificin halittun Allah a nan duniya, amma idan ya bi hantyar tauri kai, sabo da jayayya ita ce kan fado da shi zawa makaskanciyar daraja har ya zama mafi munin halittun Allah; ya zo daga wasu ruwayoyi cewa, amirul mu’uminin Aliyu dan abi dali amincin Allah ya tabbata a gare shi yana cewa; hakika Allah ya sanyawa mala’iku cikakken hankali babu sha`awa, ya sanyawa dabbobi sha’awa amma babu hankali, sannann ya sanyawa mutum dukkan wadannan abubuwa biyun, duk wanda ya rinjayar da hankalinsa a kan sha’awarsa wannan ya fi mala;ika daraja, wanda kuwa ya rinjayar da son ransa (sha’awarsa) kan hankalinsa to gwara dabba da shi ”[11]. Zamu iya amfana sosai daga wannan ruwaya mai amfani da hikimar gaske kamar; kamar nuna cewa mutum ai halicceshi da bangarori biyu ne (bangaren ransa da kuma bangaren jikinsa) don haka zai iya karkata ne tsakanin bangarori biyu (karkatuwa zuwa bangaransa na samuwa da na jikinsa) tare da ikon zabar wanda ya fi so tsakanin wadannan bangarori wadda dama ce da Allah ya ba shi tare da yancin gudanar da yadda yake sodon haka ne idan ya zabi hanyar aminci da alheri sai samu isa zuwa daukakar da dan Adam ke iya samu ta koli idan kuwa ya zabi da yar sai ya fado zuwa magangara mafi kaskanci kamar yadda Kur’ani yai nuni da shi cewa “wadannan kamar dabbobi ne ko kuma sun fi dabbobin ma lalacewa”[12]. Haka ayoyin kur’ani masu haske suka kara fayyace mana tare da yaye hijabi zuwa sanin hakikanin wannan abu shi ne cewa ko wane daya daga mutane na da dama da ikon samun wannan matsayi mafi girma; daukaka kuma mafi kamalar (cikar) da mala’iku ke iya kaiwa, anan ne matsayin amfani da hankali ke kai nmutum zuwa mafi girman alkhairai ya kai shi zuwa matsayin halifan Allah. Amma idan bai sa kansa da faidantuwa da wannan ludufin Allah ba, bai da damar samun wannan matsayi mai girma wanda Allah ya ba shi tsakanin halittunsa. Daga nan ne mutum ka fadowa zuwa tabewa ya wzama na kasan kaskantattu ya zama abin zargi, tuhuma, da tsawatarwa daga Allah. (duba tafsirul mizaan bol.18 page 527-524)

 


[1] Suratul isra’I aya ta 70

[2] Saratul bakara aaya ta 30

[3] Saratul ahzabi a ya ta 72.

[4] suratu fussilst aya ta 49,50, 51

[5] suratu shura aya ta 27

[6] suratu Ibrahim aya ta 34

[7] suratul ahzab aya ta 72

[8] suratu yasin aya ta 77

[9] suratul asr aya ta 2

[10] suratul bayyinat aya ta 6,7

[11] tafsir nurth thakalaiyn bol.3 page 188

[12] suratul a’araaf aya ta 179

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa